๐๐๐๐๐๐๐๐๐
*RAYUWAR HOSTEL*
๐๐๐๐๐๐๐๐๐
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L
Na
*MAMAN KHADIJA*
*MARYAM S BELLO*
*MRS FAWWAZ*
*FARIDAT MUSA*
*JANNAT LAMEED'O*
*RUFAIDA YUSUF*
*WANNAN SHAFIN NAKUNE MASOYA LABARIN RAYUWAR HOSTEL*๐๐๐
*SAKONNINKU NA FATAN ALKHAIRI YANA ZUWA GAREMU*
*muna kaunarku aduk inda kuke❤❤*
Page 13
*by mmn khadijah๐
*
Gyara wajen kwanciya Fatima tayi ta kwanta,zooly kuwa k'ara shiga cikin kogin tunani tayi ahaka har bacci ya kwasheta.su biyu suka kwana a ษakin dan yau Ruky bata dawo hostel ba.
Da asuba suka tashi suka mik'a ibada,Zooly ce ta mik'e ta dakko alQurani ta fara tilawa.
Wani farin ciki Fatima taji ya lulluษeta,a take ta ษaga hannu tayi adduar neman shiriya ga kawarta Zulaihat.
Ta ษauki dogon lokaci tana karatu kafin ta rufe littafi mai tsarki ta tattara wanki ta nufi bakin fanfo kasancewar yau sunday.mu dai muna gefe munata tunanin ko nasihar fatima ta shiga jikin zooly ne.
Ta taradda mutane a bakin fanfon kowa da abinda yakeyi,wasu wanki wasu wanke wanke,wasu na gefe suna ta kitso,wasu kuma hira sukeyi.ajiye bucket ษin tayi akan layi ta koma gefe kafin a iso kanta.
Salma dakema Husna kitso tace,yawwa Husna kinga yarinyar da ake taษi jiya a
Room 14,da sauri Husna ta ษaga ido tace laaa wallahi naganeta,kiga sanda ta shigo makarantar nan very gentle bazakice zata aikata abin duk da kuka faษa ba.
"iyi ba ta biyema yan iskan yaran nan ba *untouchable* yarinya da mutuncinta da komai,ni shiyasa wani lokacin bana ganin laifin iyayen da suke hana yaransu ci gaba da karatu,saboda ba kowace yarinya bace ke iya rik'e mutuncinta,sai kiga yarinya ta fito daga gidan tarbiyya amma tana shiga manyan makarantu sai ta ษai ษaice,ko rantsuwa zan iyayi nasan iyayen yarinyar nan basu san abinda takeyiba.
"Husna ce tace ke salma kiyi a hankali fa tana jinmu,."yoo tajiman ai nafison taji,ai ni bacin karta min wani fassara dana sameta na mata nasiha.
Dariya suka kwashe gaba ษaya haka suka cigaba da hirarsu kuma duk maganar dasukayi a kunnen zulaihat.
Gaba ษaya zooly taji ranta ya mata ษaci ta kasa gane a sama take ko k'asa,ko motsi kasayi tayi ta shiga kogin tunani.
"Sister ga naki can nasa miki ki matsa kusa watace ta faษa tare da taษa zooly.
"owk nagode.
Tana gama tara ta ษauki kayan ta mayar ษaki dan ji tayi zazzaษi na neman rufeta,sai da tasha kukanta sannan bacci yayi awan gaba da ita.
12:00pm su Ruky suka dawo cike da zumuษi suke tashin zooly,baby dan Allah ki tashi akwai news,dakyar ta iya tashi ta zauna fuskar nan ba walwala kamar wanda aka aiko ma da manzon mutuwa.
"Cikin haษin baki da nuna kulawa sukace baby baki da lpy ne?,.
"kai ta jijjiga alamun a'a.
"toh meya sameki?
"bata ษoye musu komai ba haka ta kwashe duk abin da taji ta faษa musu sannan ta k'ara da cewa ni yanzu nadama tazo mini,zan dena komai,zan yarda duk wani makaman iskanci , zan koma zulaihat ษina ta da,zanyi k'okari in cikama iyayena alk'awarin dana ษauka.
"Mtsss amma sweatheart kin bani mamaki,bansan har yanzu kinada k'arancin wayewaba,ashe bazaki iya tantance masu sonki da kuma masu miki hassada ba,toh wallahi wannan yarinyar bak'in ciki take miki,taga dare ษaya Allah ya ษaga darajarki,kin mallaki abubuwa da dama.
abinda har ta mutu inba wani ikon Allah da tsananin raboba ba lallai ta mallakesu ba,ko tantama banayi inda zata sami damar da kika samu bazatayi wasa da ita ba.
baby ki cire duk wani tunani a ranki ki tsaya ki kwashi arziki,kiji daษi, ki fantama, ki wataya, Ruky ta k'arasa maganar tare da kai mata kiss.
"Easher ce tai caraf tace baby ki nunamin yarin nan ko yar gidan uban waye,wallahi sai na mata cune,saita gane munci sunan mu na *untouchable*
"no ba za ai hakaba barta kawai na gane talauci ke damunta,yanzu kawai a ษaura daga inda aka tsaya.
"shiyasa nake k'ara sanki babyna,allah dai ya bar mana love.
Toh fa readers har yau dai akwai sauran rina a kaba,dan ga dukkan alamu zooly bata ganeba,muje zuwa...
*jannart Allah ya k'ara lapiya,yasa kaffara ameen*
*maryam muh'd lawal*๐
No comments:
Post a Comment