ππππππππ
*RAYUWAR HOSTEL*
ππππππππ
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
-We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_
P.M.L
*MAMAN KHADIJA*
*MARYAM S BELLO*
*MRS FAWWAZ*
*FARIDAT MUSA*
*JANNART LAMEED'O*
*RUFAIDA YUSUF*
Page 30 by
Maryam Sbello
Da k'yar su KB suka lalla6a suka mik'e daga wurin ko ina a jikinsu ciwo yake, Ruky in banda gunjin kuka ba abinda takeyi, shi kuwa KB ba zafin dukan kad'ai ya 6ata masa rai ba harda yanda mutane ke kallonsu wai harda Allah k'ara ake musu. Banda kunya data ishe su wai ace kamar su big boys da ake ji da su a makaranta wai yau su aka ma haka?
A inda suka saba zama meeting nan suka wuce kansu tsaye, kallo d'aya zakayi masu ka tabbatar da suna cikin 6acin rai ba kad'an ba, KB ya dafe gefen bakinsa inda ke zubar da jini ga azabar zafi ya bugi table d'in da ke gabansa cike da 6acin rai.
"Lallai gayen nan ya nuna mana iyakar mu yau, ace kamar mu, *Untouchables* wai yau mu aka ma haka a makarantar nan? Lallai da sake."
Ya k'arasa yana nuna kansa gami da fuzar da iskan huci daga bakinsa.
Jibson ya d'ago ya kalleshi yace
"Ay gaskiya mutumin nan ashe haka yake? Duk warning d'in da muka buga masa da tsoratar dashi da mukayi duk bai gani ba ashe? Bamu ta6a zama defeated ba a school sai yau, duk abinda muka sa gaba sai mun same shi, amma ace wai saboda Zooly kad'ai mun gagara cimma burinmu? Nooo!"
Ya fad'a yana huci sosai, ga 6acin rai da yake ciki marar misaltuwa.
Shi kuwa Big boy bai ma iya magana saboda kansa zubar da jini kawai yakeyi.
Ruky ce ta daka musu tsawa tace
"Kai da Allah ya isa haka! Kun bani kunya sai cika baki amma baku iya ta6uka komai! Kalle ku da Allah rai d'aya ya maku wannan abin, amma kuma kunzo kuna mana ihu aka, to tunda kun kasa aikata komai sai kuyi mana shiru aikin banza kawai."
KB ya mik'e cike da 6acin rai yana nuna Ruky
"Ke yarinya! Kar ki nemi ki raina mana hankali fa a nan, in ba haka ba sai na miki abinda bazaki manta ba, ki barni naji da abinda ya dameni."
Ruky tayi shewa
"Idan nak'i fa me zaka iya yi? Besides Dr ma ya maka d'an banza duka..."
Rai a 6ace KB ke mata wani irin kallo yace
"Me zan iya yi kika ce? To ki jira ki gani mana!"
Nan sukayi ta chachar baki inda har KB ya wanke Ruky da mari cikin zafin nama, itama kuwa ta rama, daga nan fad'a ya kaure tsakaninsu, da sauri Jibson ya shigo don ganin ya raba su amma memakon haka sai aka had'a dashi. Cikin wannan hali Easha ta shigo, tayi tayi ta raba su amma abu ya ci tura.
Sai da suka gaji don kansu suka bari.
Ba'a fi minti biyar ba wani malami ya shigo inda suke sunyi lik'is!
Cike da 6acin rai yace duk su tashi su zo HOD na nemansu gaba d'ayansu, duk iskancinsu kuwa yau sai da suka ji tsoro.
Office d'insa suka shiga inda suka tarar da manyan malamai sunfi su biyar, gefe kuma Dr Maheer ne da Dr Khaleed, ko wanensu fuskarsa a d'aure kamar hadarin kaji.
Nan fa su *Untouchables* ido ya raina fata, HOD ne ya kallesu sannan kuma ya daka masu tsawa yace
"Don kun raina mutane baza ku duk'a ba kun mana tsaye aka! Get down on your knees now!"
Da sauri suka duk'a jiki a sanyaye, HOD ya cigaba da magana yace
"Daman abinda yake faruwa a cikin makarantar nan kenan bamuda masaniya, Saboda Allah a turo yara karatu amma su tsaya suna irin wannan? Malam Aminu? Malam Ibrahim? Malam Musa? Kuna sane wannan abin ke faruwa a cikin makaranta?"
"Muna sane kayi hak'uri, abin ne yafi k'arfin mu sheyasa, amma kayi hak'uri."
HOD yace
"Yafi k'arfinku? Har sun isa? Su waye su? Ba'a haife su ba wallahi. Inda Dr Maheer bai sanar da mu ba da shikenan sai abubuwa suyi ta faruwa bamu sani ba? Amma bakomai tunda yanzu an sani."
Ya kalle su cike da 6acin rai
"Kai! Naji labarin baku shiga lectures sai kunga dama? Ga lalata da iskanci da kuka sa a gaba, da zuwa club, baku aje komai ba sai lalata yaran mutane ko? Ga raini da isgilanci bakuda respect ko kad'an, yanzu har Dr Maheer kuka kama zaku daka, kuka farfasa masa mota saboda raini ko? Abinda kuka ga dama kukeyi ku ga tantairai masu ji da kansu? To baku isa ba wallahi, nace baku isa ba kunyi kad'an! Bazamu d'auki irin wannan ba, kuma bashi muke koyawa ba, don haka dole zamu d'auki mataki a kanku."
Ya kalli Malam Aminu yace
"A d'auko file d'insu ko wane a kira lambar iyayensa suzo makaranta, inaso a sanar masu bad'alar da sukeyi sannan mu sallame su su tafi can su k'arata! Bama buk'atar irinku a makantar nan."
Nan fa suka hau bada hak'uri HOD ya daka musu tsawa
"Ashe ma cikin 'yan iskan ku k'anana ne?
Ay kad'an kuka gani, duk abinda kuka aikata sai an sanar da iyayenku wallahi."
Don tsorata sun tsorata don kuwa sunsan muddin aka sako iyayensu a ciki to da matsala. Don haka suka soma bada hak'uri, amma ina HOD ma ko saurarensu baiyi ba ya fara k'ok'arin kiran layin iyayensu.
****
Tsaye yake ya hard'e hannayensa yana jiran fitowar Zulaihat don suyi sallama gobe zata je gida weekend. Sanye yake da jar riga mai ratsin fari da bak'i mai dogon hannu, sai bak'in wando, ba k'aramin kyau yayi ba, fuskarsa mak'ale cikin siririn farin glass wanda ya k'ara fiddo da cikar kamalarsa. Ba'a juma ba sahibarsa ta fito tana sanye da atamfa mai ja da bak'i sai ta d'ora doguwar bak'ar hijabi da ta kusa kai mata k'asa. Dad'i had'e da farin ciki suka dirar masa a zuciya, ba k'aramin burgesa tayi ba ganin yadda a kullum take saka hijabi sai yaji ya k'ara sonta sosai.
Tana k'arasowa ta sakar masa sansassanyar murmushi mai saurin sace zuciya take ya mayar mata.
"My soul..."
Ta fad'a cikin jin kunya ganin yadda ya tsare ta da manyan idanunsa, tayi murmushi. yace
"Ya kike?"
Tace
"Lafiya lau."
Yayi murmushi yace
"Yau dai nazo miki da albishir mai dad'in gaske?"
Tace
"Allah? Meyafaru?"
Nan ya kwashe labarin komai ya fad'a mata, ya d'ora da cewa
"Yanzu dai suna hannun makaranta, insha Allah k'arshen iskancinsu yazo kenan, you can live freely babu mai takura min ke."
Tace
"Alhamdululillah, gaskiya naji dad'i sosai, Allah ya biyaka, su kuma Allah ya shiryesu."
Yace
"Amin amin."
Tace
"Gobe ma zan je weekend gida insha Allah."
Yace
"Eyyah zanyi missing d'inki sosai, amma yana da kyau kije ki gaida iyayenki ay."
Tace
"Hakane."
Ya duba agogo tara saura yace
"Bari na barki ki shirya ki kuma kwanta da wuri, gobe zan zo na kaiki tasha."
Tace
"Da wace motar my soul? Kaida taka na wurin gyara."
Yace
"Dr Khaleed zai bani tasa kar ki damu."
Sun d'an juma suna fira kafin suyi sallama ji suke kamar kar su rabu da junansu...
UNTOUCHABLESππ»♀
No comments:
Post a Comment