Friday, 8 September 2017

AUREN FANSA 42

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     🌹MARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

 _We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_

P.M.L

Ina yi ma d'aukacin musulmai barka da sallah, da fatan munyi sallah lafiya? Allah ubangiji ya maimaita mana Amin thumma Amin! ❤️

Wannan page d'in nakune Faty Ladan, Hauwee Bash, Asma'u Ammani, Hafsat Kabeer, Farida Bature, Feedn, Machika, and Aisha Basheer dama sauran wad'anda ban ambata ba, nagode da k'aunar book d'innan da kukeyi.😘

Fatan alkhairi ga Auren Fansa Fans😍Allah ya bar zumunci.❤️

       
                🌹42 🌹

Cikin girmamawa Faruk ya isa inda Baba ke tsaye ya gaishe shi ya amsa masa yace
"Meyake faruwa ne haka a nan?"
Faruk yayi murmushi yace 
"Yanzu zaka fahimci komai Baba."
Faruk ya koma inda Hajir ke tsaye yace
"Hajir ina so ki bani wayar nan dana baki zan duba wani abu."
Hand bag d'inta ta bud'e ta fiddo ta mik'a masa, ya maida dubansa ga Bilki yace 
"Ina so ki nutsu ki kalla."
Tace
"Bangane abinda ke faruwa a nan ba, don Allah ayi mana bayani mana."
Faruk yace
"Abinda nake k'ok'arin yi kenan ay."
Wayarsa ya zaro daga aljihu ya kira bugu d'aya aka d'auka yace
"Usman bud'e motata ka d'auko min system d'ina tana nan daga bayan seat, sai wasu wayoyi amma ba'a jiki suke ba suna nan a gefe sai ka d'auko mun su duka."
Bansan me Usman yace ba naji dai Faruk yace
"A'a motar a bud'e na barta kawai ka bud'e, yanzu yanzu muna jira don Allah."
Baba yace
"Wai lafiya haka Faruk? Har yanzu ban fahimci inda ka sa gaba ba."
Faruk yace yana k'ok'arin maida wayarsa aljihu
"Yanzu zaka fahimta Baba."
Bilki kuwa kamar ruwa ya cita haka kurum gabanta ya tsananta bugu, don har wata kyarma take duk da batsan abinda ke faruwa ba.
Usman ne yayi sallama hannunsa d'auke da laptop da wayoyi, Faruk ya kar6a inda ya aje ta a saman center table d'in dake ajiye a parlor d'in, yayi ta had'e had'ensa ya jona nan ya had'a can, cikin minti kad'an wani video ya bayyana a saman screen d'in laptop nasa. Ya juya ta setin da kowa ke tsaye ya danna play.
Hoton farko video Bilki inda take waya da Laila a gameda makircin da suka had'a, maganar yadda take kwasar dukiya da shawarwarin da Laila ke bata akan yadda zata dage wajen cigaba da juya dukiyar.
Next scene kuwa hoton Laila ne da Bilki suna zaune cikin d'aki suna maganar yadda suka kashe Hajiya Reema da Alhaji Adam, take Bilki ta fara zufa itada Laila, wannan abu ya basu mamaki ya akayi aka d'aukesu hoto haka? 
"Waye ya d'auki wannan videon?" Ta fad'a jikinta na kyarma, Baba kuwa kallonta kawai yana salati, inda Zarah da Meenah ke tsaye suna kuka suna mamaki.
Scene na gaba kuwa yana d'auke da video d'in Laila da Bilki inda Laila ke narrating yadda akayi kisan da kuma shawarar su cigaba da 6oye sirrinnan, har Bilki ke nuna mata tsoronta kar wata rana asirinsu ya tonu. Laila tana nuna mata asirinsu a rufe yake babu mai ji.
"Wallahi bani na kashe su ba, wallahi Laila ce ta kawo wannan shawarar."
Bilki ta fad'a tana kyarma, Laila tace
"Dana baki shawarar wa yace ki d'auka don haka kina da laifi kema."
Bilki tace
"Nidai wallahi kin cuce ni Allah ya isa wallahi."
Laila ta buga tsoki tace
"Aikin banza, yo Allah ya isarki me zatayi min?"
Faruk ya cigaba da displaying duk wani abu da aka d'auka na Bilki da Laila, tare da voice notes, Baba da zufa ta jik'e shi jagab, ya kalli Meenah da Zarah yaga yadda suke kuka, sannan ya juya ga Bilki da take borin kunya suna chachar baki itada Laila suna ta k'ara bankad'e asirinsu da kansu.
"Tun farko ina zaman zamana kika kawo wannan shawarar kika ce mu kashe su..."
"Dana kawo shawarar nace dole kibi ne? Kema a lokacin kina jin haushin Alhaji Adam, akan ya samu kujarar da kikeso mijinki ya mallaka ko nayi k'arya?"
Bilki tace
"K'arya kike munafuka algunguma, abin naki harda sharri kuma? To wallahi..."
Maganarta ta katse ne sakamakon wani zafafan mari da Baba ya d'auke ta dashi, har sai data ga gilmawan wuta sannan ta nemi ji da ganinta ta rasa na wuchin gadin.
Dafe kuncinka tayi cike da azaba kafin kuma ta ankara ya k'ara d'auke ta da wani wanda yafi na farko zafi, kyarma ta fara yi inda hawaye ke ambaliya a saman fuskarta, ya d'aga hannu zai k'ara wanke ta da wani marin cikin azama Meenah ta rik'e masa hannu gam gam tana kuka, tace
"Kar ka k'ara mata wani Baba, ka rabu da ita don Allah."
Baba ya fara k'ok'arin k'wace hannunsa yana nuna Bilki yace
"Ashe ke mutuniyar banza ce bansani ba? Shashasha marar mutunci! Ashe ke muguwa ce? Makira! Anya kinada imani kuwa? Kin bani mamaki ban ta6a zaton haka daga gareki ba..."
Sai ta fara borin kunya tana fad'in
"Yo har abin kunya ya wuce daga gareka? Kai fa kana zaune da mutum ka kasa gaya mata iyayenta na asali tsabar rufa rufa!"
Baba yace
"Ki min shiru a nan, anya kina da hankali kuwa?"
Tace
"Ras nake, yo tunda aka tona min asiri na wa zan iya rufewa kuma? Ai wallahi sai na fasa k'wan! Ke Amina! Kalleni nan Alhaji bashi ya haife ki ba! Haka nima ba nice na haife ki ba! Kije ki tambaye shi inda iyayenki suke."
Gaban Meenah yayi mummunar fad'uwa, dafe k'irjinta tayi a yayinda hawaye suke kwarara a fuskarta, Baba take kallo tace
"Ni 'yar tsintuwa ce ko?"
Faruk kuwa tsaye yayi cike da mamaki a yayinda k'walwarsa ta tsaya cak da aiki....



MSB💖

No comments: