✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_
P.M.L
🌹37 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
A zuciye ta shige ko gabanta bata gani sosai, tana shiga suka d'ago suka dube ta sai sukayi ido hud'u da Faruk, wani tsananta ya sake dira a zuciyansa ga wani zafi yana ji a k'irjinsa, yanzu a yadda yakeji baya jin son wata 'ya mace a duniya in ba Meenah ba, ya kalli inda Jiddar ke tsaye da rik'ak'en k'ugu tana kad'a jiki kamar wata mazari. Wayancewa yayi ya jefo mata tambayar rainin hankali
"Jidda ya gida?"
Ta yamutsa fuska gami da yin fari da ido tace
"Lafiya."
Yayi murmushi kad'an yace
"Kina son wani abu ne? As you can see I am busy here."
Tambayar ta bata haushi sosai ta kuma 6ata mata rai ainun, ta dube shi tace
"Inada buk'atarka ko ka manta matsayinka gareni?"
Yace
"A'a ina sane, kije zanzo muyi maganar."
Ta cika tayi fam tace
"Babu inda zanje, wai shin ya Faruk wane irin aure mukayi? Na k'iyayya ko na soyayya?"
Yace
"Bafa haka bane, nace ki dai je zanzo, idan kuma kina da buk'atar wani abu ki fad'a min."
Tayi shiru tana tunani, ta dubi Meenah da ke tsaye kamar abin bai dame ta ba, sai tayi mamakinta sosai, ta d'auka Meenah macece mai sauk'in kai har ma tayi tunanin zatasa baki a cikin maganar ko don ta taimaka mata, to me hakan ke nufi?
Kawai sai Jidda ta fita da gudu daga d'akin tana dana sanin zuwan da tayi da kuma zubar da class d'inta da take da shi a gaban kishiya da kuma mijin da bai damu da ita ba. Sai dai ta k'udiri gana ma Meenah wuta, har sai ta gane matsayinta a gidan, a shirye take don ganin hakan ta faru kuma sai ta fi kowa farin cikin ganin hawayenta!
Washe gari da safe Meenah na kitchen tana had'a kalacin safe Jidda na la6e tana jiran ta gama don ta san abinda ta shirya mata!
Sai da Meenah ta kammala abincinta soyen dankali ne da sauce d'in k'wai, ta zuba ma Faruk nasa a plate da na kowa sai ta koma d'akinsa don sanar masa ya fito ya ci abinci.
Tana ganin ta shige sai ta fito cikin sand'a ta bud'e abincin Faruk ta zazzaga ma sauce d'in uban yaji sannan ta zazzaga ma dankalin gishiri mai yawa. Tafiya taji ya sanya ta koma d'akinta a guje tana dariyar mugunta don yau zatayi kallon fad'an da Faruk zaiyi ma Meenah. Sai murna takeyi.
Meenah ta shigo d'akinta ta kalle ta tace
"Ki fito kici abinci ko."
Tayi 'yar dariya tace
"Yanzu kuwa."
Da d'an tsalle tsalle ta fito daga d'akin sannan kuma ta nutsu tabi bayan Meenah.
Kowa ya nutsu kan dinning zasu fara cin abinci, Faruk ne zai fara cin abinci har ya fara d'ebo dankalin kawai kwatsam Meenah ta lura da d'igen d'igen yaji a gefen plate d'insa sannan ga abincin ya chanza kala ya zama jawur, take ta fara tunanin yadda akayi hakan ta faru, sai ta kai dubanta ga Jidda yanayinta kad'ai ya isa ya tabbatar ba wanda ya aikatan hakan sai ita.
Cikin dabara ta kwa6ar da lemon da ke cikin cup a gaban faruk, hakan ya dakatar da shi daga cin abincin da zaiyi wanda saura k'iris ya kai bakinsa.
"Subhanalillah garin yaya hakan ta faru?"
Meenah ta mik'e da sauri tana cewa
"Kayi hak'uri wallahi ban lura ba, bari na goge."
Cikin dabara ta janye abincin Faruk ta matsar kusa da abincin Jidda ta shiga kitchen ta d'auko tsumma ta soma gogewa, ta faki idon Jidda ta sauya abincin dana Faruk sai ta tura na Jidda a gaban Faruk da sauri.
Bayan ta gama ta dawo ta zauna tace
"Sorry please, kaci abincin mana."
Yace
"Ay da kin bari sai da aka gama kika goge."
Tace
"Hakan yayi ay kaga yanzu sai aci abincin cikin kwanciyar hankali."
Ya d'ebi abincin ya kai bakinsa, Jidda nata kallonsa tana dariyar mugunta sai dai me? Bata ga komai ba sa6anin abinda tayi tsammani, ta shiga rud'ani, ta kalli plate d'inta sai taga na Faruk ne aka chanza mata, ta kai dubanta ga Meenah taga tana mata kallon irin ya kika ga nayi k'ok'ari ko?
Meenah ta k'ura mata ido tana murmushi, Faruk ya d'ago ya dubi Jidda yace
"Ya naga bakya cin abincin ne? Kici mana yayi dad'i."
Meenah tayi murmushin mugunta tace
"Eh kici abinci Jidda, yayi dad'i sosai."
Ta fad'i haka har yanzu bata bar murmushin ba, ba yadda ta iya haka ta d'ebo ta kai spoon a bakinta, take taji wani irin yaji da gishiri ya had'an mata, ta dinga taunawa da k'yar tana hawaye tana gogewa don kar a gane.
Faruk ya kammala cin abincinsa ya mik'e yana fad'in
"Zan tafi aiki, sai na dawo."
Meenah tayi murmushi tace
"Sai ka dawo, amma bari na gyara maka zaman rigarka."
Yayi murmushi yace
"To."
Ta gyara masa sannan ta fita raka sa bakin mota, suna fita Jidda tayi toilet da gudu tana faman tari da kakarin amai, sai da ta d'auki lokaci mai tsawo tana wanke bakinta sannan ta fito tana faman goge bakinta da har yanzu bai bar mata yaji ba.
Kaci6us tayi da Meenah a bakin k'ofa ta hard'e hannayenta duka biyun tana murmushi. Ganinta yasa ta d'an dafa ta tace
"Meyafaru?"
Jidda ta kwa6e mata hannu cike da masifa tace
"Muguwa! Azzaluma kawai."
Dariya ta su6uce mata tace
"Muguntar me nayi? Sannan kuma zalunci me nayi?"
Jidda ta dalla mata harara sannan tace
"Wallahi kin bani mamaki Meenah, nayi tunanin ke macece mai sauk'in kai ashe ba haka bane? Ashe haka kike?"
Meenah ta dawo tana fuskantarta ido cikin ido da hannayenta a hard'e sannan tace
"K'warai ina da sauk'in kai idan aka bini ta sauk'in kai, sannan kuma ina da wuyar sha'ani idan aka bini bata lalama ba, Jidda kar kiyi tunanin kina ganina kamar bansan abinda nakeyi ba, to da hankalina sannan kallonki nake tar! Nasan ke wacece sannan nasan wane irin zama ya kawo ki, a dah nayi niyyar muyi zaman lafiya dake, amma tunda na gano sirrinki da kuma k'udirinki na son rabani da Faruk na sake taku.
Wallahi baki isa ba, kinyi kad'an kice zaki rabani da Faruk, nasani ta yadda kika k'waci soyayyarsa ta k'arfi da kuma ta magani, anma kisani duk abinda aka d'ora shi ba bisa tirba ta gaskiya ba to labari ne."
Jidda ta daka mata tsawa
"Ke Meenah! Yafa isheki haka, shiru shiru fa ba tsoro bane gudun magana ne, kar ki nemi ki fad'a min magana yadda kikeso fa."
Meenah tace
"Ni ba fad'a zanyi da ke ba, amma kisani zan fad'a zan kuma k'ara fad'a ke baki isa ki rabani da Faruk ba, saboda yana yi min true love ne babu boka babu malami, soyayyarmu had'in Allah ce, kuma banga ta yadda zaki raba abinda Allah ya had'a ba, duk naji conversation d'inku keda k'awarki sannan a shirye nake nayi fighting back don ganin baki rabani da Faruk ba."
Jidda tace
"Haka kika ce?"
Meenah tace
"Haka nace."
Jidda tace
"Shikenan mu zuba, niko bama Faruk ba har gidannan sai na raba ki dashi, ta yadda idan kika fita har abada bazaki dawo ba."
Meenah tace
"In kin dama ki rabani da duniyar nan gaba d'aya bama gidan ba, sannan kisani babu abinda kika isa kiyi min sai abinda Allah yayi min, sannan ina so ki sani k'arya fure take bata 'ya'ya!"
Jidda tace
"Zaki gani."
Meenah tace
"Zanga alkhairi."
Daga haka ta sa kai ta fice zuwa d'akinta, inda ta bar Jidda tsaye kamar gunki in banda cizon yatsa babu abinda takeyi, gaba d'aya idanunta sun sauya daga fari zuwa ja, cikin sanyin jiki ta koma d'akinta tana mai mamakin Meenah da kuma maganganun data fad'a mata a yau.
MSB💖
No comments:
Post a Comment