Tuesday, 27 June 2017

AUREN FANSA 08

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     🌹MARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹


Another page for my Ummi Aisha thanks for all the support and care one love dear💖Allah ya k'ara basira Amin🌹


          🌹08 🌹


Laila ce ta cigaba da magana.
"Ko dai har yanzu baki fahimta ba ne?"
Ajiyar zuciya Bilki tayi, sannan tace
"A gaskiya Laila ban iyawa, kisa fa kika ce? Don ina son dukiya sai akace na kashe su, gaskiya mu chanza shawara dai."
Laila tayi kwafa.
"To sai akace mu zamu bisu mu aikata k'udirinmu? Ko kusa ba haka nake nufi ba, abinda nake nufi a nan shine..."
Nan naga ta rad'a mata wata magana daga k'arshe dukkansu suka kwashe da dariya.
Bilki tana dariya tace
"Shegiyar gari, lallai Laila sai dai a barki amma ke shu'uma ce wallahi."
Hajiya Laila ta k'yalk'yale da dariya sosai sannan tace
"Kema haka."
Bilki ta tashi tana gyara zaman d'ankwalinta tana kallon Laila tace
"Kamar naji kuman Zarah bari na dubo ta."
Laila tace
"Yi sauri kuwa nima naji."
Jim kad'an sai ga Bilki ta shigo da Zarah a hannunta da alama yanzu Zaran ta tashi daga bacci, tana zuwa Laila ta mik'a hannu ta fara mata wasa, can sai ga Meenah ta fito da alama bacci ta tashi don kuwa kanta buzu buzu yake, saboda yanayin gashinta mai cika kuma ga tsawo sheyasa ko ya ta kwanta sai yayi buzu buzu. Zuwa tayi kusa da Bilki tana murza idanu. Su kuwa sai faman ta6e baki sukeyi. Meenah tace
"Maama wunwa."
Laila ta ta6e baki tace
"Uban me tace?"
Bilki tace
"Ohon mata, ke tafi can ki bamu wuri."
Abinka ga yaro da ba ganewa tayi ba, sai ma ta matso kusa da Bilki ta jingina da ita. Da sauri Bilkin ta hankad'e ta gefe ta fad'i k'asa tim!
"Wannan yarinya anyi mayya! Mts." Cewar Laila had'e da jan tsaki.
Bilki ta jawo hannunta da k'arfi, Meenah ta fashe da kuka.
Kitchen suka nufa ta had'a mata tea a cup tana tsaki sannan ta dire mata k'asa.
"Oya zauna kisha yarinya bata aje komai ba sai ci? Haba!" Nan ta zauna ta shanye tas sannan ta fito daga kitchen d'in.
Tana gama fad'an haka ta fice taje ta had'o ma Zarah cereal ta koma parlor, Laila ke bata har ta kammala sannan aka bata ruwa.

A tare suka girka abincin rana inda Laila tayi ma Zarah wanka, sannan suka dafa fried rice da papered chicken sai had'ad'en salad.   Wuraren uku da kwata Laila tayi sallama da Bilki ta tafi gida.
Sai wurin biyar saura sannan Bilki tayi ma Meenah wanka ta bata abincin rana.

Kamar kullum bayan Alhaji ya dawo gida yayi wanka yaci abinci, suka zauna palor suna 'yar fira kafin a kira sallar magrib. Kasancewar Meenah batasan dawowar Baban nata ba, tana can d'aki tana wasa.  Sai data fito, aiko tana ganin shi ta rugo da d'an gudunta ta zo kusa da shi tana fad'in
"Dada!"
Cike da jin dad'i Alhaji yace
"D'iyar Dada ashe ana ciki, zo nan."
Tana zuwa ya d'auke ta ya zaunar kan cinyarsa yana mata surutu tana dariya. Can kuma sai tace
"Dada kaga Maama ta bije ni d'azu."
Ya ware idanu
"Me kikayi wa Maama ta bige ki?"
Tayi shiru tana kallonsa can tace
"Bakomai."
Bilki ta taso tana dariya tace
"Kai yaro ma dai daban ne, d'azu ne fa na shiga wanka nazo na iske ta tana zubar da madara, shine fa nace mata kar ta k'ara. Alhaji yayi dariya
"Ah ah Meenah a daina 6arna ba kyau kinji ko? Idan Maama tace a daina a daina kinji?"
Ta gyad'a kai. Sai kuma yace
"Bilki ya naga Meenah ta rame ne ko bata son cin abinci?"
Tayi dariya tace
"Ay Alhaji inda kasan yadda nake da fama da yarinyar nan akan taci abinci ko? Sai kayi mamaki sam batason ci na rasa dalili."
Yace
"To kuma ya baki sanar dani ba? Muka sani ko wani abin ke damunta? Kinsan yaro tunda ba fad'a zatayi ba."
Tace
"To k'ila dai."
Ya juyo da dubansa ga Meenah
"Haba Meenan Dada, meyasa baki cin abinci?"
Nan ma shiru. Yayi murmushi
"Zaki sha ice cream?"
Nan take da washe baki tana murna. Shima yaji dad'i yace
"Yauwa to bari idan na fita yanzu kafin na dawo gida zan siyo maki harda biscuit ma."
Saukar da ita yayi daga cinyarsa yace
"Bilki bari na wuce masallaci lokacin sallah yayi sai na dawo."
Tace
"A dawo lafiya."
Sai da ya fita ta bishi da harara dashi da Meenah dake tsaye a tsorace gaban Bilki.
Tana huci tace
"Gaskiya abinnan ya fara isa ta, sai wani nan nan yake da yarinyar nan amma naga ba ruwanshi ma da Zarah, lallai Alhaji ka haifi d'iya a cikinka amma ka nuna son d'iyar wata? To da sake mts."
Daga nan ta shige d'aki, Meenah na tsaye tana zare idanu.

Haka kuwa akayi Alhaji da zai dawo sai da ya tsaya ya siya ma Meenah ice cream da biscuit sai ya k'aro mata kayan lashe lashe na yara. Zarah kuwa wani d'an abin wasa ne na yara ya siya mata tunda yasan bata isa shan wad'annan kayan ba.
Yana dawowa Meenah ta tare shi tana murna, ya bata ice cream d'inta nan ta zauna ta shanye tas sannan ya bata biscuit d'inta ta tafi d'aki.
Abin wasan yara ya bama Zarah dake hannunsa yana mata wasa. Ita kuwa sai dariya takeyi. Bilki na zaune kusa dasu tana wasa da Zarah. Can Alhaji yace
"Ina Meenah tayi ne?"
Tayi tsaki a ranta tace
"Yanzu ta tafi d'aki ay ta ga k'wad'ayi kuma tunda bazata ci abinci ba."
Tashi yayi yana fad'in
"Ina zuwa."
Ta6e baki tayi tana mai jin haushin Meenah.
Yana shiga d'aki ya ishe Meenah kwance k'asa da biscuit a hannunta bacci ya kwashe ta. Murmushi yayi ya d'auko ta ya d'ora ta kan gado, ya gyara mata kwanciya sannan ya kashe fitilar ya fito.
Koda ya fito Bilki bata nuna komai ba, Zarah ta k'ar6a tayi d'aki da ita don yi mata wanka.

BAYAN KWANA BIYU

Bilki ta fito wanka da safe kiran Laila ya shigo, tana d'auka Laila tafara magana
"Kash Hajiya Bilki yanzu naji labarin iyalen Alhaji Adam sun koma Abuja gaba d'aya."
Da sauri Bilki tace
"Haba dai? To yanzu ya kenan?"
"Bansani ba nima, plan d'inmu ya rushe don gidansa na Abuja akwai tsaro sosai, ko ina sojoji ne a gidan."
Bilki tace
"Gaskiya akwai had'ari mu ce zamuyi wani motsi yanzu. Amma ki bari tukunna a sake shawara."
"To shikenan." Laila tace tare da katse kiran. Nan tayi ta sak'a da warwara ta rasa mafita.


***

Haka rayuwar ta cigaba da gudana har akayi shekara d'aya amma har yau sun rasa wata mafita.
A lokacin kuma Meenah ta shekara biyu harda rabi Alhaji ya fara shirye shiryen saka ta makaranta da kuma islamiyya. Don ya fuskanci zata iya da wuri don a yadda ya fahimce ta, ta iya saurin d'aukar abu da kuma maganarta ta fito ga surutu ba abinda bata fad'i.
Sheyasa ma yanzu Bilki ta rage takura mata don muddin Alhaji ya dawo zata kwashe komai ta fad'a masa. Tana gudun kar tun baya tunanin komai har ya fara zarginta...


MSB💖

No comments: