🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘
*RAYUWAR HOSTEL*
🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘🏘
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L
Na
*MAMAN KHADIJA*
*MARYAM S BELLO*
*MRS FAWWAZ*
*FARIDAT MUSA*
*JANNAT LAMEED'O*
*RUFAIDA YUSUF*
Page 2 by
Maryam S bello (MSB)
Bayan sun fito lecture d'in *untouchables* sukan yi k'ungiya wato group su tattauna akan abubuwan da ya shafe su. Haka zasu zauna suyi ta kallon 'yan matan makarantar suna k'are ma surorin su kallo, da yake yanayin shigar 'yan matan sai a hankali, to su a wurinsu birgewa sukayi.
Zulaiha tana tafe don komawa hostel ta hango *untouchables* suna kallonta, take ta tsargu tayi ta sauri don ita tsoronsu ma takeyi.
"Easha anya yarinyar nan zata yarda kuwa?" Jibson yayi dariya yana fad'in.
"Ke a wurinki kike ganin haka, amma ni a wurina wannan ba wani abu bane, nayi convincing wad'anda suka fita ma bare ita 'yar k'auye."
Suka kwashe da dariya. Ruky tace
"Nifa na rasa meyasa kuka nace sai ta shigo cikinmu bakuga yanayinta bane? She's is too local wallahi, yarinyar da bata waye ba kunbi kun wani ishe mutane haba."
Jibson ya doka mata harara
"Kefa kina da matsala Ruky, ke gani kike kin waye da yawa sheyasa bakya ganin wayewar wani, toh bari kuji idan yarinyar nan ta shigo cikinmu sai ta fiku wayewa gaba d'ayanku."
Eesha ta mik'e a fusace
"Kai haba! K'arya ne wallahi, ku dubi yarinya daga Allah yasan k'auyen data fito zaka had'a mu da ita."
Jibson yayi dariya, kafin yayi magana ya hango sauran clicks d'in groups d'in suna k'arasowa, sai da suka iso suka tafa kamar yadda suka saba. Kabir da suke kira da KB sai Adam ana kiransa Adamsy sai Aliyu shi suke kira da Big boy.
"Yane Baaba? Tun daga can muke jin ihunku." Cewar Big boy, Jibson yace
"Akan yarinyar nan ne fa shine suke min ihu aka, daga nace idan ta waye sai ta fisu shine fa kamar zasu dake ni..."
"Ha ha! Hakan take, ni na yarda da zancenka Baaba rabu da su yanzu hanyar da zamuyi convincing nata nake tunani."
"Kai wallahi k'arya ne ace 'yar k'auye zata fimu wayewa..." cewar Ruky
"Ke da Allah ya isa! Kin cika mutane da ihu, waya tsomo bakinki a ciki?"
Tayi tsaki.
Wata yarinya tazo wucewa Big boy ya k'walo mata kira. Da sauri ta dawo.
"Gani."
"Kar6a kije ki siyo mana Fanta da cake."
"Don Allah kuyi hak'uri wallahi lectures zan shiga har ma na makara, kuma idan lecturer ya shiga kafin mutum baya bari..."
"Ke! Ina magana kina magana? Ni sa'anki ne?"
Ya daka mata tsawa
"A'a kayi hak'uri."
Yayi tsaki
"To idan kina son kanki da arzik'i kije ki siyo mana idan ba haka ba... to! Kinsan sauran."
Sanin halinsu ya sanya bata k'ara magana ba ta kar6i kud'in ta wuce da sauri.
***
Zaune suke suna cin Indomie suna fira Zainab ta shigo idanunta jawur da alama kuka taci, gaba d'aya suka mik'e, da sauri Fatima tace
"Ke lafiya zaki shigo haka?"
Zulai ta d'ora da fad'in
"Kamar fa kuka tayi, waye ya dake ki? Wani
Abin ne ya faru?"
Bata amsa ba sai ma ta rushe da wani kukan, sai yanzu ma suka lura da yadda jikinta ya 6ace da lemo, da mamaki Fatima tace
"Waya zuba miki lemo a jiki haka?"
Da k'yar ta daidaita nutsuwarta tace
"Basu Big boy bane suka aike ni siyan lemo ba, wai dan na dad'e ina zuwa fa shine sukayi min wanka, ga lectures nayi missing
Banje ba, idan akwai abinda na tsana baifi wulak'anci ko cin fuska ba.
Ina bak'in cikin a wulak'anta ni a gaba jama'a ko suwaye, sheyasa ma bana bin hanyar inda su *untouchables* suke amma yau tsotsai yasa na bi har suka wulak'antani..."
Zulai tace
"Su waye haka kuma?"
Fatima ta numfasa tace
"Kunsan wani abu?"
Sukace "a'ah."
Fatima tace
"Zainab ta fad'a tarkon *untouchables*"
"Su waye haka wai?"
Cewar Zulai a d'an rud'e.
"Kina nufin baki san su ba, ko dayake banga laifinki ba tunda ke bak'uwa ce, to bari kiji wani group ne na matasa guda hud'u, da mata biyu, hadad'un matasa masu ji da kyau da kuma gayu, ga iyayensu mahashuk'an masu kud'i ne, ke motarsu bata k'irguwa..."
Cike da 6acin rai Zulai tace
"Mts bance ki bani tarihinsu ba, ke Fatima ki kwantar da hankalinki bai isa ya ci zarafinki ba mu k'yaleshi ba..."
Fatima ta dakatar da ita da sauri.
"Ke bakisan soyayya ce tsakaninsu ba."
Zulai tace "soyayya kuma?"
Fatima tace
"Eh soyayya, abinda nake nufi a nan shine, D'aya daga cikinsu ya nuna yana son Zainab shine tayi rejecting d'insu, kuma kowa yasan mayaudara ne 'yan k'arya. Abinda sukeyi da sun lura yarinyar ta kamu da sonsu sai su lalata ta ko kuma su watsar ita su nemi wata. To shine fa tun daga ranar yake wulak'antata a gaban jama'a.
A lokacin da suka had'u da Big boy ba irin fad'an da ban mata ba, sai tace min ay rumors ne ita bata yarda ba, aikuwa ta rufe idanunta ya yaudare ta..."
"Kamar ya?"
Cewar Zulai.
Fatima tayi murmushi
"Tun da yaga ta kamu da sonsa yake mata yawo da hankali...
Ke idan kina cikin makarantar nan dole ne ma fa ki sansu don sunyi k'auran suna, babu wanda bai sansu ba, ke duk kyan yarinya dan jan ajinta idan batayi soyayya dasu ba wai bata cika mace ba..."
Cikin kuka Zainab tace
"Nidai ina sonsa da gaske, don Allah ku taimake ni ku jawo man kan Big boy."
Cikin tsawa Fatima tace
"Ke wuce can marar zuciya wa kika aje da zai shawo miki kansa? Daman idan zaki nutsi ki kama mutuncinki to tun wuri ki kama kanki, idan kink'i to ba ruwana da ke, wannan ma ay rashin kamun kai ne kina mace ki tsaya wani banza yana 6ata miki lokaci.
Ina mamaki da ake cewa wai maza tsada sukeyi, ba komai ke ja mana ba sai mu mata da muke zubar da darajar da Allah yayi mana, instead mu kama kanmu sai mu rik'a bin maza haba, saboda me?"
Zulai da ke tsaye tana jin Fatima na masifa tace
"Lallai sai dai muce Allah ya tsare mu yasa mufi k'arfin zuciyarmu."
Fatima tace
"Amin, kema sai kinyi a hankali don muddin kika yadda kika fad'a tarkonsu sai yadda Allah yayi da ke, ki kama mutuncinki wallahi..."
*Pure moment*
No comments:
Post a Comment