Wednesday, 4 September 2019

RAYUWAR HOSTEL PAGE 21

🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘
*RAYUWAR HOSTEL*
🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
        P.M.L

Na

*MAMAN KHADIJA*
*MARYAM S BELLO*
*MRS FAWWAZ*
*FARIDAT MUSA*
*JANNAT LAMEED'O*
*RUFAIDA YUSUF*

*Page 21 by*
*mmn khadijah*πŸ’…

*WANNAN SHAFIN NAKINE KE KADAi YAR UWA AISHA ALIYU GARKUWA*
*LALLAI DAUKAKA TA ALLAH CE NAYI MURNA MATUKA ALLAH YA KARA* *DAUKAKAKI DA MA DUKKAN MUSULMI*
*ALLAH YA KARRMU DAGA SHARRIN MASU SHARRI YA TSOKALE IDON MAHASSADAπŸ‘„❤πŸ˜πŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ*

_happy birthday k'awata farida musa swerry allah ya albarkaci rayuwa yasa ayi na gaba da alkhairi_πŸŽ‚πŸ§πŸ­

duk magaΓ±Γ n da sukeyi dr Maheer najinsu dan yanΓ  tsaye a gefensu, gaba d'aya ji yake jikinshi ba dad'i kanshi kuwa haka yakejin wani dumm kamar an d'aura masa dutse.
*Allahumma ajirni fi musibaty wa akhlifni khairan min ha*abinda yaketa fad'a kenan acikin ranshi dan bakinshi ya kasa bud'ewa gaba d'aya ya masa nauyi.

Mai machine ya tare ya hau suka nufi gida.yana zuwa kwanciya yayi ko zai samu bacci dan ya samu relief, amma ina tunanin ya hanashi sak.

Zulaihat ina matuk'ar sonki,kin had'a duk wani qualities da nake nema a tattare da mace,wallahi in har kika barni bazan rayu cikin farin cikiba,ki daure mu rayu a inuwa d'aya,haka dr yaketa sanbatu shi kad'ai a d'aki.ganin ya kasa samun mafita ne ya dan'na numbern abokinshi khaleed,nan fa ya fad'a masa halin da yake ciki,nan khaleed yace yana zuwa.haka dr yaci gaba da sak'awa da kwancewa.

********
Ab'angaren zulaihat kuwa bayan fitansu ta d'auki dogon lokaci tana abu d'aya,sai da tayi ya isheta tayi shiru,nan fa ta fad'a kogin tunani,abubuwa gaba d'aya sun jagule mata ta rasa mafita gashi Fatima bata nan bare ta bata shawara,a yanzu ji take ta tsani kanta dan duk abinda ke faruwa da ita, ita tajama kanta,kukan takaici ta k'ara fashewa dashi.

K'ofa taji an turo, da sauri ta tashi zunbur ta zauna tare da goge hawayen idonta,dan ita a tunaninta su Rukky ne.
Halima shehu ta gani ta shigo coursemate dintace kuma a da kusa da dakin su zooly take zama, amma yanzu ta koma cikin gari da zama sai dai ta shigo tayi lectures ta koma gida,tun wataran da yayanta ya kawo mata sak'o daga gida da daddare yaga yadda mata suke bad'ala a bakin hostel,wajen ya cika da yan mata da samari kamar ana cin kasuwa,ga bakin duhu dan ko tafin hannunka baka gani amma a haka wai ana hira,wasu cikin mota,wasu ko akan cool down,wasu gindin bishiya wai nan duk hira ake,tunda ya fad'a a gida daddynsu yace ta tattara kayanta ta koma gidan babban yayansu da zama dan yafi kusa da makaranta.

Zama Halima tayi kusa da Zulaihat tare da sakin wani murmushi,tace "sunana Halima ni coursemate dinkice,nasan ba lallai kisanniba kasancewar munada yawa a course d'in."

Zulaihat ko da mamaki ya gama bayyana a fuskarta da kyar ta iya cewa "na ganeki sannu da zuwa".

"Yawwa "Halima tace tare da cigaba da bayani."nasan zakiyi mamakin ganina,to karkiyi mamaki dan ni da alkhairi nazo gareki,idan bazaki damuba inaso mu zama k'awaye idan har kin amince,saboda ni tunda kika shigo makarantar nan kike birgeni,dan tarbiyyarki tamin.naji wani iri alokacin dana ga kin fad'a kungiyar su untouchables tun daga nan naji kin siremin,sai kwanan nan naga kamar yanayinki ya canza kina zuwa lectures ga kuma shigarki ba kamar daba shiyasa na yanke shawarar sanar dake ko zaki karb'i k'awance na".

Duk da zulaihat tana cikin tashin hankali amma bayanin Halima saida yasa ta saki murmushin da batasan sanda tayi shiba,"Allah sarki ashe har yanzu bazan rasa masoyaba,na amince da k'awancenki Halima kuma gaskiya bani da kamarki duk fad'in Hostel d'in nan,kinzo min a lokacin da kowa ke guduna saboda bar nan dana aikata a baya".

Tashi zulaihat tayi taje bakin window sanan taci gaba da magana,"hak'ik'a na tafka babban kuskure a baya,nayima rayuwata tabonda ba lallai ya gogeba,bansan yadda akayi na fad'a cikin wannan kungiyaba,gashi yanzu sun zamamin k'adangaren bakin tulu",kwashe duk abinda ya faru da ita tayi ta fad'ama Halima dan tana matuk'an neman shawara.

Nan fa Halima tace "karta rabu da dr danyana tsananin sonta kuma kasancewa dashi kamar wani garkuwa ne a tattare da ita",ba k'aramin shawara Halima ta bata ba, kuma taji dad'i sosai danji tayi kamar ta cire mata damuwar gaba d'aya,haka suka dan tab'a hira bayan wani lokaci ta rakaka ta hau mashin dan zuwa gida.

********
Ab'angaren untouchables kuwa bayan aika - aikan dasukama dr wajen meeting d'insu suka wuce,dan basu da buk'atar datafi samun hanyar da zooly zata dawo garesu,da kuma yin abinda zasu bak'antama dr Maheer.

Sun dau tsawon lokaci suna tattaunawa daga k'arshe suka yanke shawarar sace zooly su kaita inda ba wanda zaiyi tunanin tana can,suyi amfani da ita yadda suke so dan gaba d'ayansu suna mararin tarayya da ita.

Bayan kawo wannan shawarar big boy ne yace "yanzu ta wace hanya kukega zamu bi wajen   saceta?kungafa yanzu ba zuwa inda muke takeyiba,sanann ba huld'a sukeyi da su Rukky ba,ya kukega zamuyi".?

"wannan ba abin damuwa bane,zanje wajen malam kore imani ya bani sa'a daga nan zan gudanar da komai "cewar Ruky.

wani wawan ihu suka saki wanda saida fankar wajen tayi motsi,cak suka dauki Ruky suna murna, daga nan kuma suka ajeta suka fara bata kiss ta kowani sashi na jikinta.

Bayan sun tashi Rukky ta wuce Hotel d'in da take zaune ita da wani Alhaji,wanka tayi ta shirya ta nufi wajen malam tafi da imaninka.

Anan ya tabbatar mata da cewa akwai sa'a,ba zooly ba ko dr zasu iya sacewa indai tayi amfani da wanan k'ullin maganin.

Karban maganin tayi ta saki wata shuumar dariya ta wuce ta tafi.

*danjin yadda zaa kaya ku dakacemu a shafi na gaba*

*muna kara baku hakuri da rashinnjinmu da kukayi bunch of love*πŸ‘„❤
*the untouchables*

No comments: