Wednesday, 4 September 2019

RAYUWAR HOSTEL PAGE 03

🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘
*RAYUWAR HOSTEL*
🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
        P.M.L

2017

Na

*MAMAN KHADIJA*
*MARYAM S BELLO*
*MRS FAWWAZ*
*FARIDAT MUSA*
*JANNAT LAMEED'O*
*RUFAIDA YUSUF*

*Care is a special manner that keep true friendship a live since i cant see you let my care be with you  Mummyn Sultan i really care 4 u*

 *Page 3 by:*
*FARIDAT MUSA*

Kwana Zulaiha tayi da tunanin kala-kala a ranta game da  *untouchables*ganin tunanin baya da amfani yasa ta dainawa, tare da k'udirta kauce ma duk wani hanyar da zai had'ata dasu..

*Washe gari*

Da wuri Zulaiha ta tashi tayi wanka tashirya saboda tana da lecture 7-9 agurguje tayi masu Zainab sallama ta fita.

Sanye take da hijab blue har k'asa jakanta na rataye a kafad'arta, hannunta na rik'e da wasu takardu, duk Wanda ya kalleta seya k'ara saboda tsabar nutsuwanta da yanda take tafiya a nutse.

Kanta a k'asa yake bata iya kalle-kalle inhar tana tafiya, turus taja ta tsaya ganin mutum yasha gabanta, kaucewa tayi da niyar bin gefe, nan ma akasha gabanta ja tayi ta tsaya batare da tace komai ba, tsawon mintuna biyar bata yi musu magana ba, gani bata da niyar yin magana yasa Big boy matsowa daf da ita..

" ke 'yar gidan uban waye da bazaki iya d'aga ido ki kalli mutane ba balle ki bada hak'uri"?.

"Duk wani rashin mutuncin ka ya k'are akaina amma karka kuskura kasa iyaye na aciki ".
Ruky tace "kaji 'Yar matsiya ta in aka zagi iyayen naki me zakiyi?".

"Ke dallah rufawa mutane baki ki zauna ki K'are wa kanki kallo kafin kice wani abu, kina nan lalaltacciya dake kina mace ki zauna anacin mutuncin mace dake duk yanda akayi keba mace bace".

Hannu Ruky ta d'aga da niyyar mari Zulaiha, cikin zafin nama ta rik'e hannun ta wanka mata jahilin mari, seda taga taurari a idonta tsabar zafin marin, dungular mata da hannun tayi ta nunata da d'an yatsa " wannan ya zama na k'arshe da zakiyi yunk'urin Marin wata".

Jibson ne ya d'aga hannu zai mare ta KB ya rik'e hannun " zata iya zubar mana da mutunci a skul innan dan yanzuma idon mutane ya fara dawowa kanmu".
Saukar da hannunsa yayi yana muzurai.

"Na d'auki aniya sena watsar da duk wani ikonku a makarantar nan se kunzama k'uda banza duk d'aya kuke" tana gama maganar tasa kai tayi gaba idanuwan ta arufe ko gabanta bata gani saboda b'acin rai.

Eesha dake tsaya agefe kaman an dasa ta tace " hey..... Kinyi kad'an kija damu domin Ku mud'in bana wasa bane ".

"Tunda haka kikace mu zuba mugani d'an halak ka fasa" tana fad'a tasa kai ta tafi.

"Gayu anzo gurin fa, kuji mun tsinanniyar yarinya tana nima ta raina mana hankali" Kb yace yana furzar da iska daga bakin sa.

Ruky da tunda tasha mari batace komai ba tace " koma meye ai Jibson ne yaja mana tunda tun farko seda mukace arabu da ita amma ya nace yarinya gata nan typical 'yar k'auye da ita tana niman ta raina mana tunani, wallahi tunda ta mareni se nabi duk hanyar da zanbi wajen ganin na lalata mata rayuwa se ta dawo rik'ekk'iyar karuwa me lasisi".

Ihu suka sa suna fad'in " se Ruky duk abunda kika fad'a munsan zaki iya".

A B'angaren Zulaiha kuwa tana barin wajen gidin wata itaciya taje ta zauna tasha kukan ta son ranta dan babban aiki ne a gabanta na ja da *untouchables* , ganin kukan ba mafita bane a gare ta yasata tashi ta koma Hostel zuciyarta cike da haushin rashin samun lectures...

Da sallama ta shiga d'akin su ganinta awannan lokacin yasa Fatima jefo mata tambaya "lafiya kuwa ki ka dawo yanzu?".

Hmmmm ajiyar zuciya ta sake sannan tace "inafa lafiya na had'u da lalatattun yarannan."
" kina nufin *untouchables*?".
" su fa? meya had'aki dasu?".
Kaf ta kwashe Duk abunda ya faru ta labarta mata.
"Lallai Zulaiha kin d'ebo ruwan dafa kanki".
" kaman yaya ban game ba?".
" shawaran da zan Baki shine ki fita harkarsu dan Kuwa sun wuce duk yanda kike tunani, yaran asalin hatsabibai ne ".
"Naji na Kuma na aminta da shawaran ki in Allah ya yarda bazan sake kulasu ba"...

Anya kuwa Ruky zata iya lalata Zulaiha kamar yanda tasha alwashi?

Shin Zulaiha ce xatayi nasara ko *untouchables*?

Ku biyo mu da sannu zamu warware muku duk wani k'ulli...........

*Pure moment*

No comments: