Wednesday, 4 September 2019

RAYUWAR HOSTEL PAGE 31

🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘
*RAYUWAR HOSTEL*
🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘

*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
  {We don't just entertain and educate we touch the heart of readers}

      P.M.L

*MAMAN KHADIJA*
*MARYAM S BELLO*
*MRS FAWWAZ*
*FARIDAT MUSA*
*JANNART LAMEED'O*
*RUFAIDA YUSUF*

Page 31 by
  Jannart lameed'o
  {Babyn garkuwa}

      It's too droop b'cos true love happens once in life my FANSπŸ˜»πŸ‘Œ

     *w*ashagari Zulaihat ta had'a koman tah, karfe 8 na safe ta gama shirin tah Dr Maheer kawai take ji yazo,
      Karfe 8:15 yah iso k'ofar gidan, kiranta yayi awaya tare da sheda mata yah iso, batawani b'ata lokaci ba ta fito,
    Sanye take da pink d'in riga dogo  tare da pink d'in hajibi shima Amman mai hannu tayi kyau sosai,
   Yayi da Dr Maheer ke sanye da pink d'in shadda mai aiki fari a jikin sah, kansa yasha farin hula hatta agogon hannun sa fari ce yayi kyau sosai,
     Kana ganinsa kaga d'an matashi maiji da kyau, ilimi, da nasaba, sai sheki yake,
      Tafiya take kaman tana tsoran kasa , cike da yanga, harta iso wajan Dr Maheer baisan ta iso bah saida ta isa kusa dashi tare da hure masa ido, cikin ajiyan xuciya ya dawo hankalin sah,.

    "Lafiya my soul ka wani kafeni da ido sai kace baka sanni bah?"

   Murmushi yayi, yana kare mata kallo yadda tayi wani kyau yau kaman ba itah bah.

     "My baby kece kullum cikin rud'ani kaman bake ba, kinga wani irin kyau da kikayi yau kuwa? Kaman in gudu dake nayi ta kallon ki"

    Fari tayi da idanun ta , tare da rausayar da kanta gefe,

     "My soul kenan ae duk kyau na ban kaika bah,ni har tsoro nike kar wata ta kwace mun kai muddin kana fita cikin wannan kwalliya"

    Ta karashe maganan cikin shagwa6a, da kuma kishi ganin yadda yayi wani kyau yau, she kawai ta ji gaban ta na fad'uwa,

    "Haba my sweetheart ke kanki kinsan Zulaihat ta Maheer ce haka Maheer na Zulaihat ce komin wuya komain tsanani muna tare dake,  babu abunda zai raba Zulaihat da Maheer d'in ta sai mutuwa,

      Dariya suka sake tare dukkan su kowa najin son d'aya cikin ransa.
   Sun juma suna hira kafin ya bud'e mata motan tashiga,
    Tasha ya kaita kaman karsu rabu haka suke ji, saida ya tabbatar motan tasu ya tashi kafin ya tafi cike da kewar sahibarsa,

   Zulaihat na isa gida, gida ya kaure da murnah kowa sai murnan ganin ta yake, bayan taci abinci ta huta ne , take sanar da Ummah tata abunda ya kawo to,
  Ummah ta nuna jin dad'in ta sosai tare da saka musu  albarka, yayun ta suna dawowa Ummah ta sheda Musu ,suma sunnu na jin dad'in su sosai,

******************
Bangaran su Rukky kuwa suna kulle cikin makaranta ko bari aje wajan su ba ayi,
   Tunda aka kulle su babu mai cewa komai kowa da tunanin da yake cikin ransa,
    Rukky ce ta fara magana cikin tashin hankali,

   "Wallahi KB kei ne ka jefamu cikin wannan rayuwa, kei ne ka lalata min rayuwa na, ka mai dani tamkar akuya, Allah ya isa KB, yanzo idan Dady d'ina yazo wajan nan nagama kad'ewa"
   Tsawa KB ya daka mata yana huci kaman zakin da ya kwana bai ci bah,
   
      "Ke malama saurara, nine na kawo ki yadda nake? Ko kuma na miki dole ne? Daman can da gutun iskanci ki, kikazo cikin school d'in nan dan haka karki d'aga mana hankali"
   Dubansu Eysha tayi d'aya bayan d'aya, idon ta ya kad'a yayi jah kaman garwashi sai huci take,

     "KB ,Jibson, kun cuce rayuwa ta wallahi kun barmun abun fad'i cikin al'umma, tun farko naki harkan nan , Amman saida kukasan yadda kukayi nashiga cikin ku ,Allah sai ya sakamin wallahi"
 
     Sai yanzo Jibson yasamu daman magana,

    "Da Allah Ku fura wa mutane baki, zamuji da Wanda muke ciki ne ko kuma da mitan Ku, banzaye ja kuna kawai"

     Haba nan da nan Rukky ta haure sarkin rashin hakuri,

     "Malam waye banzaye? kaji d'an akuwa mai cin duk dusan da ya gani batare da tsaya tattacewa bah"

    "Ke Dan ubanki nine Dan akuyan?"

     "A nafadi maka ko kanada abunda zakayi ne?"
 
    Ae bata gama magana ba ya d'auke ta da wani mari Wanda hakan ya tilassa mata dafe wajan,
   Daga ido tayi batare da wani tsoro bah ta tsinke Jibson da wani mariiiiiiii,

    "An fad'i d'an akuya"

Zuciya ne ta taso ma Jibson nan take ya fara dukan Rukky baji ba gani yana kuma takata da kafarsa, itama Rukky ramawa take,
   Ganin haka yasaka Eysha fara zagin KB akan yara basu, shuru ya mata shima ganin yaki kulata yasa ta cire takalmin kafarta ta kwad'a mishi,
     Cikin zuciya yayi kanta da duka,
     Fad'a ne ya kaure tsakanin su babu abunda ke tashi sai karan duka,
     Kowah na  zagi d'aya cike da jin haushin junan, kafin zuwa wani lokaci sunyi wa junan su jina_jina kaman Wanda aka saura musu halitta lokaci d'aya,

    Ganin haka yasa muka kulle musu kofar mukayo waje.........................

UNTOUCHABLESπŸƒπŸ»‍♀

No comments: