Wednesday, 4 September 2019

RAYUWAR HOSTEL PAGE 14

🏘🏘
*RAYUWAR HOSTEL*
🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘


PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
        P.M.L

Na

*MAMAN KHADIJA*
*MARYAM S BELLO*
*MRS FAWWAZ*
*FARIDAT MUSA*
*JANNAT LAMEED'O*
*RUFAIDA YUSUF*

Page14
*ʍʀs Κ„aΥ‘Υ‘aʐ* 😘

       Haka Ruky da Eesha suka dinga sake dulmiyar da zulaihat, sai tayi kamar ta saduda sai su sake mayar da ita ruwa,zaman hostel d'in ma ba sosai take yi ba don su Ruky basa son su barta a hostel don kar a samu masu gaya Mata gaskiya.
     Ana haka Rannan zooly ta tashi da wani matsanancin ciwon ciki da fever Wanda ya sa ta bata bi su Ruky yawon gal-gal d'in su ba.
      Tana kwance a d'akin sai ga fatima ta dawo daga lecture,tayi mamakin ganin zooly a hostel d'in , don rabon data kwana a hostel harta manta,k'arasawa tayi ta dafa ta tace "zulaiha ya dai na ganki a kwance?"
       Ta ce "wallahi fatima am sick"
       Tace "subhanallah me ya same ki?"
   "Cikina ke ciwo wlh ga tunda na tashi nake faman amai,ga fever sosai"
      Tace "eyya sorry dear, tashi na raka ki clinic a baki magani"
     Da k'yar Zulaiha ta iya mik'ewa,abaya kawai ta d'ora kan night gown dake jikinta,sai ta naΙ—e kanta da veil d'in abayar suka nufi clinic fatima na mata sannu.
      Suna tafiya ma Zulaiha haka ta dinga sheka amai a hanya.
       A haka har suka isa clinic d'in duk ta gama galabaita, da yake school d'in babba ce manyan doctors na zuwa 2 times a week,don haka a ranar sun yi sa'a doctor ya zo.
     Basu wani Dad'e ba suka samu ya gansu, a nutse yake ma Zulaiha tambayoyi itama kuma a nutsen take bashi answer yana rubutu a k'aramin card di'n dake gaban shiahi, sai da ya gama ya basu takaddar ya ce suje lab ayi mata test ,babu dad'ewa aka yi aka basu result suka dawo office d'in.
      Doctor ya duba yace " 'yan mata ya aka yi kika bari typhoid tayi miki wannan mugun kamu haka?"
      Bata ce masa komai ba sai dai tayi murmushi kawai ta sunkuyar da kanta k'asa.
      Magunguna ya rubuta mata sannan ya sallame su,sai da suka biya ta pharmacy suka siya sannan suka koma hostel Wanda dai-dai wannan time d'in ne su Ruky suka dawo tare da wani Alhaji mai K'aton ciki,ya sauke su.
       Tunda suka hangota  suka iso gareta suna fadin "baby ya aka yi ne naganki haka?" Wani mugun kallo Eesha tayiwa Fatima gami da ture hannun ta daga shoulders d'in Zulaiha, don tuntuni suka gano cewa tana gaya mata gaskiya.
      Fatima kuwa ganin haka yasa tace "Zulaiha Allah k'ara sauk'i bara naje shop" ta wuce sum-sum kamar munafuka.
     Zulaiha tace "to fateema tnx a lot", daga haka su Ruky suka rik:e ta zuwa hostel, Eesha ta bi bayan fateema da wani mugun kallo tace "I hate this girl" ,Ruky ma tace "wallahi kamar kina reading mind d'ina".
     
****
    A d'aya b'angaren kuma *Dr MAHEER* NE  kwance a kan tangamemen gadon shi,tunanin ta yabi ya Dame shi, haka kawai yake jin ya damu da lamarinta,da ita ya kwana a ranshi da ita ya tashi, yana son ya San halin da take ciki amma bai San ma ta ina zai fara Neman ta ba.
     Ganin tunani ba shine mafita ba ya sa shi tashi ya shirya ya nufi school d'in, ba shima da call a ranar amma haka ya tafi with the hope zai sake ganin ta.

 *** *** **

     Kwanan ta biyar tana jinya sannnan ta samu lafiya garau kamar ba ita ba.
   La'asar ce sakaliya, ansha ruwa an gama gari yayi dad'i,ganyaye sunyi green abin ban sha'awa,yanayin ya mata dad'i.
    Sanye take da short gown pink colour an rubuta *Bea* a gaban rigar da lemon colour,ta saka lemon d'in leggins, sai kuma veil d'in kanta shima lemon toms d'inta kuma pink.
       Tayi kyau sosai,da books a hannun ta, yau tayi ra'ayin shiga lectures d'in.
      Shi kuma ya fito daga clinic d'in don ya neme ta har ya gaji da nema ya hak'ura zai koma gida sai ya hango ta tana tafe tana rangaji kamar reshen bishiya a cikin yanayin damuna.
      Wani irin dad'i yaji ya mamaye mishi zuciya, yana nan tsaye yana kallon ta har ta shige lecture hall d'in.
     Sai da ta shige sannan ya dawo cikin senses d'in shi, gaba d'aya ta gama tafiya da imanin shi,lokaci d'aya yaji he's in love with her, sai dai bai so ganin ta da wannan dressing d'in ba sam.


*Ana wata ga wata kenan, shi dai doctor maheer ya ga matar aure, amma shin zooly easy zata amince da tayin shi kuwa? Shin akwai ma aure a agender dinta?, Ku biyo untouchables don ki ji yadda zata k'ark'e*

No comments: