๐๐๐๐๐๐๐๐
*RAYUWAR HOSTEL*
๐๐๐๐๐๐๐๐
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
P.M.L
2017
*MAMAN KHADIJA*
*MARYAM S BELLO*
*MRS FAWWAZ*
*FARIDAT MUSA*
*JANNART LAMEED'O*
*RUFAIDA YUSUF*
*We don't just entertain and educate,we touch the heart of the readers*
*Page 26 by*
*mmn khadijah๐
*
*And*
*Faridat musa (sweery)*
Ab'angaren zulaihat kuwa bayan tabar wajen dr wayarta ta bada caji saboda ta mutu,kuma akwai assignment ษin da zatayi.
Aษaki ta samu Halima ta baje tana ta girki,mamaki ne ya cika Zulaihat dan ita batai tunanin ganin Halima a hostel ba.
Murmushi ta sake mata tare da cewa "kaga masoyan asali,wanda tun daga siffa, kama,hali sun dace,gaskiya fa k'awata ba k'aramin dacewa kukayi da docter d'inkiba",ta k'arasa maganar cikin zolaya.
"wallahi kedai bakya rabo da tsokana da barkwanci,ni ba wannan ba nayi mamakin ganinki a hostel a dai dai wannan lokacin"
"kinsan miye?naba su mum ษina labarinki ne shine duk yan gidanmu suke kwaษayin ganinki,niko nace su kwantar da hankalinsu duk randa zanzo zamu taho tare,ษazu akamin waya dad ya dawo kinga sai muje ku gaisa ko?".
Ba musu zulaihat tace "toh " nan fa suka haษu suka gama girkin da ganan suka shirya.
Shagon mai chaji suka je dan ta karษi wayarta amma sukaga shagon a rufe,ganin a nata kiran Halima a waya daga gida yasa suka wuce da niyyar inta dawo anjima ta karษi wayar.
Ba k'aramin karษa aka ma Zulaihat ba a gidan su Halima,sun nuna mata k'auna sosai,yadda suke mata kamar dama can sun saba da juna,haka suka zauna a nata shan taษi.
Ta jima sosai a gidan dan sai yamma lis sannan tai shirin tafiya,abin Allah saida ta fito ruwa ya tsinke kamar da bakin k'warya ba yadda ta iya dole ta zauna,Halima kuwa da sauran 'yan uwanta farin ciki kamar bazasu mutu ba,domin sunyi sunyi da ita akan ta kwana tak'i wai tabar wayarta a sch.
Haka aka sha ruwa har 12am.
**************
Kamar yadda suka tsara da yamma Kb zai kawo cocaine haka ko akayi,ya kawo ya dank'a a hannun Ruky ahaka sukayi sallama,idan aiki ya kammala zata kirasu a waya.
Basu da matsala da Baba mai gadi dan tuni suka rufe masa baki dafarare bugun Abuja.
Jikin Ruky har rawa yakeyi gaba ษaya ta kosa dare yayi ta aiwatar da nufinsu akan Zulaihat.
1:00am nayi k'afa ta ษauke a hostel su Ruky suka shigo kai tsaye ษakin Zulaihat suka nufa.turawar da zasuyi sukaji k'ofa gam,dayake sunada key ษin ษakin cikin zafin nama suka buษe,abin mamki ba Zulaihat a ciki,gani suke kamar zasu ganta dan gaka suka shiga ษakin suka hau duba ta harda ษaga katifa.
Da suka tabbatar bata ษakin ne suka fito rai a ษace,kiran su Kb sukayi suka faษa mudu duk abinda ke faruwa,ba k'aramin mamaki suka yi ba,domin basu taษa tunanin Zulaihat zata tsallake ma target ษinsuba.
Suna gama waya da Ruky Kb ya danna number Dr Maheer saida ta kusa tsinkewa kafin ya ษaga.
"kai wato damu kake jako?,mu zamu rika tsara abu kana wargaza mana,toh ka sani a tarihinmu bamu taษa neman abu mun rasaba,dan haka bazamu fara akan Zooly ba,wato kaje malaminka ya faษa maka kuษirinmu akan Zooly shiyasa ka ษauketa a hosteฦ ko?,toh ka sani yau nasara na wajenka gobe kuma kasa a ranka mu keda nasara.
Cikin zafin nama ya sauke wayar tare da furzar da iska daga bakinshi.
"Guys mu wuce zanu nunama gayen nan mun fishi sanin duniya."
Zunb'ur Dr ya tashi,tuni ya nemi baccin dake idon shi ya rasa,nunbern Zulaihat ya kira yaji a kashe nan fa ya kara shiga tashin hankali.
Ya kira wayan tafi a k'irga ganiyake kaman in yakira zai shiga amma bai samu ba, ji yake kaman ya tashi ya tafi Hostel d'in amma ba hali saboda yanayin tsaro idan dare yayi, tashi yayi yayi alwala ya tada sallah, ya ringa kai kukansa ga mai sama dan yasan shine kad'ai zai iya kub'utar da Zulaihat daga sharrin *untouchable*.
Bashi ya tashi daga kan sallaya ba saida yaji kiran assalatu sannan ya tafi masallaci, a daddafe yayi salkah saboda azababben baccin dake damunsa.
A b'angaren Zulaihat ma hankalinta ba'a kwance yake ba saboda tasan Dr zai kirata kuma inhar yaji a kashe hankalinsa ba k'aramin tashi zaiyi ba, haka tayi bacci a daddafe da tunanin Dr a zuciyarta.
Tun asuban fari *untouchable* suka fito gate d'in makaranta suka tsaya duk wanda ya kallesu yasan suna cikin b'acin rai ba kad'an ba shiyasa ma d'aliban suke kaucewa insun gansu dan tsira da mutuncinsu.
Dr Maher suka hango a cikin motarsa ya kwaso da gudu da ganinsa yana cikin tashin hankali, duban juna sukayi sukayi magana da ido alamar akwai abunda suka k'ulla masa a ransu, jeruwa sukayi a daidai hanyar da zaiwuce yanda dole saiya tsaya, wani wawan burki yasha ganin mutane a gabansa "Allahumma ajirni fi musibati waklifni khairan minha" abunda ya firto kenan abakinsa ya tsaya.
Ku biyo mu danjin yanda zata kaya.
*UNTOUCHABLE*๐๐ป♀๐๐ป♀๐๐ป♀๐๐ป♀๐๐ป♀๐๐ป♀๐๐ป♀
*mmn khadijah*
&
*Sweerry*
No comments:
Post a Comment