Wednesday, 4 September 2019

RAYUWAR HOSTEL PAGE 16


🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘
*RAYUWAR HOSTEL*
🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘


PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
        P.M.L

Na

*MAMAN KHADIJA*
*MARYAM S BELLO*
*MRS FAWWAZ*
*FARIDAT MUSA*
*JANNAT LAMEED'O*
*RUFAIDA YUSUF*




*Page 16*
*by mmn khadijah💅*


K'okarin take ta tuna inda tasan wannan fuskar amma abin yaci tura,katse mata tunanin yayi da cewa."sunana dr Maheer ina aiki a clinic dake school ɗinku."owk tabbas a clinic nasan fuskar nan ta faɗi a
 zuciyarta.

Dr Maheer ya cigaba da cewa na fito yin uzirina ba zato naga abu ya faɗomin ta sanadiyya haka na kaɗeki,shiyasa na ɗakkoki na kawoki private hospital ɗina.

"tnx ta faɗa a hankali.
Kara duba kafar yayi sannan ya fuce.

Kai gaskiya na auna arziki,ni wannan kaɗan alkhairi ta zama mini,dan bacin ita bansan me waɗan nan mazan zasumin ba,Allah sarki Eeshat ko kina wani hali oho,Allah yasa basu miki komai ba,katse  mata tunanin yayi da cewa.

"me kuka fitoyi cikin daren nan?kuma ina zakuje??.

"rasa abin faɗa tayi sai kai ta sunkuyar k'asa tana dana sanin wannan fita.

Jin tayi shiru yasa Dr cigaba da magana,taya zaayi maza bazasu biyo kuba,kuna fita cikin dare sannan da irin wannan shigar,ta iya yuyuwa da kunyi shigar mutunci bazasuyi attemting zuwa wajenkuba,amma duk wanda ya ganku a irin wannan dare da kuma irin wannan shiga dole zai raya wani abu aransa game daku,dan allah  ki kiyaye badan komaiba kodan kula da lapiyarki,dr Maheer yaa ɗau lokaci yana ma zooly nasiha kuma maganganunshi da alama sun ratsata dan har kuka saida tayi,haka ya tafi ya barta jiki duk a sanyaye.


4:00pm dr ya dawo dakin Zooly dan k'ara dubata,bayan yayi komai ya gama har zai fita Zooly tace dr pls inason ka taimakeni.

"Wani irin taimako kike nema.

Gyara kwanciya tayi sannan tace "gaba kaɗan da inda ka kaɗeni na bar k'awata a wajen da sauran mazan da suka taremu,sannan motata tana wajen don allah ka taimaka kaje ka dubamin ta karasa maganar tare da fashewa da kuka.

"owk ba matsala daga nan can na nufa insha allah stop crying.

"tnx,nagode dr.

Office ya shiga da sauri ya ɗakko key na mota ya nufa inda Zooly ta masa kwatance.

Yana Zuwa kuwa yaga motar a gurin sai dai kuma ba Eesha kamar yadda ta faɗa,yayi dan dube dube ko allah zaisa ya ganta dan har k'asan motar saida ya duba amma wayam bega kowaba.

Buɗe motar yayi ya fara bincike acan kasan kujera ya hango waya beyi sanyaba ya dakko ya buɗeta saboda a kashe take,kamar jira ake ya buɗe wayar aiko saiga kira ya shigo, sweatheart ya gani akan screen ɗin wayar be kulaba haka ya barta ta karaci ringing harta katse shiko yaci gaba da bincike a cikin motar  ko zai samu information akan Eesha.

Saida akai miss calls uku kafin ya ɗaga,assala......."katse masa maganar akayi daga can ɓangare da cewa zooly kina ina inata nemanki wayarki bata shiga,nashiga tashin hankali gani a asibiti nida Eesha ba yadda take mazan da suka tareku duk su huɗun saida sukai mata fyaɗe, sannan sukasa reza suka farka mata gabanta saboda rashin kunyar datayi musu wani bawan allah ne ya tsinceta a yashe shine ya kawota asibiti dajin muryar Ruky kasan tana cikin tashi hankali.

"yanzu kuna wani asibiti dr maheer ya tambaya.

"wayyo na shiga uku malam dan allah ina zooly dama dakai nake magana bada zooly ba,plsease where is she?karkacemin wani abu ya sameta please i beg of you.
"dakyar dr ya shawo kan Ruky tai shiru ta saurareshi be ɓoye mata komai akan abinda ya faru da zooly ba,nan ya bata address ɗin asibitin da zooly take ahaka sukai sallama.

Haka Ruky taci gaba da jinyar k'awayenta koda yaushe tana hanya bata asibitin da Eesha take bata asibitin da zooly take.

Shima dr maheer ba'a barshi a bayaba wajen kula da zooly,ya bada lokacinshi sosai a wajenta kuma in har yaje ɗakin saiya mata nasiha cikin siyasa,ahankali nasiharshi ta fara tasiri a zuciyarta dan har mamari take yazo.

Dr maheer ya gano zooly tana jin daɗin nasihar da yake mata dan haka saiya canza salo ya farayin duk wani abu da zaisa ta soshi,zooly batai auneba taji son dr ya fara shiga zuciyarta.

Haka lamari yacigaba da kasancewa tsakanin dr da zooly yanzu in ka gansu zakace sun shekara tare dan ba karamin shakuwa sukayiba.

Yau itace ranar da aka sallami zooly dan saida tai sati biyu a asibiti.siyayya sosae Dr ya mata sannan ya kaita har bakin Hostel,basu tsaya wani hiraba dan yana sauri haka sukayi sallama ta shige ciki.


Bata sami kowa a ɗakinsuba suna wajen wani programme da akeyi acikin sch dan haka ta baje ƙƙledar da dr ya bata.

Kayane sosai aciki wanda ya haɗa da dogayen riguna normal ba irin wanda take sakawaba masu nuna shape ɗin jiki,takalma da turaruka ,wani murmushi ta saki mai ciki da love kamar a gaban dr take."allah sarki my honey insha allahu zan cika maka alk'awarin dana ɗauka, bazan sake shigar da be kamataba,zanyi kokari in koma *zulaihat* ɗina ta asali.

Yanzu ba laifi zulaihat ta shiryu dan kusan kowa ya fahimci haka kota yanayin shigarta,kayan da dr ya bata shi take sawa da wasu ɗinkuna na atamfa datayi amma suna kama mata jiki,gaba ɗaya ta daina fita da gyale sai hijabi.


*toh zulaihat allah yasa dai ba tuban muzuru kikayiba*
*ina labarin su ruky da kawarta a asibiti ku biyomu danjin ya aka kaya*

*the untouchables*

No comments: