ππππππππ
*RAYUWAR HOSTEL*
ππππππππ
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
P.M.L
*we don't just entertain and educate,we touch d hearts of d readers*
*MAMAN KHADIJA*
*MARYAM S BELLO*
*MRS FAWWAZ*
*FARIDAT MUSA*
*JANNART LAMEED'O*
*RUFAIDA YUSUF*
*page 32 by*
*mmn khadijahπ
*
π
Haka dr Maheer ya fito a gidan cikin farin ciki,be tsaya wani b'ata lokaciba yana isa mota ya kira sanyin idonshi zulaihat ya fad'a mata duk yadda sukayi da hajiyarshi,ita hakan yayi mata dad'i matuk'a ahaka sukayi sallama ya kashe waya.ita kuwa taci gaba da shiri
dan zata fita karatu saboda lokacin exams ya gabato.
*AFTER 3 DAYS*
Daga wanka ta fito tana shafa,wayarta ce ta fara ringing,da sauri ta d'aga "hello k'awata please kiyi sauri ki shigo ya kusa isowa,kuma kinsan babyn nawa bayason jira.shiru tayi na d'an lokaci da alamun tana sauraron maganar wancan b'agaren ne,"owk toh sai kin k'araso".
Ba'a fi five minute ba sai ga Halima ta iso tare da dr,da alamun a hanya ya ganta suka taho tare.
Ba wata kwalliya tayi sosai ba,light makeup tayi,amma ba k'aramin kyau tayiba,swiss lace tasa orange da kwalliyar sky blue,d'inkin riga da skirt,hijabi tasa sky blue, takalminta orange da dan blue a jiki,ta rataya jaka suwaga sky blue,wash gaskiya ba k'aramin kyau zulaihat tayiba,suna fita dr Maheer yayi tozali da sahibarsa baisan sanda kalman "fatabarakallahu ahsanul khaliqeen"ta fito a bakinshiba,kallanta ya dingayi har suka k'araso,cike da soyayya da kaunar juna suke aikawa junansu sak'o.
______________
Ba k'aramin karb'a gidansu dr Maheer sukayima su zulaihat ba,kowa a gidan yana haba-haba dasu,abinci da drinks ba'a magana,sun dan jima a gidan ba laifi,sannan suka tafi,wata babban leda hajiyar dr Maheer ta bata,Wanda kayan kwalliyane da tiramen atanfa masu tsada guda uku,babansuma ba'a barshi a bayaba kud'i ya basu 10k,yanayin tarbiyyan gidansu dr ba k'aramin birge zulaihat yayi ba,dan haka taji ta k'ara kaunarshi sosai a ranta.
Ad'aki suke zaune banda hirar gidansu dr Maheer ba abinda sukeyi,wayar zulaihat ce ta fara ringing,ras taji gabanta ya yanke ganin sunan dake d'auke ajikin screen d'in wayar,d'agawa tayi tare da yin sallama.
"ke zulaihat duk abinda kikeyi ki bari gobe kizo gida,ana gama fad'in haka aka kashe wayar batare da an bari tayi magana ba.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun ta fad'a tare da cire wayar a kunnenta"
"k'awata lapiya naga yanayinki ya canza?.
Ajiyar numfashi zulaihat tayi sannan tace."yayana ne ya kirani wai inje gida,daga yanayin furucinshi nasan babu lapiya.
"insha Allahu ba wata matsala k'awata,ki kwantar da hankalinki.
Da tunani iri-iri a ranta ta kwanta,dan haka da sassafe tayi shiri sai gida.
Tana isa tayi arba da Ruky zaune tayi baja-baja,tunda ta ganta jikinta yayi sanyi tasan tabbas ba alkhairi bane ya kawo ta,zama tayi ta gaida mutan gidan kowa da kyar ya amsa mata,itako Ruky sai yatsina takeyi tana wani babbasarwa.
Yayan zulaihat ne ya fara magana cikin fushi,duk abinda Ruky ta fad'a musu ya zayyanowa zulaaihat tabd'i lallai Ruky ba k'aramar shedaniya bace had'ata tayi sosai da iyayenta dan kusan duk maganganun karyane,haka yacigaba da fad'a kamar zai ari baki,itadai zulaihat banda kuka ba abinda takeyi dan gaba d'aya bata da tacewa.
Saida ya gama tsaf sannan yace nagama yanke hukunci akanki daga rana mai kamar tayau kin gama makarantan,na dakatar dake kamar yadda aka kori wannan baiwar Allah,wani dadi Ruky taji a ranta dama kuma muradinta kenan yanzu burinta ya cika.
Harya tashi zai fita zulaihat tace "yayana inada magana"komawa yayi ya zauna yace "fad'i maganarki ina sauraro".
"banzanyi gardama ko jayayya akan duk hukuncin daka yanke akainaba,saboda kai kamar mahaifine a gurina,kuma nasan bazaka yi duk abinda zaka cutar daniba.akan duk abinda Rukayya ta fad'a wannan ba halinabane kuna wallahi ba gaskiya bane, dan tabbatar da maganata gaskiyane ga numbern dr Maheer ka kira nasan zai fad'a maka komai akaina.
Ruky ce tayi caraf"eh abokin munafurcin nakiba,yaya karka yarda da wannan zancen nata,wallahi duk k'anzan kuregene".
Yaya be kula zancen Ruky ba ya karb'i numbern dr atake ya kira yayi masa bayani,dr "yace su jira yana zuwa.
Ba'a dauki lokaci mai yawaba dr Maheer ya iso gidan, nan ya fayyace ma yayanta komai akan su Ruky da sauran yan k'ungiyarsu,sannan yayi masa bayani akan yanason zulaihat da aure anan suka tsara komai.
Bayan tafiyar dr yaya yayima Ruky ta tas,sannan ya mata korar kare wanda saida ta gwammace da batazobama.
Haka alamari yaci gaba da tafiya maganar auren dr da Zulaihat tayi karfi inda aka sa ranar aurensu,nan shirye- shirye ya keta kankama.
Rana bata k'arya saidai uwar d'iya taji kunya,ayau aka daura auren dr Maheer da amaryarsa Zulaihat inda akasha hidima,an kece raini,amarya tayi matuk'ar kyau kamar ka saceta ka guduπ,dare nayi aka kai amarya d'akinta.toh sai muce dr Maheer da Zulaihat Allah ya kawo kazantar d'aki amma bata dattiba.
*Tammat bi hamdullah*
Saimun had'u a littafinmu na gaba.
*Tsokaci*
_wannan labari na rayuwar hostel akwai abin lura aciki,munga dai yadda rayuwar zulaihat ta kasance,tafito daga gidan tarbiyya karshe ta hadu da frirnds wanda suka lalata mata rayuwa,kunga inda daga baya ta tsinci kanta cikin tashin haknkali,akwai mata da yawa wanda hakan take faruwa dasu ko kuma makamancin hakan,toh mu sani kasancewarki a hostel bashi ke baki freedom nayin duk abinda kikaga damaba,hausawa sunce kowani tsuntsu kukan gidansu yakeyi,duk yadda kike haka zaa dauki tarbiyyar gidanku dan haka yan mata da matan aure ya kamata mu fad'aka mu gane,Allah yasa mu dace amin_
Godiya ta musamman ga
Rayuwar hostel fans
Pure moment of life
Mmn khady fans nvl 1and 2
Sarauniyar mace
Mmn humaira novels
Ummyn yusra novrls 1and 2
UNTOUCHABLESππ»♀
No comments:
Post a Comment