Wednesday, 4 September 2019

RYAUWAR HOSTEL PAGE 25

🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘
*RAYUWAR HOSTEL*
🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘

*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
      P.M.L

2017

*MAMAN KHADIJA*
*MARYAM S BELLO*
*MRS FAWWAZ*
*FARIDAT MUSA*
*JANNART LAMEED'O*
*RUFAIDA YUSUF*

*wannan shafin nakine yar uwa rabin jiki hajia laurat  kano mmn husnah,hakika ke masoyiyatace bani da kalaman da zanyi anfani wajen nuna godiyata a gareki sai dai a koda yaushe ina miki addua da fata na alkairi,allah yasa kifi haka ya raya miki zuria,ameen*

*Page 25*
      *By*
*Mmn khadijah*💅

Kafin takai k'asa Allah ya bata iko ta dage,dubawan da zatayi taga k'atuwar taya ce cikinta ansa xare anyi sak'a ita duk bata kula da tayan ba saboda hankalinta na can kan Dr ɗinta.
Ganin haka yasa Dr ya matso gurinta yana jera mata sannu,
 D'aga kanda zasuyi suka hango Ruky tsaye ta zuba musu ido kwafa tayi  sannan ta wuce.

Allah ya shiryeku shine abinda Dr ya faɗa,suka bar wurin.waje mai kyau suka samu anan ake zuba love,hak'ik'a sun dace da juna matuk'a,bayan sun taɓa hira dr ya faɗa mata zataɓar hostel dan har ya sama mata gida ya gama komai komawa kawai ya rage tayi.bataso hakan ba dan tana matukar kaunar zaman hostel amma bata nuna masa hakan da yayi be mata daɗiba, domin ance yaba kyauta tukuici,tayi godiya sosai amma ta sanar dashi zataje gida jibi intaje zata faɗama iyayenta duk abinda sukace zaiji.yaji daɗin jin haka daga gareta,domin hakan ya k'ara tabbatar masa da lallai zulaihat ɗinsa mai biyyayya ce da hangen nesa,domin yasan da watace ba itaba zaiyi wahala ta faɗama iyayenta,duba da yadda yasan masu zaman hostel ba zaman daɗi sukeba.

Sun jima suna shan love ɗinsu daga nan ya bata abinda ya kawo mata sukayi sallama ya tafi.

*****************
Bayan kwafa da Ruky tayi ta wuce motarta ta hau ta nufi wajen wani club da suke shanawa,bayan sunsha rawa da duk baɗalansu, kowa ya watse aka barsu,dayake haka sukeyi bayan kowa ya watse su sai su zauna zaman shan syrup su buɗe sabon babi na iskanci.

Eesha ce ta dauko kayan hawa sama bada jirgiba kirarin da sukeyi knan.

"Ruky ce tace baby aje wannan kayan akwai maganar da nakeso muyi,nan fa kowa ya samu guri suna sauraronta.

Duk abinda ya faru ita da zulaihat ta faɗa musu harda tayan data saka mata,tacigaba da cewa guys nifa ina mamakinku,anya wannan yarinyar ba wani kullin tayi muku ba?ku tuna yadda muke a baya,duk yayinyar da muka nuna muna kwaɗayi ko yar gidan uban waye sai mun sameta da karfi koda lalama,saita gundiri kowa acikinmu,amma ku duba yadda kuke sanya a lamarin zooly,ai ni inaga abin kunyanema a garemu zooly ta shigo wannan kungiya tamu ta fita a raayin kanta,kuma taci gaba da rayuwa normal duk muna kallanta,toh bara kuji idan ku kun hak'ura da kwasar kayan daɗinta toh nidai ina nan sai inda karfina ya k'are."

"Nan suka fara kururuwa kowa na faɗan albarkacin bakinshi.

"Enough guys kB ya faɗa tare da ɗaga hannu,munyi anfani da malam tafi da imani abu be yuyuba,akwaifa sauran method da muke dasu, yanzu kawai muyi anfani da cocaine inaga zaifi,kunga ku Ruky da Eesha tunda kuna shiga ɗakinta ku zamuba kuje ku shak'ama shegiya ba tare da kowama ya jiba,kunga idan ta fita a hayyacinta k'afa fara ɗaukewa a hostel sai ku fito mana da ita,bamu da matsala da baba mai gadi tunda yana karɓan farare,muna bashi aikinmu zai tafi yadda muka tsarashi.
Kuna fito mana da ita magana ta k'are,zooly mun gama da ke hhhhhhhhhhhh ya k'arasa maganar

Yes wannan shawara tayi haka duk kansu suke faɗa,nan suka aje magana akan kb zai kawo cocaine da yamma,bayan sun gama shaye shayensu suka bar wajan.

Duk abin nan da sukayi a kunnen Isa ogan masu tsaron zulaihat,dan bayan sun bar wajan Dr tsara yadda zasuyi aikin sukayi,Isa tunda shine oga yace zai rink'a bibiyar su untouchables duk wani motsinsu dole zai rik'a sani,manga da sani su zasu rik'a kula da zulaihat duk wani motsinta su rik'a sani a haka suka rabu kowa ya fara aiki.

Da Isa akasha rawa a club dan shigewa cikinsu yayi tsilif aka sha harka saboda karsu ganeshi,bayan an watse ne ya sami wani lungu ya mak'ale inda bazakayi zaton akwai mutum ba,dan ko numfashi a hankali yake ja da saukewa,saida suka gama komai suka tafi  sannan ya fito.

Wayar Dr Maheer yaita kira danya faɗa masa abinda yaji amma kash tak'i shiga is not recable at d moment ake faɗa masa,gashi bashi da numbern Dr Khaleed bare ya kira.
Haka ya tari dan acaɓa ya nufi gidan Dr ko zaici saa yana gida,yana isa wani k'aton kwaɗo yayi arba dashi a jikin kofar gidan hakan ya tabbatar masa da bakowa a gidan.jiki a sanyaye ya juya.har bayan sallan magriba yana kira numbern Dr bata shiga.

*maryam muh'd lawal*👌
*UNTOUCHABLES*🏃🏻‍♀

No comments: