Wednesday, 4 September 2019

RAYUWAR HOSTEL PAGE 04

๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜
*RAYUWAR HOSTEL*
๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
        P.M.L

2017

Na

*MAMAN KHADIJA*
*MARYAM S BELLO*
*MRS FAWWAZ*
*FARIDAT MUSA*
*JANNAT LAMEED'O*
*RUFAIDA YUSUF*

 *Page 4 by:*
*maman khadijah๐Ÿ’…*

*GAISUWA GAREKU D'ALIBAN AMINU SALEH COLLAGE OF EDUCATUON AZARE,WANNAN SHAFN NAKUNE MASU ZAMAN HOSTEL❤❤*

"Naji Kuma na aminta da shawaran ki in Allah ya yarda bazan sake kulasu ba..."

"dat's my friend.
A tare suka saki dariya.

Abinci sukaci sukayi wanka,lecture note suka d'auka suka nufi bayan Hostel dan karatu,dayake haka sukeyi kullum.

A 6angaren Ruky kuwa zuciyartace kamar zata fashe dan haushi,kallo ษ—aya zaka mata kagane tana cikin damuwa,ta keษ“e kanta ita kaษ—ai tanata zarya ko zama ta kasayi.
 "lallai wannan yarinyar ta ษ—ebo ruwan dafa kanta*MARI*" ta jijjiga kai tare da shafa fuskanta.
Ni tunda nake ba Wanda ya  taษ“a marina sai Ruky,hmmmm lallai wannan kucakar yarinyar ta gama zubarmn da aji,ko yan group ษ—inmu zasu daina ganin girmana yanzu.amma ba komai saina nunama zulai ta taษ“o babban babyn ta group ษ—in untauchable wallahi,duk a zuci ruky take kullawa da kwancewa.

Fita tayi daga inda ta keษ“e kanta ta nufi inda sauran members ษ—in group ษ—in nasu suke,tana zuwa tace "hy guys."
Cikin haษ—in baki sukace "ina kika shiga munata jiranki mu tagi club kinsan fa yau akwai casu."

"na ษ—anje wani important gurine i'm so sorry muje ko."

"KB yace "Ruky nifa naga kamar marin da yarinyar nan ta miki ne kika saka a rai......."

"pls KB stop it,wannan k'azamar yarinyar harta isa insata a rai?ai tayi babban kuskuren,kuma zata gane kuskurenta very soon,dama nazo muku da albishir bayan mun dawo daga club mu zarce wajen meeting na gano mana hanyar da zamu sameta cikin sauk'i."

"ihu suka saka tare
"yes Ruky baby munsan zaki iya."

"gaskiya mu share zuwa club ษ—in nan kawai ki faษ—a mana,kunsanfa a matse nake da yarinyar nan." big boy ya faษ—a.

"kai dalla baka da hak'uri inkai wasa kowa sai ya taษ“a kafin ka sami kale." inji jibson.

"please mu tafi kunsan fa an fara tun dazu Ruky ta faษ—a."

Sa kai sukayi suka nufi wani babban Hall,wanda naga a samanshi an rubuta College Hall,suna shiga nan fa guri ya ruษ—e mc ya fara musu kirarinsu "a big group with a big guys,you guys are *untauchable* wannan suna daku kaษ—ai ya yace aduk faษ—in makarantar nan,ure highly welcome *untouchables* group.

Wani hadaddun kujeru aka ware musu a high table suka zauna.haka aka cigaba da party,lallai anyi casu kam,muna can gefe muna hango yadda group ษ—in *untouchables* ke watsa rawa,kamar bada jikinsuba.

Bayan sun fito daga gun casu direct inda suke meeting suka zarce sabida duk sun k'osa suji hanyar da Ruky ta samo musu..

Bayan sun sami guri kowa ya zauna sun gama duk wata hauka da zasuyi Ruky ta tashi ta fara magana.

"nasan zakuyi mamakin abin da zan faษ—a amma kuma ba abin mamaki bane idan kukayi la'akari da cin fuskar da akai min,na zauna na gama karantar yarinyar nan naga hanyar da zamu iya cinma burin mu akanta saina shiga jikinta,ma'ana saimun kulla k'awance nida ita."

"taya kike ganin zulaihat zata yarda ta kulla abota dake? bayan kina ganin yadda tsanarmu take bayyana k'arara akan fuskarta?" cewar big boy.

"gaskiyafa hakane maganarka big boy ai sai hali yaxo ษ—aya ake abota inji Easha"

"baku bari na kai ayaba kun katseni,zan aje makamaina in koma mutunuyar kirki a fili,zan dena yawo daku in fact zan dena shiga cikinku gaba ษ—aya zan nunama yan sch da kowa na tuba,dole zamana zai koma cikin hostel."

"Nayi bincike akanta kullum bayan ta gama lectures suna futowa bayan hostel akwai wad'anda take koyama karatu,dole inyi k'ok'ari inga na zama ina cikinsu,kunga ta haka sai in nemi mu zama k'awaye,daga nan sai in fara aika mata da makamaina." ta k'arasa maganar tare da murmushin mugunta.

"yes wannan shawara tayi." Inji KB
"sai dai wani hanzari ba guduba ni inaga zulaihat kamar bazata ansheki a matsayin k'awa ba."

"zata ansheni ai wuyarta kawai in zama irinta,ma'ana taga na canza rayuwa,a tunanina dai zata karษ“eni."

"hahaha shegiya Ruky mikiya uwar hangen nesa." cewar jibson.

"toh yanzu yaushe zaki koma malamar?"  inji Eesha

"sai wani satun dan sainayi shopping da shirin zama a *HOSTEL*"
               
*Maryam muhammad lawal*
           
*Pure moment*

No comments: