🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘
*RAYUWAR HOSTEL*
🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L
Na
*MAMAN KHADIJA*
*MARYAM S BELLO*
*MRS FAWWAZ*
*FARIDAT MUSA*
*JANNAT LAMEED'O*
*RUFAIDA YUSUF*
Page 11 by
Maryam S bello
Hakan kuwa akayi abincin tayi mata ordering ana kawowa suka wuce hostel. Basu iske su Fatima ba da alama suna lectures. Gyalensu suka cire sukayi watsi dashi suka fara cin abinci. Sai da suka ci suka k'oshi sannan suka nemi wuri suka kwanta.
A hankali Ruky ta hawo ta kwanta bisa k'afafuwan Zooly, tana wasa da gashin kanta. Cikin salo na yaudara gami da k'warewa tace
"Anjima fa akwai had'ad'en chasu da zamuje..."
Da sauri Zooly ta tashi zaune ta ce
"Wai nikam ba'a hutawa da zuwa chasun nan ne? Kuma naga fa kwana biyu bamu shiga lectures ba, anya hakan daidai ne?"
Ruky tayi wani mayaudarin murmushi tace
"Haba mana baby, ay zuwa chasu yanzu ma muka soma zuwa, don haka dole ma ki saba da shi. Sannan maganar zuwa lectures wannan kar ki d'aga hankalinki, bakida matsala idan kina tare damu baki ba CO."
Bata ce uffan ba.
Da wayau da dabara Ruky ta ja Zooly suka fita daga hostel d'in suka koma can hotel.
Zaune suke a d'akin hotel itada Ruky da Eesha. Ruky na sanye da wani irin shegen wando marar tsawo sannan kuma ya mugun kama jikinta. Sai rigar jikinta irin mai k'irjin nan a waje ce, sannan ta matse ta sosai. Gashin kanta kuwa kalaba k'anana ce an jona mata gashin doki. Haka ma irin shigar Eesha tayi, tana can zaune tana latsa wayarta tana taunar chewing-gum tana girgiza k'afa. Ruky ce ta soma magana.
"Haba mana Zooly dan Allah kiyi sauri, haba tun d'azu fa muke jiranki, gaskiya nidai na gaji."
Eesha ta yi k'wai yayi k'ara ji kake k'ass. Sannan tace
"Ke saurinta ma ya dame ki, ay ni nan ina nan ina tunanin yadda partyn zai kasance, don Kinsan wannan shine ya kamata ya zama best party da zamuyi duk cikin parties d'in da mukeyi."
Tabbas idan akace Zooly nasan zuwa partyn nan to anyi k'arya, sai dai sam bata iya yin musu garesu koda kuwa taso yin hakan. Tashi tayi tana k'ok'ari zura wata doguwar riga matsatsa kalar ja. Ruky tayi saurin tsaida ta.
"Kar ki kuskura ki saka wannan rigar, so kike a raina mu a wurin ne? Ke ni bazan iya jerawa dake ba muddin kika saka wannan rigar, kada ki bani kunya mana, na d'auka kin waye ashe da sauranki?"
Ta d'an yamutsa fuska kad'an ta ce
"Nidai sam yau bana son zuwa partyn nan ku tafi kawai..."
Eesha tayi tsaki
"Ke nifa Zooly ban d'auke ki mai hankali ba, to wai don Allah meye amfanin rayuwar ne idan bazakiji dad'in rayuwarki ba? Kina abu kamar wadda bata waye ba..."
"Come on baby ki daure ki tashi muje ayi harkar arzik'i..."
Sam bata iya musu gardama don haka wasu kaya sukaba wanda ya fi nasu muni ta saka.
Tunda suka shiga wurin chasun, kaloli ke haska wurin, sai kaga blue, red, green, purple da sauransu ga kid'i sai tashi yakeyi kamar ana bugun k'irjinsu.
Mutane ne birjit ko wane da shigar arnaye, suna ta chashewa, haka kuma zakuga mace da namiji suna rungume da juna, wasu kuma fira kawai suke. Can kuma wasu ne hannuwansu d'auke da glass cup, wasu na shan lemo wasu kuma giya. Wani kuma abin birgewa ne a wurinsu. Idan ka kalli ko wanensu zaka ga rabinsu 'yan makarantar su Zooly ne.
Kamar kullum su Big boy na kunno kai hankali ya dawo kansu. Duk inda ka gifta ji kake ana fad'in the untouchables ne. Bayan da k'yar suka samu wurin akayi shiru kuma sai big boy ya hawo inda loudspeaker take ya fara bayani kamar haka.
"Nayi farin ciki da kuka amsa gayyatar da nayi muku. Nasan kun k'agu kuji dalilin da yasa na had'a wannan chasun. To da farko duk wanda yazo partyn jiya da muka had'a ma sabuwar k'awarmu zai ga bak'uwar fuska a cikinmu, to ba komai bane yasa haka illa mun k'aru daga mu shidda zuwa mu bakwai, kusani da farko sunanta Zooly baby, kuma zan kirawo ta nan on stage kowa ya kalle ta da kyau, don gudun kar a samu wani ya raina ta daga baya. Dan haka wannan shine dalilin da yasa na shirya wannan chasun just to welcome her to our click. Kamar yadda kuka had'u a nan, to ina mai tabbatar muku da jin dad'i, za'a ci asha, za'ayi rawa wanda ake kira da TILL DOWN!"
Gaba d'aya wurin aka d'auki tafi raf! raf! raf! Wato da alama abinda Big boy ya fad'a ya musu dad'i ya kuma burgesu. Bayan ya gama duk jawabin da zaiyi ya kira Zooly on stage, inda tsananin mamaki yasa ta kasa koda motsi. Easha ce tace
"Go on baby!" Ta dinga turata har ta isa wurin.
Gaba d'aya bayan angama gabatar da Zooly sai kuma aka shiga gabatar da party yada ya kamata.
A wannan daren anyi chasu, anyi bad'ala, an aikata 6arna ba kad'an ba, 'yan mata da samari sai dai kawai su shige ciki suna aikata masha'a. (Duniya ina zaki damu? Allah ka shirya ka tsare mana imaninmu. Amin summa amin.
Wshe gari bayn sun koma hostel suka dinga duba gifts d'in Zooly ta samu,gaskiya bata taba zaton mallakar irin wannan abubuwan ba,sai dai abin da ya fi bata mamaki bai wuce wani gift data Bud'e ta ga check na 500k,ta k'ara dubawa taga tabbas check ne sai kuma wani turarae Wanda bata jin mai dad'i kamar shi ba.
Ta ce "sweetheart ki duba wannan check d'in fa" ,Ruky ta karb'a ta ce "oh wannan Alh tanko dollars ne, ai wannan kad'an ne daga cikin irin gitfs d'in da yake ma chicks,wani freind D'ina ne da ya nace yana son ki ya Dad'e yana son kk kawai bana son na miki introducing d'in shi ne ban sani ba ko zaki yarda dashi"
Zuly ta ce "Ai gaskiya ya kamata mu had'u in mishi godiya,wannan irin kud'i haka".
Haka kuwa aka yi the next day suka had'u da Alhaji Tanko Dollars,wani bak'i dashi mai katoton ciki, a k'alla zai kai shekara hamsin amma kana ganin shi ka San naira ta zauna masa kuma daga ganin shi Tsohon alakonkon ne.
Sun D'an yi hira ya gama lallatse Ruky inda ita kuma zooly bata wani bashi fuska ba. Haka dai suka rabu yana ta lashe leb'e don ya so su D'an tab'a harka da zooly, sai da Ruky ta nuna masa ita Sabon hannu ce sai a hankali sannan ya hakura amma fa ya ci buri a kanta.
Tun daga lokacin birthday d'in zooly ta fara zama big girl, ga gifts d'in da ta sassamu,idanun ta sun bud'e da kud'i da kayan alatu na mata,shaye-shaye babu Wanda bata yi,yanzu Sam shiga lectures baya gaban ta sai dai kawai tayi ta bawa lecturers kud'i ana goge mata carry overs d'in ta.
Sannan ta zama side chick 6din Tanko dollar don har kasashen waje idan zai je ita da Ruky suke masa rakiya.
zuwa club kuwa kamar farilla, ita kenan yau wancan club gobe wancan,lokaci guda tayi suna a cikin yaran kwalta irinta, har idan ma baki San *zooly easy* ba to baki had'u ba.
Tanko dollar ya sakar mata bakin aljihun shi sosai, don har gida ya mallaka mata ya kuma siya mata mota mai tsadar gaske,ga kuma ta Jone da click d'in *Untouchable* yanzu sune family d'inta.
Sai dai duk Wannan abun da take yi bata bari a gida an gane halin da take ciki ba,idan Zata je gida kayanta Na mutunci take sawa da K'aton hijab d'inta har k'asa,kuma duk inda ta shiga ta fita bata bari sallah ta wuce ta.
Da umma take tambAyarta inda ta samu kud'i sai ta ce wai aiki ta samu a wani gidan abinci cikin hostel take D'an samun na kashewa.
Washh bari na aje alk'alamina sai dai ku biyo mu gaba kuji yadda zata kaya! Ya rayuwar Zulaihat zata kasance? Gashi tun ba'akai ko ina ba Zooly ta kasa cika alak'awarin da ta d'aukar ma iyayenta na kare mutuncinta, wanda a sanadin haka rud'un duniya da kuma sharrin shaid'an ya rinjayeta... yanzu aka fara labari sai dai kun biyo mu don jin yadda zata kaya
P.M.L
MSB💖
Mrs fawwaz
No comments:
Post a Comment