Wednesday, 4 September 2019

RAYUWAR HOSTEL PAGE 17

🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘
*RAYUWAR HOSTEL*
🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘


PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
        P.M.L

Na

*MAMAN KHADIJA*
*MARYAM S BELLO*
*MRS FAWWAZ*
*FARIDAT MUSA*
*JANNAT LAMEED'O*
*RUFAIDA YUSUF*



*Wannan shafin nakune ga duk wata mai suna khadija da hafsat ina kaunarku matuka❤😍👄*


*Page 17*
*by mmn khadijah💅*


Kwana biyu da sallamar Zulaihat aka sallami Eeshat itama ba laifi ta sami sauki sosai da yake ta samu kwararrun likitoci.

Zaune suke a d'aki suna hiransu."zooly ce tace hmmm nifa har yanzu inhar na tina abinda ya faru damu sai naji yarrr a jikina,wadan nan shegun mutane kamar wanda aka aiko?"

"ai inma aikosu akayi zasu gane sunyi kuskure babba a rayuwarsu,Alhaji Ali sabon kud'i yasa yan sandan farin kaya (SS) su bincikosu nasan wallahi in har aka ganosu zasu gane basu da wayau,danni kaina ina tausaya musu" cewqr Ruky.kamar jira ake ta rife baki sai wayar zooly ta dau ruri *Honey*shine abinda muka gani akan screen din wayar,cikin nutsuwa da soyayya dake wayarta dan saika kasa kunne sosai zakaji abinda take fad'a.

Eeshat kuwa kallan Ruky tayi suka buga tsaki a tare dan sun fahimci da Dr take waya sukuma ji suke kamar su soka masa wuk'a basa kaunar alak'arsu.

Sun dad'e sosai suna waya a karshe mukaji tace "owk sai kazo,love youuu" ta sauke wayar a kunne.

Duk wayar da tayi su Ruky suna zaune basu motsaba,bayan ta gama ne Eeshat tace "nifa wannan mutumin haushi yake bani naga sai wani shige miki yakeyi,toh maganar gaskiya wannan ba class d'inki bane,ai tuni kin wuce ajin wannan, keda kike a high class inake ina kula k'ananan kwari ,yanzu insu Alhaji suka ganki da wannan ai sai su rainamu,gaskiya karki ja mana raini,better change ur mind".


"fad'a mata dai dear,ko taji naki,dan naga bata d'auki nawaba" cewar Ruky.

Ita dai Zulaihat bata kulasuba sai murmushin da takeyi kawai,a ranta ko fad'i take ku kuke daukanshi a lower class,amma ni yafi min duk wani wanda nayi hurd'a dasu abaya.

Ringing d'in wayar Ruky ce ta dawo da ita daga maganar zucin da takeyi.

"hello Jibson,harkun k'araso.....owk ba damuwa gamunan zuwa yanzu".

 "kad'dai har sunzo cewar Eeshat.
"eh sunce muyi sauri,kunga ku tashi ku fara shiri tunkafin su k'ara kira,kun sansu da wutar ciki".

Cikin sauri Ruky da Eeshat suka hau shiri, wad'an nan shegun kayan nasu suka dak'ko kowacce ta fara k'ok'arin sawa,Zooly kuwa tana kwance ko gezau batayiba bare tayi yunk'urin tashi.

"sweatheart ki tashi mana ki shirya".

"sai kun dawo ni ina nan" ta fad'a ba tare data kalli inda sukeba.

Cak suka tsaya da abinda sukeyi,"me kike nufi da ke kina nan ?" Ruky ta tambaya tare da matsawa kusa da ita.
"tana nufin bazata ba mana" Eesha ta bata amsa.

Toh ai naga dai ba abinda zakiyi inkin zaunan ma,kuma wannan meeting d'in kinsan dashi tunda ba yau kika shiga cikinmu ba,please tashi ki shirya inba dai kuma da abinda kike nufi ba.


Tuna maganar da Dr ya fad'a mata jiya tayi,kamar yasan hakan zata faru,dama yace mata karta ce zata fita a cikinsu da k'arfi dan yasan zasu iya mata wani illan,tabisu a hankali amma dai ta rink'a baya baya dasu,sannan ya k'ara jad'dada mata ta rik'e azkar d'in daya bata sosai."i'm sorry da bacci nakeson nayi amma muje in'na dawo nayi.

Wata doguwar riga ta d'akko daga cikin wanda Dr ya kawo mata ta saka ta had'a da hijab d'inta iya guiwa,ba yadda su Ruky basu yi ba akan ta cire wannan kayan amma tayi kunnan uwar shegu dasu,ba yadda suka iya haka suka barta amma badan ransu yaso ba.


**********
A zaune suka sami su Kb kowa da kwalban lemu  a gabanshi suna zama Bigboy ya mik'a musu nasu tuni su Ruky suka fara sha,itako zooly tak'i sha dan tasan akwai k'waya aciki.bayan sunyi shaye-shaye da wasan banzan da suka saba, Kb ya tashi ya fara karanta agendan meeting.kusan duk akan zooly za'ai meeting d'in.
    Jibson ne ya fara magana ya dubi zooly ya ce "madam gaba d'aya fa mun daina gane kan ki, kin daina zuwa meeting regularly,gashi sai wani mugun dressing kike mana kamar ba big girl d'in da muka sani ba, haba sai kace ba zooly easy ba kamar wata matar liman? Gashi idan ana parties ba kya halarta. Gaskiya ya kamata ki gyara don wallahi mugun bada mu kike yi"
      Haka duk suka dinga kawo complains d'in su akan ta,ita dai tana zaune tana sauraron su amma bata ce komai ba har aka gama meeting d'in aka Watse.
     Bayan ta tafi ne Big boy yake cewa "ni fa ina ganin kamar wancan gayen na clinic ne yake warware mana tufka dole ne mu d'auki mataki a kanshi". Kowa ya yarda da wannan shawarar.
     Daga nan fa suka fara shirya irin tuggun da zasu had'awa Dr har sai zaman school d'in nan ya gagare shi.



*Tou Dr maheer ka tab'o UNTOUCHABLES  mu sai dai muyi fatan abun ya zo maka da sauk'i*


*Untouchables*

No comments: