🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘
*RAYUWAR HOSTEL*
🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L
Na
*MAMAN KHADIJA*
*MARYAM S BELLO*
*MRS FAWWAZ*
*FARIDAT MUSA*
*JANNAT LAMEED'O*
*RUFAIDA YUSUF*
Page 19 by
Maryam S bello
Haka Dr Maheer yana ji yana gani ya tari machine ya hau ya tafi asibitin don neman da ake masa.
Sai da ya gama abinda yajeyi sannan ya d'auki mechanic suka hau machine tare suka biya dole sai da ya siyo taya guda uku kasancewar yana da extra d'aya a booth nasa.
Sai da aka kwashe kusan awa ana fixing tayoyin motar kafin daga k'arshe aka gama. A ranar kud'in da Dr Maheer ya kashe ba kad'an bane.
Gidansa ya wuce yayi wanka yaci abinci ya d'an kwanta domin ya huta, tunani yakeyi tare da jinjina wannan al'amari na *Untouchables*
Duk yadda ya d'auke su sun wuce nan, kuma zasu iya aikata fiye da hakan ma. Amma ya kud'iri a ransa cewar bazai rabu da Zulaihat ba, saboda Allah yaga zuciyarsa da kyakkyawar niyyarsa, yana sonta tsakani da Allah kuma yana son aurenta, don haka dole sai ya tashi tsaye ganin yadda zai 6ullo ma al'amarin.
Washe gari da yamma ya fito daga clinic zai tafi wurin Zulaihat, turus yaja ya tsaye ganin glass d'in motarsa gaba d'aya an farfasa masa,innalillahi wa inna ilaihi rajiun abinda ya dinga fad'a kenan,sai da ya dauki kusan 3mnt a tsaye kafin ya iya d'aga kafarshi,gaban motan yaje ya tsaya yana k'areta da kallo.
A gefen glass din yaga an cusa takarda,cikin zafin nama ya ciro tare da bud'ewa,sako ya gani kamar haka:-
_dr maheer dafatan kaga aikin untouchables kamar yadda muka fad'a maka tun a farko akwai sauran aiki da zakaita gani_
_untouchables bama tab'uwa a koina dan baa banza muke bearing sunan muba_.
_Kuma duk wanda yayi yunkurin rabamu toh sai dai ya gaji ya bari_.
_har yanzu kanada sauran daman da muka baka ka rabu da zooly ka zauna lapiya idan ba hakaba ba kaiba har ita zoolyn kuna cikin matsala_
*Don forget mune dai untouchables*
Yana gama karantawa ya yayyaga takardan tare da sauke wani nannauyan ajiyar zuciya.wayarshi ce ta fara ringing bak'uwar number ya gani ba tare da tunanin komaiba ya d'aga.
"Dr ya zaka yaga mana takardanmu,ai da ka aje zatai maka anfani wani lokaci,fad'a da cikawa shine aikinmu,bama fad'an abu bamu aikataba,ko kuma dan barazana,yanzu dai kanada zab'i uku,ko ka rabu da zooly dan tamuce mu kadai,danmu kawai aka yita ko kuma kayi kararmu ga hukumar mak'aranta,kasan ba koruwa zamuyiba,ko kuma kayita ganin b'arna da batancinmu,hhhhhhhhhhhh dont forget untouchables" Ruky ta k'arasa maganar tare da hura masa iska cikin kunne, kit ta kashe wayar ba tare data tsaya danjin me zaiceba.
*********
Abangaren zooly kuwa taci gaba dayin baya baya da shiga cikinsu Ruky,lectures ko yanzu tana zuwa ba kama kafan yaro,abu d'aya ne yake damunta yadda course mate d'inta suke mata,sun kasa sakewa da ita kullum ta shiga hall sai an samu masu zancenta,wani lokacin har nunata akeyi da hannu da baki,kullum sai dai taje can baya ta zauna ita kadai,ana tashi ko da sauri take fita,
Kamar kullum yauma an tashi daga lectures tana sauri ta koma hostel dan dr yace mata zaizo,kamar ance ta waiga can gefe ta hango dr yanata faman waya,wani farin ciki taji ya lullub'eta dan ita duk sanda ta ganshi tsintar kanta takeyi acikin farin ciki da annashuwa.
Shiko be gantaba yanata faman waya,ta baya tabi inda bazai gantaba, taje ta tsaya a bayanshi ta dauki wani dogon tsinke ta shafa masa a kunne,da sauri ya waigo tare da sosai kunne,dariya ta saki harda tafa hannu tana fad'in "na baka tsoro ashe dai kai matsoracine",katse wayar yayi yana dariya shima.
"har kin gama lectures kenan"?.
Bata kai ga bashi amsaba idonta ya Kai ga motar shii duk glass a fashe.
cike da kulawa tace "honey meya sami motarka?".
Cike da wayin cewa yace "hmm abu na buga bansaniba,"ya fad'a mata hakanne dan bayason ta shiga cikin damuwa.
"Dan Allah ka fad'amin gaskiya dr,nasan ba yadda zaayi ka buga abu duka glass d'in ya fashe haka,dan Allah ka fad'a min",tuni ta fashe da kuka cikin kukan take fad'in,"nasan wannan aikin su Ruky ne dan wallahi nasan zasuyi yafi haka,ta sanadiyyana kanata shiga cikin tashin hankali,asara kala kala kanatayi daga wannn sai wannan,dan allah ka rabu dani saboda kasancewarmu tare bak'aramin tashin hankali bane,wallahi nagode da kaunar daka nunamin, ta dalilinka na dawo hayyacina,bazan tab'a mantawa dakai a rayuwataba",kuka taci gaba dayi wiwi.
maganganunta ba k'aramin sanyayama dr gwuiwa suka yiba,sun tab'a masa zuciya sosai,yana matukar son zulaihat baya kaunar ya ganta cikin damuwa,dan yanzuma kukan da takeyi har ranshi yakeji.
Cikin karfin hali yaketa ba zulaihat hak'uri tare da lallashinta da kyar ya samu tayi shiru,nanfa ya dinga bata baki,ai kuwa ta tattara dukkan natsuwara tana sauraronshi saida ya gama tsaf tace.
"Dr maker ina matukar kaunarka kuma bazan juri ganinka cikin damuwaba,ni nasan halin su Ruky da rashin mutuncinsu, yanzu dukiyarka suke tab'awa gabafa lapiyarka zasu tab'a,wanda bazan juri ganin hakanba,nayi maka alk'awari duk rintsi bazan tab'a komawa cikinsuba,yadda in an mutu ba dawowa haka nima na fita daga cikinsu ba komawa",tana gama fad'an haka ta juya da sauri ta nufi hostel.
Haka dr maheer yaita kiran zooly amma ina ko waigowa batayiba,haka ta barshi a tsaye.
*Mmn khadijah*💅
*tirk'ashi readers gafa zooly ta bar dr maheer ko zasu rabun kamar yadda ta nema*
*kubiyoni dan jin yadda zata kaya*
*the untouchables*
No comments:
Post a Comment