ππππππππ
*RAYUWAR HOSTEL*
ππππππππ
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
P.M.L
*we dont just entertain and educate,we touch d hearts of readers*
*MAMAN KHADIJA*
*MARYAM S BELLO*
*MRS FAWWAZ*
*FARIDAT MUSA*
*JANNART LAMEED'O*
*RUFAIDA YUSUF*
*Page 28*
*By*
*ΚΚs ΚaΥ‘Υ‘aΚ*
Bayan zulaihat ta fito daga lectures a bakin lecture hall d'in ta ga sahibin nata,kai tsaye wajen Shi ta zarce, ita kuma Halima ta wuce hostel
Bayan sun D'an zauna ya bata meatpie da drink d'in da ya siya musu, suna ci suna hira, ya yi gyaran murya ya ce "my zee akwai abubuwa biyu da nake son na sanar dake masu mahimmanci"
Ta tattara hankalin ta waje guda ta ce "ina jin ka my soul" ya ce "yawwa daga farko dai yau nake so ki yi parking ki koma wancan gidan don an gama gyaran shi kuma gaskiya as I can see
You are not safe here any more"
Godiya tayi masa mai yawa tare da yi masa addu'o'i Wanda suka sanyaya masa zuciya,yaji dad'i sosai
Yace "ba godiya tsakanin mu my soul ke dai ki ta mana addu'a Allah ya zab'ar mana abinda yafi alkhairi ya kuma cika mana burin mu".
Ta ce "Ameen"
Ya ce "to sai abu na biyu, ina ga its high time iyaye su shiga cikin maganar auren mu,don haka idan kin koma wancan gidan sai ki fara istibra'i daga nan sai mu yi proceeding"
*ISTIBRA'I* ta mai-maita Kalmar a cikin ranta, nan da nan idanunta suka kawo k'walla,wani irin malolo taji ya tokare ta a mak'oshi,ga wani d'aci da yake taso mata a cikin bakin ta, sai yau ta sake yin regretting abun da ta aikata, sai dai bata ce komai ba ta ci gaba da sauraron bayanin da yake mata, waton yanzu Maheer kallon karuwa yake mata kenan? A tunanin shi lalacewar ta har ta kai yanda zata dinga bin maza da yake mata zancen istibra'i? Amma babu komai Allah ne shahidi akan bata tab'a aikata zina ba sai dai ta San tana yawan kusantar ta,Kuma bata da wata hanya da zata wanke kanta daga zargin da ake mata don haka ta ja bakin ta tayi shiru.
Sun gama magana akan zata je ta kwaso kayanta su koma gidan da ya kama mata d'in
Sam bai kula da yanda yanayin ta ya canja ba don shi amincewar da tayi zata yi istibra'i ayi maganar auren su ya sa shi farinciki sosai
Tace masa zataje ta hado kayan ta sai ta zo su wuce ya ce "to my luv, bara na lek'a clinic kafin ki gama",ta ce "to"
Tana barin wajen Shi hawayen da take b'oyewa suka fara bin Kumatun ta,har bata ganin hanya sosai don yanda idanun ta ke kwaranya,a haka ta isa hostel ta samu Halima tayi musu girki ta gyara d'akin, bata bi ta kanta ba ta fad'a kan katifa ta fara gunshek'en kuka tamkar ranta zai fita,ji take kamar zuciyarta zata Faso k'irjinta ta fito saboda tsananin b'acin rai da kuma Dana sanin da take ciki.
Hankalin Halima ba k'aramin tashi yayi ba ganin halin da kawar tata take ciki, a rikice ta iso wajen ta ta dafa kafad'arta tace "Zulaihat lafiya? Me ya faru? Fad'a kuka yi da Dr. d'in? Ko kuma untouchables d'in ne suka sake k'ullo muku wani abun?"
A hankali zulaihat ta d'ago daga ruf da cikin da tayi ta kalli Halima da jajayen idanun ta tace "Halima na Dad'e ina regretting biyewa su Ruky da nayi na b'ata rayuwata a banza, amma ban tab'a yin Dana sani mai ciwo kamar wadda nake ji a yanzu ba,kaico na Halima nayi asara mai yawa,na Riga na zubar da mutunci na gaba d'aya a idanun duniya hatta a idon wanda nake matuk'ar k'auna,n abarwq 'yaya na abin fad'a" ta sake rushewa da wani kuka mai tsuma zuciya
Halima tace "me ya faru zulaihat? Me maheer ya miki?"
Nan zulaihat ta kwashe duk yanda suka yi da Dr. maheer ta gaya mata sannan ta k'ara da cewa wallahi Halima ban Tab'a sanin d'a namiji ba a rayuwata,na San nayi runs sosai da maza da mata amma ban tab'a bari wani ya keta min haddi ba,sai dai na San ko zan had'iye kur'ani ba Wanda zai tab'a yarda da hakan"
Dafa kafad'ar ta Halima tayi ta ce "I trust you my friend,na yarda dake 100% amma kuma da kin sani kin sanar da shi gaskiya"
Zulaihat ta sa tissue ta share majina a hancin ta sannan tayi murmushin takaici ta ce "ba shi da wani amfani In Sanar masa tunda ya Riga ya yanke min hukunci,ita gaskiya Ai dole wata rana zata bayyana,idan har da rabon za mu yi aure to da kanshi zai gane gaskiya ba sai na gaya mishi ba"
Halima ta ce 'to Allah ya tabbatar da alkhairi, zulaihat tace "Ameen"
Nan suka tashi suka fara parking d'in kayan, cikin lokaci kad'an suka gama had'a kayan tayi masa waya ta sanar da shi sun Gama
Untouchablesππ»♀
No comments:
Post a Comment