Wednesday, 4 September 2019

RAYUWAR HOSTEL PAGE 01

šŸ˜šŸ˜šŸ˜šŸ˜šŸ˜šŸ˜šŸ˜šŸ˜šŸ˜
*RAYUWAR HOSTEL*
šŸ˜šŸ˜šŸ˜šŸ˜šŸ˜šŸ˜šŸ˜šŸ˜šŸ˜

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
        P.M.L

Na

*MAMAN KHADIJA*
*MARYAM S BELLO*
*MRS FAWWAZ*
*FARIDAT MUSA*
*JANNAT LAMEED'O*

_Ba mu yi novel d'in nan don cin mutuncin kowa ba sai don fad'akar da 'yan mata masu irin wannan halin_

~jinjinar ban girma ga manyan mata masu Aji, manya maganin k'anana, hazik'ai kuma fasihan marubuta Wanda duk duniya ake ji damu watou~ *pure moment of life writers*
    Allah k'ara basira da zak'in hannu

        Up
           Up
              Up
*Pure moment*

Page 1 by
*ŹŹ€s Ź„aÕ”Õ”aŹ*šŸ˜˜

       Babbar university ce wadda ake ji da ita a fad'in Nigeria, ta had'a yaruka daban-daban da kuma d'alibai from different backgrounds.

      Can gefe wata akwalar taxi ce ta shigo cikin school d'in tayi parking a bakin gate d'in hostel.

       Wani Dattijo ne mai kimanin shekara 50 yake Jan taxi d'in, gefen shi kuma matashin saurayi ne mai kimanin shekara 29, sai kuma mutum hud'u da ke back seat d'in.

      Dattijuwa Baaba Hajara mai manja da kuma yaranta 'yan mata guda 3, Zulaiha ita ce babbar su wadda kuma ita aka Rako school d'in, sai kuma Khadija mai bi mata sai Aisha 'Yar auta duka suka fito daga cikin taxi d'in, inda su Khadija  ke ta fito da kaya daga boot d'in.

    Zulaiha budurwa ce mai kimanin shekara 19, bak'a ce doguwa mai cikakkiyar fuska, tana da innocent face sosai idan ka ganta zaka ce ba za a saka mata hannu a baki ta ciza ba.

      Tana sanye da yalwataccen hijab mai hannu, brown colour har k'asa.

      Gaba d'aya iyalan sun tsaya a bakin taxi d'in inda malam kabiru mai taxi ke yiwa d'iyar ta shi nasiha akan rik'e mutunci da kuma kamewa.

      "zulai, ki rik'e mutunci ki, ki kula da kanki kada ki biyewa lalatattun yaran nan da basu da mafad'i,ki mai da hankali wajen karatun ki ki yi abin da ya kawo ki maka ranta kinji d'iyar albarka "

     Zulaiha da kanta ke sunkuye ta ce "to Baba insha Allah ba zan Baku kunya ba"

       "Yawwa to Allah ya miki albarka,ga wannan kya D'an rik'e a hannun ki kafin a sake samu sai in bawa yayanku ya kawo miki"

       1000 naira note ya mik'a mata ta karb'a tayi godiya, sai Baaba Hajara itama ta kunce  kud'i daga jikin zanin ta ta mik'a mata ta ce "to zulai ga wannan kya k'ara ko,cinikin manja ne da aka yi jiya da yau na had'o miki"

       Ta ce "laaa Baaba ki barshi Wanda Baba ya bani nayi manage kafin a k'aro min wani.

      Baaba Hajara ta ce "yau ga yarinyar wofi, kika San yanda zaman naki a nan d'in zai kasance? Karb'i nan matafiyi ba ya k'in guzuri"

     Ta sa hannu ta karb'i kudin tai mata godiya.

     Su Khadija suka d'aukar mata kayan aka kai mata har d'akin su sannan suka rabu suna kukan rashin yaya zulai.

      Sai da zasu tafi ne yaya Hasheemu ya Ciro 600 ya sake k'ara mata.

      Haka suka tafi suka bar ta da kewar su.

     D'akin da aka bawa Zulaiha su uku ne a ciki,'yan d'akin kuma sun karb'e ta da mutunci, su suka taya ta shirya kayanta suka kuma dafa musu abinci a ranar.

       D'ayar tana lvl300 dayar kuma tana final zainab da fatima.

     The next day ta fara zuwa lectures, inda tun shigar ta lecture hall d'in wasu group da ake kira *untouchable* suka k'yallo ta.

      Group ne na kangararrun yara  Wanda iyayen su suka sangarta su,group d'in ya had'a maza 4 da mata biyu Wanda suka buwayi kowa a school d'in.

     Tunda suka k'yalla ido suka ganta sai suka yi sha'awar ta shiga group d'in nasu, "sai dai kuma Ai yarinyar looks too local gaskiya ba class d'in mu ba ce" Ruky ce mai fad'in hakan.

      Eesha ta ce "Dalla duba wani dogon hijab da ta saka kamar wata matar liman, kai some girls are funny wollah"

     Suka kwashe da dariya gaba d'ayan su, Jibson ya ce "amma Babyn nan ba k'aramin cash zata ja mana ba, Dole ne mu San yanda aka yi ta dawo cikin mu".

      Ana can ana lecture inda *untouchables* suke nan suna planning  yadda zasu yi Zulaiha ta dawo cikin su.

        Har aka gama lecture d'in basu gane komi da aka yi ba.

*Pure moment*

No comments: