Wednesday, 4 September 2019

RAYUWAR HOSTEL PAGE 05

🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘
*RAYUWAR HOSTEL*
🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘

*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS.*
         ( _P.M.L_).

2017
*Na:-*

*MAMAN KHADIJA*
*MARYAM S BELLO*
*MRS FAWWAZ*
*FARIDAT MUSA*
*JANNAT LAMEED'O*
*RUFAIDA YUSUF*

*Page 5*
    *Written by:*
      *_Rufaida Yusuf._*

_Dis Page is Dedicated to my one and only Khaleel (ILY)._

Haka kuwa akayi domin a k'arshen week d'in tafia taje super market tasiyo duk abinda tasan zata buk'ata Sannan sukayi sallama da frnds d'inta zata koma hostel(su a wajen skul suka kama gida).

Tana shiga school tayi parking d'in motarta wurin hostel d'in tabar Kayan data siyo a mota.
       Direct wurin dasu zulaihat take karatu taje da littafinta ta zauna tare da yimusu sallama,suka amsa dukkansu Suna kallonta cikin mamaki,ita dai Zulaiha abinda take tare cigaba dayin Tun bayan amsa sallamar,su kuwa sauran sai tsegumin  Ruky da hijab sukeyi.
6:00pm nayi kowa ya tashi ya tafi itama ta tafi hotel domin ta kwana.

   Toh haka ta kasance har tsawon sati d'aya tana zuwa tabbas kowa a makarantar ya shaida ta rabu dasu *untouchable* clique d'in anata yabawa.

       Bayan zulaihat  ta dawo daga lectures ne tasamu su Fatima a d'akinsu Suna hirar Ruky shi ne tace "gaskia Nima naga chanji sosai Allah yasa tadaina kenan" suka amsa da "Ameen".

        Da yamma tayi ne kasancewar yau Saturday kuma basayin karatu ita kad'ai takeyi tana isa bayan hostel taji kamar tanajin kukan mace tana tashi ta zagaye sai taje daf da ita tace "baiwar Allah me aka miki ke kuwa? laaa!! Ashe ma kece,me ya faru?", Wallahi zulaihat abin dunia ne kaf yabi ya tarar min,"Kinga na fita a k'ungiyarsu amma Sam mutane sun kasa karb'a ta a matsayin wacce ta shiryu ,ni sainake tunanin ko komawa zanyi inda za'a amsheni".

Zulaihat da jikinta yariga yayi sanyi tace " tashi muje d'akinmu in zaki zauna" ta rungumeta tana mata godia.
      Zulaihat ce ta tayata shigar da kayanta d'akin bayan sun gama ne suka d'an tab'a karatu daganan zulaihat tayi bacci ita kuma Ruky tafad'a chatting dasu KB.

      Washegari ma kafin su farka har Rukyn taje ta samo musu break fast ta kawo musu da suka tashi kuma ta gyara d'akin sai sannu suke mata.

         Toh a cikin watan  nan sunyi mugun shak'uwa da  Rukyn.

       Ansamu hutun mid-semester kowa zaije gida yayi sati d'aya,inda Ruky tace zatabi zulaihat gidansu suyi hutun saboda dukka y'an gidansu sunje saudiya,"ba damuwa",sun gama had'a Kayan su sukayi sallama da su Fateema Sannan suka tafi.
     Kafin su Kai saida Ruky ta tsaya a store tasai musu shinkafa,taliya,macaronic, manja,man gyad'a,hatta cefane saida tayi musu.
    Tabbas kuwa Ruky Tasha albarka wurin iyayen zulaihat.
      Sun sauka a d'akin zulaihat d'an madai-daici dashi,sosai suka saba kuma suka bata yarda da ita 100%.

        Kwanansu bakwai a gidan bayan sun gama shiri Ruky harda kukanta domin a time d'in Baba bashida lafia sosai, saida suka sai masa magani sannan suka tafi.

      A hanya sai da ta tsaya tasai musu katifar dazata ci mutum biyu domin ta zulaihat bawata katifar arzik'i bace ba.

    Sun gyara d'akinsu yayi tsaf dashi.

      Sun maida hankalinsu sosai a wannan semester d'in.
     A ranar da suka yi examz d'in su ta k'arshe sun sha kukan rabuwarsu dasu Fatima ya rage musu saura su biyu a d'akin su.

Bayan sun dawo d'akin ne aka kira zulaihat a wayarta aka cemata ta dawo gida yanzu yanzu.duk tabi ta rud'e saboda bata san dalilin kiran ba,da k'yar Ruky ta lallab'a ta Sannan suka tafi a motarta.

     Su na kaiwa bakin layin babu taron kowa kasancewar an tafi kai mahaifin nata,tana shiga taga umma tana sharar k'walla, "ni kun barni a duhu Wai meke faruwa?ina Baba? ".
Nan fa aka cemata hak'uri ake yi duk abinda kika ga ya faru shi ne k'addararka,
"ni kufad'amin menene?".

     "Allah yayiwa mahaifinki ya rasuwa".   ,kowa yana jiran yaga ta fasa ihu sai kawai tayi salati tafara hawaye,Ruky ce tabasu hak'uri, haka komai na sadaka su ita d'auki nauyinsa.

        Bayan bakwai Sannan Ruky tayi musu sallama ta koma gida.

      Angama Hutu yau kuma zulaihat zata koma makaranta,bayan tagama shiri tana jiran Ruky tazo ne umma tak'ara yimata nasiha sosai ,"Umma Dan Allah karki dinga saka damuwa a ranki Kinga kina da hawan jini".    "inshaallahu Zulaihat".

     Wuraren 12:30pm Ruky tazo bayan sun gaisa  ne Umma tak'ara yimusu nasiha,zasu tafi  takawo dubu goma  tabasu "bakya gajia da wahala y'annan"
"laa!!ba komai ai Umma anzama d'aya".
"toh Allah yamiki albarka"
"Ameen Umma sai an kwana biyu"
"Toh Allah ya kiyaye hanya",
"Ameen".

      Sun isa kafin su shiga School suka biya ta restaurant suka siyi abinci Sannan suka k'arasa cikin school, zulaihat ta shiga wanka Jb ya kira Ruky a waya tace "shegen yanzu nake shirin kiranka,yau fa zan fara kai harina"
"Toh am wishing u best of luck baby,we miss u over here",
"I will be there soon"
"we will be waiting".

    Da daddare bayan sun gama shiri sun saka kayan bacci  har sun shiga bargo coz tym d'in sanyine lokacin,sai tasaka hannunta tafara shafa bayan zulaihat, tana juyowa ta had'e bakinsu wuri d'aya.........

*Kubiyo mu a page na gaba domin jin yadda zata kaya,shin me zulaihat zatace?,shin zata amince,kaiii!!!me ma zai faru.*

*P.M.L*.

No comments: