Wednesday, 5 April 2017

KHALEEL Page 75&76

🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀
   ♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀

           🎀🎀🎀🎀🎀🎀


🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️
   ♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥️🌀♥

        PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
                  (P.M.L)

               🎀🎀🎀🎀🎀
                  *KHALEEL*
               🎀🎀🎀🎀🎀


Written by Maryam S bello {MSB}✍🏻


http://MaryamSBello.blogspot.com



              PAGE


✍🏻✍🏻75&76✍🏻✍🏻


Life moved on, Hanifah da Khaleel na zaune suna kallon indian series a ZeeWorld a yayinda Hanifah ta kwanta bisa k'irjinsa, Khaleel kuma na shafa mata gashinta. Juyo da fuskarta tayi tana kallonsa tana jin wani nishad'i a yayinda Khaleel yayi kamar bai ganta ba, don kuwa yadda take kallonsa idan yace su had'a ido baisan a wani hali zuciyarsa zata shiga ba, hannunshi ta kamo tana shafawa a hankali kafin ya kalleta finally yana d'aga mata gira sama yace.
"Yane? Ko inzo ne?."
Tayi dariya tace.
"Wai kai my only banida damar kallonka sai ka wani ce kazo?."
Dariya ta su6uce masa ba shiri yace.
"Ay indai kinga mata na ma mijinta irin wannan kallon to da magana a k'asa, nidai i won't reject you don kinsan bana gajiya dake my princess."
Tayi dariya cike da farin cikin jin kalamun shi tace.
"Nima bana gajiya da kai my only, i love you."
Yace.
"I love you more."
Hanifah ta ga yana k'ok'arin mik'ewa ta had'e rai ta kalle shi.
"Ina zakaje yanzu?."
Yayi dariya.
"Wurin budurwata mana, bana ce miki kishiya zan miki ba?."
Tayi dariya.
"Aiko bana tsoron ko wacece ta shigo ta gani idan ban kakkarya ta ba."
Yayi dariya harda duk'ewa yace.
"Hoo Hanifah! Wannan cika bakin naki fa? Yanzu da kinga da gaske nake na tabbata sai inda k'arfinki ya k'are sannan ki samu nutsuwa."
Ta harare shi da wasa tace.
"Dah kenan, banda yanzu."
Yace
"Haka kika ce?"
Tace
"Sosai ma."
Yana dariya yace
"Shikenan kar kiga laifina idan kikaga ana gyaran d'aki to ba ruwana!"
Ta tafa hannu tana dariya
"Ni zan ma taya ka gyaran d'akin."
Cikin ransa yace bari ya gwada ta ya gani. Sai ya d'auko wayarsa daga aljihu ya soma kiran k'arya. Da sauri ya bar palon ya shiga amsa waya kamar da gaske.
"Hello baby? Ya kike? Wallahi lafiya, kinsan nayi missing d'inki da yawa, yanzu ma zan shigo gidan naku ki aje min irin kazar nan da kika gasa min rannan."
Ya k'yalk'yale da dariya yana kashe murya kamar gaske yace
"Haba! Ashe kina sona kema? Insha Allah yanzu zaki ganni..."
Fizge wayar tayi da k'arfi tana huci, kallonta yakeyi yana murmushi, a yayinda ta kara wayar kunnenta da niyyar zagi, jin shiru ya sa ta duba wayar da sauri ganinta a kashe yasa ta kalli Khaleel tace.
"Au dama zolayata kake?"
Yace
"Gwada ki nayi gashi nan tun bance zanyi auren ba kin soma nuna kishinki."
Bata san lokacin da ta d'auko pilon kujera ta soma jefa masa ba, yana dariya yana kaucewa yana mata gwalo, daga k'arshe ya fice daga palon yana dariya, d'aga murya tayi tace.
"Wallahi ka kyauta my only."
Bisa kujera ta zube tana maida numfashi sannan tana dariya lokaci d'aya.


*****

Haka dai rayuwar ke gudana cikin hukuncin ubangiji wanda yanzu su Hanifah semester ta mik'a sosai, sannan kuma cikinta ya dad'a tsufa ya fito ras dashi, hakan kuma fatar jikinta kamar tayi dilka tayi haske ta kuma yin k'iba kad'an hakan ya sa tayi kyau abinta. Kwata kwata ta fita daga harkan Humaira ko magana batayi mata koda kuwa sun had'u ko kallo bata ishe ta ba. Da Rufaida suke d'an ta6a k'awance shima daga school ne kuma su rabu a nan, don ma dai suna shiri da Rufaidar amma Hanifah ta rufe k'awance don ta tsorata.

Yau lecture d'in yamma sukayi suna fitowa ta hango motar Khaleel don kuwa yanzu ya hana ta driving, da sauri ta k'arasa tana murmushi, yana hango ta ta madubin gaban motar ya saki murmushin shima, har ta k'araso yana kallonta itama shi d'in take kallo, tana shiga ya ja motar suna tafe suna fira gwanin sha'awa, kafin su isa gida sai da ya tsaya yayi mata shopping ya kuma siya mata kayan lashe lashe da yasan zataji dad'in cinsu.


*****

Tana shiga hostel d'in ta yar da jakarta kan katifa sannan ta fad'a bisa tana maida numfashi, Rufaida da itama yanzu ta shigo d'akin tana sauya kayan jikinta ta tsaya tana kallonta, can kuma taja tsaki ta cigaba da abinda takeyi.
Tana gama chanza kayan ta ga Humaira ta tashi tayi toilet da gudu sai dai Rufaida ta jiyo kakarin amai, da sauri ta k'arasa ciki tana tambayar abinda ya same ta.
Tana cikin aman sauran room mates d'insu suka soma shigowa su kusan hud'u, jin amai yasa suka shiga suna tambayar abinda ya same Humaira, Rufaida ce tabasu amsa.
"Wa ma yasani? Nima yanzu naga tana ta aman."
D'aya daga ciki tace.
"To! Allah ya sauwak'e."
Haka ta gama aman ta dawo d'akin ta zauna rigib kan katifa, gaba d'aya zuciyarta tashi takeyi ta rasa dalili.
Haka dai ta wuni tana aman a wahalce dole su Rufaida suka taimaka mata suka kaita asibiti, an gudanar da gwaji inda aka tabbatar mata da tana d'auke da d'an jaririn ciki na wata kusan d'aya. Ana fad'a mata ta zube k'asa sai ta dinga rusa ihu, sai sambatu takeyi tana kiran ta tuba wai son zuciya ya ja mata. Haka kuma aka dawo da ita still tana surutan sai cewa take ta shiga uku tana kuka wiwi, y'an d'akin nasu sun taya ta jimami sosai sannan kuma sun mata fad'a da tambayoyi barkatai akan ta fad'a musu yadda akayi ta kwaso ciki tana budurwa, wannan abin kunya ina zasu kaishi? Ita dai Humaira ba bakin magana gaba d'aya jikinta yayi sanyi, banda tunanin iyayenta da yayanta ba abinda takeyi, yanzu da wane ido zata kallesu? Tunani barkatai takeyi a yayinda take kuka sosai tana dana sani. Cikin kuka tace
"Na shiga uku ni Humaira! Yanzu ya zanyi? Na cuci kaina na cuci rayuwata, Sadiya kin cuce ni yanzu ina zan sa kaina?"
Tana magana tana d'ora hannunta saman kai, duk tafi jin Mamanta tasan ma kashe ta kawai zatayi. Duk yadda su Rufaida suka so rarrashinta abin yaci tura, ta kalli Rufaida da jajjayen idanunta tace
"Nasan kinsan abinda muka aikata, wallahi sharrin shaid'an ne ki taimake ni ki fad'a min yadda zanyi don Allah?."
Rufaida tace.
"Tabbas sheyasa akace kabi duniya a sannu sannan duk yadda kika d'auke ta haka zata zo miki, idan kika d'auke da sauk'i to fa haka zata zo miki, sannan akasin haka ma, wallahi ki nutsu kindai ga sakamakon ki tun a duniya kafin ki riske na lahira. Duk abinda kika aikata na sani kawai kallonki nake, wai Humaira har kibada kanki ga wani k'ato wanda ba muharraminki ba yayi amfani dake saboda wata buk'ata taki can ta banza? Sannan shawarata ta k'arshe a gareki shine kar kiyi gigin zubar da cikinnan koda wasa."
Humaira ta kalle ta da mamaki tace.
"Kina nufin na haifi d'an shege ina zan kai kunyar duniya?."
Rufaida tayi murmushin takaici tace.
"Kina so ki aikata laifi akan laifi kenan? Ga laifin zina gana kisan kai? Sanda kika bada kanki ga wani can bakiji kunya ba sai da kika d'auko cikin zakiji kunya? Lallai ma!"
D'ayar mai suna Hafsat tace.
"Gaya mata dai y'ar uwa, idan kunne yaji to jiki ya tsira."
Haka dai Humaira take binsu da kallo d'aya bayan d'aya tana hawaye, shikenan ita yanzu d'an shege zata haifa? Ta d'ora hannu a kai tare da fashewa da wani irin kuka.
"Wayyo ni Allah na, yazanyi da mahaifiyata? Me zance mata? Na cuci kaina gaskiya."
Hafsat tace
"Hak'uri zakiyi ki kar6i duk hukuncin daza tayi miki, saboda kin cancanta."  Humaira cikin mik'a wuya ta mik'e tsaye tana hawaye tace.
"Tabbas ya zama tilas na sanar da ita, sannan a shirye nake na kar6i ko wane hukuncin da zatayi min, fatana kar ta yafe ni, Allah yasa ta yafe min."
Rufaida tace
"Insha Allah komai zaizo da sauk'i, kidai yi addu'a sannan ki dage da isgifari don neman gafarar ubangiji."
Humaira tace
"Na tuba Allah! Allah na tuba ka yafe min..."



MSB✍🏼

No comments: