Wednesday, 4 September 2019

RAYUWAR HOSTEL PAGE 20

🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘
*RAYUWAR HOSTEL*
🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘


PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
        P.M.L

Na

*MAMAN KHADIJA*
*MARYAM S BELLO*
*MRS FAWWAZ*
*FARIDAT MUSA*
*JANNAT LAMEED'O*
*RUFAIDA YUSUF*


*kamar yanda muka tsara labarimu haka zai tafi duk wata shegiyar da ta sake ja mana Allah iyasa muma mun barta da Allah in halunki yazo dai-dai da mutanen littafin saiki fad'i magana akanmu dan rainin wayo? Mu munsankine ko munsan daga duniyar da kike ne? Abunda muka sani shine muna fad'akar da al ummah akan abunda ke faru kuma mu fatanmu shine Allah yasa rubutun mu ya zama hanyar shiryuwan masu irin halinsu Ruky duk wacce ta zagemu mun barta da mai sama, a ci gaba dagashi suya sai ran sallah*

Wannan pagen nakune
*Maryam Abdool*
*Ummu khady*
*sisin mama*




Page20 by:
*Faridat musa (sweerry)*



Hostel tayi da sauri tanaji Dr Maheer na kiranta amma tak'i waiwayawa. Kwanciya tayi ta shiga rera kuka marar sauti ita kad'ai tasan yanda takeji a cikin zuciyarta,ta tabbatar sonda takema Dr bazata iya dainawa ba tace su rabune kawai dan ya zauna lafiya, hakan ne kawai mafitar da zaisa *Untouchables* su rabu dashi.


A b'angaren Dr kuwa kasa matsowa yayi ba abunda kunnensa yakeji sai sautin kukan Zulaihat abun na tab'a masa zuciya,
"Duk rintsi bazan barki ba koda ke zaki iya rabuwa dani" irin wannan maganganun ya rink'ayi a cikin zuciyarsa har isa yanda zashi.



Kwance take a Hostel tana duba lecture note inta taji an shigo d'akin bako sallama, d'aga ido tayi dan ganin wani mai k'arfin hali ne haka, Ruky da Eesha ta gani cikin mummunan shiga abunba ko kyan gani sanye suke da kaya iri d'aya amma diffrent colours, guntun skirt ne da riga wanda baida hannu fuskar nan tasha uban heavy make up kai kuwa yasha attachment se tauna chiewing gum sukeyi irin na rik'ak'k'un karuwai.


"Zooly ki tashi ki shirya kinsan yau ne birthday d'in budurwan Big boy ko?"
Ruky ta fad'a tana ta tsina fuska abunko kyan gani babu.

Shiru tayi bata tanka ba hasalima bazakace da ita ake maganar ba.

Eesha ce ta kalli Ruky da ido tayi mata alamar ko bataji me tace bane, sake maimata maganar tayi ganin stil shiru ta sake ya tabbatar musu da taji sharesu tayi.



Cikin hassala Eesha tace "wannan wani irin iskanci ne ana miki magana kinajin mutane kin mayar dasu 'yan iska wannan ma ai rashin mutunci ne!"


Ruky tace bai kamata ki bita da masifa ba sarkin hasala kinsan yanzu haushinmu takeji saboda Dr amma ahankali zata dawo hanya, pls Zooly tashi ki shirya mutafi man kinsan bai kamata ace baki jeba Big boy bazaiji dad'i ba sam."


Duk maganar da sukeyi tak'i kulasu hasalima sun fara kaita bango an kusa zuwa stage d'in da zata iya kai mari wanda ahalin yanzu bata fatan hakan wanda tayi da farko ma ya isheta dayayi sanadin shiganta gararin rayuwa,tattara lecture notes d'inta ta fara da niyar bar musu d'akin ai inta fita suma zasu fita.


Ganin hakanne yasa Ruky sakin wani sakalin murmushi ta matso kusa da ita ta zauna ta dafa kafad'arta " Zooly menene dalilinki nak'in yimana magana? Bayan duk maganganun da muka miki?" .

"Rayuwarmu ba iri d'aya bane Ruky tun farko ninayi gangancin shiga cikinku amma yanzu Allah ya ganar dani duk wani wajen dazaku dan Allah kuna tafiya kawai batare da kunzo guna ba ku manta da mun tab'a rayuwa tare pls na rok'eku" ta k'arasa maganar tana sharan k'wallah.

Eesha ce ta dube ta cikin mamaki kana ta yatsina baki " kinyi ganganci tun farko kuma yanzu is too late k'arya kikeyi ki shigo cikinmu kuma kice zaki fita ko da da ubanki ki kike yawa Zooly".
" Enough! Eesha duk iskancinki ya k'are a kaina amma banda iyayena dan bazan lamunta ba".

"Iyayenkin har wani value suke dashi da baza'a zagesu ba ? Matsiyata ne fa!"

"Eesh ya isa mana " Ruky ta fad'a cikin b'acin rai.
Tashi Zulaihat tayi ta tsinke Eesha da mari sannanta ta nunata da yatsa " ki fita a harka ta daga yau karna kuskura na k'ara ganin k'afarki ad'akin nan if not wallahi saina miki mummunan illah banza jaka kawai".

Sake baki Eesha tayi tana jin furucin Zooly wanda da alama bata cikin hayyacinta.

Jan hannunta Rukky tayi sukayi waje ransu gaba d'aya ya gama b'aci.

Durk'ushewa awajen Zulaihat tayi tasa kuka mai tsanani tayi kaicon rayuwar da tayi a baya gashi a banza taja wa mahaifinta zagi wanda yake kwance a cikin kabarinsa.



A maimakon tayi masa addu'a se gashi tasamu masu aibatashi.

A take ta k'arajin gaba d'aya rayuwarta fita mata arai gab'a d'aya duniyar batayi mata dad'i nadama da danisani su suka addabi zuciyarta.


Daga ganin fuskokin su Ruky Jibson suka gane akwai matsala, saboda sun dad'e kuma basu fito da Zoolyn ba.


Kb ne yace " akwai matsala ko?". Girgiza masa kai Ruky tayi alamar eh.

" wai meye yarinyar nan takeji dashi ne da zatana mana haka?". Big boy ya fad'a cikin b'acin rai.
" me kuwa banda shegen Dr nan,yanzu dai ya akayi?" Jibson ya tambaya cikin sonjin abunda ke going.

Nan Ruky ta kwashe kaf abunda yafaru ta fad'a musu wani ashar Kb ya sake " lallai ma yarinyar nan tasamu kanta amma meye mafita guys?".

"Ai mafitar kenan mu b'atar da gayen nan sannan muyi sabon aiki a kanta tayanda zamu samu mu cika burinmu na kawar da k'ishin mu akanta".
Ihu suka saka sannan sukace "hege Big boy ashe kanka naja magarka tayi dai-dai yanzu next agendern mu shine b'atar da Dr".




*Anya kuwa zooly bata k'ara d'ebo ruwan dafa kanta ba?*



*shin abunda suka fad'a zai tabbata ko kuwa?*


*anya kuwa Dr zai iya satuwa?*


Ku biyo mu danjin yanda zata kaya.





*Sweerry ce*👌🏻

No comments: