Monday, 4 January 2021

AKAN YATAH 01

♠️♠️♠️AKAN Y'ATAH♠️♠️♠️


                         1


Tafiya take a hankali da ka ganta kasan ta gaji amma duk da haka bai boye farin cikin da take ciki ba, saboda yalwantatcan murmushin dake a fuskar ta, tafiya kadan tayi ta isa parking lot din Court din, daidai wata mota kirar BMW naga ta tsaya ta fiddo key a jakanta tayi unlocking motan sannan ta bude ta shige, ta dade zaune idon ta a lumshe tana murmushi, a hankali cikin muryan ta mai sanyi naji tace "Alhamdulillah" sannan ta tada motar cike da kuzari ta bar federal court of Appeal din. Daidai gate din wani tamfatsetsen gida naga ta tsaya a cikin G.R.A Malali,  horn ta danna ba'a dau lokaci ba naga an wangame gate din, a hankali ta danna kan motar ciki daidai parking lot ta tsaya, saida ta d'an duba lokaci sannan ta fito cike da gajiyar da ta d'ebo, "Sannu da zuwa Hajiya..." Wanda ya bude mata gate d'in ya fada cikin girmamawa. Ta kalleshi tana murmushi tace "Yawwa Malam Iro, an d'auko Sanah daga makaranta?" Kafin ya kai ga bata amsa taji an rungume kafafun ta, cikin jin dad'i ta duka daidai tsawon yarinyar data rungume ta d'in, kyakkyawar gaske ce, k'arancin shekarunta basu '6oye kyawun yarinyar ba, kumatunta ta kama cikin jin dad'i tace "Sanah habibty yau kin riga ni dawowa ko?" washe white teeth dinta tayi cikin jin dadin ganin Momyn  tata, tace 'Yes Mummy today I came back before you, but why did you come back late? Remember you promise to take me out" Ta idar da maganar tana wani b'ata fuska irin na idan yara basuji dadi ba. Kamo yan kananun hannunta tayi cikin sanyin murya tace "oh am sorry my love aiki ne ya rike ni yau amma I promise to take you out tomorrow, since am not going to work tomorrow ok?" Kyalkyalewa tayi da dariya ta fada jikin mom dinta alamar taji dadin zance, haka ta kama hannunta suka nufi cikin gidan.

 Iya tsaruwa gidan ya tsaru da ka gani ba sai an fada maka ba zaka san masu gidan sun kama k'asa, a hankali ta tura kofar palon dake dauke da royal chairs masu shegen kyau kalar ash da gold, palon ya hadu iya haduwa kai tsaye ta hau stairs din, saman ma palo ne dan madaidaice da study room daga gefe sai wasu dakuna guda ukku. A hankali ta murd'a handle din dakin ta shiga, fantsamemen d'aki ne na gaske, tsayawa ma fad'in girmansa da tsaruwarsa ma bata baki ne, sanyin ac ne hade da kamshin freshner da turaren wuta ne sukayi mata sallama, a gajiye ta zauna gefen gado tana mai balle buttons din hannun rigarta, kai tsaye toilet ta fada don yin wanka tana gamawa ta shafa creams masu kamshi ta nufi closet dinta, rasa kayan da zata sa tayi don kaya marassa nauyi tafi bukata a yanzu. Wani material ta hango Wanda akayi ma dinkin doguwar riga ash and black yasha stones, tayi murmushi ta daukota ta kimtsa tsaf da ita, tana gaban mirror tana taje dogon gashinta akayi knocking kofa, dan juyawa tayi gami da cewa "Yes? Come in" mai aikinta ce ta shigo gami da gaisheta "Welcome ma" ta danyi murmushi "Thanks Blessing, what is it?" Blessing cikin girmamawa tace "Ma I came to ask you if you're ready to eat, I wanna warm the food" tayi murmushi "Of course you can, set the table as well" Blessing ta dan russuna "Ok ma" sannan ta fita. 


Cikin 5 minutes ta kammala ta fito downstairs, hango Sanah tayi gaban tv zaune 'kasa tana kallon favorite cartoon d'inta wato Masha and the bear ta du'kufa tana kallo tsakaninta da Allah, murmushi tayi sosai tana kallon yar tata cike da kauna tace "Sanah?" Hankalinta naga tv tace "Yes mummy?" 

"Come here" tasowa tayi ta iso inda maman tata take tace "Mummy gani" dan shafa kanta tayi "have you eaten?" Sanah tayi murmushi "yes mummy" Maman tace "toh homework fa?" Ta dan turo baki "Mummy nayi" ta danyi dariya "I mean both na islamiyya and school?" Ta gyada kai alamun eh a k'agare take ta koma ta cigaba da kallonta. UMMU SULAIM tace "Alright love you can go" da gudu ta koma cike da murna.


Blessing ta gama had'a komai a dinning nan ta zauna taci abinci, bayan ta kammala ta mi'ke a gajiye don d'auro alwallan sallan magrib, kallon Sanah tayi tace "Oya a tashi aje ayi sallah, zo muje kiyi alwalla"


Bayan sallar isha'i suna zaune palon kasa itada Sanah, kan Sanah yana kan cinyarta tana tsefe mata kai. "Mummy na gaji" Mummy tace "Wai Sanah meyasa bakya son kitso ne? So kike kanki duk yabi ya lalace ya zube ne?" Dan turo karaminta pink lips dinta tayi, idan akwai abinda Sanah ta tsana shine kitso bata son abinda zai taba kanta, lallabata tayi har ta kammala, gobe takeso a kitse kan saboda weekend ne ba school. Bayan sun gama ta gyara mata gashin, indomie tasa Blessing ta dafa mata tare da soyayen sausage, bayan ta gama cin abincin taja hannunta suka hau sama, wani daki daban naga ta bude ta shiga opposite wanda ta shiga dazu, ko ba'a fada ba kasan wannan ne dakin Sanah, pink and purple, kanshi bed sheet din dake shimfide saman gadon pink ne mai matukar kyau tare da curtains pink, dakin kamar shagon saida toys, ba abinda babu na kayan wasan yara, d'akin kashi kashi ne akwai study room wanda yake kama da library, story books ne both English and arabic. Sai closet dinta wanda akwai kofar toilet ciki, inda toys nata suke kamar toy room yake, dakin dai ya tsaru iya tsaruwa ba abinda kake ji sai sanyin ac. 

 Wanka tayi mata ta shirya ta cikin pajamas dinta pink and yellow masu zanen teddy na bacci an rubuta goodnight a jiki, bayan ta kwantar da ita kan gado kujera taja ta zauna gefenta tana shafa mata fuskanta a hankali, addu'an bacci tasa ta, tayi ta shafe mata jikinta gaba daya, sannan ta dauko daya daga cikin story book din ta fara karanta mata tai tayi har bacci ya dauke ta, koda baccin ya kwashe Sanah kasa tashi Ummu Sulaim tayi, k'ura ma yar tata ido tayi cike da 'kauna ga wani irin tausayinta da ke fizgarta lokaci daya taji hawaye na neman zubo mata, take zuciyanta ya mata nauyi kokarin gani take hawaye bai zubo mata ba, amma ina saida stubborn one ya zuba, gogewa tayi tare da manna mata kiss a goshi sannan ta mik'e a sanyaye ta kashe mata wutan dakin ta fita.


Dakinta ta shiga tayi wanka ta fito daure da towel, kanta ta kalla ta mirror idanunta sunyi jawur, murmushi tayi da yafi kuka ciwo ta zauna a sanyaye ta shafa mai, kayan baccinta ta zura ta hau gado lamo ta kwanta, tana kwanciya da minti kusan biyar wayarta ta fara ringing. D'auka tayi ganin mai kiran yasa ta mik'e tana murmushi, jingina tayi da gado ta dauka. D'ayan bangaren akayi sallama Ummu Sulaim ta amsa sallaman tace "Mama bakiyi bacci ba har yanzu?" Mama tayi murmushi tace "Wallahi banyi ba Ummu Sulaim ina dai shirin yi" Ummu Sulaim tace "Ayya Allah sarki, to ya sanyi sanyi?" Mama tace "Alhamdulillahi, akwai sanyin garinnan ba kadan ba" Ummu Sulaim tace "Ayya to yaushe zaki dawo ne mama?" Mama tace "Ranar Monday inshaa Allah, hope kuna lafiya? Ina Sanayah?" Ummu Sulaim tayi murmushi "Tayi bacci wallahi, Allah kaimu ya dawo mana dake lafiya" mama tayi yar dariya "Amin, a shafa man kanta idan ta tashi' Ummu Sulaim tana murmushi tace "Inshaa Allah Mama, ay tayi missing naki sosai" Mama tace "Nima haka ay nayi missing dinta sosai" Ummu tayi murmushi, shiru sukayi dukkansu can Mama tace "Goodnight dear" Ummu Sulaim tace " Toh Mama Allah kaimu goodnight" katse wayar Ummu tayi ta kwanta da tunani iri iri a ranta. 


Washe gari bayan Sanah ta dawo daga islamiyya, kitso akayi mata bayan an gama ta shiryata kamar yadda tayi mata alkawarin zata fita da ita, palo suka fito tana rike da hannun Sanah duk sun sha kyau sai kamshi suke zubawa. "Uwani!" Uwani dake kitchen tana goge cooker ta fito da sauri tace "Hajiya gani?" ta furtan hakan tana mai russunawa. "Zamu fita nida Sanah, Idan kin gama aikinki kice ma Blessing ta bude freezer ta fiddo kaji guda 3 ta gasa man su, sannan ki fada mata na chanza kitchen time table ta duba sai a d'ora girkin rana" Uwani tace "Toh Hajiya Allah ya tsare" cikin murmushi tace "Ameen" 

Ramat shopping mall naga sun tsaya. Fitowa sukayi tana rik'e da hannun Sanah suka shiga ciki. Duk abinda Sanah takeso take dauka, sai da suka cika shopping trolley din dam sannan suka hak'ura, bayan sun fito direct Havillah ta tsaya, a nan suka tsaya suka sha, suna gamawa suka wuce City Central Amusement Park, Sanah was over the moon, she was so happy she had fun, nan ma sun shak'ata sosai, sai da Sanah tace ta gaji sannan ta kamo hannunta suka fito daga park din....


A gajiye suka shigo palon misalin karfe 5 saura, Sanah na gaba Ummu Sulaim na biye da ita a baya, Malam Iro ne ke ta shigo da ledoji daga mota, sai daya gama sannan ta kwashi kayan ta hau sama dasu, sallan Asr sukayi itada Sanah sannan suka sauko downstairs, da Blessing suka ci karo tana d'auke da plates zata sauke su bisa dinning, da fara'a ta gaishe da Ummu Sulaim  "Good afternoon ma, you are welcome ma" itama cikin fara'a ta amsa mata tana fad'in "Thank you Blessing, kin gama komai?" Blessing tace "Yes ma" Ummu Sulaim tace "Alright weldon, you can go" Blessing tace "OK ma" bude kulolin tayi taga Lafiyayen jollof rice ce, sai tray din coleslaw, gefe kular kajin da tace a gasa mata ne, sai drinks kala kala. Zaunar da Sanah tayi sannan ta zuba mata abincin, wani plate ta samu ta d'ibar ma su Blessing kazar sannan ta kirata ta bata, itama ta zuba nata ta tsiyaya masu drink din a cups. Zaunawa tayi ta fara cin abincin, amma kana kallon fuskanta kasan ba walwala kawai dai daurewa take in banda juya abincin ba abinda takeyi, ajiyar zuciyar data saki shi ya janyo hankalin Sanah ta dago tana kallonta, abincin ta kalla ganin bata ci ba tace

"Mummy why didn't you eat your food?" K'ak'alo murmushi tayi da sauri tana shafa kan Sanah tare da kai spoon daya baki tace

"N...nothing habibty...the food...is...ho...ho...ot..." Sanah ta kalli maman duk da karancin shekarunta hakan bai hanata gane mummynta na cikin damuwa ba, dama jefi jefi mood din Ummu Sulaim ya kan chanza, za'a ga kamar dai tana cin damuwa.

