✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_
P.M.L
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
_wannan sune safikan mu da zakuna ziyarta dan neman nvl d'in mu. Fatan mu Allah ya baku ikon zuwa Ameen_
🌹47 🌹🔚
A ranar sukaje wajen Dada, ya dad'e yana sa masa albarka tare da fatan dacewa, sannan ya ce lallai lallai sai ya bashi takardar Jidda don data warke ya mik'a mata, yasan dole zata koyi hankali. Haka Faruk ya rubuta ya mik'a ma Dada, haka ma Mama tayi masa fatan dacewa da sanya albarka. Daga nan suka wuce gidansu Meenah ya shaida ma Baba, Baba ya bishi da doguwar addu'a ya sanya masa albarka.
Sai dai tun ana gobe zai tafi hankalinsa ya tashi bai ta6a tunanin daidai da kwana d'aya zaiyi nesa da Meenah ba gashi har za'a shafe watanni bai ganta ba, yana shigowa d'aki a lokacin tana kwance kan gado ya zauna gefenta yace
"A gaskiya Meenah bazan iya tafiya na barki ba, kawai kiyi hak'uri ki shirya mu tafi tare." Ta juyo tana dubansa tace
"Nidai jeka ka barni, ina nan gida Nigeria bazan iya binka ba a yadda nake jina d'innan."
Ya tur6une fuska ya shiga zayyano mata matsalar da zai shiga idan bata bishi ba, har da cewa tayi differing semester d'in mana idan suka dawo sai ta gyara. Da k'yar ta lalla6a sa yayi hak'uri ya barta, amma idanunshi sun kad'a sunyi ja, haka itama ta wuni tana kuka har bacci yayi awon gaba da ita. A daren ranar Meenah taga tarairaiya kamar wata k'wai, ya dad'e yana shayar da ita zuma kafin kuma suyi bacci mai dad'i.
Washe gari ya fara shirin tafiya, kafin ya tafi sai da ya nemo mata wata mata dattijuwa da zata zauna da ita har ya dawo, haka suna ji suna gani sukayi bankwana har airport ta kaishi, sai data ga tashin jirginsu sannan ta dawo zuciyarta na k'una ta rasa meke mata dad'i.
Haka ta kwana tunaninsa har ciwon kai ya sauko mata wanda kafin safe zazza6i mai zafi ya rufe ta, sai da tayi ta shan magaunguna sannan ta samu taji sauk'i.
Shi kuwa gogan naka yana sauka masaukinsa dama ya siya sabon sim, yana sawa ya kirata, bugu biyu ta d'auka.
"Hello."
"Baby ya nake jin muryarki can k'asa ko jikin ne?"
Ta lumshe idanu tace
"Eh to zazza6i ne yake d'an damuna amma da sauk'i."
Ya rude ya shiga mata tambayoyi.
"Kinsha magani? Yanzu meke miki ciwo? Ya kike ji yanzu?"
Tayi murmushi
"Wallahi yanzu kam bana jin komai sai kasala, so ya hanya? Ya kuma gajiya?"
Yace
"Alhamdulillah, gani nan na sauka masaukina yanzu zanyi wanka sai na kwanta na huta."
Tace
"Ai gara kayi bacci kam, sannu."
Yace
"Yauwa baby, kema sannu."
Sun dad'e suna fira kafin suyi sallama, kowane yana jin kewar d'an uwansa.
Meenah ta cigaba da karatunta cikin kwanciyar hankali, kullum cikin missing Faruk takeyi sai dai kullum suna mak'ale a waya suna fira basa gajiya da junansu.
Sun cigaba da zumuncinsu itada Zarah kusan kullum suna ziyartar juna, haka ma Anisah wacce ke fama da tsohon ciki itama tana k'ok'ari wajen ganin tana zumunci dasu Meenah.
****
BAYAN WATA BAKWAI
Meenah na zaune a parlor tana cin guava kamar a mafarki taji horn, ta yunk'ura da k'yar ta lek'a ta window ganin motar haya ya sanya ta fara mamakin ko waye?
Bata gama mamaki ba sai data ga ana fiffido da akwatina daga boot, gabanta ya fad'i batayi tsammanin ganinsa yanzu ba, yayi wani kyau yayi k'iba sai k'yallin hutu yakeyi. Ga k'asumbar nan tasha gyara sai walk'iya takeyi.
Ta lalla6a ta fito bakin k'ofa daidai nan ya k'araso yana murmushi, take ya ware hannuwansa duka biyun alamun ta iso gareshi. Ta dafe cikinta daya turo gaba tare da sunkuyar da kanta k'asa, yayi murmushi tare da takowa daf da ita sannan ya rungume abarsa tsam tsam kamar za'a k'wace masa ita don ma tulelen cikinta ya hana shi ya rik'e ta sosai.
Ya sumbace ta a goshi yana dubanta yace
"Wow! Baby cikinnan fa yayi miki kyau sosai."
Ya k'arasa yana kashe mata ido d'aya, tayi murmushi, ta zum6uro baki cikin shagwa6a tace
"Shine zaka taho ban sani ba?"
Yayi dariya
"I'm sorry baby, just wanted to surprise you daman."
Hannunta ya rik'o suka k'arasa ciki, ta taimaka masa ya rage kayan jikinsa yana ta zolayarta wai yanzu ta zama k'atuwa ko tafiya da k'yar takeyi, ita dai sai dariya takeyi. Bayan ya huta kuma ya shiga bubbud'e akwatina yana fiddo mata tsarabarta, kaya ne mak'il akwati guda na kayan baby wanda babu abinda babu a ciki, kaya masu kyau da tsada, sai akwati guda nata wanda ya k'unshi leshi, atamfa da su kayan bacci da kayan kwalliya da sauransu, tayi murna tayi ta masa godiya ba adadi.
A ranar dukkansu sunyi kwanan farin ciki da kuma kewar juna.
Washe gari sai ga Jidda itama ta warke ras, tazo neman gafara kuma duk sun yafe mata, tace ta samu mijin aure, sun taya ta murna da fatan alkhairi inda har Faruk yayi mata alk'awarin bata tasa gudumuwar.
A kwana a tashi ba wuya wurin Allah yau Allah ya sauki Meenah da misalin k'arfe biyu na dare, Faruk yana tare da ita har ta haifi santalelen d'anta k'ato mai k'oshin lafiya, bayan an gyare shi tas aka mik'a ma Faruk shi sai kallonsa yakeyi cike da sha'awa, ya sumbati kumatun Meenah yace
"Wane suna zamu sa masa?"
Tayi murmushi tace
"Duk sunan da kaga ya dace dashi ka sa masa."
Yayi masa hud'uba da sunan mahaifinsa wato Adam amma za'a ringa kiransa da Khalifa.
Ranar suna anyi taron suna lafiya kuma ya k'ayatar mai jego tayi fes da ita tana sanye cikin wani golden lace sai k'yalli takeyi kamar wata amarya.
Mai jego da d'anta sun cigaba da samu kulawa sosai a wurin Faruk, ga yalwatar arzik'i musamman da akayi masa k'arin girma kud'i sun zauna masa sosai, hakan yasa Meenah ta bashi shawarar ya gina masallaci ya kuma ringa bada tallafi a gidan marayu, ba k'aramin dad'i shawarar nan tayi masa ba, yayi tasa mata albarka yana jin dad'i.
A haka har sukayi arba'in inda ta cigaba da karatunta a lokacin ne kuma ita Zarah ta haifi d'iyarta mace sun sha suna babyn taci sunan mahaifiyar Nabeel wato Sadiya, za'a ringa ce mata Nasreen.
A yanzu su Meenah har sun kammala karatunsu suna jiran result.
****
Zaune take tana shayar da Khalifah Faruk ya fito daga d'aki da alama bacci ya tashi, yana zuwa ya rank'wafo yana sumbatar kanta, yace
"Zo muje na baki wani abu."
Ta mak'ale kafad'a alamun a'a tace
"Nak'i wayon, nasan dalilin da yasa ka kirani."
Yayi murmushi yace
"A'a fa result d'inki zan nuna miki."
Da sauri ta aje Khalifah ta mik'e tsaye tana murmushi tace
"Da gaske? Mu je nagani."
Ya wuce tabi bayansa suna shiga yasa ma k'ofar key yana dariya k'asa k'asa, tace
"La daman wayau zakayi min ko? Ni gaskiya ka bud'e min na fita."
Yace
"Nak'i, ga key d'in zoki k'wata."
Ta nufo sa ta fara k'ok'arin k'wace key d'in aikuwa ya damk'e ta yace
"Wana kama?"
Ta fara kukan shagwa6a tana fad'in.
"Wayyo my soul, mun bar Khalifah shi kada'ai a parlor fa kar yayi kuka."
Yace
"To tsaya mu nema masa k'anwa sai ki tafi."
Tace
"Nidai a'a."
Yace
"Aiko baki isa ba."
Ya fara k'ok'arin zage mata zip da k'yar tayi nasarar k'wace kanta tana ta faman dariya sosai sannan ta d'auki pillow ta jefe shi da shi har yanzu bata bar dariya ba. Nufo ta yayi ya chafke ta yace
"Zan baki punishment, kina jifan mijinki."
Kafin tayi magana ya had'a bakinsa na nata....
ALHAMDULILLAH!!!
Alhamdulillah da Allah ya nuna min farkon book d'innan da k'arshensa lafiya! Darasin dake ciki Allah ya bamu ikon d'auka, kuskuren da ke ciki Allah ya ka yafe mana.
Godiya ta musamman ga dukkanin masoya na da wanda na sani da wanda bansani ba kusani a duk inda kuke ina k'aunarku.
Fatan alkhairi ga duk wani mai karanta novel d'ina, Allah ya bar zumunci Amin.
Daga k'arshe ina mai bak'in 😭😭cikin sanar da masoya na cewar zan dakatar da rubuta 😭😭😭novel zuwa wani lokaci bisa wasu dalilai wanda basai na fad'e su ba da fatan masoya na zasuyi min uzuri zasu kuma fahimce ni, nagode da k'aunar da kuke nuna mun nima kusani ina k'aunar ku a duk inda kuke.😘
MSB💖
No comments:
Post a Comment