Tuesday, 27 June 2017

AUREN FANSA 05

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     🌹MARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹

Dedicated to mairo😜 aka Maryam Gafai I heart you sis❤️ and my sisi Ammin SS 😘😘😘


          🌹05 🌹


BAYAN KWANA BIYU

Ranar suna yarinya taci sunan mamanta marigayiya Amina, daman bawani taron sunan da akayi wane taro ma ana zaman makoki?
Amina duk da tana jaririya Allah ya zuba mata hak'uri ga bata kuka sosai sai dai idan taji yunwa ko wani abin na damunta. Kammaninta sak na mahaifiyarta ta d'ebo hartta gashinta irin nata ne lub lub, hasken ne kawai bata d'ebo ba sa6anin marigayiya da take fara tas kamar yayanta Hamza amma Amina babyn ita ba fara bace tas, sai dai tana da kyau duk da batada hasken ana ganin kyawunta. Idan ta bud'e ido ta kalli mutum zaka gansu manya ne farare tas!

Baya 'yan kwanaki a lokacin Amina ta kwana 20 cif a duniya Goggo ta kira Hamza da Bilki gidanta akan cewa tana son magana dasu.
Bayan sun iso suka gaisa Goggo ta d'auko Amina dake kwance kan gado tana bacci, ta mik'a ma Hamza ita tana murmushi tace
"Hamza kamar yadda kasani marigayiya ta baka amanar rik'on Amina kuma ka d'auki alk'awarin haka, don haka yau na damk'a maka Amina a matsayin d'iyarka halak malak, da fatan zaka rik'e ta bisa amana."
Sai kuma ta juyo ta kalli Bilki tace
"Bilkisu ga amanar Amina nan ki rik'e ta amana saboda kar ki manta marainiya ce gaba da baya idan har kika ci zalinta Allah zai mata sakayya."
Hamza yace
"Insha Allah Goggo kar ki damu ina k'auanar Amina kamar 'yar dana haifa haka nake jinta a raina. Insha Allah zamu rik'e ta amana, Allah ya taya mu rik'o."
Goggo tace
"Amin, daga cikin dukiyar da mahaifinta ya bar mata a ciki ake siya mata su pampers da su madara, sai kayan sawa da sauran abinda ba'a rasa ba, amma ba kasafai nake amfanin da kud'in ba sai idan ba kud'i hannuna, amma tunda yanzu zata dawo hannunku da zama sheyasa zan damk'a maka kud'inta a hannunka ka adana mata ko ka juya mata su duk yadda kaga ya dace."
Jiki a sanyaye Hamza yace
"Insha Allah Goggo."
Daga haka Goggo ta tashi ta had'o kayan Amina tas sannan ta kira mai gadinta ya saka cikin mota.
Sai da suka ci abincin rana sannan suka koma gida, inda ko a mota Bilki ce ta rik'e Amina sannan ga mamakin Hamza bata nuna komai ba har rungume ta tayi tana fad'a ma Hamza d'iyar ta shiga ranta sosai. Ba k'aramin sanyaya mishi zuciya hakan yayi ba, duk wata fargaba dake ransa ta kau yadda yaga Bilki na tarairayar Amina kamar 'yar cikinta.

Bayan sun koma gida da daddare Bilki ta had'a ruwan zafi tayi ma Amina wanka tas sannan ta shirya ta cikin kayan baccinta wato overall pink wadda tayi mata kyau, gashin babyn ya wani yi irin pam d'innan sannan duk da haka a nannad'e yake gwanin kyau.
Bayan ta gama ta had'a mata madararta ta bata tasha ta k'oshi, sannan ta rirrigata ta tayi bacci, duk akan idon Hamza wanda yake mata kallon mamaki, abinda baiyi zato ba yau gashi Bilki nayi.
Bayan ta rirriga Amina tayi bacci zuwa tayi kusa da Hamza tana rok'on gafarar abubuwan da ta masa, bai gasgata ba sai da ya ga Bilki na kuka sosai tana rok'onsa, take ya yarda ta yi nadama don haka sai ya yafe mata suka shirya.