"No mummy the food is warm not hot, please Mummy tell me why do you look so worried? Did I offend you?" Da sauri Ummu ta rik'e mata hannu tana girgiza kai tace

"No darling it's nothing don't worry, is just stress you know the nature of my work, am really tired" Sanah ta kalli maman tata

"Am sorry mummy, I wish I can do anything to ease your stress" Ummu Sulaim tayi murmushi "Of course you can sweetheart" cike da jin dadi Sanah tace "Tell me mummy" Murmushi tayi tana shafa gefen fuskanta

"I want you to study hard in school, be a good girl, that's the only way you'll ease my stress" G'yada kai Sanah tayi tana murmushi

"InshaAllah Mummy I promise" Ummu Sulaim tayi murmushi "That's my baby"

Haka tayi weekend dinta tana ba Sanah kulawa kamar ko wace weekend saboda yanayin aikinta, kuma harga Allah tana son ganin y'arta cikin walwala da annashuwa,  haka takeyi ko wace weekend suna fita yawo just to spend some time together, har bataso ace Sunday tazo. 


Ranar monday tunda ta tashi sallar asuba bata koma bacci ba, tana kan sallaya tana azkar aka turo kofar aka shigo, Zainab mai aiki ce ta shigo, budurwa ce bazata wuce 23 years ba, sallama tayi Ummu Sulaim tana addu'a bayan ta shafa ta amsa sallamarta tana mai bata izinin shigowa ciki, har k'asa ta zauna ta gaisheta ta amsa da fara'a kamar kullum  sannan Zainab din tace "Anty me Sanah zatayi breakfast dashi yau?" Shiru tayi tana tunani can tace "Toh Zainab nakega ki mata French toast amma kiyi amfani da butter wurin frying dinsa, sai ki dama custard" Zainab tace "Toh Anty" sannan ta mik'e ta fita. 

Saida Ummu Sulaim ta gama azkar d'inta sannan ta mike ta ninke sallayar ta fito daga d'akinta, d'akin Sanah naga ta shiga, tana shiga ta kunna fitila su Sanah anata bacci daga gani baccinta take mai dadin gaske, Ummu Sulaim ta dan taba ta tare da kiran sunanta, juyi tayi tana kokarin bude idonta, take kuma ta koma baccinta, dariya taba Ummu Sulaim don haka kawai sai ta jawota gaba daya ta direta k'asa ba shiri ta tashi tana murza ido. Hannunta ta kama har toilet tasa ta wanke fuskanta tare da yin brush, ruwan wanka ta hada mata ta cire mata kaya, Ummu Sulaim tana k'ok'arin fitowa daga toilet din ta juya tana kallon Sanah dake shirin fara wanka, tace "Sanayah hurry up kinji ko? Kar kiyi late and kiyi alwalla daga nan" Sanah tace "Ok mummy"  Kafin Sanah ta gama har maman ta gama hada mata uniform d'inta da komai ta aje mata kan gado. Bata d'auki lokaci sosai ba ta fito d'aure da pink towel. Ummu Sulaim ta gama shirya ta tsab fes da ita tasa tayi sallah sannan ta kamo hannunta har downstairs, kan dinning ta zaunar da ita ta zuba mata breakfast d'inta, Ummu Sulaim ta kira Zainab dake kitchen tana tattara ma Uwani kayan wanke wanke ta amsa tare da fitowa daga kitchen d'in tace "Anty gani" Ummu Sulaim tace "Zainab kin hada ma Sanah abinci a lunch box dinta?" Zainab tace "Eh Anty na hada" Ummu Sulaim tace "Yauwa jeki d'auko" da toh ta amsa sannan ta wuce kitchen. Bayan Sanah ta gama breakfast Malam Iro ya leko bakin k'ofa da sallama sannan yace "Hajiya, Bala driver yazo yana jiran Sanah" Ummu Sulaim tace "Ok Malam Iro kace masa gata nan" wucewa yayi yana fadin "Toh Hajiya" Har bakin mota ta rakata kamar kullum, Ummu Sulaim na gaisawa da  Bala ta mik'a masa lunch box din Sanah, da sauri ya bude back seat Sanah ta shiga tana daga ma mamanta hannu, Ummu Sulaim ta shafi fuskanta tana fadin "Be good, ayi karatu da kyau, Allah ya bada sa'a" Sanah tace "ameen Mummy" Ummu Sulaim ta mata peck tace "Love you" Sanah ta mata peck itama tace "love you too Mummy" 


Ummu Sulaim na shiga ciki tayi wanka tare da brush, sauri sauri ta shirya ta fito downstairs tana rufe briefcase dinta, da Blessing taci karo ta gama had'a mata lafiyayyen breakfast tasa mata a warmers "Good morning ma" Ummu Sulaim na murmushi tace "Morning Blessing" hanyar kofa tayi da sauri tana duba time a wayanta 9:20am ta gani, har ta kai bakin kofa ta juyo tare da cewa "Blessing where is Zainab and Uwani?" Blessing tace "They are inside ma" Ummu Sulaim ta nufo dinning tana fad'in "Please call them for me Blessing" ciki tayi tana fadin "Ok ma" gaba daya suka fito daga kitchen din bayan sun iso Ummu Sulaim tace "Yau zan dawo gida da wuri, inason ayi general cleaning yau Mama tana hanya, a girka abinci da dan yawa, kuyi shinkafa da miyar kaji, ku hada salad, sai ayi zo6o, Uwani don Allah kuyi aikin nan yadda ya kamata" suka amsa da toh sannan ta cigaba "Zainab ki d'auko sabon bed sheet a shimfida wa Mama, a wanke toilet din a share mata dakinta sosai kafin na dawo" Zainab tace "Toh Anty" Ta kalli Blessing tace "Blessing I told them mama is coming back today, I want you to cook rice and stew use the chicken to make the stew then salad, including zobo too, please I want everything to be perfect before I come back" cikin girmamawa Blessing tace "Ok ma" 

Sauri sauri ta isa motanta Blessing na biye da ita a baya rike da warmers a hannu. Bude motanta tayi ta shiga inda Blessing ta zaga ta gaba da saka mata warmers din tana mata a dawo lafiya. Tana murmushi ta tada motar gate aka wangame tana danna kan motanta waje, Malam Iro na d'aga mata hannu har ta bar anguwar.....


♠️♠️♠️AKAN Y'ATAH♠️♠️♠️


Littafi ne da ya kunshi alamura Akan fyad'e da ya zama ruwan dare yanzu, mun rubuta wannan littafin ne saboda  karfafa masu guiwa Akan su tashi su nemi hakkin su, sannan su san cewa they can fight for their right akan cuta masu da akayi.

Sannan Kuma susan cewa suna iya rayuwar su kamar kowa ba tare da sun tsangwami kansu ba, saboda babu wanda yafi karfin kaddara.


Littafin yana kunshe da cin amana, tsangwaba da jajircewar *UWA AKAN YARTA*


Muna fatan zaku bamu goyan baya Akan abunda muke so mu isar, mun gode.


AKAN Y'ATAH NA KUDI GA MAI BUKATAR LITTAFIN, 


NAIRA 300 ne


DUK WANDA KESON BIYA YA TINTIBI WA'INNAN NUMBERS DIN.


0802 874 8204 ko 07035642883


   "Karku Bari a Baku labari"


♠️♠️litattafan  marubutan♠️♠️


KOMIN NISAN DARE

TAGWAYE NE?

KHALEEL

BA'KUWA

AUREN FANSA

RAYUWAR HOSTEL

FAWZAN KO ADEEL?


THANKS FOR PATRONIZING US

1 comment:

Timothy Eric said...

I was checking for solution in the internet when i miraculously came Across Dr USELU who is an american base herbalist that Cure Numerous individuals OF HERPES VIRUS (HSV 2) INFECTION, I was diagnosed of herpes virus Match 2nd 2017, then i contacted his Email:via (dr.uselucaregiver@gmail.com) and explained everything to him. He mailed me a herbal medication which i took for 2 weeks and was cured of my HERPES VIRUS totally after using his Herbal medicine, So My friend why wait and suffer from this horrible disease when there is someone like Dr USELU that can cure any type of virus and disease such as HIV/ CANCER/ HEPATITIS B VIRUS,LOW SPERM COUNT,ALS,LUPUS VIRUS. email Dr on (dr.uselucargiver@gmail.com) or Whats App him on ‭+2347052898482