Monday, 7 August 2017

AUREN FANSA 33

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     🌹MARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

 _We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_

P.M.L

     
Kuyi sorry Fans muna fama da matsalar rashin wuta🤗


                🌹33 🌹
   


http://MaryamSBello.blogspot.com


Bayan ta kammala abincin suka ci sai ta zarce zuwa gida don kai ta, Bilki bata zargi komai ba sai ma murnar samun mai taya ta aiki dama Zarah keyi to zata fara zuwa makaranta ga bikinta da za'a sanya.
Nan aka gabatar mata da ayyukan da zata rik'a yi tun daga su shara, wanki, wanke-wanke, girki da sauransu.

Kafin ta tafi sai da shiga wurin Baba da ke zaune parlor yana kallon news, ganin Meenah ta shigo ya sanya yayi murmushi, ya bita da kallon k'urilla a lokacin da take zama kan carpet.
"Baba ina wuni?"
Ya gyara zamansa yana kallonta yace
"Lafiya lau Amina, ya gida ya kuma mai gidan naki?"
Tace
"Duk lafiya lau Baba yana wurin aiki."
Yace
"Madallah, naji zancen zai k'ara aure hakane?"
Ta had'iye miyau mai d'aci tace
"Hakane Baba."
Yace
"Kinsan komai muk'addari ne daga Allah Amina, kar ki d'aga hankalinki ki jure, ki zamo mace mai hak'uri da biyayya kinji? Allah ya za6a maku mafi alkhairi, ya bada zaman lafiya."
Tace
"Amin Baba nagode, daman zan wuce gida yanzu."
Yace
"To ki gaida mijin naki, da fatan baki buk'atar wani abu?"
Tace
"A'a Baba."
Yace
"Kuma zaku tafi jami'ah, ku kula sosai, karatu kukaje yi shi zakuyi Allah ya taimaka."
Tace
"Insha Allah Baba, amin."
Sukayi sallama ta tafi gida.


K'arfe goma saura ya shigo gidan, tana zaune tana karatun alk'ur'ani, daga bakin k'ofa yaja ya tsaya yana sauraron muryarta tana karanta suratul Mujadala, yayi tsaye shi bai shigo ba haka ma shi bai fita ba, take kuma ya tsinci kansa cikin nutsuwa don karatun yana masa dad'i.
Sai data kai aya sannan ya shigo, ganinshi ya sanya tayi saurin mik'ewa ta isa garesa gami da amsar brief case d'insa, tayi murmushin da bai kai zuci ba tace
"Sannu da zuwa."
"Yawwa." Kawai yace ya wuce zuwa ciki, ranta ya sosu ta dai daure ta bishi ciki a lokacin data shiga taji alamun watsa ruwa. Sai kawai ta fito ta zauna parlor tana kallo abinta.
Shiru bai fito ba har kusan sha d'aya ta wuce, ga ita kuma tana kunyar binshi d'aki yanzu kada ya fassara ta, sai kawai ta mik'e ta tattara abincin tasa fridge ta wuce d'akinta.
Gaba d'aya ta kasa bacci sai uban tunani, ko a mafarki akace mata Faruk zai mata haka bazata yarda ba. Ganin hakan bashi ne mafita ba ya zama tilas ta kai kukanta ga Allah don shine zai share mata, toilet ta fad'a ta d'auro alwalla ta fara sallah tana kai kukanta ga Allah.
Tana wurin har akayi sallar asuba, hakan yasa tana gama sallah kanta ya fara yi mata barazanar ciwo, ta lalla6a ta kwanta ba'a d'au lokaci ba bacci yayi awon gaba da ita.


Cikin baccin ne taji kamar ana ta 6arar da abubuwa, a gigice ta farka tana salati, duba lokaci tayi k'arfe 11:41am lallai tasha bacci.
Hijabinta ta d'auko ta sauko daga gadon, tana lek'owa taga mutane maza suna ta aiki a gidan, gabanta ya yanke ya fad'i, maganar Faruk ta dawo mata a cikin kanta.
"Gobe za'a fara gyaran gida, za'a k'ara fasa d'aki da parlor da kitchen daga can baya."
Dafe kanta tayi da ke juya mata sannan ta fara bin bango ji take kamar zuciyarta zata fad'o k'asa.
Note ta gani a bisa drawer d'inta hannunta na kyarma ta d'auko ta warware ta ta soma karantawa...

"Na tafi office, kamar jiya yau ma azumi nakeyi kar ki wahalar da kanki yin wani girki sai dare zan dawo, idan masu aikin nan sun gama da na yau ki shiga d'akina ki d'auko 5k ki basu zan kirasu na masu bayani."
Wani k'ululun bak'in ciki ne ya tokare mata mak'oshi, ta daure tayi ta maza ta maida note d'in ta ajiye a inda ta d'auka, ta rasa dalilinsa na shan ruwa a waje, at least ko bai dawo da wuri ba ay ya kamata ya ci abincin data girka masa komai dare, amma ta lura kamar baya son cin abincin ne gaba d'aya a nan.
Da k'yar ta sha ruwan tea ta koma d'aki ta kwanta, k'arar aikin gidan ne ya ishe ta shi yasanya ta kasa baccin kirki.
Allah ya taimake ta Zarah tazo zasuje makaranta registration, tayi ta murna ta kirasa don shaida masa amma bai d'aga ba sai kawai ta aika masa da sak'o.
Cikin sa'a kuwa suka kammala komai suka dawo gida, Zarah tsabar haushin gyaran inda kishiyar yayarta zata zauna yasa ko gidan bata iya shiga, daga waje sukayi bankwana ta tafi gida.

Yanda ya umarce ta hakan tayi don kuwa k'arfe shiddan yamma suka gama, ta shiga ta d'auko masu kud'in ta basu suka tafi.

Haka kullum sai sun zo da safe su gama k'arfe shidda, da yake ana sakin kud'i sai gashi ginin har ya mik'a sosai.
A zamantakewar auren Meenah kuwa babu abinda ya chanza gaba d'aya Faruk ya chanza mata kamar bashi ba, bai damu da ita ba bare cinta, shanta da kuma lafiyarta.
Abincinta ma baya ci ko tayi masa, tun yana bata excuse har ya fara fitowa 6aro 6aro yana ce mata bazai ci ba. Ga abu kad'an fad'a da masifa, nan da nan sai ya hau fad'a ba dalili.
Nan kuwa yana can ya tare wurin Jidda, wani lokacin can yake da anyi sallar isha'i har goman dare. Kuma komai ta bashi ci yakeyi, gaba d'aya ya sussuce ya rikice.
Hakan yasa aka sanya bikin sati uku masu zuwa, don ya kusa kammala aikin gidansa saura kad'an ya rage, haka aka tattara aka sanya bikin aka had'a dana su Zarah da Nabeel.
Shi kuma ya cigaba da had'a lefe da kuma akwati biyu na kayan fad'ar kishiya da zai kai ma Meenah.




MSB💖

No comments: