Tuesday, 27 June 2017

AUREN FANSA 06

✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹Na🌹

     🌹MARYAM S BELLO🌹
             (MSB)

🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹



          🌹06 🌹

Kan dinning suka nufa inda Daddy da Anisah ke zaune suna labari harda dariya, zama sukayi itada Faruk
da Daddy ke musu fira a yayinda Mummy ta zuba ma kowa abincinsa. Wurin kuma yayi tsit sai k'arar spoon ake ji. Anisah ce ta katse shirun ta hanyar jefo ma Daddy tambaya.
"Daddy idan na girma me zan zama?"
Daddy dake shirin kai loma a bakinsa ya dakata yana kallon Anisah kafin kuma yace
"Anisah kenan, duk abinda kike so shi zaki zama ay."
Anisah tayi dariya
"Ni banason na zama komai nafiso na shiga aljanna."
Kowa a wurin sai da ya maida hankalinsa gareta kafin kuma Mummy tace
"Insha Allah zamu shiga aljanna kinji ko?"
Mummy tace
"Abban Faruk ya batun baka manager d'in ko sun fasa?"
Daddy yayi murmushi
"Ba fasawa sukayi ba Reemah, sai sun duba cancanta kafin su bada, idan na dace a bani manager zasu bani, idan kuma wani ya dace a ba za'a bashi."
Tayi murmushi
"Haka ne kuma, nidai fatana Allah ya baka sa'a a dukkan lamuranka"
Yaji dad'in addu'ar matarsa ba kad'an ba, abinda ke k'ara masa sonta kenan kullum cikin yi masa addu'a takeyi yana murmushi yace
"Amin ya Allah Reemah."
"Ka fidda ranar da zamu tafi Disney world d'in kuwa?"
Reemah tace bayan ta had'iye abincin dake bakinta. Daddy ya sha cup d'in Apple juice kafin yace
"Eh zuwa upper week dai insha Allah lokacin su Faruk sun gama exams a islamiyya."
"Yeeyy! Mummy Disney world zamuje da gaske?"
Mummy tayi murmushi tace
"Eh Mamana ko bazaki ba?"
Anisah ta zum6ura baki
"O'o ni zanje."
Faruk yace
"Kalle ta to baza'a dake ba."
Anisha ta sa kuka
"Daddy wai baza'a je dani ba?"
Daddy yayi murmushi
"Ya isa yace bazaki ba, ay kece head d'in tafiyar gaba d'aya zamu iya barinsa amma ke bazamu iya barinki ba."
Gwalo ta ma Faruk tana share hawayenta. Faruk yasa dariya. Anisah tasa kuka.
"Mummy kinga Ya Faruk na min dariya ko?"
Mummy ta harari Faruk
"Zaka fara ko Baba na? Meyasa kakeson ganin kukan k'anwarka ne?"
Yayi dariya
"Aww dariya ma kakeyi Faruk? Bazaka bata hak'uri ba?''
Ya buga k'afa.
"Wannan 'yar yarinyar zan ba hak'uri? Tab bazan bada ba."
Daddy yace
"Just say sorry Faruk, you know she won't stop crying unless you apologize."
Mummy tace
"Oya Faruk now!"
"Ok sorry!"
Take ta bar kukan inda kuma ta cigaba da cin abincinta kafin kuma ta kalli Daddy
"Daddy zansha ice cream."
Mummy tace
"Me nace miki akan zak'i?"
Anisah ta turo baki
"O'o ni zansha."
Mummy zata k'ara magana Daddy ya d'aga mata hannu
"Ba ruwanki Reemah, zan siya mata ice cream."
Anisah tashi tayi da gudu ta wuce parlor tana tsallen dad'i.
Daddy yayi dariya Mummy na taya shi tace
"Anisah kenan, badai rigima ba."
Daddy yayi dariya
"Lokacinta ne, kema kinyi naki ay."
Mummy tace
"Daddy Faruk fa na wurin."
Yayi dariya
"To sai me? Sai na fad'i abubuwan da kikayi ay" Da sauri ta tashi tana fad'in
"Haba Daddy!"
Yayi dariya
"Kina tantama ne? Bari kiga..."
Kafin ya k'arasa tayi sama da sauri tana dariya. Daddy ya tashi ya bi bayanta
"Guduwa kikayi Reemah!"
Faruk tsayawa kallonsu yayi yana dariya cikin ransa yace
"Allah ka k'ara had'a kanmu what a lovely family!"


***

Meenah na zaune kan carpet tana wasa da abin wasanta haka kawai kuma sai tasa kuka, Bilki dake zaune saman kujera tana shan rake tana kallon wani movie da take so kukan Meenah ya cika mata kunne. Tsawa ta daka mata
"Ke da Allah kiyi mana shiru yarinya sai shegen kuka haba!"
Abinka ga yaro wannan tsawa da aka daka mata ita ta firgita ta yasa ta k'ara fashewa da wani irin kuka. Haushi ya cika Bilki yasa ta tashi tayi shigewarta d'aki ta bar Meenah nan na ta faman kuka kamar zata shid'e. Meenah tayi kuka baiwar Allah har ta gaji. Nan ta kwanta k'asa tayi ta ajiyar zuciya har baccin wahala ya kwashe ta a nan.

Bilki na kwance a d'aki ta jiyo k'arar shigowar motar Alhaji. Da sauri ta fito tazo ta d'auki Meenah dake a k'asa ta rungume ta tare da zama kan kujera tana rirriga ta.
Haka Hamza ya shigo ya same ta, da murmushi a saman fuskarsa ya k'araso. Yana zama Bilki ta kalle shi
"Sannu da zuwa Alhaji."
Yana murmushi yace
"Yauwa sannu da aiki Bilki, Meenah bacci akeyi?"
Tayi murmushi
"Eh wallahi yanzu ta gama rigima sai na rirrriga ta tayi bacci."
Yayi murmushi
"Meenah kenan, ay batada rigima ma k'ila dai baccin takeji daman."
Tayi yak'e
"Sosai ma ay Meenah baiwar Allah ce batada rigima."
Yace
"Hakane Allah ya raya mana ita."
Tace
"Amin."
Yace
"Bari naje na watsa ruwa na gaji."
Tace
"Ok sai ka fito."
Tana ganin shigewarsa ta kalli Meenah taja dogon tsaki, sannan taje ta kwantar da ita a d'akin Meenah d'in kan gado.

Bayan Alhaji ya gama wanka suna zaune kan dinning suna cin abinci ya kalli Bilki yace
"Bilki a gaskiya ba abinda zance miki sai dai nace Allah ya saka da alkhairi akan aikin ladar da kikeyi. Allah ya baki lada."
Ta kalli Alhaji tace
"Haba Alhaji meye na godiya ay yi wa kaine, kuma ma Meenah kamar d'iyar dana haifa haka na d'auke ta. Idan har kana min godiya sai naji kamar baka d'auke ta a matsayin 'yar cikina ba."
Yayi murmushin jin dad'i
"Wallahi ko kusa ba haka bane, kawai dai na yaba da k'ok'arinki."
Tayi dariya
"Allah sarki. Uhm uhm Alhaji dama madararta da pampers sun k'are shine nace  ya kamata a bad a siyo mata wasu."
Yace
"Wannan ba damuwa zan baki isashen kud'i ki siyo mata wanda zai dad'e, naga kamar tafison madarar ma akan abinci."
Tace
"Hakane."
Bayan sun gama ya d'auko kud'i har dubu goma ya bata. Amsa tayi tace
"Shikenan zanje na siyo mata.
Yace
"Toh ko ki bari idan na fita na siyo mata mana."
Da sauri tace
"Kai haba kai ina kake da lokaci? Ni da nake gida kullum ka bari zan siyo mata."
Yayi murmushi
"Toh shikenan."


***

Watan haihuwar Bilki ya kama. Kullum sai ta tambaye shi kud'in siyayya bai ta6a hana ta ba saboda har ga Allah ya d'auka Bilki ta shiryu.
Wata rana nak'uda ta kama Bilki gadan gadan, Hamza ya kaita asibiti, suna zuwa ba'a jima ba ta haifi 'ya mace. Kyakkyawa fara tas mai k'oshin lafiya.
Haka aka cigaba da zaman barka inda komai Hamza yayi mata daidai gwargwado komai yana tafiya daidai.
Ranar suna yarinya taci sunan kakarta ta wurin Hamza wato Fatima. Haka aka gama taron suna aka watse lafiya kowa ya koma gidansa....



MSB💖

No comments: