Wednesday, 4 September 2019
RAYUWAR HOSTEL PAGE 24
ππππππππ
*RAYUWAR HOSTEL*
ππππππππ
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
P.M.L
We don't just entertain we touch the heart of d readersπ
*MAMAN KHADIJA*
*MARYAM S BELLO*
*MRS FAWWAZ*
*FARIDAT MUSA*
*JANNART LAMEED'O*
*RUFAIDA YUSUF*
_thankz yhu for my beautiful bufday wishes! I fell grateful and lucky to have so many amazing by my side, fan's bohoot/bohoot shukriayh!!!_ One love#π
Serious sick!!!!π₯needed ur du'a friends
Page 24 by
*jannart lameed'o*π
(Babyn garkuwa)
Mutane 3 suka samu
maza, suka musu bayanin aikin da zasu musu, babban ne mai suna Isah ya fara magana,
"Insha Allah ogah zamuyi iyakan kok'arin mu wajan bata kariya yadda ya dace"
Dafa kafad'ar sa Dr Maheer yayi yana mai murmushi wanda yake k'ara masa kyau,
"Good Isah haka nike so, mutukar kukamun aiki yadda ya dace ni kuma Zan muku dukkan abunda kuke so"
"Insha Allah zamuyi kok'ari Oga"
Sallaman su yayi sannan ya sheda musu gobe zasu fara aiki, bayan tafiyan su Dr Khaleed ya dube Dr Maheer,
"Abokina da alaman nasara atare damu akan *untouchables*"
"Sosai mah, insha Allah mune da nasara , fatana Allah ya shiga tsakanina da *untouchables*"
"Ameen y Rabbi abokina, Amman ka dage da addu'a don zasu iyayin komai don ganin sun mallaki Zulaihat"
"Wannan hakane, kuma insha Allah Zan k'ara akan Wanda Nikeyi"
motan Dr Khaleed suka nufah, shi yake jansu suna tafe sunah hirah, Dr Khaleed ne ya ajiye Dr Maheer a gidan sah sannan ya d'auki hanyan gida.
Dr Maheer nashiga bedroom nashi toilet ya fad'a yayi wanka, tare da alola bayan ya fito ne ya tayar da sallah cikin nutsuwa ya dad'e yana kai kukasan gurin Mahaliccin sah, sannan yah shafa,
Kan bed nashi ya komah tare da d'aukan phone nashi dake kan bed d'in number Zulaihat ya kira, bugu d'aya yayi ta d'auka,
"Assalamu alaikum my soul, yah kake?"
"Lafiya qalau my dear, hope kina cikin k'oshin Lafiya?"
"Lafiya qalau my soul"
"Haka nakeson ji, yah karatu kuma? Fatan zan sameki anjima?
" alhadulillah my soul, eh zaka same ni babu inda zanje"
Hirah suka tab'a kad'an kafin sukayi sallamah kowa da tunanin d'aya cikin ransa,
Bayan gama wayansu Zulaihat tashi tayi domin yau so take tayi wah Dr Maheer kwalliya mai kyau, meckup tafarayi wanda rabonta dashi harta manta, ta nayi tana murmushi kaman Wanda Dr Maheer ke gabanta,
Tana cikin yi kenan Rukky ta shigo d'akin, ganin yadda Zulaihat take ta faman murmushi ita d'aya, yah tabbatar mata da Dr Maheer ne zaizo, nan take taji zuciyar ta tafara matah wani irin zafi Amman ta daure, ta dubi Zulaihat,
"Zooly yau kintuna da kwalliya ce? Koko kin dawo kan hanya ne?
Shuru Zulaihat tayi saima ci gaba da kwalliyan ta tayi,batare da takula Rukky bah, Rukky ganin tak'i kulata ne yasa ta kuma cika, tazo har wuya sauran k'iris ta fashe,
" Zooly ba magana nake miki bah?"
Sai a sannan Zulaihat ta d'ago idon tah, gami da kallan Rukky wacce tayi tsaye kaman gunki,
" Inace mungama wannan babin dake, nace miki sunana Zulaihat bah Zooly bah, muddin kinason iringa amsa miki magana to kik'irani da sunana na gaskiya bah shirme ba"
Rukky sake baki tayi tana kallon Zulaihat wacce tai mungun bata mamaki ,ji take kamar ta shak'eta Amman babu halin haka,
Juyawa kawai tayi tabar mata cikin d'akin,
Zulaihat kuwa hakan ya mata dad'i don cigaba da kwalliyan tah tayi abunta,
Bayan ta gama kwalliyan ta, tasanya wani black d'in dogon Riga mai adon red ajiki kayan sunyi matuk'ar mata kyau sosai kaman ba ita bah, rolling d'in d'ankwalin tayi, tana cikin faisah turare phone d'in tah yah fara k'ara alaman yana naiman agaji, dasauri ta d'auka ganin Wanda ke kiran ne yasa tayin wani murmushi sannan ta d'auka tare da karawa a kunnan tah,
"Hello my soul, harka iso ne?"
Mudai bamuji abunda yace mata bah saidai kawai munji tace "owk gani nan fitowa"
Takalmi ta zurah a k'afarta ta fitah, tundaga nesa ta hangoshi yayi matuk'ar mata kyau, k'ananan kaya shima yasa red and black kayan sun amsheshi sosai,sai aikin murmushi suke sakarwa junan su,
dap zata isa wajansa ne taji ansa mata Abu ak'afa tayi yuuuiiiiiii zata..................
*tofahπ€da magana anya Dr Maheer Zaiyi nasaran fitar da Zulaihat daga hostel kuwah? Danjin yadda za akayi kubiyomu*
UNTOUCHABLESππ»♀ππ»♀ππ»♀ππ»♀ππ»♀ππ»♀ππ»♀ππ»♀
*jannart ceπ*momyn Janan
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment