Saturday, 26 August 2017

AUREN FANSA 38

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     🌹MARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

 _We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_

P.M.L

     
                🌹38 🌹
   
http://MaryamSBello.blogspot.com


Daddare bayan sallar maghrib Faruk ya kirawo su a babban parlor yana son magana dasu. Bayan sun iso ya fara magana kamar haka.
"Abinda yasa na tara ku a nan shine, na farko ina so ku sani shi aure ba abin wasa bane, sannan ban k'ara aurennan da wata manufa ba sai alkhairi, kamar yadda kuka sani ana yi wa ko mace kwana biyu ko uku, don haka na ware kwanaki biyu zan rik'a yi wa ko wacenku, ranar girkinki ya zagayo zaki kar6i girki, saboda Meenah ba baiwa bace da zata rik'ayi maki girki sai dai kici. Sannan banison raba abinci, idan girkin d'aya ne to zata dafa ma duka gidan abinci, da fatan kun fahimta?"
Meenah tace
"Mun fahimta."
Yace
"Yauwa daman shine maganar."
Jidda ta k'ule meye na ci mata mutunci a gaban Meenah?


***

Da safe Faruk na d'aki yana shirinsa zai fita aiki Jidda ta shigo sai faman zum6uren baki takeyi, ya kalle ta ya kawar da kansa tare da cigaba da abinda yakeyi, ta matso kusa dashi tace
"Ya Faruk ina son magana da kai."
Ba tare da ya kalleta ba yace
"Ina jinki."
Kai tsaye tace
"Mota nakeso ka siya min."
Ya dakata daga abinda yakeyi ya juyo yana kallonta cike da mamaki yace
"Mota fa kika ce? Anya kina da hankali kuwa?"
Tace
"Da hankalina ai itama d'ayar matar taka tana hawa mota, ni bana hawa, don haka ance kayi adalci a tsakaninmu nima sai ka bani mota."
Yayi ajiyar zuciya yana fad'in
"Jidda, Jidda, a gaskiya rigimarki ta fara isata, idan kina maganar mota dana bawa Meenah ina kikaga tana zuwa inba makaranta ba? Ke kuwa ba zuwa makaranta kike ba saboda bakici Jamb ba koba haka ba? Don haka tunda bakya zuwa makaranta ni ba motar da zan baki, da dai kina zuwa ne wannan is understandable sai na d'auki d'aya daga cikin motocina na baki kema kina zuwa makaranta, don haka kar na k'ara jin wannna maganar a bakinki ma."
Ta juyo cike da masifa tace
"Ni gaskiya baka kyauta min ba, kawai don nace ka bani mota sai ka min gori? Ni gaskiya ka bani mota tam."
Yace
"Bazan bada ba zo ki k'wata, ko ita Meenah ba rok'a na tayi ba ni naga dacewar hakan na bata, don haka kema idan naga ya dace na baki zan baki."
Ta fara jijjiga jiki tana masifa
"Kawai don nace a bani mota shine mene? Naga dai motocinnan kana da su to meye don ka bani d'aya?"
Yayi tsaki yace
"Ke kinga tashi ki fita ki bani wuri, mota kuma zo ki k'wata sai muga ta tsiya, sakaryar banza wadda batasan ciwon kanta ba, kullum ke kenan rigima daga kice wannan sai kice wannan? Haka kikaga 'yar uwarki nayi ne? Haba!"
Tashi tayi ta fita tana wannan cika tana batsewa ita a dole an 6ata mata rai, shi kuma Faruk tsaki kawai yakeyi har ya kammala shirinsa.


Haka ta koma d'akinta zuciyarta na rad'ad'i ta dubi agogo k'arfe bakwai da minti hud'u 7:04am, Faruk mamaki yake bata kafin suyi aure kamar zai maida ta cikinsa, amma sunayin aure komai ya chanza mata, gashi bata son sanar da Luby halin da take ciki gudun kar ta mata dariya sheyasa ma ta bar abin a ranta.



BAYAN KWANA BIYU


Bayan kwana biyu kuma ta samu Faruk ya lafa mata tunda har yana kwana d'akinta kuma yana kulata, don haka sai ta fara jijji da kanta a gaban Meenah, wai ita nan ta fara samo kansa.
Meenah ta kira Faruk a waya ta tambayesa zataje gida kuma ya barta, don haka ta shirya tsab direba zai aje ta, don yau ma Zarah zataje gida itama, ta fito parlor nan ta iske Jidda nata faman shan kankana duk ta 6ata wurin, Jidda badai k'azanta ba.
Jidda ta d'ago ta dube ta a shek'e ta ta6e baki sannan tace
"Fita zakiyi ne?"
Meenah tace
"Gida zanje."
Jidda ta bushe da dariya sannan ta dubi Meenah tace
"Haba Malama ke dai fad'i gaskiya, ashe duk k'aryar banza ce kikace kissa tafi magani, tunda gashi zaki fita neman maganin kema? Sai dai kin makaro don kinga yanzu Faruk ya k'ara dawowa hannuna kuma, kuma kisani na riga nayi miki nisa  sannan a sannu zan tantance miki da magani da kissa wane yafi tasiri, kuma yanzu kika soma ganin chanji don nayi alk'awarin sai kin bar gidannan kika k'aryata ni, to muje dai zuwa, don haka kema kinbi sahu ay sai mu goga ni da ke."
Meenah tayi murmushin da ya k'ara bayyanar da kyawunta tace
"Ko shakka babu ni na fad'a miki kissa tafi magani tasiri kuma zaki gani, babu boka babu Malami, nayi alk'awarin nuna miki tasirin da  kissa take da shi, ki fara k'irga daga yanzu na baki kwana bakwai kima fara lissafi tun daga yanzu, sannan banga ta yadda kina k'azanta zaki iya zama da miji lafiya ba ko wannan kad'ai ya isheki, ni na tafi sai na dawo."
Tasa kai ta bar gidan, Jidda ta sake bushewa da dariya tana wani huro chewing-gum d'in da ke bakinta tayi k'wai tace
"Da sannu dai zan ci ubanki sai kin gwammace kid'a da karatu."


****

Gaba d'aya Meenah ta dage da addu'a ba dare ba rana, sannan ga extra kula tana masa da kuma kaucewa duk wata hanya da zata sa su samu sa6ani, lalla6a sa takeyi kamar k'wai, shiyasa ma take ganin chanji sosai.

Yau da rana abinda yake so tayi masa wato waina da miya, ta masa zo6o mai dad'i da kunun aya tayi masa tasani sarai yafison abubuwan gargajiya akan tarkacennan. Yana cikin cin abincin ne Jidda ta shigo ta wani kashe d'ankwalin ture kaga tsiya tana taunar chewing-gum, da sauri ta janye plate d'in tana ma Jidda wani irin kallo. Tace
"Baby ban yarda da abincinnan ba, ka daina ci kazo na had'a maka wani."
Meenah ta mik'e tace
"Sai dai ki jira zuwan ranarki."
Faruk yace
"Kinga Jidda don Allah ki wuce ki bamu wuri banason tashin hankali."
Cike da mamaki ta kalle shi tana kad'e kai tace
"A gaskiya bazakaci abinnan ba, saboda sam ban aminta dashi ba."



MSB💖

No comments: