🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘
*RAYUWAR HOSTEL*
🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L
Na
*MAMAN KHADIJA*
*MARYAM S BELLO*
*MRS FAWWAZ*
*FARIDAT MUSA*
*JANNAT LAMEED'O*
*RUFAIDA YUSUF*
*HERE IS YOUR PAGE MY AUNTIES*
*Aunty sakeena (Ummeen Yusrah)*
*&*
*Aunty sadiya (Sadnaf)*
*you are so special in my heart i loves you loadi-lodi*❤❤❤❤❤❤❤
*Page 18 by:* *Faridat musa (swerry)*
Untouchables ne zaune a majalissarsu suna shan iska kamañ yanda suka saba,wannan ya wuce su zageshi wannan ya wuce suyi masa dariya..
Motar Dr Maher suka hango tana shigowa cikin harabar makarantar, dariya sukayi suka tafa,da alama da wani abunda suke k'ullawa.
Tashi sukayi cikin ta kunsu na isa da tak'ama, suka nufi wajensa.
Parking yayi cikin kwanciyar hankali ya fito zuciyarsa d'aya ba tare da tunanin komai a ransa ba.
Turus yaja ya tsaya ganin sun kewayesa, ko wannensu fuskarsa ba annuri ballantana walwala.
Jibson ne ya matso daf dashi ya kallesa shek'ek'e tun daga sama har k'asa ya kwashe da dariya.
Ganin abun nasu na rainin wayone yasa Dr cewa " wannan wani irin iskancine zaku zo kusani a gaba da dariya, ni sa'ankune?, wato iskancinku ya tashi daga kan students ya dawo kaina kenan? To wallahi ku sani bazan tolereting nonsense ba…".
"Heyy!! Enough Dr", Eesha ta katsesa ta hanyar dakatar dashi.
Kb yace "ba dogon turanci muke nima ba munzone danmu kashema concrete warning, akan zooly, ka fita a hark'armu bama son shishshigi a lamarinmu, daga yau ka fita a hark'ar Zooly if not u will regret".
Jibson yace "Zamu iyayin komai akan Zooly, saboda haka ka d'anja guntun mutuncinka da muke gani,tun kafin mu fara sauk'e maka buhun rashin mutunci".
Ruky tace " is better fa kabi advice d'inmu, in bahaka ba zaka wahala, inkunne ya ji…jiki ya tsira" tana k'arasa maganar tasa dariya.
Tsaye yayi kaman mutum-mutumi yana kallonsu, a zahirin gaskiya ya tsorata da lamarinsu, amma kuma bazai bari su gane hakan ba, danzasu iya raina sa, dariyan k'arfin hali yayi ."naji nagode da advice amma kuje da abunku bana buk'ata, kuma ku sani tarayyata da Zulaihat yanzu na fara ba gudu bajada baya".
"Ince haka kace ko?to mu zuba mu da kai muga wanda zaici riba".Ruky ta fad'a tana huci.
"Haka nace 'yan mata" ya fad'a yana kashe mata ido, ya ratsa ta gefensu ya wuce.
Binsa sukayi da kallo har ya k'ule sannan Big boy yayi k'wafa " Amma fa gayennan zaisan damu ya ke magana,sai mun zamo masa k'adangaren bakin tulu… guys muje ko" yana gama fad'a suka sa kai suka tafi kamar dama command d'insa suke jira.
Ab'angaren Zulaihat kuwa suna gama meeting d'insu tayi Hostel, kwanciya tayi da niyar yin bacci amma ya gagareta inta rufe ido ba abunda take tunawa sai Dr wani masifaffan sonsa takeji yana ratsa dukkan wani sassa na jikinta,ganinta na niman zaucewa ne yasata tashi ta d'auki littattafanta tayi skul area, _wannan kenan_.
**********************
Zaune yake a office d'insa yana duba wasu files da alama zaiyi aiki ne akansu, wayarsa ne ta fara ruri alamar tana neman taimako, da sauri ya d'auka yasa a kunne, a d'aya b'angaren akace ya zo ankawo patient a clinic d'insa ba yanda take tana ta bleeding.
Cikin sauri ya tashi ya rataya jakar lapton d'insa ya fita, wajen motarsa ya dosa.
Jiki a sanyaye ya tsaya ganin an sace masa dukkan tayoyin motan, gumine ya fara karyo masa, badan komai ba sai dan tunanin nisan dake tsakanin inda yake da gate, gashi yamma tayi duk colleagues d'insa sun tafi.
Horn yaji anayi masa kaman za'a chire masa kunne, hmmm!! Sassauk'ar ajiyar zuciya yaja dan atunaninsa d'aya daga cikin abokan aikinsa ne, juyawa yayi da niyar ganin ko waye.
*untouchables* ya gani sunyi parking suna k'ok'arin fitowa, ji yayi kaman ya gudu amma ya dake kasancewarsa namijin duniya kuma na gaske.
"Barka da yammaci Dr Maherr" Ruky ta fad'a tana d'aga masa gira.
"Barka dai Ruky" ya bata amsa cikin zak'ewa.
"Hala fita zakayi yanda naga kad'au saurinnan ammafa saidai hak'uri d'azu munzo wucewa mukaga motarka anan, haka kawai mukaji mu sace tayoyin,ya ka gani abun yabada kala ko?" Jibson ne yayi wannan maganar cikin tak'ama da gadara.
"Wannan duk ba damuwa na bane kowa yayi na gari dan kansa,kuma kusani lokaci ya kan maimaita kansa *"kama tudini tudan"*ni dai fatana agareku shine Allah ya shiryeku". Yana gama maganarsa yasa kai ya fara tafiya.
" 'Dan dakata Dr " Kb ya tsayar dashi.
Big boy ya matso wajensa cikin sarsarfa yace " wannan d'aya ne a cikin d'ari ammafa inbaka fita sabgarmu ba,inka fita shike nan inko kak'i kenan casa'in da tara na baya".
Mtssss tsaki yayi ya girgiza kai yace "Allah ya shirya" ya ci gaba da tafiyarsa yana jinsu sunata haukarsu.
*Anya kuwa Dr bai d'auko ruwan dafa kansa ba?*
*shin da gaske Zooly ta shiryu ko da sauran rina a kaba?*
Ku buyomu danjin warwaran k'ullin dake ciki.
*Sweerry ce*👌🏻
No comments:
Post a Comment