šš
*RAYUWAR HOSTEL*
ššššššššš
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L
Na
*MAMAN KHADIJA*
*MARYAM S BELLO*
*MRS FAWWAZ*
*FARIDAT MUSA*
*JANNAT LAMEED'O*
*RUFAIDA YUSUF*
Page15
*ŹŹs ŹaÕ”Õ”aŹ*
Ya Dad'e tsaye a wajen hana tunanin abinyi har ta gama lectures d'in ta fito,sai dai kash tana fitowa yaga ta nufi inda untouchables ke zaune suna tata rashin mutunci, a duniya ya tsani yaran don ya kula basu da mutunci kuma da alama sun Gagari kowa a school d'in.
Ganinta tare da su ba k'aramin sanyaya masa guiwa yayi ba, daga gani she's part of them, sai dai kuma she looks soo innocent, bata yi kama da lalatattu irin su ba.
Haka ya juya ya shiga motar shi zuciyar shi a jagule,ya rasa abinda ke masa dad'i a duniyar nan. Tambayoyi ne fal Cikin zuciyar shi, shin ita wacece ne? Kuma menene alak'arta da Wannan sangartattun yaran marasa tarbiyya? Lallai dole ne ya San yanda zai raba ta dasu tun kafin suyiwa rayuwar ta illa ( muko muka ce zancen yaushe?)
Haka ya shiga gida yana ta faman tunani da Neman hanyar da zai bi ya samu information a kan ta.
*** *** ***
Da dare misalin 12:00am Eesha da zooly na ta faman shiri zasu je birthday d'in wata k'awar su, sun yi shiga ta rashin arzik'i, kan nan yasha attachment. sai dai inda zooly take burge kowa bata tab'a shafa wani mai da zai jirkita mata complexion ba, bak'a ce kuma she's proud of her colour don a cewarta "black Is beauty".
Ruky bata nan sunyi tafiya da wani Alhajinta.
Kowacce ta cokala uban takalmi suka fito, da motar Zulaiha zasu tafi don haka ita ke driving,suna cikin tafiya sai motar ta tsaya a tsakiyar hanya, iyakar k'ok'ari sunyi wajen ganin motar ta tashi amma Abu ya gagara, suna nan tsaye sai suka ji alamar ana tahowa wajen su, d'aga kan da su yi sai gani suka yi wasu manyab maza sun kewaye su suna fadin" 'yan mata ya akayi ne? Motar ce ta tsaya," dayan ya kai hannu kan bum d'in Eesha ya ce WoW "amma fa akwai ki da kayan aiki" Eesha ta buge masa hannu ta ce "kai Dalla ja can da wani tsamin hannun ka kana tab'a mutane,mannerless human being kawai".
Lashe inda ta buge d'in yayi had'i da kallon ta ya lashi leb'enshi ya ce "ina son jarumar mace kamar ki".
Ita kuwa Zulaiha gaba d'aya ta gama tsorata da ganin Wannan bayin Allah, hankalin ta gaba d'aya a tashe yake,jikinta sai rawa yake yi tana faman had'a gumi.
Da taga abun na Neman ya fara nisa sai ta ce musu "Dan Allah kuyi hak'uri kar kuyi mana komi wlh Indai kud'i kuke so da motar duka zamu Baku amma kar Ku mana komi please I beg of you".
Wanda da alama shi ne babba a cikin su yace "Ai 'yan mata baki da kud'in da zaki bamu ya kashe mana thirst d'in da muke ciki a yanzu, kawai Ku D'an bamu abun duniya mu D'ana don ni da ganinki na kwad'aitu da ke sosai" ya k'arasa maganar yana mik'a hannu kan bust d'inta da suka yi tummm a cikin Riga sleeveless,sai kuma leggings da ta saka daga k'asa,ita kuwa Eesha bum shorts ne a jikinta da wata top wadda ko cibiya bata rufe mata ba.
Zulaiha kuwa Ganin ya mik'o hannu zai tab'a mata bust ya sata ja da baya tana mai nadamar fitowa a wannan uban Daren ga su babu suturar arzik'i a jiki,sai yanzu taga wautar su Daba su bi su j.b ba suka taho su kad'ai.
Ganin tana na ja baya ya sa shi sake mastawa kusa da ita da niyyar kai hannu jikin ta,Ai bata San sanda ta ranta a na kare ba, mutum biyu suka rufa mata baya.
Gudu take a kan titi ba tare da sanin inda zata je ba, ga uban takalmi a k'afar ta Wanda idan ba k'wararriya ba tafiya ma ba lallai mutum ya iya da shi ba, amma ita har da gudunta,ana haka ne ta gurd'e k'afa dunduniyar takalmin ta cire,amma ina Zulaiha bata tsaya ta bi ta kan k'afar ba haka ta ci gaba da gudunta.
A dai-dai kan kwana bata Ankara ba sai kawai jin wani Abu tayi kamar an jona mata electric shock,daga haka bata sake sanin inda kanta yake ba.
Su kuwa ganin haka yasa suka koma inda suka bar Eesha da wasu mutum biyun har sun turmushe ta suna k'ok'arin raping d'inta.
*********
A hankali ta bud'e idonta,ta ga fanka na jujjuyawa, sai da ta gama zagaye wajen da idon ta kafin ta gane wannan d'akin asibiti ne, sai a lokacin ta tuna abinda ya faru.
Tana cikin tunanin wane hali Eeshat take ciki sai ta ji an turo k'ofar d'akin,takai duban ta ga k'ofar don ganin wanene?
Sai taga fuskar kamar ta tab'a ganin shi, to amma a ina? Tabbas he looks familiar,kafin ta kai ga tuna inda ta sanshi ya ce mata "malama ya jikin?"
Voice d'inta a dashe tace "da sauk'i".
"to Allah ya k'ara sauk'i"
"Ameen".
"Yanzu ina ne yake miki ciwo?" Tace "k'afa da kai".
Sai a lokacin ne ta tuna Ashe fa ta gurd'e da takalmi,ta kai duban ta ga k'afar taga an nad'e da bandages.
*Tou mu dai sai mu ce Zooly Allah ya k'ara lafiya, Amma shin waye Wannan da ya kad'e zooly? Kuma ina ta San shi? Shin me ya faru da Eeshat a wannan Daren? Shin Dr.maheer zai sake had'uwa da zooly kuwa? Idan sun had'u ya zata kasance?* _Ku biyo mu don samun wannan answers din._
*pure moment*
No comments:
Post a Comment