Thursday, 29 June 2017

AUREN FANSA 09

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐
๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน
๐ŸŒน✨⭐✨⭐✨⭐✨๐ŸŒน
✨๐ŸŒน✨⭐๐ŸŒž⭐✨๐ŸŒน✨
⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐
✨⭐✨๐ŸŒน✨๐ŸŒน✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒŸ


๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
AUREN FANSA!!!
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

๐ŸŒนNa๐ŸŒน

     ๐ŸŒนMARYAM S BELLO๐ŸŒน
             (MSB)

๐ŸŒŸ๐ŸŒนPure Moment Of Life Writers๐ŸŒŸ๐ŸŒน



          ๐ŸŒน09 ๐ŸŒน

http://MaryamSBello.blogspot.com

Haka kuwa akayi washe gari da safe Hamza da Bilki suka fita don saka Meenah a makaranta. Gobarau Academy itace makarantar da suka nufa, da zuwansu da komai basu wuce minti talatin ba aka kammala komai aka saka ta Pre nursery, duba da shekarunta kuma a k'a'idar makarantar idan yaro bai kai shekara 3 ba to baza'a saka shi nursery ba daman. Daman 'yan pre nursery ba'a saka musu uniform.
A ranar aka barta makaranta kuma ko kuka batayi ba da su Hamza zasu tafi don ta samu abin wasa sai dad'i takeji.
K'arfe 12 suke tashi don haka dole Bilki ke d'auko ta don Hamza na wurin aiki lokacin, ba yadda ta iya haka nan take hak'ura tana d'auko ta d'in.

Haka rayuwar ta cigaba da gudana cikin hukunci da hikimar ubangiji, Meenah har ta shiga nursery. Meenah Allah ya bata k'walwa komai aka koya mata ta iya sai dai idan ba'a koya mata ba, kuma idan ta dawo gida ta dinga yi kenan ko gajiya batayi.

Ba'a saka Zarah makaranta ba sai da Meenah ta shiga nursery 2 a lokacin ita kuma Zarah tana da shekara 3 a duniya yayinda Meenah keda hud'u.


Ranar wata juma'a akayi ma su Meenah hutu suna zuwa gida Meenah ta fara neman babanta don nuna mai report card nata, sai
dai rashin sa'a yayi tafiya zuwa Lagos a safiyar ranar, tayi ta kuka tana kiran ita Baba.
Bilki tana tsaki ta ansa report card nata dana Zarah tana dubawa, abin takaici a wurinta wai Meenah na d'aya tayi ita kuwa Zarah na ashirin tayi cikin su ashirin da shidda. Bilki kamar tayi kuka don takaici. Wato Meenah dai tafi d'iyarta k'ok'ari kenan?
"Gaskiya da sake!" Ta kalli Meenah tace mata "Ke! Zo nan!" Meenah tayi tsaye idanunta k'wal hawaye a duniya tana tsoron Bilki, fizgo ta tayi da k'arfi.
"Ke dan ubanki sai da kika yi na d'aya wannan karon ma? Kin manta bugun da nayi maki last term kenan? Salon kija babanta ya dawo ya zane Zarah ko? Ke ga mai k'ok'ari ko? Shegiya mai kama da mage! Wuce ki bani wuri!" Da gudu Meenah tayi d'aki tana kuka sosai, jawo Zarah tayi ta rungume tace.
"Don Allah d'iyar Baba ki dage kifi waccan yarinyar k'ok'ari kinji?" Zarah ta gyad'a kai.

Da rana ta zuba ma Zarah abinci ta shiga wanka, Meenah na zuwa Zarah tace.
"Zo muci." Ba musu ta zauna suka fara cin abincin tare.
Ba'a jima ba Bilki ta fito wanka tana lek'owa taga Meenah nacin abin da d'iyarta abinda ta tsana! Da tsawa tace
"Ke!" A firgice Meenah ta tashi tana kyarma,
Bilki ta k'ara daka mata tsawa.
"Bana hana ki cin abinci tare da Zarah ba? Shegiya wuce ki tafi d'aki." Tayi d'aki da gudu a tsorace. Zarah ta aje cokalin hannunta tace
"Bazan ci ba nima sai da Meenah." Daman Bilki tasan abinda zatace kenan, tsaki taja tace
"To sai dai kar kici wallahi amma bazakici tare da Meenah ba, kinji na fad'a miki!"
Aikuwa aje cokalin tayi tana fushi sosai ta bar parlon. Tsaki Bilki ta k'ara yi tana k'ara jin haushin Meenah...


***

Sauri yakeyi ya dawo gida don nuna ma iyayensa result nasa na shedar kammala jss3 nasa. Driver na yin parking ya fito da gudu yana murna shigarsa keda wuya ya taradda abinda ya d'aga masa hankali, ya kuma gigita shi a lokaci guda, take zuciyarsa ta fara bugawa da sauri a yayinda k'walwarsa ta tsaya cak! ta bar aiki lokaci d'aya!!!
Iyayensa ne kwance jina jina, a yayinda wasu mutane kusan su bakwai ke tsaye cikin bak'ak'en kaya hartta fuskokinsu an rufe da black mask!
Tsaye yayi ya kasa tantance a wace duniyar yake, take kuma ya fashe da kuka yana fad'in.
"Su waye ku? Mey...asa ku...ka kashe min iyaye?"
Direwa yayi k'asa yana kuka yana jijjiga iyayen nasa a yayinda yake kiran Anisah! Mutumin yayi dariya yace.
"Ka bar kuka yaro, sun tafi inda ba'a dawowa kaima kuma yanzu zaka bisu!" Yakece da dariya sannan ya saita bindigar daodai saitin k'irjinsa ya harba.
A gigice ya farka duk da Ac d'in da ke aiki amma hakan bai hana sa yin sharkaf da zufa ba. Ta6a jikinsa ya soma yi amma baiga jini ba, ajiyar zuciya ya sauke ya shiga yin addu'a don ba k'aramin tsoro yaji ba.
"Wane wane irin mafarki ne haka..... ?"
Ya fad'a yana mai k'ara tunawa da mafarkin da yayi. Zumbur! Kuma ya mik'e ya fice da gudu don duba lafiyar iyayensa don gani yake kamar da gaske ne....!




MSB๐Ÿ’–

Tuesday, 27 June 2017

AUREN FANSA 08

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐
๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน
๐ŸŒน✨⭐✨⭐✨⭐✨๐ŸŒน
✨๐ŸŒน✨⭐๐ŸŒž⭐✨๐ŸŒน✨
⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐
✨⭐✨๐ŸŒน✨๐ŸŒน✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒŸ


๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
AUREN FANSA!!!
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

๐ŸŒนNa๐ŸŒน

     ๐ŸŒนMARYAM S BELLO๐ŸŒน
             (MSB)

๐ŸŒŸ๐ŸŒนPure Moment Of Life Writers๐ŸŒŸ๐ŸŒน


Another page for my Ummi Aisha thanks for all the support and care one love dear๐Ÿ’–Allah ya k'ara basira Amin๐ŸŒน


          ๐ŸŒน08 ๐ŸŒน


Laila ce ta cigaba da magana.
"Ko dai har yanzu baki fahimta ba ne?"
Ajiyar zuciya Bilki tayi, sannan tace
"A gaskiya Laila ban iyawa, kisa fa kika ce? Don ina son dukiya sai akace na kashe su, gaskiya mu chanza shawara dai."
Laila tayi kwafa.
"To sai akace mu zamu bisu mu aikata k'udirinmu? Ko kusa ba haka nake nufi ba, abinda nake nufi a nan shine..."
Nan naga ta rad'a mata wata magana daga k'arshe dukkansu suka kwashe da dariya.
Bilki tana dariya tace
"Shegiyar gari, lallai Laila sai dai a barki amma ke shu'uma ce wallahi."
Hajiya Laila ta k'yalk'yale da dariya sosai sannan tace
"Kema haka."
Bilki ta tashi tana gyara zaman d'ankwalinta tana kallon Laila tace
"Kamar naji kuman Zarah bari na dubo ta."
Laila tace
"Yi sauri kuwa nima naji."
Jim kad'an sai ga Bilki ta shigo da Zarah a hannunta da alama yanzu Zaran ta tashi daga bacci, tana zuwa Laila ta mik'a hannu ta fara mata wasa, can sai ga Meenah ta fito da alama bacci ta tashi don kuwa kanta buzu buzu yake, saboda yanayin gashinta mai cika kuma ga tsawo sheyasa ko ya ta kwanta sai yayi buzu buzu. Zuwa tayi kusa da Bilki tana murza idanu. Su kuwa sai faman ta6e baki sukeyi. Meenah tace
"Maama wunwa."
Laila ta ta6e baki tace
"Uban me tace?"
Bilki tace
"Ohon mata, ke tafi can ki bamu wuri."
Abinka ga yaro da ba ganewa tayi ba, sai ma ta matso kusa da Bilki ta jingina da ita. Da sauri Bilkin ta hankad'e ta gefe ta fad'i k'asa tim!
"Wannan yarinya anyi mayya! Mts." Cewar Laila had'e da jan tsaki.
Bilki ta jawo hannunta da k'arfi, Meenah ta fashe da kuka.
Kitchen suka nufa ta had'a mata tea a cup tana tsaki sannan ta dire mata k'asa.
"Oya zauna kisha yarinya bata aje komai ba sai ci? Haba!" Nan ta zauna ta shanye tas sannan ta fito daga kitchen d'in.
Tana gama fad'an haka ta fice taje ta had'o ma Zarah cereal ta koma parlor, Laila ke bata har ta kammala sannan aka bata ruwa.

A tare suka girka abincin rana inda Laila tayi ma Zarah wanka, sannan suka dafa fried rice da papered chicken sai had'ad'en salad.   Wuraren uku da kwata Laila tayi sallama da Bilki ta tafi gida.
Sai wurin biyar saura sannan Bilki tayi ma Meenah wanka ta bata abincin rana.

Kamar kullum bayan Alhaji ya dawo gida yayi wanka yaci abinci, suka zauna palor suna 'yar fira kafin a kira sallar magrib. Kasancewar Meenah batasan dawowar Baban nata ba, tana can d'aki tana wasa.  Sai data fito, aiko tana ganin shi ta rugo da d'an gudunta ta zo kusa da shi tana fad'in
"Dada!"
Cike da jin dad'i Alhaji yace
"D'iyar Dada ashe ana ciki, zo nan."
Tana zuwa ya d'auke ta ya zaunar kan cinyarsa yana mata surutu tana dariya. Can kuma sai tace
"Dada kaga Maama ta bije ni d'azu."
Ya ware idanu
"Me kikayi wa Maama ta bige ki?"
Tayi shiru tana kallonsa can tace
"Bakomai."
Bilki ta taso tana dariya tace
"Kai yaro ma dai daban ne, d'azu ne fa na shiga wanka nazo na iske ta tana zubar da madara, shine fa nace mata kar ta k'ara. Alhaji yayi dariya
"Ah ah Meenah a daina 6arna ba kyau kinji ko? Idan Maama tace a daina a daina kinji?"
Ta gyad'a kai. Sai kuma yace
"Bilki ya naga Meenah ta rame ne ko bata son cin abinci?"
Tayi dariya tace
"Ay Alhaji inda kasan yadda nake da fama da yarinyar nan akan taci abinci ko? Sai kayi mamaki sam batason ci na rasa dalili."
Yace
"To kuma ya baki sanar dani ba? Muka sani ko wani abin ke damunta? Kinsan yaro tunda ba fad'a zatayi ba."
Tace
"To k'ila dai."
Ya juyo da dubansa ga Meenah
"Haba Meenan Dada, meyasa baki cin abinci?"
Nan ma shiru. Yayi murmushi
"Zaki sha ice cream?"
Nan take da washe baki tana murna. Shima yaji dad'i yace
"Yauwa to bari idan na fita yanzu kafin na dawo gida zan siyo maki harda biscuit ma."
Saukar da ita yayi daga cinyarsa yace
"Bilki bari na wuce masallaci lokacin sallah yayi sai na dawo."
Tace
"A dawo lafiya."
Sai da ya fita ta bishi da harara dashi da Meenah dake tsaye a tsorace gaban Bilki.
Tana huci tace
"Gaskiya abinnan ya fara isa ta, sai wani nan nan yake da yarinyar nan amma naga ba ruwanshi ma da Zarah, lallai Alhaji ka haifi d'iya a cikinka amma ka nuna son d'iyar wata? To da sake mts."
Daga nan ta shige d'aki, Meenah na tsaye tana zare idanu.

Haka kuwa akayi Alhaji da zai dawo sai da ya tsaya ya siya ma Meenah ice cream da biscuit sai ya k'aro mata kayan lashe lashe na yara. Zarah kuwa wani d'an abin wasa ne na yara ya siya mata tunda yasan bata isa shan wad'annan kayan ba.
Yana dawowa Meenah ta tare shi tana murna, ya bata ice cream d'inta nan ta zauna ta shanye tas sannan ya bata biscuit d'inta ta tafi d'aki.
Abin wasan yara ya bama Zarah dake hannunsa yana mata wasa. Ita kuwa sai dariya takeyi. Bilki na zaune kusa dasu tana wasa da Zarah. Can Alhaji yace
"Ina Meenah tayi ne?"
Tayi tsaki a ranta tace
"Yanzu ta tafi d'aki ay ta ga k'wad'ayi kuma tunda bazata ci abinci ba."
Tashi yayi yana fad'in
"Ina zuwa."
Ta6e baki tayi tana mai jin haushin Meenah.
Yana shiga d'aki ya ishe Meenah kwance k'asa da biscuit a hannunta bacci ya kwashe ta. Murmushi yayi ya d'auko ta ya d'ora ta kan gado, ya gyara mata kwanciya sannan ya kashe fitilar ya fito.
Koda ya fito Bilki bata nuna komai ba, Zarah ta k'ar6a tayi d'aki da ita don yi mata wanka.

BAYAN KWANA BIYU

Bilki ta fito wanka da safe kiran Laila ya shigo, tana d'auka Laila tafara magana
"Kash Hajiya Bilki yanzu naji labarin iyalen Alhaji Adam sun koma Abuja gaba d'aya."
Da sauri Bilki tace
"Haba dai? To yanzu ya kenan?"
"Bansani ba nima, plan d'inmu ya rushe don gidansa na Abuja akwai tsaro sosai, ko ina sojoji ne a gidan."
Bilki tace
"Gaskiya akwai had'ari mu ce zamuyi wani motsi yanzu. Amma ki bari tukunna a sake shawara."
"To shikenan." Laila tace tare da katse kiran. Nan tayi ta sak'a da warwara ta rasa mafita.


***

Haka rayuwar ta cigaba da gudana har akayi shekara d'aya amma har yau sun rasa wata mafita.
A lokacin kuma Meenah ta shekara biyu harda rabi Alhaji ya fara shirye shiryen saka ta makaranta da kuma islamiyya. Don ya fuskanci zata iya da wuri don a yadda ya fahimce ta, ta iya saurin d'aukar abu da kuma maganarta ta fito ga surutu ba abinda bata fad'i.
Sheyasa ma yanzu Bilki ta rage takura mata don muddin Alhaji ya dawo zata kwashe komai ta fad'a masa. Tana gudun kar tun baya tunanin komai har ya fara zarginta...


MSB๐Ÿ’–

AUREN FANSA 07

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐
๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน
๐ŸŒน✨⭐✨⭐✨⭐✨๐ŸŒน
✨๐ŸŒน✨⭐๐ŸŒž⭐✨๐ŸŒน✨
⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐
✨⭐✨๐ŸŒน✨๐ŸŒน✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒŸ


๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
AUREN FANSA!!!
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

๐ŸŒนNa๐ŸŒน

     ๐ŸŒนMARYAM S BELLO๐ŸŒน
             (MSB)

๐ŸŒŸ๐ŸŒนPure Moment Of Life Writers๐ŸŒŸ๐ŸŒน



          ๐ŸŒน07 ๐ŸŒน

Fatima Zarah fara ce tas sa6anin Meenah da take ba fara ba tas, murna a wurin Bilki ba'a magana don yanzu gani take wata sabuwar dama ce ta samu ta yadda zata dinga samun kud'i a hannun Alhaji ba tare da wani matsala ba.
Kulawa ta musamman take samu a wurin mahaifiyarta wadda takeji kamar ta had'iye don so. A idon Alhaji kuwa had'awa takeyi da Meenah tana kulawa dasu wanda bata gajiya, bayan idonsa kuwa Meenah bata samun wata kulawa, tun daga kan wanka, chanza pampers, cin abincinta, chanza kaya idan sun 6aci sam bata damu ba. Sai  Alhaji ya kusa dawowa take tashi tayi mata wanka ta bata abinci yadda komai tsiyarshi baya ganewa. Zarah kuwa sai ayi mata wanka sau uku, abinci kuwa duk bayan awa uku ake bata, sheyasa tun kafin suyi arba'in ta takura tayi k'iba tayi fam, kamar balloon.


Watan Zarah biyu a duniya Meenah ta shekara d'aya cas. Tayi kyau tayi wayau abinta. Gata ta iya magana ba abinda bata fad'i kai kace 'yar shekara uku. Yadda ta taso ta d'auka Bilki ce mahaifiyar haka ma Alhaji ne babanta sai dai tafi shak'uwa da Alhaji saboda muddin yana gida to suna tare. Sheyasa yanzu idan zai fita sai da wayau saboda ta dinga kuka kenan kamar zata sik'e.

***

Ranar wata juma'a Alhaji ya dawo fuskarsa a cinkushe daga gani yana cikin damuwa, yana shigowa gaban Bilki ya yanke ya fad'i dama da safe ya fad'a mata ana neman sa banki don haka tana ta murna don tasan mijinta ya zama manager na banki. Yana fita ta hau gyaran gida tayi ma su Zarah wanka tayi masu kwalliya sosai. Ta shirya abinci mai rai da lafiya kafin k'arfe d'aya ta gama komai tana zaman jiransa ya dawo.
Yana shigowa ta tare sa daga bakin k'ofa tana ta murna kamar zata shige cikin jikinshi. Sai dai kula da yanayinsa ya sanya jikinta yin sanyi lak'was.
Bayan sun zauna ta fara tambayarsa.
"Alhaji wai ya ake ciki ne? Baka ce komai bafa."
Ya kalle ta na 'yan second kad'an kafin ya numfasa yace
"Bani akaba ba abokin aikina aka ba."
Dafe k'irji tayi tare da zaro idanu waje. Tace
"Me kace? Kana nufin basu baka ba? Haba ! Gaskiya ba'ayi adalci ba sam."
Yayi murmushi
"Bilkisu kenan, ni banga abin d'aga hankali a nan ba, kar ki manta komai na duniya rabo ne, idan bakada rabo komin yadda kakeson abu bazaka same shi ba."
Shiru tayi tana ayyanawa a ranta. "To wa aka ba?"
Ta tambayi kanta.
"Alhaji Adam Ishaq." Aka ba.
Tashi tayi tsaye
"Haba yanzu kayi magana, ay daman na dad'e da sanin sun fison su ba Adam, saboda shi yafika kud'i ko?"
"Haba Bilki! Bana son tashin hankali tunda an riga an bashi kina da yadda zakiyi ne? Ni ban damu ba kuma na taya sa murna nima idan lokacin nawa yazo zan samu. Alhaji Adam mutumin kirki ne, kuma muna mutunci dashi don haka na taya sa murna sosai, ke kuma idan na k'ara jin maganar nan kin tada ita a bakin aurenki!"
Dole taja bakinta tayi shiru, amma tana nan tana jira ya fita ta kira aminiyarta Hajiya Laila ta fad'a mata wannan mummunan labarin.

Aiko ana gama sallar magriba ya fice daga gidan, yana fita ta kira k'awarta Laila tana d'auka Bilki tac ce
"Wai bakisan meya faru damu ba ko?"
Hajiya Laila cikin d'aga murya tace
"Meyafaru?"
Nan Bilki ta kwashi komai ta fad'a mata tana gama magana Laila tace
"Ke iya nan kina sani kenan? Tab! Alhaji Adam dai an amsa transfer zuwa Abuja kiji in fad'a maki, yayi kud'i abinsa dama kinsan mahashuk'in mai kud'i ne ba kad'an ba."
Bilki ta zaro idanu waje kamar Laila na ganinta tace
"Haba ki bari Laila, ta yaya akayi kika sani?"
Laila tayi shewa tace
"Kina nufin baki sani ba? To bari in tak'aice maki labari Alhaji Adam Ishaq babban d'an kasuwa ne, sannan yana saida motoci ke kampanin k'era motoci ke gareshi a k'asashe daban daban. Bayan nan ga super market da yake dasu ba iyaka, ga gidajen mai nan tun daga nan Katsina, Kaduna, Abuja ke babu inda babu. Matarsa ma shagon saida kayayyaki ke gareta babu abinda babu k'atuwar mall ce sai dai kin gani."
Bilki da jikinta yayi sannan taji maganar kud'i yasa tace
"Wai da gaske kike?"
Laila tace
"Ba maganar wasa a nan Hajiya Bilki wallahi gaskiya na fad'a miki, bakiga kullum basu k'asar ba? Ke wallahi rayuwarsu abin sha'awa daga shi sai matarshi sai yaranshi guda biyu kacal ke cin wannan uban dukiya. Ke suna fantamawa fa. Kinsan gidanshi dake sabon titin GRA can wuraren Governor road d'innan ay ko?"
Bilki tace
"Kar dai kice kusa da wannan makarantar premier boarding school ta mata?"
Laila tace
"Nan fa toh wannan fa, gidanshi nan nan na nisa sosai, kullum na wuce ta hanyar sai na k'ara kallon gidan don gidan ya had'u ba kad'an ba."
Bilki tace
"Tabbas na gane gidan, nima ina ganin gidan, lallai Alhaji Adam ba k'aramin dukiya ya tara ba..."
Laila tace
"Uhm kedai bari zanzo idan nazo zaki k'arasa jin sauran bayanan don maganar bata waya bace."
Bilki tace
"Haka ne, gaskiya ina jiranki Laila kar ki shanya ni."
Laila tayi dariya
"Wallahi zanzo."
"Yaushe to?"
Laila tace
"Zuwa jibi."
Bilki tace
"Ina jiranki."
Daga haka sukayi sallama zuciyar Bilki cike da tunani kala kala, da kuma sha'awar dukiyar Alhaji inama ace tata ce, abinda take ta ayyanawa a ranta kenan.


        BAYAN KWANA BIYU

Da safe wuraren k'arfe sha d'aya Laila ta diro gidan Bilki, aiko murna a wurin Bilki ba'a magana, nan aka kawo mata kayan motsa baki. Bayan sun gama gaisawa Laila tace
"Bilkisu mai gadon zinari kenan, yau gani nazo a gidanki akan labarin da kikeson ji, wato maganar kud'i."
Bilki tace
"Ina jinki k'awata."
Laila tace
"Ay kamar yadda na fad'a miki rannan toh haka maganar take, kuma zuwa nan da sati d'aya zasu tattara su bar garinnan. Niko inada shawara amma bansani ba ko zaki yarda da ita."
Bilki tace
"Fad'i shawararki."
Laila ta gyara zama bayan ta shanye lemon da ke cikin glass cup ta soma magana.
"Bilki tunda kinga dani dake duk muna son kud'i me zai hana mu had'a k'arfi da k'arfi mu k'waci dukiyar Alhaji Adam."
Bilki ta zaro idanu waje
"Kamar ya? Ban fahimce ki ba."
Laila tayi dariya
"Abinda nake nufi a nan shine, mu had'a k'arfi nida ke mu k'waci dukiyar Alhaji Adam koda hakan na nufi mu kashe su."
Da sauri Bilki ta zabura had'e da zaro idanu waje tana kallon Hajiya Laila...




MSB๐Ÿ’–

AUREN FANSA 06

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐
๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน
๐ŸŒน✨⭐✨⭐✨⭐✨๐ŸŒน
✨๐ŸŒน✨⭐๐ŸŒž⭐✨๐ŸŒน✨
⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐
✨⭐✨๐ŸŒน✨๐ŸŒน✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒŸ


๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
AUREN FANSA!!!
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

๐ŸŒนNa๐ŸŒน

     ๐ŸŒนMARYAM S BELLO๐ŸŒน
             (MSB)

๐ŸŒŸ๐ŸŒนPure Moment Of Life Writers๐ŸŒŸ๐ŸŒน



          ๐ŸŒน06 ๐ŸŒน

Kan dinning suka nufa inda Daddy da Anisah ke zaune suna labari harda dariya, zama sukayi itada Faruk
da Daddy ke musu fira a yayinda Mummy ta zuba ma kowa abincinsa. Wurin kuma yayi tsit sai k'arar spoon ake ji. Anisah ce ta katse shirun ta hanyar jefo ma Daddy tambaya.
"Daddy idan na girma me zan zama?"
Daddy dake shirin kai loma a bakinsa ya dakata yana kallon Anisah kafin kuma yace
"Anisah kenan, duk abinda kike so shi zaki zama ay."
Anisah tayi dariya
"Ni banason na zama komai nafiso na shiga aljanna."
Kowa a wurin sai da ya maida hankalinsa gareta kafin kuma Mummy tace
"Insha Allah zamu shiga aljanna kinji ko?"
Mummy tace
"Abban Faruk ya batun baka manager d'in ko sun fasa?"
Daddy yayi murmushi
"Ba fasawa sukayi ba Reemah, sai sun duba cancanta kafin su bada, idan na dace a bani manager zasu bani, idan kuma wani ya dace a ba za'a bashi."
Tayi murmushi
"Haka ne kuma, nidai fatana Allah ya baka sa'a a dukkan lamuranka"
Yaji dad'in addu'ar matarsa ba kad'an ba, abinda ke k'ara masa sonta kenan kullum cikin yi masa addu'a takeyi yana murmushi yace
"Amin ya Allah Reemah."
"Ka fidda ranar da zamu tafi Disney world d'in kuwa?"
Reemah tace bayan ta had'iye abincin dake bakinta. Daddy ya sha cup d'in Apple juice kafin yace
"Eh zuwa upper week dai insha Allah lokacin su Faruk sun gama exams a islamiyya."
"Yeeyy! Mummy Disney world zamuje da gaske?"
Mummy tayi murmushi tace
"Eh Mamana ko bazaki ba?"
Anisah ta zum6ura baki
"O'o ni zanje."
Faruk yace
"Kalle ta to baza'a dake ba."
Anisha ta sa kuka
"Daddy wai baza'a je dani ba?"
Daddy yayi murmushi
"Ya isa yace bazaki ba, ay kece head d'in tafiyar gaba d'aya zamu iya barinsa amma ke bazamu iya barinki ba."
Gwalo ta ma Faruk tana share hawayenta. Faruk yasa dariya. Anisah tasa kuka.
"Mummy kinga Ya Faruk na min dariya ko?"
Mummy ta harari Faruk
"Zaka fara ko Baba na? Meyasa kakeson ganin kukan k'anwarka ne?"
Yayi dariya
"Aww dariya ma kakeyi Faruk? Bazaka bata hak'uri ba?''
Ya buga k'afa.
"Wannan 'yar yarinyar zan ba hak'uri? Tab bazan bada ba."
Daddy yace
"Just say sorry Faruk, you know she won't stop crying unless you apologize."
Mummy tace
"Oya Faruk now!"
"Ok sorry!"
Take ta bar kukan inda kuma ta cigaba da cin abincinta kafin kuma ta kalli Daddy
"Daddy zansha ice cream."
Mummy tace
"Me nace miki akan zak'i?"
Anisah ta turo baki
"O'o ni zansha."
Mummy zata k'ara magana Daddy ya d'aga mata hannu
"Ba ruwanki Reemah, zan siya mata ice cream."
Anisah tashi tayi da gudu ta wuce parlor tana tsallen dad'i.
Daddy yayi dariya Mummy na taya shi tace
"Anisah kenan, badai rigima ba."
Daddy yayi dariya
"Lokacinta ne, kema kinyi naki ay."
Mummy tace
"Daddy Faruk fa na wurin."
Yayi dariya
"To sai me? Sai na fad'i abubuwan da kikayi ay" Da sauri ta tashi tana fad'in
"Haba Daddy!"
Yayi dariya
"Kina tantama ne? Bari kiga..."
Kafin ya k'arasa tayi sama da sauri tana dariya. Daddy ya tashi ya bi bayanta
"Guduwa kikayi Reemah!"
Faruk tsayawa kallonsu yayi yana dariya cikin ransa yace
"Allah ka k'ara had'a kanmu what a lovely family!"


***

Meenah na zaune kan carpet tana wasa da abin wasanta haka kawai kuma sai tasa kuka, Bilki dake zaune saman kujera tana shan rake tana kallon wani movie da take so kukan Meenah ya cika mata kunne. Tsawa ta daka mata
"Ke da Allah kiyi mana shiru yarinya sai shegen kuka haba!"
Abinka ga yaro wannan tsawa da aka daka mata ita ta firgita ta yasa ta k'ara fashewa da wani irin kuka. Haushi ya cika Bilki yasa ta tashi tayi shigewarta d'aki ta bar Meenah nan na ta faman kuka kamar zata shid'e. Meenah tayi kuka baiwar Allah har ta gaji. Nan ta kwanta k'asa tayi ta ajiyar zuciya har baccin wahala ya kwashe ta a nan.

Bilki na kwance a d'aki ta jiyo k'arar shigowar motar Alhaji. Da sauri ta fito tazo ta d'auki Meenah dake a k'asa ta rungume ta tare da zama kan kujera tana rirriga ta.
Haka Hamza ya shigo ya same ta, da murmushi a saman fuskarsa ya k'araso. Yana zama Bilki ta kalle shi
"Sannu da zuwa Alhaji."
Yana murmushi yace
"Yauwa sannu da aiki Bilki, Meenah bacci akeyi?"
Tayi murmushi
"Eh wallahi yanzu ta gama rigima sai na rirrriga ta tayi bacci."
Yayi murmushi
"Meenah kenan, ay batada rigima ma k'ila dai baccin takeji daman."
Tayi yak'e
"Sosai ma ay Meenah baiwar Allah ce batada rigima."
Yace
"Hakane Allah ya raya mana ita."
Tace
"Amin."
Yace
"Bari naje na watsa ruwa na gaji."
Tace
"Ok sai ka fito."
Tana ganin shigewarsa ta kalli Meenah taja dogon tsaki, sannan taje ta kwantar da ita a d'akin Meenah d'in kan gado.

Bayan Alhaji ya gama wanka suna zaune kan dinning suna cin abinci ya kalli Bilki yace
"Bilki a gaskiya ba abinda zance miki sai dai nace Allah ya saka da alkhairi akan aikin ladar da kikeyi. Allah ya baki lada."
Ta kalli Alhaji tace
"Haba Alhaji meye na godiya ay yi wa kaine, kuma ma Meenah kamar d'iyar dana haifa haka na d'auke ta. Idan har kana min godiya sai naji kamar baka d'auke ta a matsayin 'yar cikina ba."
Yayi murmushin jin dad'i
"Wallahi ko kusa ba haka bane, kawai dai na yaba da k'ok'arinki."
Tayi dariya
"Allah sarki. Uhm uhm Alhaji dama madararta da pampers sun k'are shine nace  ya kamata a bad a siyo mata wasu."
Yace
"Wannan ba damuwa zan baki isashen kud'i ki siyo mata wanda zai dad'e, naga kamar tafison madarar ma akan abinci."
Tace
"Hakane."
Bayan sun gama ya d'auko kud'i har dubu goma ya bata. Amsa tayi tace
"Shikenan zanje na siyo mata.
Yace
"Toh ko ki bari idan na fita na siyo mata mana."
Da sauri tace
"Kai haba kai ina kake da lokaci? Ni da nake gida kullum ka bari zan siyo mata."
Yayi murmushi
"Toh shikenan."


***

Watan haihuwar Bilki ya kama. Kullum sai ta tambaye shi kud'in siyayya bai ta6a hana ta ba saboda har ga Allah ya d'auka Bilki ta shiryu.
Wata rana nak'uda ta kama Bilki gadan gadan, Hamza ya kaita asibiti, suna zuwa ba'a jima ba ta haifi 'ya mace. Kyakkyawa fara tas mai k'oshin lafiya.
Haka aka cigaba da zaman barka inda komai Hamza yayi mata daidai gwargwado komai yana tafiya daidai.
Ranar suna yarinya taci sunan kakarta ta wurin Hamza wato Fatima. Haka aka gama taron suna aka watse lafiya kowa ya koma gidansa....



MSB๐Ÿ’–

AUREN FANSA 05

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐
๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน
๐ŸŒน✨⭐✨⭐✨⭐✨๐ŸŒน
✨๐ŸŒน✨⭐๐ŸŒž⭐✨๐ŸŒน✨
⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐
✨⭐✨๐ŸŒน✨๐ŸŒน✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒŸ


๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
AUREN FANSA!!!
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

๐ŸŒนNa๐ŸŒน

     ๐ŸŒนMARYAM S BELLO๐ŸŒน
             (MSB)

๐ŸŒŸ๐ŸŒนPure Moment Of Life Writers๐ŸŒŸ๐ŸŒน

Dedicated to mairo๐Ÿ˜œ aka Maryam Gafai I heart you sis❤️ and my sisi Ammin SS ๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜


          ๐ŸŒน05 ๐ŸŒน


BAYAN KWANA BIYU

Ranar suna yarinya taci sunan mamanta marigayiya Amina, daman bawani taron sunan da akayi wane taro ma ana zaman makoki?
Amina duk da tana jaririya Allah ya zuba mata hak'uri ga bata kuka sosai sai dai idan taji yunwa ko wani abin na damunta. Kammaninta sak na mahaifiyarta ta d'ebo hartta gashinta irin nata ne lub lub, hasken ne kawai bata d'ebo ba sa6anin marigayiya da take fara tas kamar yayanta Hamza amma Amina babyn ita ba fara bace tas, sai dai tana da kyau duk da batada hasken ana ganin kyawunta. Idan ta bud'e ido ta kalli mutum zaka gansu manya ne farare tas!

Baya 'yan kwanaki a lokacin Amina ta kwana 20 cif a duniya Goggo ta kira Hamza da Bilki gidanta akan cewa tana son magana dasu.
Bayan sun iso suka gaisa Goggo ta d'auko Amina dake kwance kan gado tana bacci, ta mik'a ma Hamza ita tana murmushi tace
"Hamza kamar yadda kasani marigayiya ta baka amanar rik'on Amina kuma ka d'auki alk'awarin haka, don haka yau na damk'a maka Amina a matsayin d'iyarka halak malak, da fatan zaka rik'e ta bisa amana."
Sai kuma ta juyo ta kalli Bilki tace
"Bilkisu ga amanar Amina nan ki rik'e ta amana saboda kar ki manta marainiya ce gaba da baya idan har kika ci zalinta Allah zai mata sakayya."
Hamza yace
"Insha Allah Goggo kar ki damu ina k'auanar Amina kamar 'yar dana haifa haka nake jinta a raina. Insha Allah zamu rik'e ta amana, Allah ya taya mu rik'o."
Goggo tace
"Amin, daga cikin dukiyar da mahaifinta ya bar mata a ciki ake siya mata su pampers da su madara, sai kayan sawa da sauran abinda ba'a rasa ba, amma ba kasafai nake amfanin da kud'in ba sai idan ba kud'i hannuna, amma tunda yanzu zata dawo hannunku da zama sheyasa zan damk'a maka kud'inta a hannunka ka adana mata ko ka juya mata su duk yadda kaga ya dace."
Jiki a sanyaye Hamza yace
"Insha Allah Goggo."
Daga haka Goggo ta tashi ta had'o kayan Amina tas sannan ta kira mai gadinta ya saka cikin mota.
Sai da suka ci abincin rana sannan suka koma gida, inda ko a mota Bilki ce ta rik'e Amina sannan ga mamakin Hamza bata nuna komai ba har rungume ta tayi tana fad'a ma Hamza d'iyar ta shiga ranta sosai. Ba k'aramin sanyaya mishi zuciya hakan yayi ba, duk wata fargaba dake ransa ta kau yadda yaga Bilki na tarairayar Amina kamar 'yar cikinta.

Bayan sun koma gida da daddare Bilki ta had'a ruwan zafi tayi ma Amina wanka tas sannan ta shirya ta cikin kayan baccinta wato overall pink wadda tayi mata kyau, gashin babyn ya wani yi irin pam d'innan sannan duk da haka a nannad'e yake gwanin kyau.
Bayan ta gama ta had'a mata madararta ta bata tasha ta k'oshi, sannan ta rirrigata ta tayi bacci, duk akan idon Hamza wanda yake mata kallon mamaki, abinda baiyi zato ba yau gashi Bilki nayi.
Bayan ta rirriga Amina tayi bacci zuwa tayi kusa da Hamza tana rok'on gafarar abubuwan da ta masa, bai gasgata ba sai da ya ga Bilki na kuka sosai tana rok'onsa, take ya yarda ta yi nadama don haka sai ya yafe mata suka shirya.


Haka cikin dare da Amina tayi kuka Bilki zata tashi ta bata madara har ta koma bacci, gashi sam bata kukan dare yunwa kad'ai ke tashinta da kuma an bata madara zata koma shikenan kuma sai asuba.
Da safe ma haka tayi mata wanka tas ta bata madararta, koda wasa Hamza bai yi tunanin za'a samu wata matsala ba daga wurin Bilkin ba.
Don haka sai ya saki jikinsa ya manta da maganar k'arin aure.
Duk sadda Hamza ke gida to Amina na hannunsa yana mata wasa, yana ce mata
"Meenah!" Ya bata madara, ya chanza mata pampers, ya mata tsarki, sannan ya rirriga ta har sai tayi bacci.
A haka har sunan ya bita don Hamza Meenah yake ce mata idan yana mata wasa.

Watan Meenah biyar amma ta zama wata irin k'atuwa tayi nauyi sosai, da k'yar ake d'aga ta, ga bata wasa da abinci komai ci takeyi, sai dad'a kyau takeyi kullum.
Hamza na matuk'ar nuna mata kulawa kullum yana manne da ita especially weekends ranar da ba aiki, baya zuwa ko ina zai zauna gida yana kula da Meenah. Sannan komai yana siya mata daidai gwargwado bai ta6a nuna gazawarsa ba, tsaye yake kai da fata wajen ganin Meenah ta taso cikin ingatacciyar rayuwa.

Watan Meenah bakwai daidai Bilki ta samu ciki, Allah cikin ikonshi cikin baya bata wahala, murna had'e da godiya ga Allah suka yi ba adadi.
Zo kuga zakwad'i da rawar kai wurin Bilki. Tun cikin bai tasa ba ta fara siyayyar kaya kamar hauka a 6oye, tasan Hamza zai bata kud'i idan lokacin yayi amma tsabar son abin duniya yasa bata iya hak'uri. Ko kuma ta d'auka idan ya aje da yake bai ta6a tunanin tana masa sata ba sheyasa bai farga ba, sai dai idan yaga kamar kud'in ba daidai suke ba yayi ta tunanin yadda akayi ya kashe su.


***

Faruk ne kwance bisa gadonsa na alfarma yayi ruf da ciki yana game cikin system d'insa. Sai yanzu na k'are ma d'akin nasa kallo, color d'in d'akin dark da light blue ne, hartta gadonsa blue ne da bed-sheet d'in da ke shimfid'e a sama. Carpet d'in da ke shimfid'e a d'akin blue ne. Gefe guda kuma study table ne shima blue, sai cikin wata k'atuwar box kayan wasansa ne wanda mafi yawa nafi hango jirgin wasa kala kala, hartta kan gadonsa jirgin wasa ne yakai biyar gefensa, d'aya kuma a hannunsa, a raina nace to shi kuma son jirgi yake?
 Mummy ce tsaye bakin k'ofa tana kallonsa kafin kuma ta k'araso tare da zama a kusa dashi ta dafa shi.
Juyowa yayi yana kallonta kafin yace.
"Mummy na."
Murmushi tayi tana shafa gashin kansa sannan tace
"Faruk ya naga kana game? Ba nace kazo ka koyi hardarka ba, ba gobe zaka bayar ba a islamiyya?"
Murmushi yayi yace
"Nayi Mummy."
Tace
"Anya Faruk?"
Yace
"Allah yanzu na gama."
Tace
"Ok zo muje muyi dinner Daddy da Anisah (auta 'yar shekara uku) suna jiranmu."
"Ok." Yace a yayinda ya d'auki jirginsa ya bi bayan Mummy....



MSB๐Ÿ’–

AUREN FANSA 04

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐
๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน
๐ŸŒน✨⭐✨⭐✨⭐✨๐ŸŒน
✨๐ŸŒน✨⭐๐ŸŒž⭐✨๐ŸŒน✨
⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐
✨⭐✨๐ŸŒน✨๐ŸŒน✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒŸ


๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
AUREN FANSA!!!
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

๐ŸŒนNa๐ŸŒน

     ๐ŸŒนMARYAM S BELLO๐ŸŒน
             (MSB)

๐ŸŒŸ๐ŸŒนPure Moment Of Life Writers๐ŸŒŸ๐ŸŒน


Dedicated to my Zarah Surbajo and Sadnaf๐Ÿ’˜❤️๐Ÿ’˜

          ๐ŸŒน04 ๐ŸŒน


Zuciyarsa har wani zafi take masa, kwanciya yayi kan gadonsa yana mai maida numfashi sama sama, meyasa Bilki bazata ta6a chanza halayenta ba? Yasani tun kafin suyi aure yake fama da iri iren halayenta na nuni da maita akan kud'i, sam bata gajiya da tambayarsa kud'i, ko lokacin auren su Goggo taso ta hana don sam tarbiyyar Bilki bata yi mata  ba, batada kamun kai ga shegen yawo, sai dai a lokacin yadda yake tsananin sonta baijin zai iya hak'ura da ita, a haka yayi ta lalla6a Goggo har ta amince akayi auren. Gashi sam bai iya mata fad'a idan tayi masa laifi sannan bai iya hanata kud'i idan ta tambayesa ya rasa dalilin da yasa haka. So da yawa idan ta tambayesa sai yaji kamar kar ya bata amma sam sai ya kasa haka yayi ta rayuwa da ita tana cutarsa ba tare da ya ankara ba. Gashi da anyi abu ta iya kukan k'arya kuma nan da nan sai zuciyarsa ta karaya yaji yana tausayinta, a haka ta gano lagonsa abu kad'an zata sa masa kuka.
Ajiyar zuciya ya saki tare da gyara kwanciya yanzu yasan mafita d'aya ce ya k'ara aure k'ila hakan zai sa ya gane banbancin zama da Bilkin, wata k'ila ma wadda zai aura batada halayen Bilki ya yarda ya amince zai k'ara auren, tashi yayi da niyyar shiryawa yaje ya sanar da Goggo ya shirya ko yau za'a iya d'aura masu aure, wayarsa ta fara ruri. Goggo ya gani a saman screen d'in wayar haka kawai gabansa sai da ya fad'i. A sanyaye ya d'auka gami da yin sallama, da sauri Goggo tace
"Hamza kana ina yanzu?"
Yace
"Ina gida Goggo, lafiya dai ko?"
Tace
"Babu lafiya Hamza, maza maza ka taho asibiti k'anwarka na nan na nak'uda, kuma  ta kafe tak'i shiga d'akin haihuwar wai sai ka zo, kuma ga haihuwar tazo kar ta haihu a gaban d'aki Hamza, kayi sauri don Allah."
A rud'e yace
"Gani nan yanzu wace asibiti ce?"
Tace
"Alheri clinic kayi sauri."
"To." Kawai yace ya fito da gudu daga d'akin, takalmansa ma daban daban yasa tsabar rud'u ga gabansa sai fad'uwa yakeyi. Haka dai ya daure ya figi mota ya fice da sauri, duk da asibitin batada nisa daga gidansa amma gani yake bazai isa da sauri ba. Cikin k'ank'anin lokaci Hamza ya iso Alheri clinic da gudu ya shiga ciki yana tambayar suna ina. Koda yaje hanashi shiga akayi sai da ya kira Goggo yace gashi nan sun hana shi shigowa. Da k'yar ta rok'esu suka barshi ya shigo.

Yana shiga ya iske Amina sai faman nak'uda takeyi mai zafi tana kiran sunan Hamza tana kuka. Da sauri ya isa gareta tana ganinsa ta k'ara sautin kuka tana fad'in
"Ya Hamza na gode da kazo, wata magana zan fad'a maka."
Jikinsa yayi sanyi yace
"Koma meye ay sai ki bari ki haihu tukunna..."
"Ya Hamza bazaka gane ba bazan iya bari sai na haihu ba, amma don Allah ka tsaya ka saurareni!"
Ta fad'a cikin muryar tsawa, tashi yayi ya fara safa da marwa idanunsa sun kad'a sunyi ja, yasan tatsunniyar gizo bata wuce ta k'ok'i, tabbas yasan maganar da ta saba fad'a masa yau ma ita d'in ce zata fad'a masa. Don haka sai yace
"Ko meye zaki fad'a na riga na sani, don haka ki tashi a shiga dake d'akin kar ki haihu a nan."
Duk'awa tayi tare da fasa wata irin giggitaciyar k'ara wadda bama Hamza ba har Goggo da malaman asibitin sai da suka rud'e, fad'i take
"Bazan shiga ciki ba ya Hamza sai kayi min alk'awari na k'arshe."
Da sauri ya kalleta
"Haba Amina! Meyasa kin faye kafiya ne? Ba mun gama maganar nan tun tuni ba? Meyasa kike tado zancen kuma, ki bari ki haihu zamuyi magana."
Girgiza kanta tayi tana hawaye
"Kayya ya Hamza, don Allah kayi min alk'awarin kawai."
Goggo ce ta sa baki tace
"Hamza kasan zafin haihuwa, kawai kayi mata alk'awarin a shiga da ita."
Da k'yar ya iya bud'e bakinsa yace
"Na maki alk'awari Amina, Allah ya sauke ki lafiya."
Duk da zafin nak'udar da Amina keyi ba hanata yin mumushi ba, sannan tace
"Nagode ya Hamza nagode!"
Juya mata baya yayi don bazai iya jure ganin Amina cikin wannan halin ba, a haka aka shiga da Amina rik'e da hannun Goggo wadda aka samu aka raba su da k'yar."
Goggo kuka takeyi sosai ji take kamar Amina bazata fito ba idan ta shiga. Hamza ya zo ya dinga rarrashinta har ya samu tayi shiru.

Minti kusan talatin ana abu d'aya Amina ta kasa haihuwa, har an fara shawarar ayi mata CS don da k'yar idan zata iya haihuwa da kanta. Har sun fara shawarar a sanar da 'yan uwanta Allah cikin ikonshi ta haihu. Su Hamza suna jin kukan jariri suka fara murna suna hamdala.

Jim kad'an wata sister ta fito da jariri tana zuwa su Goggo suka yo kanta, Goggo ce ta fara cewa
"Alhamdulillah! Ta haihu lafiya."
Hamza kuwa hannu yasa ya kar6i babyn yana kallo kafin kuma ya kalli nurse d'in yana murmushi sosai. Nurse d'in ce tace
"Ta haifi mace."
"Alhamdulillah!!" Shine kawai abinda suke cewa. Kafin kuma Goggo tace
"Ina ita Aminar? Ba'a gama kimtsa ta ba mu shiga?"
Nurse d'in ce tace
"Sai dai kuyi hak'uri..."
"Me kike nufi da kalamanki?" Cewar Hamza a d'an rud'e, Goggo ma ta rud'e tace
"Bamu gane abinda kike cewa ba."
Nurse d'in tace
"Abinda nake nufi shine kuyi hak'uri Allah ya amshi kayanshi, ma'ana Amina ta koma ga mahaliccinmu."
Saura kad'an Hamza ya saki d'iyar sai da nurse d'in tayi saurin amsar ta, Goggo kuwa in banda salati ba abinda takeyi kafufuwanta kasa d'aukarta sukayi ta zauna da sauri.
Hamza zaman k'asa yayi dirshen yana salati kafin kuma ya fashe da kuka kamar k'aramin yaro.
"Daman Amina tafiya zakiyi da gaske? Tasha fad'a min mutuwa zatayi na kasa yarda." Haka yayi ta sambatu kamar zautacce a yayinda Goggo ke kuka rungume da babyn.
Sai da aka fiddo da gawar Amina lullu6e cikin farin zanin gado bisa gado mai taya a lokacin kuma suka gasgata ta mutu d'in. Wurin ya kuma rud'ewa inda Hamza ya rugo ya rugume gadon yana magana da gawar Amina. Goggo na tsaye tana kuka tana tausayin Hamza, da k'yar aka 6am6are shi daga jikin gadon aka sanya ta cikin doguwar ambulance.

Hamza na tuk'i yana kuka har baya ganin gabanshi, ga kukan baby dake k'ara rud'a shi. Can gidan Goggo dake cikin G.R.A suka nufa. Suna isa aka shiga da gawar a cikin gida.
Bayan anyi ma Amina wanka an mata sutura sai kuma aka d'auketa za'a kaita makwancinta na k'arshe, gidanta na gaskiya! Hamza na ji na gani ya saka Amina cikin kabarinta, Masha Allah Amina tayi mutane don kuwa har tutse akeyi wurin sakata a makwancinta.
Bayan an gama kuma suka juyo gida inda su Hamza suka cigaba da kar6ar gaisuwa.

Itama Bilki kullum sai tazo amma bata ta6a dafo komai ba a matsayin abincin sadaka ba hasali ma sai tayi kwalliyarta take zuwa bata nuna wata damuwa ba.

A haka aka yi sadakar uku ana zaman makoki, inda Hamza ya dangana yana amsar gaisuwar kowa saidai fa baya magana sai dai yayi shiru ya k'ura ma wuri d'aya ido kamar yana tunani. Ko kuma idan akayi masa gaisuwa sai ya dad'e yana kallon mutum kafin kuma ya amsa gaisuwar.
Shikenan Amina ta tafi, mutuwa mai yankar k'auna mai raba tsakani, saidai Allah baya barin wani don wani yaji dad'i. Allah kasa mu dace, Allah kayi mana kyakkyawan k'arshe Amin thumma Amin.



MSB๐Ÿ’–

AUREN FANSA 03

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐
๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน
๐ŸŒน✨⭐✨⭐✨⭐✨๐ŸŒน
✨๐ŸŒน✨⭐๐ŸŒž⭐✨๐ŸŒน✨
⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐
✨⭐✨๐ŸŒน✨๐ŸŒน✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒŸ


๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
AUREN FANSA!!!
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

๐ŸŒนNa๐ŸŒน

     ๐ŸŒนMARYAM S BELLO๐ŸŒน
             (MSB)

๐ŸŒŸ๐ŸŒนPure Moment Of Life Writers๐ŸŒŸ๐ŸŒน


Dedicated to my darling Maman Ihsan  (SAFNA) much love darl๐Ÿ’•๐Ÿ’˜❣️

          ๐ŸŒน03 ๐ŸŒน

***

Daddare sai da Bilki ta k'ara tada masa da maganar wasu kud'in inda a ranar sai da ya yi 6ata mata rai fiye da tunaninta sannan ya nuna mata ta cika son kud'i, duk dai abubuwan da ya dad'e  dasu a ransa shekara da shekaru sai da ya amayar mata dashi, sum sum ta tashi ta koma cikin d'aki tsabar borin kunya.
Jingina yayi da kujerar parlon tare da lumshe idanu don ya samu nutsuwa sai dai bai kai ga yin hakan ba wayarsa ta fara ruri, kallon screen d'in wayar yayi yaga sunan da ya bayyana wato My sister, murmushi ya saki na tsananin farin ciki a lokaci guda kuma damuwarsa ta 6ace 6at, d'auka yayi gami da yin sallama, d'ayan 6angaren aka amsa sannan tace.
"Ya Hamza! Da fatan an wuni lafiya?"
Sai da yayi murmushi sannan yace
"Lafiya lau Amina ya gida?"
"Alhamdulillah, ya Anty Bilki?"
"Tana nan lafiya ya zafi kuma?"
"Lafiya lau ya Hamza, da fatan komai lafiya?"
Yace
"Alhamdulillah ya jiki kuma?"
Ta d'an yi murmushi kad'an sannan tace
"Alhamdulillah gashi nan muna ta fama."
Dariya yayi yace
"To Allah ya raba lafiya."
Tace
"Amin."
Sannan ta kuma cewa
"Ya Hamza akan maganar mu dai ce yasa na kira ka, kaga yanzu cikina ya shiga watan haihuwa kuma nasha fad'a maka idan na haifi babyn nan na baka shi ka rik'a..."
"Amina! Insha Allah ke zaki rik'a babynki sai dai ki dinga kawo min shi hutu."
Tayi murmushi mai bayyana hak'ora sannan tace
"Ya Hamza na kenan, yaya na na kaina, nidai kayi min alk'awarin rik'a abinda zan haifa koda bayan raina ne, shine kad'ai burina a halin yanzu."
Haka kawai sai yaji gabansa ya fad'i cikin firgici yace
"Kinga Amina, nasha fad'a maki mutuwa lokaci ne kuma insha Allah zaki ga abinda zaki haifa har ma ki shayar da shi ki daina fad'in maganganu haka ba dad'in ji."
Tayi dariya
"Ya Hamza mutuwa fa na kan kowa sanin gaibu sai Allah nidai alk'awari na zaka rik'e min kaji?"
Nannauyan numfashi ya saki sannan ya d'ora
"Naji shikenan are you happy now?"
"Yeey! Allah ya bar mana kai ya Hamza, nagode!"
Dariya yakeyi sosai itama tana taya sa, sanann ya kawar da wancan zancen ta hanyar jefo mata tambaya
"Ya kingama rubuta list d'in abubuwan da kike buk'ata?"
Tace
"Eh na gama ya Hamza yana hannun Goggo na bata."
Yace
"Ok zan kar6a insha Allah sai na ga abinda za'a siya."
Tace
"Toh ya Hamza Allah ya k'ara bud'i."
Sai da suka d'an ta6a fira kad'an sannan sukayi sallama ko wane yana mai farin cikin ganawa da d'an uwanshi.

Amina k'anwar Hamza ce uwa d'aya uba d'aya, bayan nan kuma su kad'ai ne Goggo ta haifa bayan Amina sai haihuwar ta tsaya, tunda ta haifi Hamza sai bayan shekara kusan bakwai sannan ta haifi Amina, kasancewar su biyu ne kacal yasa suka shak'u da juna sosai Hamza na son Amina  kuma yanaji da ita, kullum suna mak'ale da juna tun suna yara har kawo yanzu da aure ya rarraba su kuma, amma kusan kullum sai sunyi waya.
Amina tasha ci ma Bilki mutunci akan halayanta da take nuna ma Hamza saboda bazata iya jure ganin d'an uwanta cikin bak'in ciki da k'unci ba. Mijinta ya rasu tun tana da ciki wata biyar Allah ya amshi ransa, ga bashi da uwa bashida uba haka ma shi kad'ai ne mahaifiayarsa ta haifa, bayan rasuwar tasa ta zauna nan gidanta da ke cikin garin Katsina a G.R.A.
Wannan kenan!


***

        BAYAN 'YAN KWANAKI

Yau weekend ne Hamza baya zuwa aiki don haka yana gida yana hutawa, bayan ya gama waya da Amina kamar kullum Bilki ta shigo cikin shirin fita unguwa ta sha ado sosai tana ta zuba k'amshi. A hankali yake binta da kallo kafin kuma ya sauke su kan shigar da tayi. Sanye take da wata silky doguwar riga mai dogon hannu kalar brown an mata aikin duwatsu ba laifi rigar ta kamata sai ta yafa gyalen kayan. Haka ma takalminta mai tsini ne kalar kayanta da jaka kalar kayan. Har tazo ta zauna bai bar kallonta ba cike da mamaki, Bilki tace.
"Hamza zan fita."
Ya kalleta da mamaki yace
"Ina zakije?"
Ta had'e rai
"Gidan Hajiya Laila."
Shima ya had'e rai
"Ba inda zakije."
Ta mik'e zumbur!
"Me kace?"
Yayi banza da ita, ta rik'e k'ugu tana sassarfa masifa
"Hamza! Gaskiya ka takura min haka kawai! Kuma ay dah ba haka kake ba wannan k'anwarta taka duk ta zuge ka."
Tashi yayi a fusace yana nuna ta da yatsa
"Kar ki k'ara saka Amina a cikin zancen mu saboda babu ruwanta, kina ji na?"
"Ahayye nanaye, an ta6o masa rabin rai, to an fad'a Amina ce ke zuge ka kayi abinda zakayi."
Bai san lokacin da ya d'auke ta da mari ba yace
"Kisani ni mijinki ne, kuma nafi k'arfin ki wulak'anta ni, sannan wallahi kika k'ara fad'in magana makamancin wannan a bakin aurenki!"
Ta zaro idanu waje
"Iyye! Kan mage ya waye, lallai Hamza yanzu kayi baki, amma tunda ka mare ni don na fad'i gaskiya shikenan kaje Allah zai saka min."
Yace
"Nidai na fad'a miki ki iya bakinki, kuma fita bazakiyi ba ay inace dai sai na bada izini ko? To mugani idan kin isa!"
Har ya tafi ya dawo yace yana mata mugun kallo.
"Magana ta k'arshe ina so ki sani aure zan k'ara na gaji da zama da mace irinki wadda batasan inda duniyar ta dosa ba, na aure ki don ina tsananin sonki amma kisani dole zan k'ara aure."
A fusace ta cakumo masa wuyan riga kamar kura taga nama.
"Aure Hamza! Baka isa kayi min kishiya ba, ni kad'ai ce babu k'ari!"
Yayi dariya gami da cire mata hannu daga rik'on da tayi masa sannan yace
"Kin isa ne ki hana? Ay baki isa ba aure kamar anyi ne an gama."
Yana gama fad'in haka yayi shigewarsa d'aki ko kallonta baiyi ba. Yana jin ihuta tana fad'in
"Wallahi babu wacce ta isa ta shigo min gida ta zauna lafiya, wallahi koma wacece sai na kashe ta!!!"



MSB๐Ÿ’–

AUREN FANSA 02

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐
๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน
๐ŸŒน✨⭐✨⭐✨⭐✨๐ŸŒน
✨๐ŸŒน✨⭐๐ŸŒž⭐✨๐ŸŒน✨
⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐
✨⭐✨๐ŸŒน✨๐ŸŒน✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒŸ


๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
AUREN FANSA!!!
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

๐ŸŒนNa๐ŸŒน

     ๐ŸŒนMARYAM S BELLO๐ŸŒน
             (MSB)

๐ŸŒŸ๐ŸŒนPure Moment Of Life Writers๐ŸŒŸ๐ŸŒน

Dedicated to Ummi Aisha and Zeebee๐Ÿ’˜

          ๐ŸŒน02 ๐ŸŒน


"Daman nasan bazaka amsa ni ba Hamza, kuma ni har ga Allah bazan maka dole ba. Sai dai kana buk'atar kaje kayi tunani sosai akan maganar, idan kana da ra'ayin aure to zaka iya yi, idan kuma bakada shi babu damuwa."
Shiru yayi yana nazari, yana son faranta ma mahaifiyarsa rai sannan bayason tashin hankalin Bilki, don haka sai ya k'ak'alo murmushin dole yace.
"Goggo zan je inyi shawara da Bilki kome kenan zan zo na sanar dake."
Murmushi tayi tace
"Allah ya nuna mana."
Yace "Amin."
Bai bar gidan ba sai wurin tara ta wuce na dare, gida ya wuce kai tsaye. Yana shiga ya wuce d'akinsa yayi wanka ya sanya kayan bacci ya fito parlor.
Bilki na zaune tana latsa waya tana kallon wani American series, jin alamun shigowa yasa ta kalleshi lokaci guda kuma tace
"Har ka dawo?"
Yace
"Na dawo." A lokacin da yake zama kan kujera yana gyara zaman glass d'in idonsa. Matsowa tayi kusa dashi tare da kwantawa bisa k'irjinsa. Dukansu kowa yayi shiru kafin Bilki ta katse shirun nasu
"Hamza, wai ya maganar mu ne?"
Yace
"Wace magana kenan?"
Ta zum6uro baki tace
"Ba dai har ka manta ba?"
Yayi shiru tabbas yasan maganarta bata wuce tana son kud'i.
Tayi murmushi tana mai kashe murya had'e da shagwa6a tace
"Kace zaka bani kud'i naje Dubai mana saro kaya."
Shiru yayi gami da sauke nannauyan numfashi yace
"Bilki kenan, ay mun gama wannan maganar tun rannan kuma nace zan baki, sai dai ba dole sai kinje ba yanzu ay inace sautu ake badawa kuma bama haka ba, ina k'awarki da ke yawan zuwa basai ki bata ba ta kawo maki."
Ba haka taso amma ya zama dole ta lalla6a shi don haka sai tace
"Duk d'aya ay kuma bakomai sai na bata d'in nawa zaka bani?"
Yace
"Zan baki dubu 100 ki fara da ita daga baya sai na k'ara maki."
Da sauri ta tashi zaune
"Dubu d'ari kuma? Ni gaskiya ta mani kad'an."
A fusace ya tashi tsaye yace
"Toh idan har bakiso gaba d'aya a barshi mana, ya zan baki ki raina? Gskiya ki chanza halinki."
Daga haka ya tashi ya shigewarsa d'aki yayi kwanciyarsa maganar auren da basuyi ba kenan don ya fusata.

Washe gari ta kama Monday, kamar kullum ya tashi ya shirya kasancewar aikin banki yake yasa tun asuba idan ya tashi baya komawa bacci.
K'arfe bakwai daidai ya kimtsa ya fito daman baya jiran breakfast don Bilki bayi takeyi ba, a hanzarce yake komai tashinta yayi daga bacci ya ce mata zai tafi aiki, juyi d'aya tayi tashi tace masa "Toh" sannan ta ja bargo ta rufe har kanta. Girgiza kansa yayi ya shiga motarsa ya harba titi.
Wani shop ya tsaya ya sayi bread da yoghurt sai lemo sai kuma kayan tea da biscuit don na office d'insa sun k'are, daman ya kan aje saboda ko yaji yunwa sai yaci kawai.
A haka ya isa office d'insa ya soma aikinsa kamar kullum. Haka ya wuni yana juya maganar Goggo a ransa yanata sak'e sak'e, haka dai yake sukuku dashi har lokacin sallah sannan ya tashi ya fice tare da sauran abokanan aikinsa musulmai.

Kamar kullum yau ma sai kusan k'arfe 6 ya diro gida, gajiya kam ya gaji ba kad'an ba ga yunwa data addabe shi ga uwa uba ana zafi agarin.
Yana shiga gida ya ci karo da Bilki a bakin k'ofa taci ado tayi kwalliya na fitar hankali ga gidan sai k'amshi ke tashi. Taro sa tayi bakin k'ofa tana mai aika masa da sak'koni ta ko wane fanni, a hankali ya ture ta yace
"Kinga Bilki na gaji bari naje na fara watsa ruwa kafin lokacin sallah yayi."
Murmushi tayi ta sake sa sannan ta koma parlor ta zauna tana binsa ta kallo har ya shige d'akinsa.
Sai da ya kimtsa ya fito sannan ya wuce kitchen don neman abinda zaici. Tana kallonsa ya fito da cup d'in tea da biscuit a hannunsa ya zauna kan dinning yaci. Sai da ya kammala tazo ta zauna a kusa dashi tana yatsina baki tana wani yanga da kwarkwasa. Can kuma tace
"Alhaji."
Bai kalle ta ba yace
"Na'am."
Tace
"Alhaji daman k'awata zatayi bikin k'anwarta shine nake so ka bani kud'i na bata guddumawa ta..."
Da sauri yace
"Haba Bilki daga dawowata zaki tare ni da zancen wasu kud'i ay sai ki bari na huta dai ko?"
Murmushi tayi tace
"Haba Alhaji duk bai kai ga tashin hankali ba ka huta sai muyi magana."
Bai k'ara magana ba illa tashi da yayi ya fita don yaga lokacin sallar magriba ta gabato.


***


"Mummy!" Yaro d'an kimanin shekara goma ya rugo da gudu, Maman tasa na zaune kan wata irin makekiyar kujera tana duba magazine da glass d'in karatu a idanunta. A hankali ta d'aga ido ta kalli yaron da ke ta gudu kafin kuma ya haye bisa cinyar ta yana mai hugging d'inta. Itama hugging d'insa tayi tana kallonsa cike da so tace.
"Lafiya ka shigo da gudu haka FARUK?"
Yaron da ta kira da Faruk yana mai tsananin murmushi kafin ya rufe baki wani babban mutum dogo fari ya shigo yana sanye da kayan hausawa harda babbar riga, sai da yazo daidai bakin k'ofar da zata sadasa da parlon yaja ya tsaya yana murmushi, sannan kuma yace.
"Ay Faruk ya d'auko grade mai kyau, sannan ya lashe baki gaba d'aya wato overall as always."
Dukansu suka d'aga ido suka kalli mutumin dake tsaye ya hard'e hannayensa biyu yana murmushi.
Matar da aka kira da Mummy ta rungume Faruk sosai a jikinta tace
"That's my boy, haka nake so Allah ya k'ara maka basira, toh saura na Islamiyya, idan har kayi k'ok'ari shima akwai kyautar dana tanadar maka ta mussaman."
Cike da jin dad'i Faruk yace
"Allah Mummy?"
Tace
"Kayi ka gani I promise."
Mutumin dake tsaye ya tako ya shigo parlon, kusa da kujerar dasu Faruk ke zaune ma'ana doguwar kujera, sai da ya cire babbar rigarsa sannan ya zauna yana shafa kan Faruk yace.
"My boy aje a cire uniform ayi wanka ko sai kazo muci abinci."
Faruk yace
"Ok Daddy."
Sannan ya tashi da gudu ya shige d'akinsa.
Matar da ke zaune kusa dashi mai suna Reemah wadda na k'are ma kallo kyakkyawar gaske ce fara mai yalwar gashi don kuwa har gaban goshinta ya fito. Bana tantama ta had'a iri da larabawa. Kamo hannun mutumin tayi mai suna Adam tace
"Muje ka watsa ruwa kaci abinci ko?"
Murmushi yayi yana jin son matarsa na k'ara fizgarsa sannan yace
"Muje sahibata."
Murmushi tayi sannan suka mik'e a tare suka nufi kan bene inda hannunsu na mak'ale da na juna...



MSB๐Ÿ’–

AUREN FANSA 01

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน⭐
๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน⭐✨⭐๐ŸŒน
๐ŸŒน✨⭐✨⭐✨⭐✨๐ŸŒน
✨๐ŸŒน✨⭐๐ŸŒž⭐✨๐ŸŒน✨
⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐
✨⭐✨๐ŸŒน✨๐ŸŒน✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐ŸŒน✨⭐✨๐ŸŒŸ


๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
_AUREN FANSA_!!!
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

๐ŸŒนNa๐ŸŒน

     ๐ŸŒนMARYAM S BELLO๐ŸŒน
             (MSB)

๐ŸŒŸ๐ŸŒนPure Moment Of Life Writers๐ŸŒŸ๐ŸŒน

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM!
Wannan shafin tukuci ne gareku members na pure moment...!

FATY AXLAND SUHANA JANNART,  AUNTY KHADY, HUSNAH, DEEJA WAZIRI, ZEE YABOUR, UMMUHANEEF, MOMYN SULTAN, UMMYN YUSRAH, ZARAH SURBAJO, MOMYN KHADIJA, UMMA YAHYA MUSA (SISIN MAMA), BIEBIE DEE, NANA FA'AD,
 FAtY MANSUR (XARAH), FATY KHALID NA SHUKA, SHAFA ABDUL, SUMYNBASH, SALMA ALI WADA, ROOKY KAZ, AISHA ALI GARKUWA, UMMI HAMBALI, UMMEE GARKUWA, RUFAIDA YUSUF, HAFSAT MUSA, SADNAF, FHARIEEDAT, RAFEE'AT, SAMRAH, BIBA WADATA, SEEMALUV, NEERATU LUV, AYSHA HANWA, AYSHA GANA, UMMU SAFWAN, DELU CHOGAL, MRS FAWWAZ
(YESMEN TAFEESU), RAFI'AT DIKKO, MAMAN IHISAN.❤️๐Ÿ’–๐ŸŒน

          ๐ŸŒน01 ๐ŸŒน


Sautin kuka ne ke tashi a cikin d'akin, daga jin mai yin kukan har cikin ranta takeyin shi,  wanda zan iya cewa koma dai menene, ta dad'e a haka, don kuwa idanunta sunyi jajir sannan fuskarta ma tayi ja saboda farar mace dama idan tayi kuka fuskarta ta kanyi ja.
A hankali aka turo k'ofar d'akin aka shigo, daga bakin k'ofa yaja ya tsaya yana k'are ma  matar tasa kallo a lokaci guda kuma yana girgiza kansa cike da takaici. Sai da yaja numfashi ya had'iye 6acin ransa sannan ya soma takowa a hankali har yazo daidai bakin gadon da matar tasa ke kwance tana kukan fitar rai.
A hankali ya dafa ta had'e da kiran sunanta cikin wata irin sigar rarrashi.
"Hajiya Bilki."
Bata d'ago ba amma ta dakatar da kukan da takeyi hakan ya nuna cewa taji kiran mijin nata.
A hankali ya soma magana.
"Haba Hajiya Bilki, dama ace bazaki iya d'aukar kaddara ba? Har ki zauna kina kuka saboda Allah ya jarabe mu? Haba Bilki! Kin bani mamaki wallahi."
Shi d'inma k'arfin hali kawai yakeyi amma zuciyarsa ta raunana!
Tashi tayi zaune gami da share hawayen fuskarta tana fuskantar mijin nata da har yanzu yake tsaye bai zauna ba. Sannan itama ta soma magana cikin 6acin rai.
"Don Allah Alhaji ka barni, na gaji da wa'azain nikam gaskiya hak'uri na ya k'are haba! Ta yaya za'ayi ace mun shekara akalla sha biyu da aure amma duk shekara sai nayi 6ari? Meyake faruwa ne? Ka duba fa ka gani kaf danginka bak'ina suke gani gaba d'aya sun tsane ni sun sa min ido! Abin ya fi d'aga min hankali sai jiya da muka je sunan gidan Hajiya Karima bakaga yadda ake nuna ni ba! Gaba d'aya na zame musu tamkar wata mujiya haba!"
Ta k'arashe tana cigaba da kuka. Alhaji ya runtse idonsa yana mai jin rad'ad'i a cikin zuciyarsa, tabbas yasan haka maganar take sai dai kuma yasan basufi k'arfin Allah ya jarabe su da rashin haihuwa ba, shi ya d'auki hakan a matsayin kaddara. Don haka sai ya nutsu ya fara magana.
"Hajiya Bilki a kullum bazan gaji da fad'a miki ba Allah ubangijinmu mai baiwa ne sannan mai hikima ne, kar ki manta ke d'in baiwarsa ce sannan duk yadda yaga dama yayi dake haka zaiyi dake, Allah yayi miki baiwa da yawa ba dole sai kin samu haihuwa
zakiji dad'in rayuwarki ba, ki gode masa da ya baki kyau, arzik'i ya wadata ki
da lafiya, sannan uwa uba ya barki da ranki, har akwai abinda yafi wannan jin dad'i a rayuwa?"
Gwauron numfashi ya saki tare da zama a kusa da ita yana kallon cikin k'wayar idonta sannan ya cigaba da magana.
"Haihuwa ta Allah ce, idan yaga dama zai baki idan kuwa bai ga dama ba duk dabararki bazai baki ba, duk yanayin da kika tsinci kanki kamata yayi, ki d'aga hannunki sama ki gode masa sannan ki rok'e sa gafara da rahama.
Wad'annan maganganun nasha fad'a miki su ba tun yau ba amma naga kamar ta iske suke bi. Wallahi ki nutsu kar garin garajenki kije kiyi sa6o, kina jina?"
Ta d'aga kanta a hankali yayin da ta sa yatsanta ta share hawayenta. Yayi murmushi irin nasu na manya yace.
"Bilki duk ba wannan kizo ki bani abinci yunwa nakeji."
Ta6e baki tayi tace
"Kayi hak'uri na manta ban girka ba."
Yayi murmushi yace
"Bilki kenan ya za'ayi mijinki ya fita aiki tun safe amma ya dawo gidansa abincin ci ya gagare shi?"
Tace
"Haba Alhaji! Yau sati na d'aya fa dayin 6ari ya kamata ka barni na huta mana."
Inda sabo ya saba da halin Bilki amma da yake Allah ya zuba masa hak'uri sai kawai yayi murmushi yace
"Haka ne Allah ya baki lafiya."
"Amin" kawai tace yayinda ta koma ta kwanta gami da bashi baya. Tashi yayi ya fice daga d'akin yana mai jinjina hali irin na Bilki.

D'akinsa ya fad'a kai tsaye yayi wanka yana fitowa ya zumbula jallabiya fara ya fito ya nufi kitchen, fura da nono ya had'a mai yawa ya dawo parlor ya zauna had'e da kunna T.V yana kallon tashar Aljazeera. Sai da ya gama shan furar tas sannan ya koma ya kwanta tare da lumshe idanu a lokaci guda kuma ya fad'a kogin tunani a haka har bacci ya sace sa.

Awarsa biyu daidai ya farka ya duba agogon da ke mak'ale a bangon hannunsa, k'arfe 4:19pm, zumbur ya mik'e yaje yayi alwala yayi sallah, bayan ya kammala kansa tsaye ya wuce d'akin Bilki tana kwance kan gado tana latsa waya, kiranta  yayi a hankali.
"Bilki." Tana taunar chewing gum sai da yayi k'ara k'as sannan ta d'ago ta kalleshi tace
"Na'am." Ajiyar zuciya ya sauke ya fara magana fusakarsa ba annuri ko kad'an.
"Yanzu kina ganin bacci ya kwashe ni amma har lokacin sallah ya wuce ki kasa tashi na inyi sallah?"
Tace
"Kayi hak'uri na manta ne."
Girgiza kansa yayi yace
"Allah ya kyauta, zan fita daga can zan wuce na gaida Goggo (mahaifiyarsa) sai na dawo."
Ko kallonsa batayi ba tace
"To sai ka dawo, daga nan ka siyo man nama mana."
Fita yayi daga d'akin yaje ya sake yin wanka ya shirya cikin farin yadi kalar kunun kanwa marar nauyi ya fice daga gidan.

Sai da akayi sallar magriba sannan ya wuce gidan Goggo dake cikin Layout a garin Katsina, yana shiga ya fad'a d'akinta kamar yadda ya saba bayan sun gaisa tasa aka kawo masa tuwon masara miyar kuka da man shanu ya ci ya k'oshi ya kora da fura. Nan suka d'an ta6a fira kamar kullum sannan ta soko masa zancen da kullum baya son shi.
"Ya maganar aure Hamza?"
Yayi dum ya kasa cewa uffan, tabbas shima yana son k'ara auren sai dai kuma yana gudun tashin hankalin Bilki, don haka bai ce komai ba kansa dai na k'asa.


MSB๐Ÿ’–