🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀
♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀
🎀🎀🎀🎀🎀🎀
🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️
♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
(P.M.L)
🎀🎀🎀🎀🎀
*KHALEEL*
🎀🎀🎀🎀🎀
Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻
http://MaryamSBello.blogspot.com
PAGE
✍🏻✍🏻79&80✍🏻✍🏻
Ammi dake waje tana jiyo kukan jariri sai ta fara murna tana hamdalla, wai yau Hanifanta har ta girma haka? Ikon Allah kenan.
Khaleel kuwa manne ma Hanifah yayi yana tsokananta akan bashin kiss d'insa.
Minti biyu tsakani nurse d'in tazo da babyn nannad'e cikin showel dark blue. Mik'o shi tayi da sauri Khaleel ya amshe shi yana masa kallo cike da sha'awa! Tare suke kallon babyn dukkansu sun kasa d'auke ido daga garesa.
"Masha Allah!" Shine kad'ai abinda Khaleel ke iya fad'i. Hanifah ta kalli babyn sanye cikin overall mai layi layi dark blue da light blue wanda yayi matuk'ar kyau cikinsu, y'ar hular da aka sa masa ma kalar kayan sai motsi yake yi da hannuwansa yana motsa baki. Khaleel ya kalli Hanifah yace.
"Bari na kai ma Ammi shi ta gani tana nan waje kinga kafin na dawo an gyara miki jikinki ko?"
Ta gyad'a kai tana kallon mijinta cike so da k'auna marar misali, shima haka sannan yace cikin kalmar rad'a rad'a.
"I love you."
Tayi murmushi tace.
"Love you more."
Daga haka ya fice inda nurse d'in ta soma gyara Hanifah.
Khaleel na fita Ammi ta taso da sauri ta kar6e first jikanta daga y'ay'anta guda biyu abar k'auanarta. Kallonshi takeyi take k'walla ta cika mata ido kafin kuma ta shiga tofe shi da addu'o'i. Bayan ta kammala ta kalli Khaleel tana murmushin jin dad'i tace
"Allah ya raya mana shi! Allah ya albarka ce shi ya sa masa albarka! Allah ubangiji yasa mahaddacin alk'ur'ani ne."
Khaleel nata amsawa da "Amin." Har Ammi ta mik'o masa shi tace
"Wane suna zaka sa masa?"
Yayi murmushi yace.
"Sunan Baba za'a sa masa Abdul'aziz sai ana kiransa da Adnan."
Ammi ta ware baki cike da mamaki tace.
"Allahu akhbar Allah ya raya Abdul'aziz kasa musulmin k'warai ne, Allah ya jik'an kakkaninsa." Sai kuma tace
"Ashe ma mai gida ne? To Allah yasa dai ba raggon namiji bane don dole a kawo min kud'in cefane kullum."
Khaleel na dariya yace.
"Ay Adnan ba raggo bane Ammi don zakisha mamaki idan ya zama soja nan gaba."
Tace
"Soja? To Allah yasa haka..."
Bata rufe baki ba Adnan ya fara mitsilniya, can kuma sai yasa kuka kamar an aiko sa. Ammi tace
"Ahaf! Ay daman nasani wannan raggon namiji ne, kawo shi nan."
Khaleel ya mik'a mata yana ta dariya, tana rirriga sa tace
"Kai arr! Ashe raggo ne ma? Khaleel kar6i kayanka akai ma Mamansa yasha."
Ya kar6e sa yayi masa hud'uba sannan ya wuce d'akin da Hanifah ke ciki.
Yana shiga ya tarar har an gama kimtsa Hanifah har ta chanza kaya ma. Yana zuwa ya mik'a mata shi sannan ya zaro wayarshi daga aljihu ya shiga d'aukansu hoto Adnan da Hanifah, sunyi kyau so cute! Take ya fara sending pictures d'in Adnan a family group d'insu, bada jimawa ba aka fara turo reply.
Nurse ce ta shigo tace.
"Za'a kaita d'akin hutu k'ila zuwa safe a sallame ta ko can daddare."
Yace
"Ok."
Ya kalli Hanifah yana son zolayarta yace
"Kalle ki da Allah kin wani rik'e sa sai kace da ke yake kama."
Tace
"Dama wayace yana kama dani? Da dai mace ce."
Yace
"Ay dole kice haka, don kingansa kyakkyawa yana kama da babansa kina kishi ne hala?"
Tace
"Wane kyau? Ji hancinsa fa a baje."
Ya k'yalk'yale da dariya yace
"Lallai yarinyar nan bakisan kyau ba, kowa yagansa yasan yakai inda namiji ya kai."
Tayi tsaki cikin wasa tace
"Oho dai, ya sunansa? Usman ko?"
Yace
"Usman kuma? Abdul'aziz dai, sai ana kiransa da Adnan."
Take ta d'an 6ata rai tace
"Amma fa ce maka nayi a saka Usman idan namiji ne ko?"
Yace
"Kiyi hak'uri duk d'aya ne idan kika k'ara haifan wani sai asa masa Usman d'in. Yanzu ki barsa a mijin Ammita."
Tayi murmushi
"Allah ya raya mana ya jik'an su Baba."
Yace
"Amin ya Rabbi, zo muje a kaiki ki huta ko?"
Tana murmushi tace
"To."
Ba'a sallami su Hanifah ba sai washe gari k'arfe takwas na safe.
Suna zuwa gida daman Halisa ta sanya ruwan zafin wanka ta d'ora ruwan kunu, suna zuwa ruwa yayi kawai sai aka zuba Halisa tayi wa mai jego wanka ta gashe mata jikinta tas, sannan Ammi tayi wa jariri wanka ta sum6ule shi da mai da hoda sannan ta sa masa overall plane light blue sai zanen teddy na bacci, ta nannad'e sa cikin shawul mai taushi sosai.
Khaleel yasa aka gasa mata rago aka kawo mata tana ci.
Kafin k'arfe d'aya na rana Saif sun iso, gidan ya kacame da murna Saif kamar ya cinye babyn dan so.
A hankali gida ya fara cika da y'an ganin baby, Rufaida ma tazo ganin baby kuma tayi murna. Y'an uwa ma sun fara hallara ganin baby, duk wanda yaga babyn sai yace Khaleel ne sak.
Kullum Khaleel na manne da Hanifah sai Ammi tayi da gaske yake fita saboda mutane na shigowa.
Da yafita can bayan minti kad'an zai fara lek'e sai da Ammi ta fito tayi mai tatas sannan ya bar zuwa. Haka aka sha zaman barka.
Ranar suna ba'ayi wata bid'a ba, an dai ci ansha. Amarya tayi kyau tayi fari da fresh sosai. An sha hotuna dai kamar ba gobe. Ana gama suna Khaleel ya cigaba da mak'ale ma Hanifah Ammi har ta fara gajiya tace suzo su koma gidansu. Khaleel murna ita kuma Hanifah tace bata komawa sai tayi 40, Ammi na jinsu suna gardama sai dai tayi dariya kurum.
Saboda yadda Hanifah ke samun kula sai gashi kafin suyi arba'in ta girgije itada babyn, duk wannan kumburin haihuwar ya tafi ta zama y'ar cas da ita. Adnan wani irin girma yakeyi sosai idan ka ganshi sai kayi zaton d'an wata biyu ne ya wani zama k'aton gaske, gashi kullum sai dad'a kyau yakeyi ya zama Khaleel sak.
Suna yin arba'in Hanifah ta tarkata ta koma gidanta saboda Khaleel ya matsa.
Tana komawa kuma suka soma lectures yanzu ta shiga level 2, gashi kuma sun bud'e sabon babi na soyayya ita da Khaleel d'inta.
Bayan wata Biyu.
Bayan wata biyu kuma Salma ta haifi kyakkyawar d'iyarta mai kama da Saif. Daga nan kuma aka fara gudanar da shagalin suna. Yarinya taci sunan Ammi ana kiranta da Amal.
MSB✍🏼
No comments:
Post a Comment