Wednesday, 15 September 2021

YAR AGADEZ PAGE 49 and 50

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 49&50}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com




Yau ta kama asabar suna zaune da yamma tana kwance kan cinyarshi in banda shagwaba babu abinda Zarah ke zubawa wai ita a dole sai ya samo mata awara da wainar flour kuma ita bata son home made sai dai na saidawa, irin na bakin hanya. Da yaga abin nayi ne don dole ya tashi ya fita yaje ya samo mata don yaga alama weekend dinsa bazaiyi shi in peace ba don yanzu haka kuka take masa bil hakki sheyasa ma ya tafi jiki na rawa ya bata hakuri akan xaije ya siyo mata. Saida ya fita abin ya soma bata dariya wai dama dai yadda ake fadan cikinnan ashe dai haka yake da sai ta ringa ganin kamar abin bai kai haka ba, sai yanzu ta tabbatar ma kanta da abinda ake ji. Kallon da takeyi taji gaba daya ya gundure ta a hankali ta mike taje zata kashe tv taji an kwankwasa kofa, takawa tayi har bakin kofar tace, "Wanene?" Jin anyi shiru yasa ta bude a hankali wara idanu tayi ganin Hafsat da yayanta Yasir ay batasan lokacin datayi hugging dinsu ba tana ta ihun murna gaba daya bata iya misalta farin cikin da take ciki a yanzu, hannun Hafsat ta jawo har cikin parlor tana jan traveling bags dinsu da sukazo da ita, Yasir yana binsu a baya, zazzaunawa sukayi ita kuwa tana zaune kusa da Yasir ta kasa boye farin cikinta, "Ya Yasir shine baka kirani ba kace zaka zo ba?" Yayi dariya, "Bake kin iya bawa mutane surprise ba? Tou ya kikaji dana rama?" Tayi dariya, "Afuwan angon Hassatu, bari na kawo maku abinci ko?" Yasir yace, "Sallah zanyi amma ina mutumin?" Tace, "Ya fita amma bazai jima ba zai dawo!" Yace, "Ok naga masallaci a nan layin ku bari in tafi in dawo..." a haka ya fita ita kuma taja Hafsat guest room dinsu wanda yake a gyare tas tace ta shiga tayi alwalla tayi sallah, sai bayan tayi sallah ne tayi wanka suka ci abinci lokacin har Yasir ya dawo daga mosque. Tunda suka gano dukkansu suna dauke da jariran ciki ba karamin murna sukayi ba especially Zarah ta taya dan uwan nata murna ba kadan ba. Suna kitchen da daddare suna dafa dinner don kuwa Ashraf da Yasir sun fita zaga gari. Zarah ta kalli Hafsat cikin sigar zolaya tace, "Yanzu Inlaw wai ciki gareki ko? Na kasa yarda wai ya Yasir zai haifa mana da ko diya is so hard to believe he's going to be a father soon!" Dariya Zarah ta bata yadda take maganar kamar itama ba cikin ne gareta ba. "Kajiki yadda kike magana sai kace ke ba cikin ne dake ba? Kawai Ashraf yayi mana ajiya a cikin wannan shafaffen cikin naki." Dariya tayi daga haka ta samu ta kashe ma Zarah baki kuma bata sake tankawa ba har suka gama dafa macaroni da sauce din kaza suka jera kan dining, ta kai komai harda coconut drink dinta da basu sha da rana ba ta fiddo yayi sanyi sosai bayan sun gama suka gyara kitchen din sai suka hau kallo sunayi suna yar fira cike da nishadi. Jim kadan suka shigo hannuwansu niki niki da leda, kan dining suka aje sannan suka dawo parlor suka zazzauna suna cigaba da fira cike da nishadi. Hafsat ta kalli Zarah tace, "Ohni ko kunya mijinki na dawowa zaki fara murmushi?" Dariya tayi sosai parlon aka kwashe da dariya, Ashraf yace, "Hafsat ina ganin mutuncinki fa ki kyale man mata." Aka sake sa dariya, suna kallon Ashraf sai wani ririta Zarah yakeyi ko wurin cin abincin ma kamar ya tauna mata ita kuwa gaba daya kunya ta rufe ta, hararar wasa kawai take galla mashi akan ya daina akwai baki. Ta kasan table Yasir ya kamo hannun Hafsat, "Uhm anya Hafsat zamanmu gidannan zai yuwu? Ni gaba daya sunsa ni jin kunya!" Wani murmushin mugunta Hafsat ta sakar masa "A'a muyi zamanmu ay jibi ne fa zamu koma barsu suci karansu ba babbaka." Hararar wasa Zarah ta maka ma Hafsat, "Wallahi ki kiyayeni wannan Inlaw din tam!" Dariya akasa gaba daya, mikewa Ashraf yayi ya jawo hannun Hafsat, "Tou bari mu barku haka nan dare yayi ku cigaba da soyewa lafiya." Itadai Hafsat banda dariyar mugunta babu Abinda takeyi, dafata tayi, "Inlaw afuwan bari mu wuce mu kwanta sai da safe." Mikewa tayi zata cafko ta Hafsat ta saki yar kara ta boye bayan Yasir, "Fito nan mana kigani inba ga tsoro ba." Yasir ya saki dariya, "A'a malama ki bimin mata a hankali." Dariya suka fashe da ita sannan suka masu saida safe suka tafi daki don su kwanta. Suna tafiya ya jawota ta fado masa a hankali ya rungume ta, "Ya dai yan mata? Ba mun shirya ba ko har yanzu fadan mukeyi?" Dariya ma abin ya bata wato ma har ya saba da fadansu yanxu, dukan wasa ta kai masa tana dariya, "A'a fada man tun yanzu in bada hakuri ba sai anjima ba..." dariya tayi tana kokarin zillewa, "Don Allah ka daina." Ta fada tana binshi da hararar wasa, janta yayi cikin daki rungume da ita kamar za'a kwace masa ita. Ranar dasu Yasir zasu tafi har kuka Zarah tayi dan uwa mai dadi, da xasu tafi ta dauki atamfa guda biyu da turare ta ba Hafsat, har airport suka kaisu ko wane cike da kewarsu, a hanyarsu ta dawowa ne taga kiran Hoodah ya shigo video call da sauri ta dauka cike da farin ciki, ganin fuskar Hoodah yasa ta turbune fuska, "Ya zaki nuna man wannan fuskar taki bani babies dina ni in gansu." Hararar wasa Hoodah ta watsa mata, "Aikuwa ni zaki gani basu ba..." Zarah tace, "Don Allah kiyi hakuri in gansu." Hoodah tayi dariya sannan ta seta camera din inda suke kwance suna ta bacci peaceful, Zarah ta dafe kirji, "Awwwn so adorable MashaAllah," sun kara kyau sunyi bulbul MashaAllah kamar ta sace su, Hoodah ce ta bayyana a screen din, "Happy now? Sai ki shafa man lafiya, yanzu dai ina yayan nawa yake?" Zarah tayi dariya ta saita masa wayar ya karba, kalla yayi yana murmushi, "Lil sis how far?" Itama tana murmushi tace, "Fine fine ya kuke?" Yace "Alhamdulillah ina babies dina?" Ta nuna mashi shima cike da sha'awa yace, "Blessed them." Tace "Thank you," yace "Ina sarki?" Tace "Yanzu ya fita fada." Yace "Ki gaishe min dashi," tace "InshaAllah." Ya mika ma Zarah wayar, "Tou mai ciki naga ma kamar baku gida bari na barki." Zarah tace, "Eh wallahi su ya Yasir muka kai airport." Hoodah tace, "Haba sunzo ne?" Ta gyada kai tana murmushi, Hoodah tace "Ayyah Allah ya kaisu gida lafiya." Tace "Ameen ya Rabbi, take care." Daga haka sukayi bankwana. Wani shopping mall suka tsaya suka siya groceries da abinda take bukata harda kayan lashe lashe. Wurin snacks sukaje ta kwashi frozen ones da su frozen yogurt da ice cream. Suna isa gida ta dinga taya shi kwasar kayan saida ya nuna mata da gaske fushi zaiyi sannan ta daina saida ya gama kai kayan tas sannan ita dauko robar ice cream ta bishi cikin gida. Katuwar robar a ciki ta dauka ta rufe fridge din ta juyo tana kallonshi kanta ko dankwali babu, "Wallahi kwadayi nakeji muje muna kallo zakaga mun shanye shi." Dariya yayi yana shafa cikinta, "Kai kuwa bawan Allah ka cika kwadayi ka barmu mu dan sarara haka nan mana!" Dariya tayi tana kai mashi dukan wasa gaba tayi da robar ya bita parlon yana dariya, "Tou daga fadan gaskiya sai kiyi gaba ki barni tsaye ni kadai?" Cokalin hannunta ta dauka ta jefa mashi ya kauce yana dariya.

FEW MONTHS LATER...

Zarah na zaune kan 3 sitter tana sanye da kayan bacci tana cin goruba, cikinta ya fito yayi tulele ya rinjayeta, tana gidansu inda ta tafi can haihuwa, Khadija tana bata kulawa sosai tana kula da ita ta gyara mata dakin kasa a nan zata zauna idan ta haihu. Mummy ce ta sauko daga sama ta xauna gefenta, take Zarah aka wani shige cikin jikin Mummy, "Zarah kinaso ranki ya baci ko?" Zarah ta dago tana kallon Mummy, "Mummy menayi?" Mummy tace "Kinyi wanka yau?” Zarah tace "Meye amfanin wankan Mummy? Na zama katuwa nayi muni nayi nauyi!" Mummy mikewa tayi ta jawo hannunta da kyar take jan kafarta saboda tsananin nauyi, har dakinta ta kaita ta hada mata ruwan wanka, nan ta shiga cikin kwamin da aka cika da ruwa tayi zamanta a ciki tana wasa da bubbles, Bayan ta gama wankan ta fito daure da towel. Shiryawa tayi cikin loose cotton pink gown, turare masu dadi ta shefe jikinta dasu, gashinta ya kara tsawo ya kara zama baki wulik maybe saboda cikin ne. Wayarta ta dauka ta duba time karfe 2:10pm. Sallaya ta shiimfida ta fara sallah, tayi raka’a biyu tana na ukun ne ta ji muryar Ashraf. Dama tun tana sallar takejin bayanta na ciwo da mararta haka nan dai ta daure ta karasa sallar a haka, shiru tayi a tunaninta kawai normal pains ne saboda daman tana dan jin haka kwanan nan, sai kawai ta fita batun. Duk suna parlor suna kallo Yasir ne kawai babu don shima shekaranjiya Hafsat ta haihu baby boy ansa masa Khaleel. A hankali ta tashi ta shiga daki daidai bakin kofa kawai ta fasa wata irin kara ta zube nan dafe da cikin, a rude kowa yayi kanta, Mummy ce ta kamo ta Ashraf ya taimaka mata suka sata mota, Khadija ta dauko box din haihuwanta da sauri tayi mota. A haka suka isa aka karbesu da gaggawa. Ba Zarah ba hartta Ashraf zufa yakeyi yana kallon yadda take kokarin kawo babynsu duniya. Cikuikuye Ashraf tayi cikin kuka tace, "Bazan iya ba Allah mutuwa zanyi." Kara rungume ta yayi yace "Zaki iya princess just try!" Nurse din tace, "Naga head din just push one more time okay?" Nan suka dinga bata kalaman karfafa guwiwa ay batasan lokacin data fasa ihu ba sai jin kukan jarirai sukayi har biyu. "My princess did it! Weldon! Now look we have two babies!" Zarah ta fashe da kuka, nurse din tace "Congratulations it's girls!" Bisa kafadunta aka dora mata ko wane side take ta kara fashewa da wani kukan tana shafa kansu tana kissing dinsu Ashraf yana tayata.

Congratulations princess, we did it...!” Tayi murmushi cikin kuka.

Tace "We did it!" Yace "Thank you." yace yana hugging kanta yana mata kiss a goshi.

“Thank you..." ya sake cewa yana kokarin maida hawayen da suke shirin zubowa. Bayan an kimtsa babies din aka gyare su tas itama akayi stitching dinta aka kimtsa ta. "Ya sunansu?" Ya shafa gashinta, "You can decide princess." Tace "Your mother's name and my mother's name, sai mu dinga kirnasu Alinah da Alishah." Yayi murmushi yana kara hugging dinta, "Thank you." Zuma aka lasa masu sannan ta dora kanta bisa kafadar Ashraf tana lumshe ido kamar mai bacci, tana dauke da Alishah a cinyarta, bude ido tayi ta kalleshi, "They're so cute.." tace tana kissing kanta, dan turo baki Ashraf yayi, "Am jealous the babies have been receiving kisses but none from me." Zarah tayi dariya, "You’ll get yours idan na tashi daga bacci..." tayi hamma, don ta gaji ba kadan ba, Ashraf ya gyada kai yana tashi tsaye, "Bari naje nayi wanka, kema ki kwanta ki huta yanzu su Mummy zasu shigo wurinki..." yayi kissing dinta tare da twins din sannan ya juya yayi hanyar kofa. Har ya kai kofa ya juya yana murmushi, "I like the names you choose for them." Tayi murmushi "I like it too..."

Alishah and Alinah.

Washe gari su Hoodah suka iso nan da nan murna ta barke tsakaninsu, Su Aman sun girma sun kara kyau kai kace wasu black indians. Kowa ya gansu sai yaji sha'awar daukarsu ga su da shegiyar kyuya in ba Hoodah ba basu yarda da kowa sai Zarah shima ba ko yaushe ba. Da kyar suka saba da kawun nasu wato uncle Ashraf take ya shaku da yaran suka cigaba da makale masa. Haka aka cigaba da zaman barka mai jego da babies na samun kulawa wurin Mummy. Ranar suna anyi taron suna lafiya kuma ya kayatar mai jego tayi fes da ita tana sanye cikin wani golden lace sai kyalli takeyi kamar wata amarya. A haka aka sha pictures anci ansha an watse sai fatan Rabbi ya raya su cikin aminci.

-----

Bayan Zarah ta haihu da wata daya akayi bikin Khadija da angonta Dr Hafiz duk da mahaifiyar tashi batayi na'am da ita ba amma hakan bai hanata tayi hidimar bikin dan nata ba. Bayan an gama taron biki lafiya amarya tana dakinta suna zaman amarci lafiya, ba karamin gwargwamaya aka sha ba kafin mother Inlaw din tata tayi accepting dinta amma yanzu Alhamdulillah komai yana tafiya yadda ya kamata suna zamansu lafiya itada mijinta. Kawai matsalar ta daya rashin haihuwa duk yadda zataso walwala in ta tuna sai taji komai ya fice mata kai, Dr Hafiz ma ke bata kwarin gwiwa akan ay wannan ba abin tada hankali bane ba.

-----

Haka rayuwar ta cigaba da gudana inda Khairy yanzu haka danta ya warke har ma ta samu mijin aure wani carpenter wanda ya amince ya aure ta haka aka tattara aka aurar da ita dayake shima yana dauke da irin cutarta a haka suka cigaba da xamansu tare suke zuwa karbar magani, yanxu haka Hoodah ta bata kudi taja jari ba karamin godiya tayi ba. A bangaren Karimah kuwa abin sai wanda ya gani bayan doguwar jinyar da tasha Allah yayi mata cikawa ta rasu ranar wata alhamis da tsakar dare inda a ranar ta dinga kururuwar fitar rai take ta rasu inda aka rufe ta washe gari bayan an sanar da Abba har inda take yazo ba karamin girgiza yayi ganinta ba, nan yayi mata addu'ar rahamar Allah tare da fatan Allah yasa iyakar wahalar kenan. 

-----

Haka rayuwar ta cigaba da gudana a kowane bangare ko wace sai sam barka yanzu haka twins din Hoodah shekararsu daya harda yan watanni inda ta kara samun wani cikin, suna nan twins sai dada kyau suke suna samun kulawa don a yanzu haka ana kiransu prince and princess, duk inda kaga daya zakaga dayan, Hoodah kuwa bata fasa aikata aikin alkhairi ba sai bunkasa garin suke yanzu haka da wuya kaje kaga almajiri na bara ko daya baka gani duk a sanadiyar Hoodah, kullum soyayyarsu dada bunkasa takeyi suna kara samun cigaba a rayuwarsu..... 






             ALHAMDULLAH!


MashaAllah Alhamdulillah a nan na kawo karshen novel dina mai taken YAR AGADEZ, darasin dake ciki Allah ya bamu ikon dauka, kuskuren dake ciki Allah ya yafe mana 🙏🏻🙏🏻, A Gaskiya naji dadin yadda kuke bani kwarin gwiwa da comments naku nagode sosai Allah ya bar zumunci love you all.🔥🔥💕❣️🧡❤️

1 comment:

Latestnovels.net said...

Really, I don't say anything more when you have taken some precious time to read the series of stories that I have been sharing. Thank you so much dear readers.
And today's series of stories I share with you: "THE END OF THE WORLD’S POISONOUS MOM AND MONSTER BABY"
Welcome to read it right here: https://latestnovels.net/novel/the-end-of-the-worlds-poisonous-mom-and-monster-baby