Haka cikin dare da Amina tayi kuka Bilki zata tashi ta bata madara har ta koma bacci, gashi sam bata kukan dare yunwa kad'ai ke tashinta da kuma an bata madara zata koma shikenan kuma sai asuba.
Da safe ma haka tayi mata wanka tas ta bata madararta, koda wasa Hamza bai yi tunanin za'a samu wata matsala ba daga wurin Bilkin ba.
Don haka sai ya saki jikinsa ya manta da maganar k'arin aure.
Duk sadda Hamza ke gida to Amina na hannunsa yana mata wasa, yana ce mata
"Meenah!" Ya bata madara, ya chanza mata pampers, ya mata tsarki, sannan ya rirriga ta har sai tayi bacci.
A haka har sunan ya bita don Hamza Meenah yake ce mata idan yana mata wasa.

Watan Meenah biyar amma ta zama wata irin k'atuwa tayi nauyi sosai, da k'yar ake d'aga ta, ga bata wasa da abinci komai ci takeyi, sai dad'a kyau takeyi kullum.
Hamza na matuk'ar nuna mata kulawa kullum yana manne da ita especially weekends ranar da ba aiki, baya zuwa ko ina zai zauna gida yana kula da Meenah. Sannan komai yana siya mata daidai gwargwado bai ta6a nuna gazawarsa ba, tsaye yake kai da fata wajen ganin Meenah ta taso cikin ingatacciyar rayuwa.

Watan Meenah bakwai daidai Bilki ta samu ciki, Allah cikin ikonshi cikin baya bata wahala, murna had'e da godiya ga Allah suka yi ba adadi.
Zo kuga zakwad'i da rawar kai wurin Bilki. Tun cikin bai tasa ba ta fara siyayyar kaya kamar hauka a 6oye, tasan Hamza zai bata kud'i idan lokacin yayi amma tsabar son abin duniya yasa bata iya hak'uri. Ko kuma ta d'auka idan ya aje da yake bai ta6a tunanin tana masa sata ba sheyasa bai farga ba, sai dai idan yaga kamar kud'in ba daidai suke ba yayi ta tunanin yadda akayi ya kashe su.


***

Faruk ne kwance bisa gadonsa na alfarma yayi ruf da ciki yana game cikin system d'insa. Sai yanzu na k'are ma d'akin nasa kallo, color d'in d'akin dark da light blue ne, hartta gadonsa blue ne da bed-sheet d'in da ke shimfid'e a sama. Carpet d'in da ke shimfid'e a d'akin blue ne. Gefe guda kuma study table ne shima blue, sai cikin wata k'atuwar box kayan wasansa ne wanda mafi yawa nafi hango jirgin wasa kala kala, hartta kan gadonsa jirgin wasa ne yakai biyar gefensa, d'aya kuma a hannunsa, a raina nace to shi kuma son jirgi yake?
 Mummy ce tsaye bakin k'ofa tana kallonsa kafin kuma ta k'araso tare da zama a kusa dashi ta dafa shi.
Juyowa yayi yana kallonta kafin yace.
"Mummy na."
Murmushi tayi tana shafa gashin kansa sannan tace
"Faruk ya naga kana game? Ba nace kazo ka koyi hardarka ba, ba gobe zaka bayar ba a islamiyya?"
Murmushi yayi yace
"Nayi Mummy."
Tace
"Anya Faruk?"
Yace
"Allah yanzu na gama."
Tace
"Ok zo muje muyi dinner Daddy da Anisah (auta 'yar shekara uku) suna jiranmu."
"Ok." Yace a yayinda ya d'auki jirginsa ya bi bayan Mummy....



MSB💖

No comments: