Tuesday, 27 June 2017

AUREN FANSA 07

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     🌹MARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹



          🌹07 🌹

Fatima Zarah fara ce tas sa6anin Meenah da take ba fara ba tas, murna a wurin Bilki ba'a magana don yanzu gani take wata sabuwar dama ce ta samu ta yadda zata dinga samun kud'i a hannun Alhaji ba tare da wani matsala ba.
Kulawa ta musamman take samu a wurin mahaifiyarta wadda takeji kamar ta had'iye don so. A idon Alhaji kuwa had'awa takeyi da Meenah tana kulawa dasu wanda bata gajiya, bayan idonsa kuwa Meenah bata samun wata kulawa, tun daga kan wanka, chanza pampers, cin abincinta, chanza kaya idan sun 6aci sam bata damu ba. Sai  Alhaji ya kusa dawowa take tashi tayi mata wanka ta bata abinci yadda komai tsiyarshi baya ganewa. Zarah kuwa sai ayi mata wanka sau uku, abinci kuwa duk bayan awa uku ake bata, sheyasa tun kafin suyi arba'in ta takura tayi k'iba tayi fam, kamar balloon.


Watan Zarah biyu a duniya Meenah ta shekara d'aya cas. Tayi kyau tayi wayau abinta. Gata ta iya magana ba abinda bata fad'i kai kace 'yar shekara uku. Yadda ta taso ta d'auka Bilki ce mahaifiyar haka ma Alhaji ne babanta sai dai tafi shak'uwa da Alhaji saboda muddin yana gida to suna tare. Sheyasa yanzu idan zai fita sai da wayau saboda ta dinga kuka kenan kamar zata sik'e.

***

Ranar wata juma'a Alhaji ya dawo fuskarsa a cinkushe daga gani yana cikin damuwa, yana shigowa gaban Bilki ya yanke ya fad'i dama da safe ya fad'a mata ana neman sa banki don haka tana ta murna don tasan mijinta ya zama manager na banki. Yana fita ta hau gyaran gida tayi ma su Zarah wanka tayi masu kwalliya sosai. Ta shirya abinci mai rai da lafiya kafin k'arfe d'aya ta gama komai tana zaman jiransa ya dawo.
Yana shigowa ta tare sa daga bakin k'ofa tana ta murna kamar zata shige cikin jikinshi. Sai dai kula da yanayinsa ya sanya jikinta yin sanyi lak'was.
Bayan sun zauna ta fara tambayarsa.
"Alhaji wai ya ake ciki ne? Baka ce komai bafa."
Ya kalle ta na 'yan second kad'an kafin ya numfasa yace
"Bani akaba ba abokin aikina aka ba."
Dafe k'irji tayi tare da zaro idanu waje. Tace
"Me kace? Kana nufin basu baka ba? Haba ! Gaskiya ba'ayi adalci ba sam."
Yayi murmushi
"Bilkisu kenan, ni banga abin d'aga hankali a nan ba, kar ki manta komai na duniya rabo ne, idan bakada rabo komin yadda kakeson abu bazaka same shi ba."
Shiru tayi tana ayyanawa a ranta. "To wa aka ba?"
Ta tambayi kanta.
"Alhaji Adam Ishaq." Aka ba.
Tashi tayi tsaye
"Haba yanzu kayi magana, ay daman na dad'e da sanin sun fison su ba Adam, saboda shi yafika kud'i ko?"
"Haba Bilki! Bana son tashin hankali tunda an riga an bashi kina da yadda zakiyi ne? Ni ban damu ba kuma na taya sa murna nima idan lokacin nawa yazo zan samu. Alhaji Adam mutumin kirki ne, kuma muna mutunci dashi don haka na taya sa murna sosai, ke kuma idan na k'ara jin maganar nan kin tada ita a bakin aurenki!"
Dole taja bakinta tayi shiru, amma tana nan tana jira ya fita ta kira aminiyarta Hajiya Laila ta fad'a mata wannan mummunan labarin.

Aiko ana gama sallar magriba ya fice daga gidan, yana fita ta kira k'awarta Laila tana d'auka Bilki tac ce
"Wai bakisan meya faru damu ba ko?"
Hajiya Laila cikin d'aga murya tace
"Meyafaru?"
Nan Bilki ta kwashi komai ta fad'a mata tana gama magana Laila tace
"Ke iya nan kina sani kenan? Tab! Alhaji Adam dai an amsa transfer zuwa Abuja kiji in fad'a maki, yayi kud'i abinsa dama kinsan mahashuk'in mai kud'i ne ba kad'an ba."
Bilki ta zaro idanu waje kamar Laila na ganinta tace
"Haba ki bari Laila, ta yaya akayi kika sani?"
Laila tayi shewa tace
"Kina nufin baki sani ba? To bari in tak'aice maki labari Alhaji Adam Ishaq babban d'an kasuwa ne, sannan yana saida motoci ke kampanin k'era motoci ke gareshi a k'asashe daban daban. Bayan nan ga super market da yake dasu ba iyaka, ga gidajen mai nan tun daga nan Katsina, Kaduna, Abuja ke babu inda babu. Matarsa ma shagon saida kayayyaki ke gareta babu abinda babu k'atuwar mall ce sai dai kin gani."
Bilki da jikinta yayi sannan taji maganar kud'i yasa tace
"Wai da gaske kike?"
Laila tace
"Ba maganar wasa a nan Hajiya Bilki wallahi gaskiya na fad'a miki, bakiga kullum basu k'asar ba? Ke wallahi rayuwarsu abin sha'awa daga shi sai matarshi sai yaranshi guda biyu kacal ke cin wannan uban dukiya. Ke suna fantamawa fa. Kinsan gidanshi dake sabon titin GRA can wuraren Governor road d'innan ay ko?"
Bilki tace
"Kar dai kice kusa da wannan makarantar premier boarding school ta mata?"
Laila tace
"Nan fa toh wannan fa, gidanshi nan nan na nisa sosai, kullum na wuce ta hanyar sai na k'ara kallon gidan don gidan ya had'u ba kad'an ba."
Bilki tace
"Tabbas na gane gidan, nima ina ganin gidan, lallai Alhaji Adam ba k'aramin dukiya ya tara ba..."
Laila tace
"Uhm kedai bari zanzo idan nazo zaki k'arasa jin sauran bayanan don maganar bata waya bace."
Bilki tace
"Haka ne, gaskiya ina jiranki Laila kar ki shanya ni."
Laila tayi dariya
"Wallahi zanzo."
"Yaushe to?"
Laila tace
"Zuwa jibi."
Bilki tace
"Ina jiranki."
Daga haka sukayi sallama zuciyar Bilki cike da tunani kala kala, da kuma sha'awar dukiyar Alhaji inama ace tata ce, abinda take ta ayyanawa a ranta kenan.


        BAYAN KWANA BIYU

Da safe wuraren k'arfe sha d'aya Laila ta diro gidan Bilki, aiko murna a wurin Bilki ba'a magana, nan aka kawo mata kayan motsa baki. Bayan sun gama gaisawa Laila tace
"Bilkisu mai gadon zinari kenan, yau gani nazo a gidanki akan labarin da kikeson ji, wato maganar kud'i."
Bilki tace
"Ina jinki k'awata."
Laila tace
"Ay kamar yadda na fad'a miki rannan toh haka maganar take, kuma zuwa nan da sati d'aya zasu tattara su bar garinnan. Niko inada shawara amma bansani ba ko zaki yarda da ita."
Bilki tace
"Fad'i shawararki."
Laila ta gyara zama bayan ta shanye lemon da ke cikin glass cup ta soma magana.
"Bilki tunda kinga dani dake duk muna son kud'i me zai hana mu had'a k'arfi da k'arfi mu k'waci dukiyar Alhaji Adam."
Bilki ta zaro idanu waje
"Kamar ya? Ban fahimce ki ba."
Laila tayi dariya
"Abinda nake nufi a nan shine, mu had'a k'arfi nida ke mu k'waci dukiyar Alhaji Adam koda hakan na nufi mu kashe su."
Da sauri Bilki ta zabura had'e da zaro idanu waje tana kallon Hajiya Laila...




MSB💖

No comments: