Wednesday, 5 April 2017

KHALEEL Page 73&74

🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀
   ♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀

           🎀🎀🎀🎀🎀🎀


🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️
   ♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥

        PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
                  (P.M.L)

               🎀🎀🎀🎀🎀
                  *KHALEEL*
               🎀🎀🎀🎀🎀


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com



              PAGE


✍🏻✍🏻73&74✍🏻✍🏻

Bayan Sati Ukku!

Bayan sati ukku Su Hanifah suka soma komawa makaranta.
A yau ne Humaira ta tashi tana ta baza sauri wanda duk abinda takeyi akan idon Rufaida, shirinta ta gama tsab tare da d'auko wayarta ta latsa wasu numbers, can tace
"Hello? Kina ina?."
Humaira tace
"Yauwa mu had'u wurin round yanzu don gani nan zan bar hostel. Yauwa sai nazo."
Ta juyo tana kallon Rufaida wanda take ma tunanin tana bacci, Rufaida kuwa da sauri ta maida idonta ta rufe don kar ta gane. Ganin haka yasa Humaira tayi murmushi ta fice daga hostel d'in,  hakan ya sanya Rufaida tayi wuf! Ta mik'e gami da dauk'o hijabinta da nik'af tabi bayanta.
Da dubara ta samu tayi ta bin Humaira har suka fito wajen gate daga wani lungu take hango komai inda take tsaye. Ganin sun tsaida adaidaita ya sanya ta tsaida wata da sauri ta cigaba da bin bayansu har taga sunyi tafiya mai nisa.
Daga wajen gari taga suka tsaya tare da fitowa, sai da ta bari sunyi  nisa tukunna ta fito itama sanye da nik'af tabi bayansu, wata y'ar bukka ta tsaya inda ta samu bayan ginin ta la6e tana hangen komai kuma tanaji. Ga mamakinta wani mutumi taga ya fito da carbi a hannunsa inda suka baje nan k'asa. Malamin ne ya soma tambayarsu.
"Meke tafe daku?."
Wadda suka je tare ce ta fara magana
"Allah gafarta Malam, kamar dai yadda na maka bayani a waya jiya shine ya kawo mu, yau d'in."
Ya gyara zamansa yana kallon k'awarta wadda taji Malamin na kira da Sadiya, yace.
"Naji dai, amma dai Sadiya kin mata bayanin yadda nake aikina?."
Tace
"Tabbas na mata bayani Malam, kuma ta yarda."
Yace
"Madallah, yanzu ke a naki jawabin kince wani saurayi kike so ki mallaka sai yadda kikayi dashi? Sannan yanada mata hakane?."
Humaira ta girgiza kanta alamun eh tace
"Haka ne Malam, a taimaka min Malam, ni buk'atata dukiyarsa nakeso da nace ya bani zai bani ko nawa ne."
Malamin yace
"Ba damuwa, taso ki shigo daga ciki."
Ba musu ta tashi ta shiga, nan taba Sadiya ajiyar jakarata.
Duk Rufaida na tsaye ta cika da mamaki marar misaltuwa!
Can sai gasu sun fito Malamin ya mik'a mata wasu magunguna Rufaida ta kasa kunne tana jin bayanin sosai, sannan tayi sand'a ta fita da gudu.


Da daddare suna bacci Rufaida ta tashi ta chanza magungunan da aka ba Humaira, wasu ma cikin k'aramar jarka suke masu kama da rubutu, tayi dabaru ta zubar ta chanza wasu, haka ta kwanta zuciyarta fal farin ciki, kuma haka ta k'udiri aniyar wargaza duk wani shiri da zatayi don samauwar farin cikin rayuwar auren Hanifah.


******

Karatu ya fara kankama na second semester, karatu suke ba kama hannun yaro.
Rayuwar Hanifah sai wanda ya gani, don Khaleel yanzu ba abinda yake bata sai kulawa, soyayya da kuma farin ciki, ko aikin gidan baya bari tana yi, tattalinta yake kamar k'wai, ga cikinta yanzu ya turo ya fito ana ganinshi.
Kullum Hanifah cikin gode ma Rufaida takeyi akan hallacin da tayi mata, don ta taimake ta ba kad'an ba, yanzu gashi suna gudanar da rayuwarsu cikin farin ciki da walwala tare da kulawa da junansu.

Ranar wata Juma'a Saif ya kira Khaleel bayan sun gaisa ne Saif yace.
"Ya Khaleel gamu nan zamu kama hanya zamu zo Kaduna."
Cike da farin ciki Khaleel yace
"Seriously? Can't wait sai kun iso."
Bayan sunyi sallama ya sanar da Hanifah aikuwa tayi ta jin dad'i.

Washe gari asabar sanin Khaleel ya hana ta ko wane aiki ya sa Hanifah bashi surprise, a hankali tayi kitchen ta had'a masa had'dad'en breakfast mai rai da lafiya tabi da kunun gyad'a a sama sai k'amshi ke tashi. Toilet ta wuce ta tsantsara wanka ta sanya wasu kaya masu bayyanar da surar jiki da wani fitanannen turare mai dad'i. Kitchen ta koma ta jera komai kan tray ta nufi d'akinsa. Yana kwance yana bacci peacefully a hankali ta d'ora tray d'in saman side drawer sannan taje gefensa ta zauna tana kallonsa cike da sha'awa da k'auna marar misaltuwa!
Gefen fuskarsa take shafawa a hankali tana kallon yadda yake motsi sai ya k'ara mata kyau da kwarjini. Jin ana masa yawo a fuska yasa ya bud'e idanunsa tar akan Hanifansa!
Wani kallo yabi ta dashi yana smiling, light kiss ta masa a kumatu sannan taje daidai kunnensa ta rad'a masa, gaba d'aya ta kashe masa jiki da k'amshin turarenta. Dama Hanifah tasan a rina don duk cikin turarukanta ya fison wannan sheyasa ma ta feso shi.
"Good morning handsome! I made you breakfast in bed."
Ya kalleta sai kuma ya had'e rai yace.
"But why my princess? Bana hana ki ba?."
Hannu tasa a bakinsa tace.
"Shhh! I'm sorry my only, don't reject my offer, i just want to show you how much i love you, that's all, pleasee."
Ta k'arasa cike da shagwa6a wanda tasan idan har tanayi to fa tana kashe ma Khaleel jiki, gaba d'aya ya narke da shagwa6ar Hanifah.
A hankali ta mik'ar dashi tace.
"Muje kayi brush."
Ba musu ya mik'e har toilet ta sa masa Maclean ta mik'a masa yana yi tana basa  ruwa, har ya gama suka fito daga toilet d'in.  Kamo ta yayi ta fad'o jikinsa ya shiga aika mata da best kiss of her life, take itama ta shiga maida masa, sun d'auki tsawon lokaci kafin ya sake ta ya kamo ta yana jan karan hancinta, cike da zolaya yace.
"Tunda kika dafa abincin nan to fa tare zamu cinye shi."
Dariya tayi wanda ke k'ara mata kyau tace.
"Allah ko? To mugani dan ni bana jin yunwa."
Yana dariya yace.
"Ay baki isa ba, don d'ure zan miki."
Ta k'yal'kyale da dariya tace.
"D'ure ya Khaleel? Sai kace dai yarinya?"
Yace.
"Duka duka yaushe ma kika girman? Da wake baki abinci?"
Ta turo baki tace.
"Oho."
Yace
"Kingani ko? Kema kinsan gaskiya don haka yi miki d'ure bazai min wahala ba."
Ita dai sai dariya takeyi.
A haka suka k'arasa kan gado Khaleel na zolayarta tana dariya, suka karya cike da farin ciki a zukatansu.

Da yamma suka shirya sukaje gida, a nan suka tarar da su Saif. Nan da nan gidan ya rikice da fira, itama Salma cikinta har ya fara fitowa.
Da daddare suna zaune suna cin abinci Khaleel ya kalli Ammi yace.
"Gaskiya Ammi kiyi wa Hanifah magana wai ita dole sai ta dawo gida wankan jego."
Kowa ya bud'e baki cike da mamaki, Saif yace.
"Kai Ya Khaleel! Ko kunya bakaji kana maganar nan a gaba Ammi."
Khaleel yace
"Kunya? Mamata ce fa wace kunya?."
Ammi tace.
"Wai kai ina ruwanka ne Saifullahi? Meye naka a ciki?."
Saif ya ta6e baki.
"Dama nasan hakan zata faru, Ammi akwai kushe mutum akan Khaleel."
Khaleel yayi dariya.
"Kana kishi ne? Ammi tafi sona."
Saif yace.
"Naji d'in."
Hanifah da Salma na gefe suna dariya, Hanifah cikin dariya tace.
"Nifa da gaske nake gida zan dawo haihuwa."
Ammi tace
"Gidanku, kya bari dai mijinki ya baki izini ay ko?."
Hanifah ta turo baki cike da shagwa6a tace
"Ni gaskiya a'a Ammi."
Khaleel na kallonta yana dariya yace
"Dama wayace bazaki haihu nan ba? Amma dai ay duk d'aya ne da nan da can d'in ko?"
Hanifah tace
"Naji nidai dan Allah nan."
Ammi ta mik'e tana hamma
"Kunga tafiyata sai da safe."
Khaleel yace
"To muma ku tashi mu tafi gida."
Hanifah tace.
"To ay bamu gama magana ba."
Khaleel yace
"Idan mukaje gida ma k'arasa."
A haka sukayi bankwana suka tafi. A mota ne Hanifah tace
"Ina jinka my only."
Yayi dariya ya kwaikwaiye ta.
"Ina jinki my princess."
Ta soma bubbuga kafad'a tana kukan shagwa6a. Yana ta mata dariya yace
"Kar ki damu my princess zaki dawo gida kinji? Don't worry."
Cike da jin dad'i tace
"Da gske my only?"
Yace
"Sosai ma! Anything for my princess." Bisa fad'ad'an Kafad'unsa ta kwantar da kanta had'e da lumshe idanu, a hankali tace.
"Thank you my only. I love you so much."
Da hannu d'aya ya shafi gefen fuskanta yana murmushi yace.
"Love you more."
A haka suka isa gida tana kwance bisa kafad'arsa.



MSB✍🏼

No comments: