Tuesday, 29 August 2017

AUREN FANSA 41

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     🌹MARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

 _We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_

P.M.L

     
                🌹41 🌹

   
http://MaryamSBello.blogspot.com


A hankali ta bud'e idonta juyi d'aya tayi ta hango shi bakin wardrobe da alama wanka ya fito yana shirin fita, duba agogo tayi k'arfe 8:30am, zumbur ta mik'e tana mamakin abinda ya haddasa masa makara yau, zaune ta mik'e tana kallonsa yana k'ok'arin d'aura agogo a hannunsa, ta sauko daga gadon ta kamo hannunsa tana cigaba da sa masa.
"Yau ka makara my soul."
Jin yayi shiru ya sanya ta d'ago tana dubansa da mamaki, damuwa ta gani k'arara bayyane a fuskarsa wanda idanuwansa ma sun nuna hakan.
"Meyake damunka my soul?"
Yace
"Babu komai, kije kiyi wanka yau tare zamu fita, sannan ki sanar da Zarah ta tamabayi mijinta ya bata izini zamu fita tare da ita."
Tayi shiru tana tunani can kuma tace
"Lafiya?"
Yace
"Koma me kenan zaki gani nan da lokaci kad'an, kedai kawai ki kirata ki sanar da ita."
Tace "To." Sannan ta wuce tana tunanin dalilinsa nace mata haka.

Tayi wanka ta sanya bak'ar after dress, tea kawai suka sha inda a waje sukayi kaci6us da Zarah inda take shaida musu da mijinta zasu tafi yace zai kaita, haka ma Anisah tazo a daidai sadda zasu shiga mota, itama ta shaida musu mijinta zai kaita, nan kuma kowa ya fara shirin tafiya.
A mota babu wanda yayi magana ko wane da tunanin da yakeyi, ta kai dubanta ga Faruk da alama ya zurfafa cikin tunanin, ta ta6o sa tace
"My soul wai meke faruwa haka ne? Sannan duk ina zamuje da su Anisah?"
Ya karkato kad'an ya kalle ta sannan ya maida kansa ga titi yace
"Ki gafarce ni my baby."
Tace
"Akan me fa?"
Yace
"Kawai ki yafe min akan abinda zai faru yau."
Cikin rashin fahimta tace
"Me zai faru yau?"
Bai kai ga bata amsa ba wayarsa tayi ringing, ya d'auka yace
"Hello Usman."
Usman yace
"Muna hanya ka turo mana address d'in."
Yace
"Muma muna hanya, zan turo maka sai mun had'u d'in."
Ya kashe kiran ya tura masa address d'in.
Meenah da zuciyarta fal damuwa tace
"Kaji my soul, wai meke faruwa?"
Yace
"Kiyi hak'uri zaki ga koma menene."
Ganin ya d'auki hanyar unguwarsu ya sanya tace
"Daman gida zamu shine kak'i sanar dani?"
Ya d'anyi murmushin k'arfin hali a zuciyarsa yace
"Nasan yau zanyi breaking heart d'inki my baby, amma abinda zanyi ya zama dole in ba haka ba hankali na bazai ta6a kwanciya ba."
Ya kalle ta yaga ta zurfafa cikin tuanani, yayi ajiyar zuciya a lokacin da ya karya kwanar layinsu Meenah.
Ganin motoci a k'ofar gidansu ya sanya ta d'an razana kad'an gami da zaro idanu waje, ya kalleta ya kawar da fuskarsa gefe, yasan kota masa tambaya baisan abinda zai ce mata ba.
Yayi parking ya fito daga mota, yana d'an kalle kalle, ganin ba motar Usman ya sanya yasan bai iso ba, amma motoci hud'u sun iso na abokanan aikinsa, su Zarah duk sun iso inda take ta tambayar abinda ke faruwa. Amsa d'aya take samu wato,
"Nima bansani ba."
Su Najeeb ne kad'ai suka san abinda ke faruwa saboda ya sanar musu daman.
Ya d'auki waya ya kira Hajir ya sanar mata yana k'ofar gida. Tace she's ready tun d'azu. Nan suka cigaba da tsara plan d'in nasu.
Ita dai Meenah bata k'ara magana ba illa dai gabanta da ya tsananta bugu.

A 6angaren Bilki kuwa tunda ta tashi da safe k'awarta ta iso akan yau zasu walimar bikin d'iyar wani sanata da za'ayi a cikin garin Abuja, Baba kuwa yana d'akinsa yana wanka zai fita, shiryawa tayi cikin wani dank'areren leshi mai matuk'ar tsada sai k'yalli takeyi, wayoyin da ke hannunta sun kai kala uku kuma manyan wayoyi masu tsadar gaske, ta fito parlor sai zuba k'amshi take kamar shagon saida turare, kaci6us tayi da Hajir sanye cikin bak'ar after dress tayi tsaye a bakin k'ofa idanunta manne cikin bak'in glass wato no respect.
Suka ja suka tsaya Bilki ta kalle ta daga sama har k'asa tace
"Ke Atika meye haka? Ina aikin dana saki zaki zo kiyi wa mutane tsaye a ka haka! Matsalar d'an k'auye kenan ka wayar da shi sai daga baya ya nuna yafika wayewa. Mts."
Laila tace
"Gaskiya kam da alama don wannan yarinyar 'yar rainin hankali ce, ke Malama ki bamu wuri zamu wuce."
Hajir ta kalle su da chewing-gum a bakinta sai hannunta dake hard'e tace
"Wacece Atika don Allah?"
Bilki tace
"Ahh! Kiji min neman magana fa, yo wacece Atika 'yar aiki in ba ke ba? Kaji min yarinya zata nemi ta maida ni k'aramar yarinya."
Laila tace
"Gaskiya wannan ta samu wuri da yawa. Da nice ke da tuni na sallame ta don bazan iya ba, zan iya farfasa mata jiki."
Bilki tace
"Eh gaskiya ne, ke Atika! Ki wuce kije ki d'ora girkin rana kafin mu dawo."
Hajir ta kallesu a wulak'ance tace
"I'm sorry to say Hajiya, amma bazanyi ba, sai dai idan kece zaki je ki d'ora."
Suka fara salallami suna tafa hannu, Laila tace
"Wai bazaki gaura mata mari ba, ni wallahi sheyasa kikaga bani d'aukar 'yan aiki saboda bansan wadda zan kwaso ba, ya za'ayi ki zauna kina fad'a tana fad'a? Ki d'auki mummunan mataki akanta mana."
Bilki tace
"Lallai kin k'oshi da sadda aka kawo ki kamar zakiyi min sujjuda amma yanzu kin k'oshi kin mik'e k'afa ko? Lallai sannu Atika, to wallahi kizo ki kwashi kayanta ki bar min gida munafuka kawai."
Hajir tayi murmushin mugunta tace
"Daman yau zan bar miki gida Hajiya kar ki damu."
Bilki tayi tsaye ta rasa ma me zatace sai tafa hannu kawai takeyi.

Minti goma tsakani Faruk ya doka sallama, Bilki ta washe baki tace
"Ah kinga surukinmu ne yazo, sannu da zuwa Faruk."
Ya shigo yana k'are ma gidan kallo, yana d'aga kwalar rigarsa yace
"Ki gyara kalamanki Hajiya ba Faruk zakice ba, Inspector Faruk Adam Ishaq zaki ce."
Suka kalli juna itada Laila, Laila ta rad'a ma Bilki a kunne
"Adam Ishaq fa yace, me hakan ke nufi kenan?"
Hajir tayi murmushi ta cire after dress d'inta     ta dawo kusa da Faruk tace
"Sunana Inspector Hajir ba Atika ba."
Bilki tace
"Ke kamar ya keba Atika bace, to wacece ke?"
Meenah da Zarah da Anisah suka shigo ganin Ikon Allah a daidai nan Baba ya sauko yana gyara hular kansa ganin mutane da hayaniya ya sanya yaja tsaya yana tambayar lafiya?



MSB💖

No comments: