Tuesday, 8 August 2017

AUREN FANSA 34

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     🌹MARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

 _We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_

P.M.L

     
                🌹34 🌹
   
http://MaryamSBello.blogspot.com

Meenah kuwa duk wani abu bazata fasa yi masa ba, har girki sai tayi koda kuwa bazaici ba, ga tana k'ok'ari wajen ganin ta kai zuciyarta nesa don gudun fitina, sauk'inta ma yanzu shiryen-shiryen bikin Zarah ya fara kankama hakan yasa ta rage yawan shiga damuwa, don kuwa tana gida kuma bata cika dawowa ba sai yamma.

Karo na farko da ta fara shiga gidan Aneesha tunda sukayi aure, bayan ta shirya cikin green d'in material d'inkin doguwar riga sai ta gyala gyale marar kauri sosai. Da sallama da shiga gidan, Aneesah na kitchen tana fama da girki taji sallama ta lek'o, murmushi tayi tace
"Bismillah shigo."
Bayan ta zauna Aneesah ta shiga kawo mata lemo da kayan motsa baki, yau duk kunya ta kama Aneesah ganin itace k'arama kuma ko sau d'aya bata shiga gidan ba. Meenah tayi murmushi tace
"Baki gane ni ba ko?"
Aneesah tace
"Nagane ki mana, matar ya Faruk ce nasanki."
Meenah tace
"Allah sarki ya gida?"
Tace
"Lafiya lau."
Shiru ya biyo ba, na 'yan mintina sai suka kafa ma tv ido ana wani film. Meenah ta katse shirun ta hanyar mik'a mata kati
"Daman Iv na kawo maki na bikin sister d'ina."
Aneesah tayi murmushi tace
"Allah sarki, Allah yasa alkhairi yasa munada rabon gani."
Tace
"Amin ni zan koma."
Aneesah tace
"Haba tun yanzu? Na d'auka sai kin ci abinci tukunna."
Meenah tace
"Kai haba, bamuda nisa ta yaya zan cinye ma amarya girkin angonta?"
Aneesah tayi murmushi cike da kunya tace
"Kai a'a wallahi ba haka bane."
Meenah tayi dariya tace
"Kedai wasa nake miki, idan na dawo next time zanci insha Allah."
Aneesah tace
"To ina zuwa."
Ta mik'e ta shiga ciki, can ta dawo hannunta d'auke da leda tana murmushi tace
"To ga wannan."
Meenah tace
"La harda wahala haka?"
Aneesah tace
"Ba wata wahala wallahi."
Meenah tace
"To nagode ni zan tafi."
Aneesah tace
"Nima zan shigo, ay kina WhatsApp ko?"
Tace
"Eh inayi."
Aneesah tace
"Zamu rik'a gaisawa insha Allah, nagode sosai wallahi."
Meenah tace
"Babu komai wallahi."
Sukayi bankwana ta tafi, tunda Meenah ta tafi Aneesah ke raya kyawunta da kirkinta, sai taji haushin kanta da meyasa bata ta6a shiga sun gaisa ba, amma ta k'udiri a ranta zasu fara zumunci daga yau.

****

Meenah sun soma lectures, yanzu damuwarta ta ragu sosai, kuma tayi sa'a yana bata mota idan zata tafi.

Ranar litinin da daddare sai ga Faruk ya shigo da akwatina guda biyu, tunda Meenah ta ganshi tasan na menene, don haka bata nuna damuwarta ba ko kad'an, sai ma fatan alkhairi da tayi masa.
Hakan ba k'aramin mamaki ta basa ba, kuma sai ta bashi tausayi, nan ta bubbud'e akwatina ta gani bayan ta gama ta tashi ta shiga ciki. Ya dad'e zaune ranar farko da ya ji auren ya fita a ranshi kuma.

Mik'ewa yayi cikin sanyin jiki ya bita ciki, tana kwance a d'aki tayi ruf da ciki idanunta a lumshe, hakan ya k'ara bayyanar da zara zaran eye lashes nata. Ya dad'e tsaye yana kallonta kafin ya tako a hankali yatsaya yana k'are mata kallo. Sanye take da 'yar k'aramar vest pink color sai tasa pink dogon wando, harta ribbon d'in kanta pink ne, daga gani ba bacci take ba amma kuma tak'i bud'e idanunta.
"Meenah..."
Ta bud'e idanunta a hankali ta sauke bisa fuskarsa da yake kallonta kafin ta amsa da
"Na'am."
Sai kuma ya rasa abin cewa, ya sosa kai yace
"Dama zuwa nayi naji ko kina lafiya."
A ranta tace
"Sabon salo sai kace damuwa yayi da ni bare kuma lafiyata."
A fili kuwa cewa tayi
"Lafiya lau."
Shi yadda take sharesa d'innan yaji ba dad'i,  yayi missing kula da shi da takeyi, amma yanzu ko kallonsa bata son yi, magana ma da k'yar take amsa masa. Da yanzu ta tambeyesa ko yana buk'atar wani abu, amma yanzu ta daina.
"Ko kana buk'atar wani abu ne?"
Yayi sauri yace
"A'a, sai da safe."
Tace
"Allah ya kaimu."
Ta rufe idanunta alamun bacci, ya dad'e tsaye yana kallonta kafin ya fita daga d'akin a sanyaye.

Yana shiga d'akinsa ya iske miss calls ba iyaka daga Jidda, kiranta yayi bugu d'aya ta d'auka.
"Haba my dear ina ka shiga inata kiranka?"
Yace
"Sorry na shiga wanka ne."
Yace
"Ok daman kud'in da zan siya anko ne na 'yan mata baka bada ba..."
Yace
"Kud'in anko kuma?"
Tace
"Eh da kud'in k'unshi."
Yace
"To fah har nawa?"
Tace
"Gaba d'aya dubu 500 ne!"
Yace
"What? Dubu 500? Gaskiyar magana ko banida su, bazan iya baki dubu 500 ba."
Tace
"Haba mana my dear, wai nan fa na maka sauk'i."
Yace
"Dubu 100 zan baki, idan baki so good and fine."
Tace
"Wai wannan fad'an na menene daga tambayarka kud'i?"
Yace
"Jiya jiya kika tambayeni dubu 200 na baki, shekaranjiya dubi 50, yanzu kuma dubu 500, to banida su."
"Don Allah kayi hak'uri ka bani, daga yau bazan k'ara tambayarka wasu kud'in ba."
A fusace yace
"Ke kar ki raina min hankali fa! Na riga nace bazan baki ba, don haka sai da safe."
K'it ya kashe wayar, cike da jin haushinta, gaba d'aya haushinta yakeji. Yau ko baccin kirki ya kasa, haka yasa ya mik'e ya lek'a d'akin Meenah tana kwance tana bacci peacefully, ta masa kyau sosai, sai dai dole ya koma d'akinsa ya kwanta amma ina ya kasa bacci, sai gabansa dake ta fad'uwa ya rasa dalili.


Washe gari sai ga 'yan jere, nan sukayi ta hidimarsu ita kuma Meenah ko fitowa ma batayi ba, tana d'aki tana jinsu suna ta aikin jerensu, har dare suna nan basu gama ba, har washe gari sai da suka dawo da safe suka k'arasa wanda basu idasa ba.
Itama Meenah jeren Zarah suka tafi the next day, hakan ba k'aramin dad'i yayi mata ba.
Biki nata matsowa yau saura kwana biyu a d'aura aure....


MSB💖

No comments: