ππππππππ
*RAYUWAR HOSTEL*
ππππππππ
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
P.M.L
*we dont just entertain and educate,we touch d hearts of readers*
*MAMAN KHADIJA*
*MARYAM S BELLO*
*MRS FAWWAZ*
*FARIDAT MUSA*
*JANNART LAMEED'O*
*RUFAIDA YUSUF*
*Page 27*
*By*
*Mmn khadijah*π
&
*ΚΚs ΚaΥ‘Υ‘aΚ*
Fitowa dr yayi rai a b'ace,kallo d'aya zaka masa ka gabe yana cikin b'acin rai,dan gaba d'aya fuskarshi ta sauya,muma muna gefe muna mamakin yadda cikin kankanin lokaci dr ya canxa,dana ya iya b'acin rai haka.
Cikin kakkausar murya yake magana,"Kai wannan wani irin iskancine haka?,na lurafa kuna nema ku wuce gona da iri,toh ku sani bafa tsoranku nake ji ba,kuma ba na rasa hanyar da zanbi bane wajen ganin nayi maganinku,ku da kuke 'yan iskan k'arshen zamani,kafin kuyi iskanci mutum nawa sukayi? kuma wacce riba suka samu? In baku saniba yau ku sani a iskancin ma ku burbud'i kuka samu,in har baku fasa mana wani abu nida zulaihat ba kun raina iyayenku 'yan iska kawai marasa mutunci,wallahi3,duk shege ko shegiyar da bai bani hanya na wuceba sai na taka shi,kuma inga uban da zaimin maganar.
Cikin zafin nama ya koma cikin mota tare da rufe k'ofar motar da k'arfi ya bata key ya nufosu gadan-gadan.
Da sukaga da gaske yake yi zai iya taka duk wanda be matsaba,tuni suka watse a kan titin.
Ruky da ta sanya cokalelen takalmi har tana gurd'ewa amma bata kula ba don ta tsorata da yanda taga ya fafaro motar a million.
Yan zuwa saitin su ya d'an rage gudu yace "k'anaun 'yan iska Ashe ma k'aryar rashin kunya kuke yi" ya figi motar shi yayi gaba
Yana gama parking hostel di'n ya nufa dubo Rabin ran nashi, a dai-dai lokacin kuma suka shigo school d'in ita da Halima, yayan Haliman ne ma ya kawo su tare da k'annen ta guda biyu.
Halima tana ganin shi ta zunguri Zulaihat tace "k'awata duba can kiga" ta kalli inda Halima ke mata nuni sai kuwa karaf idanunsu ya had'u,wani irin tattusan murmushi suka sakar wa junan su inda shi Dr ya ji tamkar ya je ya rungume zulaihat d'in don tsabar farin cikin Ganinta cikin k'oshin lafiya.
Sai da ta yiwa yayansu Halima sallama ta fito ya nufi wajen shi tana masa murmushi,shima d'in murmushin yake mata domin yana matuk'ar jin dad'in yanda ta d'auki shawarar shi take suturta jikinta,yanzun ma hijab d'inta k'ato ne ta sanya shi har k'asa maroon colour sai takalminta ma white da d'igon maroon a jiki tayi matuk'ar yi masa kyau, darajar ta kuma ta saja ninkuwa a zuciyar shi
Da ta k'araso yace "waton my heart kina so ki saka min hypertension ko?"
Sai da tayi farrr da idon ta sannan ta ce "haba my soul wace ni da wannan danyan aikin? "
Wannan fain da tayi masa ba karamin daukar masa da kasala yayi ba,ya kara jin wani irin singa na ratsa masa zuciya,ganin yayi shiru yana kallonta ya sa tayi snapping yatasan ta a dai-dai idon shi ta ce "soulmate ya dai? Irin wannan kallo haka?"
Dariya yayi yace "to ya Maheer ya iya da zulaihan shi? ta kashe waya kuma ta gudu a hostel ba notice duk ta tayar da hankalin Maheer d'in ta".
a yanda yayi maganar cikin shagwab'a ya sa ta sake fad'awa shauk'in son shi,kafin tace wani abu Halima ta zo wajen tace "to love birds lokacin shiga lecture yayi"
Dr ya ce "ni kam k'awa gaskiya fushi nake yi dake kin min fashin mata duk kun d'aga min hankali don haka sai kun answer query".
Dariya tayi tace "tuba nake yi Angon Zulaiha ba laifina bane ruwa ne ya tare ta shi yasa bata dawo ba"
"To kuma shine harda kashe waya?"
Sai a lokacin zulaihat tace "Ai wayar ma fa tana wajen chaji yanzu idan na fito lectures zan karb'o"
Yace "its Ok yanzu dai kuje lectures d'in zan jira ki gama don akwai important issue danake son nai discussing dake"
*****
B'angaren untouchables kuwa yau sun sha mamakin yanda Dr yayi reacting a Kansu, gashi garin haka har Ruky ta ji ciwo a k'afa sai da suka kaita asibiti aka mata d'aurin kafar.
Eeshat tace "gaskiya guys wannan gayen fa yaga wajen kwanan mu,ka duba yanda muka Dad'e muna kafa masa tarko yana tsallakewa amma yau d'aya yayi mana muguwar b'arna haka?" Ta fad'i gana kallon k'afar Ruky da ta sha bandage
Big big yace "gaskiya gayen nan ba k'aramin shu'umi bane,amma duk da haka ba zamu hak'ura ba sai mun d'aukar ma Babyn mu fansar wannan jinyar da ya saka ta".
UNTOUCHABLESππ»♀
No comments:
Post a Comment