ππππππππ
*RAYUWAR HOSTEL*
ππππππππ
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
P.M.L
*MAMAN KHADIJA*
*MARYAM S BELLO*
*MRS FAWWAZ*
*FARIDAT MUSA*
*JANNART LAMEED'O*
*RUFAIDA YUSUF*
Page23 by
*ΚΚs ΚaΥ‘Υ‘aΚπ*
&
*Maryam s BΙllΦ
*
The next day Ruky tayi shirinta tsaf na zuwa wajen boka domin dubawa ko can ta baro maganin, sai dai to her greatest surprise ba a can ta Bari ba.
Sai ta ce
"To boka tunda ba a ga wancan d'in ba ina ga Ai sai ka bamu wani don a matsae muje kwarai da aikin nan."
Boka yayi dariya ya ce "Ruky mai duniya, Ai kin makaro domin Wannan maganin shi ne na k'arshe da ya rage min, kuma kayan had'in shi ma wahala suke yi sai dai ki yi hak'uri.
Ba k'aramin tashin hankali Ruky ta shiga ba da jin bayanin boka ba.
Haka Ruky ta mik'e jiki a salu6e ta koma da tsabar takaicin 6atan maganin nan.
*****
A B'angaren Doctor Maheer kuwa friend d'insa ne mai suna Dr Khaleed, Dr Maheer ya kwashe labarin komai ya fad'a masa game da Zulaihat da kuma *untouchables*
Bayan ya gama ne Dr Khaleed ya bashi shawarwari sosai akan kada ya rabu da zulaihat domin rayuwar ta tana cikin damuwa, gwara ya zamo jajirtacce akan lamuranta tunda yana sonta, kuma idan ya aure ta ma jahadi yayi.
Tabbas Doctor Maheer nason Zulaihat so na hak'ik'a sai dai 6angare d'aya na zuciyarsa yana tsoron karawa da *untouchables* domin ya riga da ya lura wasu irin yara ne da basa jin magana, kuma gasu 'yan duniya wanda duk wani abinda suka ce zasuyi to zasuyi d'in. Sheyasa yanzu dole sai ya bi a hankali idan yana son cimma burinsa.
Dr Khaleed yayi ajiyar zuciya ya dafa kafad'ar Dr Maheer yace
"Abokina bari na baka wani tak'aitaccen labarin abinda ya faru da wata yarinya a baya."
Dr Maheer yace
"Ina jinka Khaleed."
Dr Khaleed yace
"Wato akwai wata yarinya a baya da suka nemi ta shiga cikin k'ungiyarsu, sai yarinyar tak'i basu had'in kai, sai suka rik'a bibiyarta ta k'arfi da kuma ta magani, suka rik'a binta, suka takura ma yarinyar sosai suka hana ta sukuni, to sai Allah ya tsare ta bata shiga k'ungiyar ba, da suka ga duk wata hanya da zasu bi su dawo da ita cikinsu abin ya ci tura sai suka haukata ta, abin takaicin kuma kowane a cikinsu sai da yayi mata fyad'e.
To a gaskiya nidai zan baka shawara kar sake ka rabu da Zulaihat, sannan kar ka barta ta cigaba da zama a hostel, ni a ganina ka d'auke ta ka kaita can wani wuri kamar can cikin gari ka kama mata gida cikin mutane, kuma wanda daga can zata dinga shiga makaranta tana dawowa, sannan ka sanya masu tsaronta sosai, wanda ita kanta bazata san da su ba, saboda komai zai iya faruwa, so we have to be very careful sosai, sannan dole ne fa sai makaranta ta d'auki mummunan mataki akansu, don barin irinsu *untouchables* had'ari ne sosai."
Dr Maheer ya numfasa yace
"A gaskiya aboki na wannan shawara taka tayi, kuma nagode sosai Allah ya saka da alkhairi, sannan da na fara karaya da al'amarin amma yanzu shawarar da ka bani ta taimaka min sosai, na kuma samu k'warin gwiwa, kuma insha Allah sai na auri Zulaihat."
Dr Khaleed yayi murmushi yace
"Haka nakesonji daga bakinka, anjima sai muje a nemo mata suitable gida, da kuma irin mutanen da suka dace su tsare maka ita."
Dr Maheer yace
"Haka ne Allah ya shige mana gaba."
Dr Khaleed yace
"Amin."
Da yamma suka tafi neman gida, inda sukayi sa'a suka samu gida irin estate d'innan kuma wurin yayi kyau sosai, nan suka gama duk wani abinda ya dace suka tafi neman wad'anda zasu sanya da zasu tsare Zulaihat...
To masu karatu shin ya *untouchables* zasuji idan aka ce Zulaihat ta bar hostel? Kuma shin Dr Maheer zai auri Zulaihat kamar yadda ya fad'a? Sai kun biyo mu a next page don jin yadda zata kaya.
MSB AND MRS FAWWAZ
(Maman Ameema and Maman Inteesar)πππ
UNTOUCHABLESππ»♀️
No comments:
Post a Comment