Thursday, 3 August 2017

AUREN FANSA 32

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     🌹MARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

 *_We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_*

P.M.L

Alhamdulillah duk wani masoyina da ya damu dani nagode sosai Allah ya saka da alkhairi! Naga sak'konnin gaisuwarku na kuma gode da kulawa Allah ya bar zumunci ameen. 😘
Haka masu kirana da turo man sak'ko don jin lafiyata kuma nagode sosai Allah ya bar zumunci.😘😍

Wannan page d'in naku ne members na AUREN FANSA FANS, thank you so much for everything!😍🌹
     
                🌹32 🌹
   
http://MaryamSBello.blogspot.com


Duka duka batafi minti ashirin ba ta dawo hannunta d'auke da tray mai d'auke da lemo a cikin glass cup da aka riga aka zuba, gefe kuma kwalin lemon 5alive ne. Tafe take tana faman smiling tana kashe ido, tafiyar ta kuwa kamar tana tsoron taka k'asa, fuskarta cike da fara'a da nishad'i kallo d'aya zakayi mata ka tabbatar da hakan.
Da isowarta sai ta rissuna a hankali ta ajiye tire d'in, sannan ta dawo ta zauna a kusa dashi tace
"Ya Faruk ga ruwa kasha."
Kallonta yake bako kyaftawa zuciyarsa tana ayyana masa abubuwa da dama game da ita.
A hankali ta mik'o masa lemo tace
"Bismillah."
Bai iya mata musu yakeji koda kuwa yaso hakan, don haka sai ya kar6a ya fara kur6a kad'an kad'an, kuma a hakan suna ta6a fira.
"Kamar yadda na fad'a ma Dada cewar nazo mu daidaita kanmu to kema haka zan sanar da ke, don haka me zakice game da hakan? Duk da kuwa na dad'e da sanin sirrin da ke ranki shiru kawai nayi, amma duk da haka ina so naji ta bakinki, kin shirya aure na ko kuwa?"
A cikin ranta mamaki take yadda tashi d'aya ta sato zuciyarsa a tafin hannunta! Lallai indai kuwa hakane komai zaizo mata da sauk'i tunda har ya kamu da wuri haka.  A fili kuwa murmushi tayi tace
"To yadda za'ayi ka samu Dada da maganar don maganar tana hannun manya, amma tambayar amsar ka itace, eh na yarda kuma na shirya aurenka ya Faruk."
Yayi murmushi
"Kina so na kenan?"
Ta gyad'a kai cike da farin ciki, yayi murmushi yace
"To ba matsala ay, kuma gaskiya bana son aja lokaci mai tsawo, in zan samu ne ma nan da sati biyu yayi min, amma da yake zanyi gyaran inda zaki zauna ana iya sashi nan da wata d'aya."
Tace
"To duk yadda kace ni yayi min."
Da zai tafi ya fiddo kud'i masu tsoka ya bata, yace
"Kya sa kati da wannan, sai munyi waya."
Ta kar6a tace
"Nagode."
Sukayi bankwana ta shige d'aki, tana zuwa ta kira Luby, ta kwashe labarin komai ta fad'a mata, ta sanar mata ya bata kud'i masu tsoka.
Luby tayi shewa
"Duniya sabuwa, kinga a nan kenan kin harbi tsuntsu d'aya da igiya biyu."
Jidda tayi dariya tace
"A gaskiya nagode Luby bansan ya zanyi ba idan baki ba, kin taimaka min sosai."
Luby ta k'yalk'yale da dariya tace
"Somin ta6i ne ay, ya Faruk sai ya raina kansa, sai ya dawo kamar zai maki sujjada"
Jidda taji dad'i tace
"Nagode 'yar uwa sai munyi magana gobe."
Sukayi sallama ta kwanta rigingine tana tunanin ranar da zata mallaki Faruk a matsayin mijinta.


Koda ya koma gida bai iske Meenah a parlor ba, kuma sai yaji bai wani damu ba, d'akinsa ya wuce kansa tsaye yayi wanka ya kimtsa cikin kayan bacci ya hau gado ya kwanta, sam ya kasa bacci sai tunanin Jidda da ya addabe shi, wayarsa ya d'auko ya kira ta amma har ta tsinke ba'a d'auka ba, ya sake kira a karo na biyu nan ma sai da ta kusa tsinkewa ta d'auka.
"Hello ya Faruk..."
Ya lumshe idanu kafin ya bud'e, sannan yaja ajiyar zuciya yace
"Kar dai har kinyi bacci na tashe ki?"
Tayi murmushi
"Eh na fara sama sama dai, da fatan ka koma gida lafiya?"
Yace
"Lafiya lau, gani nan ma har nayi shirin bacci."
Ta mik'e da sauri daga kwance da take tace
"La ya Faruk kuma shine ka kira ni? Idan amaryarka ta farka taga kana waya dani fa?"
Yayi murmushi
"Kar ki damu bazata farka ba, besides tama san da maganarmu so kar ki damu."
Tayi wani shu'umin murmushi tace
"To shikenan ya Faruk sai da safe."
Ya 6ata rai
"Kar dai har mun gama firar?"
Tace
"Eh."
Yace
"Gashi ban gaji da jin muryarki ba."
Tayi dariya
"La ya Faruk, nima haka, amma bacci nakeji yanzu.
Yace
"To shikenan sai da safe."
Tace
"Allah ya kaimu love you."
K'itt! Ta kashe bata jira ya bata amsa ba. Ya sagale wayar a kunnensa ya kasa cirewa. Haka ya kwanta da tunaninta har garin Allah ya waye.


Kallo d'aya zakayi mata ka tabbatar da tana cikin matsananciyar damuwa, banda idanunta da suka rikid'e suka koma ja alamar rashin bacci da kuma kukan da tayi a daren jiya.
Sanye take da wani navy-blue atamfa d'inkin riga da skirt sai wani yalolon gyale data gyala a saman kanta. Kwata kwata yau batada kumari haka take jinta wani iri tunda ta tashi batada walwala.
Tsaye take a kitchen tana faman had'a masa kalaci mai rai da lafiya. Sai da ta kammala komai ta jera saman dinning sai ta koma ta kimtsa kitchen d'in.
Tana tsakar yi ne taji alamun tafiya, hakan ya dakatar da ita gami da fitowa daga kitchen d'in. Sanye yake da uniform d'in aikinsa wato komai in black tun daga sama har k'asa, ta k'ara dubansa a karo na biyu gami da yin murmushi. Maimakon ya maida mata murtani sai ya fara k'ok'arin gyara zaman belt d'in wandonsa. Hakan ba k'aramin k'ona ranta yayi ba gami da bata mamaki tsantsa.
Ta daure tare da had'iye 6acin ranta ta k'araso inda yake tsaye tace
"Ina kwana?"
Bai motsa ba ya amsa
"Lafiya."
Ta dai daure tace
"Naga kana shirin fita baka karya ba."
Sai a sannan ya d'ago yana dubanta amma fuskarsa babu annuri ko kad'an kamar wanda aka aiko ma da sak'on mutuwa. Yace
"Azumi nakeyi."
Tace
"To... wane iri naga yau ba Monday ba kuma ba Thursday ba?"
Ya k'ule da tambayarta sai ya kalle ta kad'an yace
"Dole sai wannan ranakun Allah ya halasta azumi? Mutum yana iya yi ko yaushe don samun lada."
Ta k'ak'alo murmushi tace
"Haka ne kam, Allah ya bada lada."
Yace
"Amin, ni zan wuce sai dare zan dawo yau."
Tace
"To a ina zaka sha ruwa?"
Yace
"Zan siya abinci, don yau aikin da ke gabana da yawa da k'yar zan samu dawowa wannan lokacin yau."
Tace
"To."
Har yayi hanyar waje sai kuma ya dakata tare da karkatowa kad'an yace
"Gobe za'a fara gyaran gida, za'a k'ara fasa d'aki da parlor da kitchen daga can baya."
Bata tanka ba don ta gane inda maganar ta dosa, shi kuwa gogan daga haka kawai sai yasa kai ya fice don shi ko ganinta bai son yi yau, Jidda kawai yake tunani.
Yana fita ta fashe da kuka mai tsanani don ko maganar auren da ya tarkato bata d'aga mata hankali irin yau da taga yadda ya chanza mata.

***

Yana office yana shirin fita don an kirasa wai akwai wani kisa da akayi a wani gida, zasu je bincike. Yana tsakar tattara mahimman abubuwan da zai buk'ata aka shigo da sallama. Ya amsa tare da bada izinin shigowa, sai dai a yadda ya tsaya yana kallonta cike da mamakin sauyawar da tayi kamar ba Hajir ba, gaba d'aya ta zama bak'auya sak!
Sanye take da wani tsanwar atamfa ta k'ok'e sosai, d'inkin k'auyawa riga da skirt, sai d'ankwalin daban, fuskarta harda d'ige d'igen kwalliya. Hakan ba k'aramin dariya ta basa ba. Sai da yayi mai isarsa sannan ya dakata yana kallonta yana tafa hannu.
"Bravo! Lallai kinyi k'okari Hajir, aww na manta Atika ashe. Aikinki yayi kyau, are you ready?"
Tace
"Yes sir."
Yace
"Good, d'auko kayanki inada wani aikin da zamuje muyi yanzu, amma ina iya kaiki gidana da zarar na dawo sai mu kaiki gidan da zaki zauna."
Tace
"Haka ma yayi sir."
Kayanta ta d'auko dake cikin ghana most go tabi bayansa.


Da sallama suka shiga, tana zaune a parlor tana karatun wani novel, ganin Faruk ya shigo yasa ta dakata gami da amsa sallamar tasa. Tare suka shigo da Hajir, bayan sun zauna Faruk ya soma magana.
"Meenah wannan 'yar aikin da kika ce a samo miki ce, sunanta Atika, yanzu ina sauri zan koma aiki, so zan barta nan sai na dawo sai mu kaita ko?"
Taji dad'i sosai suka gaisa da Hajir a mutunce sannan tace masa.
"Ay naji kace yau zakayi dare a wurin aiki, why not ka bari na kaita da kaina ko ya ka gani?"
Ya mak'e kafad'a alamun oho yace
"Hakane tunda kin iya mota ki d'auki d'aya daga cikin nawa sai ki kaita, ni zan koma."
Ta masa a dawo lafiya ya fice. Meenah ta kalli Hajir tace
"Don Allah ki tashi daga k'asa ki koma kan kujera."
Hajir ta koma kan kujera tana ta faman murmushi. Meenah tayi murmushi tace
"Ko kefa, bari na k'arasa abincin rana kici sai na kaiki ko?"
Hajir tace
"To nagode."
Meenah tayi murmushi ta mik'e ta shiga kitchen.


MSB💖

No comments: