Monday, 30 August 2021

YAR AGADEZ PAGE 46

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 46}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com





Da asuba Ashraf  ya farka a hankali ya zare jikinsa daga nata sannan yaje bathroom ya dauro alwalla ya wuce masallaci, dama Zarah taji motsinsa don haka itama sai ta mike ta tafi don yin tata alwallar. Tana gamawa tare da azkhar dinta da addu'ointa ta haye gado ta koma bacci. Sai wurin karfe tara ta farka mamaki tayi yadda ta ganta kwance bisa kirjin Ashraf, saida tayi dubara sannan ta samu ta zare jikinta ta wuce dakinta, brush tayi ta wanke fuskarta sannan ta hau gyaran gida tas ta tsabtacce ko ina ta kunna turaren wuta ta fesa freshner ta kunna ac kafin kace me gidan ya fara bada wani scent mai dadin gaske. Tana gamawa tayi wanka ta shirya cikin wani dinkinta na atamfa doguwar riga tasha stone work sai kamshi ke tashi daga ko wane bangare na jikinta. Tana gamawa ta fada kitchen dama already kafin ta shiga wanka duk ta fera dankali ta yanka albasa da sauransu tana xuwa kawai ta dora wuta kan gas ta cigaba da aikinta a natse. Tana tsakar hada breakfast din tana rera waka in a low tone amma ana jin sautin kadan. "Yaya xanyi in misalta soyayya? Yaya zanyi in fisalta soyayya?.....Itace ba'a siye da kudi duk dukiya... itace mai gida na mulki shine zuciya... ta sanya mai karfi ya sunkuya..... ya zubda hawayen idaniyaaa....." ta dora mai a bisa pan da yayi zafi sai ta saka sausages din suna soyuwa sannan ta cigaba da wakarta.... "idanuna suka jani kafafu sukka ka kaini zuciya tana dauki.... nasan xan kece raini zai zamto ba kamar ni kin kirani angonki... ko nawa aka ce gareni indai har za'a bani xan biya sadakinki.... da zan zamo miji gunki... zan kare dukka hakkinki... in zamo adali a mulkinki.... mai martaba a fadarki..." Ba zato kawai taji an rungumeta ta baya, "Ashe dai idan na biya sadaki zaki kira angonki? Dont mind yanzu ay na riga na biya sadakin tuni har ma kin shigo fadata kuma zan zama adali a mulkinki..." yar dariya yayi ganin yadda ta dan xama shocked alamar batayi expecting dinsa ba. Juyowa tayi tana faman turo baki, "Ni gaskiya ka bani tsoro sannan kuma ban shiga fadarka ba."

Murmushi yayi ya lakuci hancinta, can kuma sai ya bata rai, "Ni ay fushi ma nake dake ko kice ma ya jiki ko?" Da yake kwana biyu yayi fama da ciwon kai marar dadi, ya hade rai gamida bata baya, saurin rungumo shi tayi ta baya ta rike shi gam gam, "Am sorry wallahi I didn't forget, ya jikinka? Kaji sauki ko?" Ta tambaya fuskarta cike da tausayi karara, Ashraf yayi murmushin mugunta ya juyo a hankali tare da tallabo fuskarta yana fadin, "My cry cry baby, kar dai kiyi min kuka kinji? In kina so nayi hakuri sai kin bani hot kiss wanda baki taba yi min irinsa ba a nan..." ya karasa yana nuna bakinsa wanda yake light pink naturally haka yake duk cikin fuskarsa babu abinda ke kara masa kyau kamar bakin nan nasa, Zarah ta zaro idanu waje tare da juya fuskarta cike da kunya, dama ta kwashe komai da sauri ta hada cikin warmers ba tare data sake kallonsa ba ta wuce da sauri dining tana jera kayan, tana ajiye flask din zata juya taje da dauko masu plates da cups kawai tana juyawa sai ganinsa tayi tsaye ya dauko plates din da cups yana faman yi mata murmushi ita kuwa da sauri ta sadda kanta kasa, bama taso ko da hada idanu suyi, kanta kasa ta zo zata wuce ta gabansa kenan taji ya riko mata hannu da sauri ta dago kanta tana kallonsa take yayi mata wink, janye hannun nata tayi da sauri ta wuce kan kujera ta zauna kanta kasa ta fara masu serving abincin, saida ta kammala zuba masu sannan suka fara karyawa a natse. Shi kuwa Ashraf babu abinda yake mata sai magana ita kuwa taki koda kallonsa bare yasa ran zata amsa masa. Kallonta yayi yace, "Tou Zarah nidai zan tafi office mata nacan suna jiran the most handsome man..." ya fada yana dariya kasa kasa ganin yadda take mood dinta ya chanza ta hade fuska kishi bayyane saman fuskarta kafin tace, "Wai wama ya dauke ka wannan aikin? Ni kwatakwata banso Mummy ta samo maka aikin bankin nan ba, yawancin duk mata ne ke sa matsatsun kaya ko kuma ka gansu da dogon wando, ga Christians nan duk sun sha dagaggun skirt duk kafafunsu a waje...." Dariya yayi sannan ya fara bata amsa, "Zarah kenan, ah sosai fa zan rika ganin mata kala kala har sai na darje, gara ki rike Ashraf dinnan fa kar ki bari ya fita yanzu..." Dariya tayi sosai sannan ta dan bigi kafadarsa tana cigaba da dariya. Har ya fita ya dawo yana fadin, "Am joking princess, besides yau ba aiki sai gobe inshaAllah it's a public holiday today remember?" Tayi murmushi tana gyada kai, key din gidan ya bata don yana so ya kulle ta gaba duniyar yanzu ta zama abinda ta zama, "Ga key dinnan karki sake ki bude ma wanda baki sani ba har sai na dawo." Tace "InshaAllah." Har bakin kofa ta raka shi sannan ya bata spare key din ta rufe gidan, tana dawowa ciki ta saka wayarta charge sannan ta gyare dakinsa ta wanke bathroom sai ta dora abincin rana. Saida ta kammala tas  ta zauna parlor ta kunna kallo har bacci yayi gaba da ita.

******

2 WEEKS LATER... 

Yau satin Zarah  biyu da taje ganin gida da kuma duba jikin yar uwarta Khadija, Ashraf ji yake tafi shekara biyu bata tare dashi gaba daya gidan ya masa girma saukinsa ma yana zuwa aiki kuma kullum suna waya da chatting. Ranar da tayi shirin dawowa tayi niyyar bashi surprise kasancewar yau Tuesday ta kama tasan definitely yana office, saida ta wuce gida ta sauke boxes dinta tas sannan ta kullo gidan ta dauki hanyar bankinsu Ashraf, koda ta shigo sai ta iske wayam office dinsa babu kowa nan suke sanar mata ay sun fita shida manager din bankin sun tafi wani branch din, xama tayi kan kujera tana bin office din da kallo yadda ya kawatu duk da ba yau bane ta fara zuwa amma sai taga duk ya chanza mata lallai central bank ta hadu, bisa table din hotonsu ne na biki ansa cikin frame ya aje shi a tsakiyar table din, gefe kuma wasu files ne wanda basu kai ashirin ba, sai laptop dinsa dake ajiye a gefe kwatakwata dai office din very simple yet classy, ac duk ta cika wurin ga kamshi na musamman na tashi, murmushi tayi a cikin ranta ta kagara ya dawo, tana cikin wannan tunanin ne kawai taji alamun shigowarsa, tana juyawa ta ganshi tsaye idanunsa waje bakinsa bude yana kallonta itama cike da murna ta daka wani uban tsalle wane karamar yarinya taje ta rungume shi, shi farin ciki ma ya hana shi magana, fuskarsa cike da murna hade da mamaki, kara rungumota yayi yana rufe kofar office din nasa da kafa, "Oh my princess is back, ya Allah am so happy I really miss you princess." Ya fada yana juyi da ita tsakiyar office din ita kuwa sai dariya takeyi tana kara makalkale shi, "Meyasa baki fada man yau zaki dawo ba princess? Ko duk missing din nawa ne yasa bazaki iya kirana ba? Da ba sai inje airport in dauko ki ba?" Tayi dariya, "I wanted to surprise you ne fa,  kuma ni na kosa na ganka bazan iya jira har sai kazo ba, mu tafi gida ko baka tashi ba?" Dariya yayi ya aje file din da ya dawo dashi saman table sannan ya dauko key din motarsa, hannayensu rike cikin na juna ko wanenensu fuskarsa dauke da farin ciki sai binsu ake kallo cike da sha'awa, "Kasan yadda nakeji kuwa da na tafi? Ji nake kamar zuciyata zata fashe tsabar yadda nayi kewarka." Yayi dariya tare da rungumota ta gefe, yace "Wai ya naga kin kara kyau da haske ne? Kodai wayau kikayi man kika tafi can Mummy ta dinga baki kayan dadi kina ci ke kadai a can?" Shi ya fara bude mata motar ta shiga sannan ya zaga ta side dinsa ya shiga shima tana ta dariya tana girgiza kai kafin a hankali taji saukar lips dinsa a goshinta, kunna motar yayi ya fita da reverse, saida ya hau titi ya juyo yaga ta langa6e kan kujera idanunta na rufewa sama sama ga gajiya nan bayyane saman fuskarta da kasala. "Anya Zarah? Dama na lura tun kafin ki tafi kike wannan yawan kasalar, yanzu kuma jirgi fa kika hau balle ace gajiyar hanya ce." Idanu ta bude waje da sauri ta mike tana auna maganganusa, ganin yanayinta yasa ya kyalkale da dariya yace, "Wasa nakeyi koma kiyi baccinki rankishi dade." Daga haka ya cigaba da driving dinsa can taga ya tsaya pharmacy bai jima ba ya dawo wanda batasan meya siyo ba, daga nan kuma taga ya tsaya kfc ta dago tana kallonsa, "Na dauka gida xamuje inyi wanka in chanza kaya?" Yayi murmushi "Bari na siya mana abinci tunda nasan bazaki iya mana girki ba ganin yanayinki a halin yanzu..." yana gama fadan haka ya fita daga motar yana dariya itama ta fito, family size ya siya masu da chips sai katuwar coke. A haka suka dawo gida yana driving da hannu daya dayan kuma ya rike ma Zarah hannu dashi. Bayan sun fito a mota ta tayashi daukar kayan suka shiga ciki, tayi mamakin ganin gidan tsab don ita dazu ma ko lura batayi ba ajiye kayanta kawai tayi ta fito, gidan babu datti ko guda daya kitchen dinnma haka ba karamin mamaki tayi ba, batayi zaton haka zata iske gidan ba. Tana zaune kan gado daga ita sai karamin towel tana kokarin warware kanta, rabon data data gyara kan tun kafin tayi tafiya duk ya curkude wurin daya, shigowa yayi ya aje ledar kan side drawer kafin ya zauna gefenta yana kama gashin nata yana tayata kwance inda ta kitse shi, "Wai meyasa bakyason yin kitso ne Fatima? Gashi kullum sai ya wahalar dake, dama ance duk masu gashi basu san ta6a gashinsu tou gashi nan na tabbatar dai a kanki." Dariya tayi tana tayashi warware kan nata, "Ni banma san yadda xanyi ba tunda na tafi ko ta6ashi banyi ba, Ashraf kasan yau sai nayi ciwon kai tsabar wahalar da zansha." Lumshe idanu yayi a hankali kafin ya bude, "Tou ko a wanke kan yau? Dama kin dada baki wanke shi ba nasan bazaiyi zafi ba idan har na wanke maki da kaina?" Dariya tayi tana kwantawa saman gadon tana kallon kyakkyawar fuskarsa tana murmushi. "A'a kabari sai gobe don nagaji sosai, kaji yadda nakejin bacci kuwa? Yanzu ma wanka nakeso in shiga sai in kwanta..." ledar daya aje ya jawo ya rike a hannunsa kamar za'a kwace masa ita, "Wai meye a cikin ledar nan kake ta faman rike shi kamar ranka?" Ita da wasa ta fada amma shi har ransa yaji, gyara zama yayi yana faman dagata saura kadan towel din ya fadi tayi saurin riko shi gam, "Ashraf!" Yanda ta rude sai abun ya bashi dariya, mika mata ledar yayi, ta bude nan taga PT strip ne da sauri ta dago tana kallonshi, "Wannan fa? Ba shi bane ka siyo kafin inyi tafiya muka gwada mukaga negative? So kake yanzu ma in sake gwadawa in kara ganin wata negative din ko? Kuma ranar duk ka nuna damuwarka da ya nuna negative har kwalla nayi ranar da daddare..." jawota yayi ya rungume ta a jikinsa yana kissing gashinta daya baje bisa bayanta, "I know princess, kawai mu sake gwadawa, I promised you in babu bazan sake gwadawa ba har sai ya fito da kansa cikin," gyada kayi tayi alamun eh sannan ta tashi ta shiga bathroom sai da abun yayi reading sannan ta fito ta dora shi bisa drawer ta bar wurin da sauri she don't want be disappointed again kuma. Tashi yayi bayan minti biyar ya leka abin ya dago mata shi, nan ya jawota ta fasa ihu hade da runtse idanu gabanta na faduwa, "Menene?" Da wani irin murmushi yake kallonta yana kara rungumeta, kissing fuskarta ya fara yi cike da farin ciki kafin yace, "Thank you so much Zarah! It's positive Alhamdulillah!" Rumgume shi tayi tana hawaye she can't believe wai zata haifi gudan jinin Ashraf Allah mai iko. Kara rungumeta yayi yace "I love you so much Zarah, kin biya ni yau am so happy, so so happy! Am the happiest man right now Zarah, zaki haifa man jinina! Ina sonki Zarah kinji?" Hawaye suka kara shatata daga idanunta ta rungume shi gam gam tana jin yadda farin ciki ke sauka saman zuciyarta...

--------

FEW WEEKS LATER!

Sintiri kawai yake yi a bakin kofar labour room din, Ashraf da Zarah ma ko wane cike da damuwa ji take kamar ta shiga taga meke faruwa a ciki, Ashraf kuwa damuwar data bayyana a fuskarsa yama kasa koda magana ne, sarki Sultan kasa shiga dakin labour room din yayi ba yadda ba'ayi dashi ba akan ya shiga amma fir yaki don gani yake yana shiga za'a ce mashi ta mutu amma shi kansa ya tabbatar da cewar Hoodah na mutuwa tou shima babu abinda zai hanasa ya bita. An fi minti talatin can wata Doctor ta fito duk ta hada xufa fuskarka dauke da damuwa, "Your wife's life is in danger your highness, don a halin yanzu ta kasa haihuwa da kanta kuma babu abinda takeyi sai kuka tace ka shigo ka tsaya gefenta, sannan maybe we have to save one of them ko uwar ko dan." Da wani irin expression yake kallon likitan, "What are you saying to me Doctor?" Ya fada yana goge idanunsa da hawaye ke zubo masu, suma kansu su Ashraf ko wane ya zama speechless hankalinsu tashe, gasu Ummi da isowarsu kenan suka tsaya cike da shock suna kallon doctorn, Doctor din ta sauke ajiyar zuciya, "Bance ko bazata haihu lafiya ba amma dai  ina nufin rayuwarta na cikin hadari kudai tayata addu'a." Tana fadan haka ta kalli Sultan, "Wa kake da bukatar muyi saving the mother or the baby?" Kasa tsayuwa Sultan yayi nan ya fada kan kujerun da ke ajiye a nan Ashraf yayi saurin rike sa, sai ya fashe da kuka kamar karamin yaro, "Ya zakiyi min wannan tambayar doctor? You know I love my wife more than life itself, I also love my child wanda ban riga na gansa ba, but If I am to choose I will have to choose my wife over and over again, so yes Doctor save my wife first!" Ya fada cike da karfin hali kafin ya rungume Ummi yana cigaba da kuka, Zarah kasa daurewa tayi ta fita da sauri ta nufi bathroom ta dauro alwalla, ta tafi masallacin asibitin ta fara sallah tana rokon Allah yayi saving dukansu gaba daya. Nan Doctor din ta wuce ciki ta barsu cikin wani irin mawuyacin hali. Ummi ta dafa Sultan, "You did the right thing son Allah zai baku wani InshaAllah." Ya gyada kai cikin karfin hali yana goge hawaye. A hankali suke jiyo kukan jarirai har guda biyu a tare gaba dayansu suka sauke ajiyar zuciya cike da mamaki, Sultan zubewa kasa yayi yana ma Allah godiya daidai nan Zarah ta shigo da saurin jin sautin kukan babies na tashi, batasan sadda ta rungume Ummi ba tana hamdala. Bayan mintina kadan sai ga Doctor din ta sake fitowa fuskarta dauke da murmushi, "Congratulations your highness, it's twins! Matarka da yaranka suna nan cikin koshin lafiya!" Ay bata karasa magana ba Sultan ya mike da hanzari yayi hanyar dakin. Ita kuwa Ummi da Zarah kara rungume juna suke yi suna dariya kamar wasu kananan yara. Iyakar wahala tasha ta, hannunta ne taji a cikin nashi basai ta bude ido ba ta tabbatar da Sultan ne, nan ta bude idonta a hankali tana saukewa bisa fuskarsa wacce ta sauya kala tayi jajir sannan ga farin ciki nan saman fuskarsa, zama yayi gefenta yana kara kamo hannunta yana sauke mata kiss a hankali, Hoodah ta goge hawayen farin ciki ta mike zaune da kyar tana kallonsa, "Congratulations my king a boy and a girl..." ya kalleta yana juya kansa don neman babies din tayi murmushi, "An tafi dasu for general checkup." Ya gyada kai sannan yace, "Kin tuna alkawarinmu?" Ta gyada kai "And we both won!" Bata karasa magana ba ya hade lips dinsu wuri daya sun dade a haka kafin ya janye a hankali ta sadda kanta kasa, shigowa nurse din tayi hannunta dauke da jariran biyu ko wane an kimtsa shi tsab sai dan motsi sukeyi sunata baccinsu a natse, a hankali ya mike ya isa inda suke ya tsaya yana kallonsu kamar wani statue ya tsura masu idanu sosai idanunsa na kawo ruwa. Amsar su yayi take ya lumshe idanu yana jin son yaran na fizgarsa, kisses yake aika masu ko ta ina a fuska kafin ya taka inda Hoodah ke kwance ya zauna gefenta, duka su biyun ya daura mata bisa cinya sai a lokacin ta saki hawayen da take rikewa, shafa fuskarta yayi yana goge mata hawayen, yace "Banida bakin da zan gode maki kin bani kyauta ta musamman, Alhamdulillah na gode ma Allah da ya bani wannan gagarumar kyauta wanda ba kowa yake bamawa ba, yau da ace na rasa ki Hoodah de sai dai na biki nasan take zuciyata zata buga nima in mutu..." da sauri ta toshe masa baki da hannunta, rike hannun yayi ya rungume sannan ya mike ya fita ya kaiwa su Ummi yaran. Bai jima kwarai ba ya dawo ya zauna gefenta tare da rungume  ta a jikinsa, "Ina fatan banyi katsalandan ba don inaso ki bani izini na maida sunan mahaifiyarki a macen..." da sauri ta kalle shi speechless toshe bakinta tayi kawai sai ji yayi ta makalkale shi tare da fashewa da wani irin kuka, "Thank you so much for this Sultan, Allah ya biya maka bukatunka na alkhairi." Wani irin kiss ya kai mata a goshi, "No need my queen you deserve the best..." a haka ta dora kanta bisa kirjinsa har bacci yayi awon gaba da ita, Sultan hannunsa ya dora bisa kan nata yana shafa gashinta a hankali yana lumshe idanu...

Saturday, 28 August 2021

YAR AGADEZ PAGE 45

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 45)


To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com




Bayan Mummy ta kammala bata abinci kamar kullum sai ta mike ta nufi kitchen kafin Mama Hauwa tazo ta tattara kitchen din, ita dai Khadija tabita da kallo har ta dawo hannunta dauke da cup da ledar maganinta, dawowarsu kenan daga therapy har yau Mummy bata sake mata kuma hakan ba karamin damun Khadija yake ba gaba daya ta rasa meke mata dadi, zama Mummy tayi kan kujera ta ballo mata duka magungunan nata ta zo bata kenan Khadija tasa hannunta mai Lafiyar ta rike ma Mummy hannu idanunta na kawo ruwa, girgiza kai Khadija keyi sannan ta fashe da kuka sosai kuka take kamar ranta zai fita, saida kukan ya tsaigata sannan ta dubi Mummy da itama idanunta cike da hawaye tace, "Nasan banida isassun kalmomin da suka dace inyi amfani dasu wajen baki hakuri Mummy, fushin nan da kikeyi sam banga laifinki ba saboda ya dace ma kiyi fiye da haka, na butulce ki upon irin kaunar da kika nuna min da soyayyar ki a gareni sai gashi abinda na saka maki dashi kenan..." hawayen ta share kafin ta cije lebe wasu na kuma taruwa a idanunta, "Kamar yadda nace fushin da kikeyi ya dace dani amma kuma bazan iya jurewa ba Mummy, sam bana jin dadin yadda kike treating dina saboda na saba da care dinki na saba da kulawarki, na saba da kaunarki wallahi zuciyata bazata iya dauka ba Mummy don Allah ba don halina ba kiyi hakuri ki yafe man koda na samu nutsuwa a cikin raina..." ta karasa cikin tsananin kuka, Mummy ta share hawayen fusakarta ta mika mata maganin bayan ta sha sai kawai ta mike ta kai cup din kitchen tazo tabi ta gaban Khadija zata wuce kawai sai Khadija tayi sauri ta damko mata hannu gam, Mummy ta juyo tana faman goge hawaye kafin ta janye hannun nata a hankali tayi hanyar sama, dama Khadija ta dauko wata yar karamar wuka, Mummy har ta kusa hayewa sai Khadija ta saita wukar daidai wuyanta tana kuka tace, "Fine! Tunda bazaki yafe mun ban banga sauran amfanina ba a duniya, Mummy you're my whole world, don haka barina duniya shine yafi alkhairi...." Cak Mummy ta tsaya gamida juyowa da sauri idanu ta zaro waje kafin ta juyo Khadija ta fara kokarin caka maka kanta wukar nan, aiko Mummy tana isowa ta warce wukar a tsorace tana kallon Khadija cike da shock, durkusawa Mummy tayi har wata kyarma takeyi tace "Khadija meye haka? Are you mad? Mekike shirin aikatawa?" Khadija tayi murmushi, "Dama nasan har yanzu kina sona Munmy, why are you pretending?" Mummy ta juya fuskarta gefe kafin tace, "Saboda kin aikata babban laifi a gareni! Na saki a inuwa sai kika tunkuda ni rana Khadija you betrayed me, meye namiji? Da har zaki cuci yar uwarki akansa? Haba Khadija!" Khadija Ta girgiza kai cike da karfin hali tace, "Nasani, amma yanzu na gane kuskurena, don Allah don annabi ki yafe mun, ni mai laifi ce na kuma amsa laifina, ki yafe man Mummy." Mummy ta rungumeta a hankali, "It's okay Khadija na yafe maki, ya wuce kinji? Koda wasa kar ki sake aikata makamancin haka kina jina?" Da sauri ta girgiza kai cikin kuka tace, "Never Mummy InshaAllah." 

---------

2 WEEKS LATER...

A hankali Mummy ke tura ta a bisa wheelchair har sai da suka tsaya daidai office din Dr Hafiz, Mummy ta gyara mata wheelchair din yadda zata iya tura kanta don wani botton ne kawai zata danna keken ya fara tafiya, sannan ta dan sunkuyo tana murmushi, "As always ki shiga zan jiraki a inda na saba jiranki kinji ko?" Ta gyada kai sannan Mummy ta juya ta fara tafiya, ita kuma tasa hannu ta fara knocking kofar a hankali, ji tayi ance mata "come in." tasa hannu ta bude kofar ta fara tura kanta a ciki, saida ta isa daidai table din office din sannan ta tago tana kare masa kallo, a dan tsorace ta fara kokarin tura keken nata zata fita dan ita a tunaninta ma ba office dinsa ta shigo ba saidai kuma data sake bin office din kallo tsab sai taga lallai office din nasa ne komai yana nan a yadda ta saba gani, daidaita kanta tayi sannan tace "Salam? Good morning?" Ta furta a hankali tana kallon bakuwar fuskar data tsareta da idanu, "Wslm, morning too, Khadija ko? don ya sanar dani ke kadai ce yakeda appointment dake yau ko?" A hankali ta gyada masa kai tana kallon kasa, "Ina yake?" Ta tambaya tana kara kallon kofa koda zataga Dr Hafiz din ya shigo, "Wani emergency yake attending to so bazai samu damar ganinki ba a halin yanzu, sunana Dr Aliyu yau ni ne zan maki therapy." Kafin ya mata bayani har tanada niyyar juyawa ta fita sai kuma ta dakata tana saurarensa, tana tunanin yau Allah ya hadata da mai surutu, a hankali ya mike yana murmushi ya kamo keken nata sannan ya shiga janta zuwa wata yar kofa inda zata sadaka da therapy room din. Duk wani abu da ya kamata Dr Hafiz yayi mata Dr Aliyu yayi har ma fiye, har ma cikin aikin nasa ya kan tsaya yana mata yar hira ko tambayoyi don ma ya dauke mata hankali daga pain din da takeji a jikinta, hannun nata yake massaging a hankali cikin kwarewa, ganin tana dan cije lips dinta sai ya dakata yana kallonta fuskarsa dauke da murmushi yace, "Khadija yanzu what do want to do with your life? Kinga kamar ni kullum karatun likitanci baya kare min, kullum cikin research nake amma still ina samun lokaci inyi karance karancen novels da poems, and also ina da babban shop a nan garin ina siyar da kayan maza kamar su shadda, jallabiya, shoes, hula everything da kika sani na maza ina dasu, ke me kikeso kiyi?" Ya tambaya yana cigaba da mata therapy din, dan murmushi tayi mai cike da hawaye sai tace, "Koda ina so amma a halin yanzu bazan iya yi ba saboda condition dina..." Shiru yayi yana kallonta kafin ya sauke ajiyar zuciya, yace, "No Khadija don't say that, you can do it kar ki sake bari lalurarki ta hanaki purchasing dreams dinki," tun tana yarinya babu abinda takeso kamar fashion and design especially idan ya zamana tana designing kayan da kanta tana zanawa, saidai tunda wannan abin ya faru da ita taji komai ya fice mata a kai, murmushi tayi ya taimaka mata ta tashi zaune a hankali tana sunna kai, "Ina son fashion and design especially a harkar designing kaya bawai a dinka min ba a'a na dinga dinkawa da kaina kuma ina designing, I so much love it." Murmushi yayi ganin ya samu hanyar da zai taimaka mata yace, "Tou yanzu Khadija idan aka baki paper da pen zaki iya farawa? Kuma kin iya ko kuwa kina bukatar training?" Da murmushi mai gaggawa ta daga mashi kai, a hankali yayi lifting rigarta zuwa cinyarta ya tsugunna daidai kafar ya fara mata massaging kafar, sannan ya jawo wani machine mai kamar bicycle ya dora mata kafar ta fara exercise din kafin tace, "Zanyi sosai, akwai abubuwa da yawa wanda bayan fashion and design zan iya mantawa dashi, nidai for me wannan ne kadai ke sani farin ciki I think it's the best gift, my opinion though." Mamakin kanta ma take yaushe rabon da tayi magana har haka? Balle ma ta tsaya dogon bayani, cike da salo da dubara ya cigaba da mata massage dinnan har saida ya kasance sam bataji wani wahala ba kamar yadda take ji a wurin Dr Hafiz sai taji yau salon nasa na daban ne, nan ya gama lura da ita akan cewar fa da gaske take har kasan ranta tana son fashion and design, bayan ya gama sai ta daga waya ta kira Mummy, Mummyn tace, "Ina kika yadar wayarki ina ta faman kiranki baki dauka ba?" Khadija ta duba wayar cike da mamaki tace "Wallahi Mummy ban ji ba kiyi hakuri." Mummy tace "Bakomai, dama ince maki wallahi wani emergency meeting ne manager din company dinmu ya kirani wai yana son ganina da gaggawa, tou ga Audu driver nan na kirashi yace min zaizo ya dauke ki, nace wa Mama Hauwa ta bashi key din dayar motar tawa zaizo ya dauke ki kinji? Ki samu nurses sai su taimaka maki ki shiga mota, am truly sorry daughter." Khadija ta marairace tace, "Ok Mummy bari in kira Audun yanzu." Mummy "Ok tou, sai na dawo take care kinji?" Khadija tace "Thank you." Sannan ta katse wayar ta shiga kiran number din Audu kamar da wasa taki shiga, ta dago kamar zatayi kuka tace "Number driver dinmu taki shiga, kuma Mummy ta tafi wani meeting." Dr Aliyu yace, "Tou yanzu ya za'ayi kenan Khadija?" Tace "Ko in dan kara jira nasan zaizo tunda Mummy tace tayi magana dashi." Yayi ajiyar zuciya, "It's ok, am sorry Khadija na shafa'a ko ruwa ban kawo miki ba." Tayi murmushi "Ba damuwa ay bana jin kishirwa." Zama yayi a gabanta yana binta da kallo kafin yace, "Tou malama Khadija baki fada man sunanki ba?" Da wani yanayi take kallonsa irin ba yanzu ka gama kiran sunana ba? Amma sai ta dake tayi murmushi tace, "Sunana Khadija." Ya girgiza kai, "Ni kinga sunana Aliyu Haiydar Mahmud, ke meye sunanki?"da kyar ta kakalo murmushi kafin tace "Sunana Khadija Hamza." Bata jira cewarshi ba ta juya kan wheelchair dinta ta fita daga office din, dan fadan sunanta ya taso mata da dukkanin damuwar da take kokarin dannewa. Saidai kuma idan ta tuno da abinda takeso a rayuwa wato fashion and design sai taji sanyi a ranta, tana hango kanta a matsayin fashionista sai ta saki dan karamin murmushi har ta isa harabar asibitin bisa yar verandar a waje a nan ta tsaya, bata kai minti biyar a zaune ba sai kawai taga mutum tsaye a kanta ta dago tana kallonsa amma da alama baisan abinda zai fada mata ba, can yayi yar dariya cike da zolaya kamar yadda ya saba yi mata yace, "Kece?" Ya tambaya kamar wani sakarai yana kokarin danne dariyarsa, hade fuska tayi tamau "Nice wa?" Ya hade hannu waje daya, "Sorry malama Mummy ta kirani akan nazo na dauke ki, so dana zo naga kin tasani a gaba da kallo so I thought bake bace bama." Ta kara hade rai, "Am sorry Doctor but ni ba inda xan bika saboda Mummy tace man driver ta aiko ba kai ba." Yayi yar dariya gamida zaro wayarsa aljihu yana adjusting glass dinsa, ya dadanna wayar kafin ya sa a speaker, Mummy ce ta daga, "Hello Mummy ina wuni?" Mummy tace "Lafiya lau Dr Hafiz, har ka ganta?" Yace "Eh naganta Mummy gamu nan tare gida zan kaita ko?" Tace "Eh, amma don Allah kayi hakuri doctor na taso ka aiki nace ka maidata, wallahi babu yadda zanyi ne na kasa samun driver dina don na kirashi yace man zaije har dai na gaji da jira ashe shi baima je gidan ba, sheyasa na kiraka am sorry to disturb your work." Yayi murmushi yana tsareta da idanu, "Mummy bakomai ay yanxu mun zama daya karki damu.... yauwa thank you." Daga haka ya katse wayar yana kallon Khadija wacce tunda ya fara wayar take binshi da kallo cike da mamaki, wai me yake nufi? Shi zai kaini gida kenan? Da guntun murmushi a fuskarsa ya kamo wheelchair din tata ya fara janta a hankali, "Tou malama Khadija yanzu kin yarda xaki bini kenan?" Gyada kai tayi kawai har suka isa inda ya paka motarsa ya bude gaba ya taimaka mata ya sata motar sannan ya nade kaken ya sashi booth ya zaga side dinshi ya rufe motar har yanzu fuskarshi murmushi yakeyi, bayan ya harba titi saida tafiyar tayi nisa sannan yayi magana amma can kasan makoshi, "Are you hungry? Zan tsaya restaurant na karbi abinci." Juyowa tayi taga yana magana sannan ta girgiza kai a hankali, "A'a thank you." Daga haka suka cigaba da tafiya, can sai kuma taga sun shiga gidan mai, suna nan tsaye ana zuba masu man sai ya juyo yaga idanun Khadija sunyi rau rau, da mamaki yace "Khadija lafiya?" Da sauri ta share hawayenta batasan lokacin da tace "Don Allah ka ara man kudin in ba matar can." Bata taba tambayar namiji abu ba yau ta tsinci kanta da hakan, don ko bakada imani matar sai ta baka tausayi, ta window ya dan leke ya kalli matar yaga tana kallonsu take ta bashi mugun tausayi, yasa hannu aljihu ko tsayawa kirgawa baiyi ba ya mika ma Khadija, bude motar tayi tana shafar fuskar yaron sannan ta mika ma matar kudin, "Gashi nasan ba lallai bane suyi maki maganin matsalarki amma ina rokon Allah yayi maki maganin duk wata damuwar da kike ciki ya yaye maki alfarmar annabi (SAW)." Matar babu abinda takeyi sai godiya ta sa6i yaronta wanda daga gani baida lafiya ta goya shi tana goge hawaye, bata tsammaci samun kudi koda rabin haka bane a yau, tayi masu sallama gamida godiya marar adadi sannan ta juya ta cigaba da tafiya, kofar motar ta rufe tana bin matar da kallo cike da tausayawa, daga nan Dr Hafiz yayi payment sannan suka cigaba da tafiya. Saida yayi yar tafiya kadan sannan ta juyo tana murmushi, "Nagode sosai, idan muka je gida zan mayar maka." Murmushi yayi mata ganin yadda take kokarin maida hawayenta ita ta rasa yaushe ta zama mai tausayi haka sosai? "tou ay ni kaina bansan ko nawa bane saidai ki maida man da wani abin amma ba kudi ba." Kallonsa tayi tana auna maganarshi kafin tace "Ay ba kudi zaka bani ba, amma dai me kakeso?" Lokacin ne yayi daidai da zubar hawayenta, dan jim yayi yana kallonta kafin yace, "Yanzu a bar maganar bashin nan Khadija, first of all ki goge hawayenki." Batayi masa musu ba tasa hannunta mai lafiyar tana ta faman goge hawayen amma kamar ana kara tunkudo su. Har suka isa bakin restaurant din Khadija na kuka saida ya kashe motar kafin ya juyo yana dubanta gaba daya jikinta rawa yakeyi, hanky ya ciro daga aljihunsa ya mika mata, saida tayi kamar bazata karba ba sai kuma ta amsa ta fara share hawayenta, gaba daya tausayi take bashi ko ba'a fada ba yasan tana cikin kunci da bakin ciki, yasan ba ganin almajirar nan kadai yasa ta kuka ba, dama dai akwai abubuwa cunkushe a cikin zuciyarta, tabbas kukan nan nata yanada nasaba da mummunar kaddarar data afka maka kwanakin baya amma bawai don an mata fyaden kadai take kuka ba akwai connection gameda fyaden. Saida ta gama share hawayen sannan ta mika masa maimakon ya amsa sai ya dauko bottle water dake ajiye gefensa ya mika mata, "Wash your face Khadija, kar mu shiga cikin mutane suyi tunanin sato ki nayi ko kuma cutar dake zanyi." Khadija batasan lokacin data maka masa wata uwar harara ba, (ashe ma satowa) ta fada cikin ranta, dariya ya fashe da ita, "Ashe dama kin iya masifa? Irin wannan harara haka ay sai kisa tari ya sarke ni!" Bata tanka sa ba ta karbi ruwan ta bude kofar motar ta wanke fuskarka yana zuba mata har tagama, juyowa tayi bayan ta mika masa murfin kwalbar tace, "Thank you." Haka kawai sai ta fara dana sanin kukan da tayi a gabansa ta fara tunanin kar ya fara raina mata wayau ko kuma makamancin haka. Amma duk da haka bayan tayi kukan sai takejin ranta yayi sanyi zuciyarta tayi mata wasai, tana Kallonsa ya bude motar ya fita ya zagayo ya dauko wheelchair dinta sannan ya gurgurota a gabanta, "Muje ko? Bari na taimaka maki." Da sauri ta girgiza kai, "Ay da ka barni a nan ka tafi ka karbo ni zan zauna a mota." Ta mirror take kallon kanta yadda kwayar idanunta ta kada tayi jajir, sannan ita sam bataso a ganta akan wheelchair tazo restaurant, "A'a baza'ayi haka ba Khadija, ya kamata kizo muje tare nasan bakici komai ba, kuma nasan halinki sarai yadda Mummy ke fama dake akan abinci kullum, yanzu kuma ga kukan da kika sha in ba so kike abu biyu ya hade maki ba ga damuwa ga yunwa su karasa rayuwarki gaba daya." Da kamar bazata je ba can kuma ta gyada kai da haka yayi mata murmushi sannan ya taimaka mata ta hau kan wheelchair din kafin ya rufe motar, a hankali yake janta as if idan ya tura ta da karfi zataji zafi, wuri ya sama masu kusada window suka zauna kafin ya bada order abinda zasuci dan yasan ko ya tambeyeta ba lallai bane ta fada masa abinda takeso, shiru duk sukayi alamu sun nuna Khadija ta koma duniyar tunani, dan snapping finger dinsa yayi yana daga mata kai, "Hello what happened?" Da sauri ta girgiza kai tana kakalo murmushi, "Bakomai am fine." Ya tsareta da idanu, "Are you sure?" Ta sake girgiza kai da sauri, "Am sure." Suna nan aka kawo masu order dinsu, jollof din shinkafa da half chicken sai salad, saida suka gama cin abincin ya biya sannan yajata suka tafi mota, bayan sun shiga Dr Hafiz ya juyo yana kallonta, "Dr Haiydar yace man kina son fashion and design, kina son na siya maki keken dinki?" Bata san lokacin data daga kai ba tace eh, sai can kuma ta tuna me tayi, ya za'ayi ta bari Dr Hafiz ya siya mata keken dinki? After all bada paper ake siya ba, da sauri tace, "What i mean is inaso, amma bawai aje a siya ba...." dariya kawai Dr Hafiz ya fara yi, "Karki damu zan siya maki, I will make sure nayi maki dukkanin abinda na san zai saki farin ciki Khadija..."  da sauri Khadija ta girgiza kai, "A'a don Allah kar ka siya, kai kasan bazan iya dinki ba and I also need proper training." Yayi murmushi "Tunda na hadu dake Khadija ban taba ganin farin cikinki ba sai da Dr Haiydar yayi man expressing how happy you are, and I promise myself am going to make you happy no matter what Khadija, you don't need to start using it now if you don't want to, xaki iya aje shi har sadda kikeso kinji ko?" Ya karasa yana mata murmushi sosai, gyada kai tayi cike da farin ciki marar iyaka, kafin su wuce inda zai siyo mata keken kamar yadda yayi mata alkawari, aikuwa haka akayi keke ya siya mata har guda biyu yayi making payment da komai ba tare da ya tsaya jin tsadar su ba bai ma damu da wata tsada ba shidai burinshi kawai yasa Khadija farin ciki wanda yasan cewar her happiness lies in his happiness, he don't know how it happened but all abunda ya sani shine ya kamu da kaunar Khadija kuma kauna bata wasa ba, sai daya ya gama ya biya motar da zata daukar masu har gida suma ya biyasu kudin dauka, sannan yaja ta mota babu abinda Khadija keyi sai share hawayen farin ciki, daidai harabar gidansu yayi parking yana kallonta, "Zan maki registration inda zakiyi training dinki na cikar burinki." Tayi murmushi, "Dr banida bakin da zan gode maka akan abinda kayi nagode sosai sosai, registration dinma na gode." Hanky dinsa wanda ke hannunta da ya bata dazu ta share hawayenta ta dalilin kuka da tayi ta mika masa, kin karbar hanky din yayi yace, "Shi hanky din kyauta na baki, duk sadda kikayi kuka zaki shiga mutane sai ki goge hawayenki dashi, amma da bashina na dazu da kudin registration wata rana zance ki biyani." Ya karasa yana sakar mata wani irin kayattacen murmushi, itama murmushin ta mayar masa kafin ya zagayo ya bude mata ya taimaka mata ta hau kekent, Mama Hauwa ce ta fito ta jata ciki, nan kuma yasa mai gadi ya shigar mata kekenta duka biyun cikin gida, bakin motar ya tsaya yana kallonta har saida suka shiga ciki kafin a hankali ya juya ya shiga motarsa ya tada ya bar gidan....

-------

Kusan rabin jikinta a nashi yake wai kuma a haka kallo take, robar ice cream ce a hannunsa yana bata a hankali duk da ya hanata shan abu mai sanyi amma akan ice cream sai su tada gari ta dinga mishi kuka kenan indai bata sha ba, wani lokaci da gangan zai ki bata ice cream din sai ta juyo ta kalleshi sai ya dan sunkuyo yayi mata peck a kumatu kafin ya sake bata tasha. Zuwa yanzu soyayyar da Gimbiya Hoodah ke wa Sultan ta kara linkuwa kan wacce take masa a da har ma ji take duk soyayyar da tayi masa ba komai bace compared to yanzu da take jinsa har can kasan ranta, daga karshe ma ta kwantar da kanta saman kafafunsa tana kallon fuskarsa dauke da kyakkyawan murmushi tace, "Ka gaji ko?" Aje ice cream din yayi kan center table din parlon yana kallonta, "Abba fa yazo na fada maki kuwa?" Da sauri ta kalleshi, "Abbana? Shine ko ka fada man inje in gaishe shi?" Yayi yar dariya, "Bai iso da wuri bane shine ma yayi min umarni akan kar na fada maki sai gobe da safe, amma yace da kinji sakonsa da safe ki garzaya wurinsa don yayi kewarki da yawa." Wani irin dadin murna ta fara yi wane an mata albishir da gidan aljanna shi kuwa Sultan kallonta ya tsaya yi fuskarsa cike da annuri. Sai kuma ya bata fuska, "Nifa gaskiya Hoodah ina da complain, an jima rabon da kice man I love you..." ya kara tsuke fuska, tayi dariya, "La abinda ka tsiro dashi yau kuma kenan? Tou shikenan kayi hakuri kaji?" Ya kara bata rai, "Aww tsurowa ma nayi kenan? Wato kin daina sona ma kenan ko?" Ta fashe da dariya sosai, kara tsuke fuska yayi yana kokarin dagata daga jikinsa ta makalkale shi, "Tou wai bana baka hakuri ba?" Turbune fuska tayi shima ya bata rai, "Ay ban hakura ba tunda har yanzu kin kasa furta kalaman da nake son ji a bakinki." Gani tayi dai da gaske yayi fuska  sai abin ya burgeta ba kasafai take ganin fushinsa ba da wuya kafin tagani. Akwai ranar data bashi haushi sosai yace mata, "Hoodah sonki da nake yasa bana iya fushi da ke, amma duk ranar da nace zanyi fushin da ke abin bazaiyi kyau sheyasa ban taba yarda har ma in yarda inyi fushin dake." Kara makalkale shi tayi tsam, "Tou wai fushin na menene? Ina sonka Sultan, I love you so much! Shikenan happy?" Da sauri ya kalleta amma can kasan makoshi ta furta, "Ay banji ki ba, maimaita." Dariya sukayi dukkansu ta jawo kansa ta saita bakinta daidai kunnensa ta fada cikin wani irin tsawa, "Ina sonka mijina!" Wani irin toshe kunnensa yayi ita kuwa ta kyalkyale da dariya, ji tayi ya rungumeta tsam a jikinsa, bata ankara ba taji ya dagata duk da katon cikinta kuwa bai ji nauyinta ba, idonta a rufe sai data ji karar kashe tv tayi sauri ta bude idanunta tace, "Ina zamuje?" Dariya ya danyi yana kissing kumatunta sosai, sannan ya duko daidai kunnenta yayi maganar kamar rada rada, "Bacci zamuyi mana naga yau soyayyar da gaske kike yinta." Dariya kawai tayi ta kulle idanunta hade da kara makalkale shi wani irin farin ciki yana sauka cikin zuciyarta....





Na gode da addu'oinku Allah ya bar zumunci🤝❤️

Thursday, 12 August 2021

YAR AGADEZ PAGE 44

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 44}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com




Kura ma ceiling idanu tayi dakin bakajin karar komai sai karar machines alamun ICU, jikinta in banda ciwo babu abinda yake mata hawaye kuwa sunkasa tsaya mata, kanta nade yake da katon bandage, fuskarta manne da oxygen mask, drip kuwa ansa mata kala biyu daya na ruwa daya na jini duk suna shiga a kowane hannu, zagaye kwayar idanunta takeyi sannan ta tabbatar a asibiti take, "Alhamdulillah kin tashi?" Taji muryar wata ta fada a gefenta, matar ta share mata hawayen da suka kasa tsaya mata, hannu Khadija tasa ta zare oxygen din a hankali bakinta na kyarma ta furta, "Where's my Mummy?" Dafa ta tayi ta mata murmushi, "Bari na kira Doctor, yanzu zaizo ya duba ki, you're a brave girl everything will soon be alright sannu ko?" Ta fita ba jimawa ba sai ga Mummy ta shigo kamar an tunkudo ta, dah da farko tsaye tayi saboda itama har yanzu ba karamin kuka take ba, tsaye tayi bakin kofa tana ta goge hawaye saida ta tabbatar kukan ya dan tsagaita sannan tayi ajiyar zuciya ta karasa ciki, a hankali ta tsaya gefen gadon tana kare mata kallo, Khadija ta juyo da fuskarta suka hada idanu sai ta fara kokarin tashi zaune, Mummy tasa hannu ta dafata tana ce mata, "No don't get up, an maki surgery a kasanki doctor yace mana karki yi moving Khadija, wait sai wurin yayi sauki tukunna." Ko sauraren Mummy batayi ba tana sheshekar kuka tana kokari tashi zaune, Mummy ta riketa gam tana girgiza kai hawaye na faman zubowa daga idanunta, "Why am I still alive?? Why do you save my life? Ay da bari kukayi na mutu meyasa kuka ceto rayuwata? Meye sauran amfani na kuma? Rayuwata batada wani amfani kuma." Ta fashe da wani irin kukan fitan hankali, da sauri Mummy tayi hugging dinta, "Karki ce haka Khadija, ba kanki aka fara fyade ba, kuma kaddara ce bata wuce kan kowa so please ki daina fadan haka Khadija rayuwarki nada sauran amfani a garemu we all love you so much...." ture Mummy ta shiga yi tana shesheka, "No! Mine is different Mummy! My own father raped me! He molested me over and over again, mahaifina! How do you expect me to continue living my life? Just how?!" Mummy ta kara rungume ta zuwa yanzu ta kasa controlling kanta kuka takeyi kamar ranta zai fita, a hankali aka turo kofar dakin Doctor ne ya shigo nurse na biye dashi a baya, Mummy ta janye jikinta daga na Khadija tana share hawaye tana kakalo murmushin dole, "My patient how are you feeling today? And why are you crying?" Ya furta yana kokarin zama gefenta, bata bashi amsa ba sai ma kukanta da ya karu, umarni ya ba Mummy da nurse din akan su bashi wuri ya ga patient din tasa zai kirasu back, fita sukayi shi kuma ya maida dubansa ga Khadija wacce ke shar6ar kuka kamar wacce ake yanka ma naman jiki. Dr Hafiz bai ce mata komai ba yabita da idanu har sai data tsaigaita da kukan da takeyi sannan yace mata, "Feel better?" Ta gyada kai tana share hawaye, murmushi yayi sannan ya dauko ruwan dake cikin bottle kan side table din dake gadon da cup ya tsiyaya mata half cup ya mika mata, "Drink thisvwater you'll feel much better." Ta karba a hankali tasha ta mika masa, gyara zamansa yayi sannan yace mata, "Komai da kikaga ya faru da mutum kaddara ce, Allah yana san bawa ya dauki kaddara mai kyau ko marar kyau, duk abinda ya hukunto maki ki karba hannu bibiyu sai kiga komai yazo maki da sauki...." girgiza kai ta shiga yi wasu sabbin hawayen na wanke mata fuska, "Doctor mahaifina.... he....he...." kasa karasawa tayi saboda kukan da yaci karfinta, don dole ya mike ya kira nurse taje ta siyo allurar bacci akayi mata, itama tana fizge fizge da surutai babu abinda take fadi sai, "Mahaifina ne.... mahaifina ne... shine ya cuceni.." abu daya take ta nanatawa babu abinda Mummy keyi sai kuka wane an aiko ta, sai can bacci yayi gaba da Khadija sai sannan Mummy ta samu yar natsuwa cikin ranta, ta jima a nan zaune tana bin Khadija da kallo kafin Doctor din yace, "Meet me in my office Hajiya I want to speak to you privately." Gabanta ya dan fadi can dai ta dake tace "Ok Doctor."  Daga haka yayi gaba nurse din ta sake gyara Khadija ta chanza mata drip sannan ta fita. A corridor ta iske Zarah, Hoodah da Hafsat zaune jugum jugum ko wane ya rafka tagumi, Mummy ta dafa Hoodah, "Hoodah ya kamata ki koma gida kije ki huta sai Zarah ta tafi dake ta bude miki dakina, you need rest my dear you see your condition bai kamata kina stressing kanki ba...." Hoodah tayi murmushi "An not stressed I am okay Mummy." Mummy zata sake magana Zarah tace "Don't worry Mummy she's fine." Mummy ta kakalo murmushi "Okay, em... Zarah ga Khadija nan please look after her zanje in dawo." Ta gyada kai Mummy ta wuce inda ta tadda Ashraf, Yasir da Sultan suma suna zaune ko wane da tunanin da yake, tace masu "The Doctor wants to see me, I think you should come with please," suka gyada kai suka mike a sanyaye. Da sallama suka shiga dakin Dr Hafiz da alama su yake jira yana ganinsu yayi murmushi yace "Please come in." Suka shigo a sanyaye, bayan sun zauna ya sauke ajiyar zuciya, "Kamar yadda kukasani Khadija was molested and abused, lokacin da aka kawo mana ita munyi mata duk wani gwajin da ya dace muyi mata thankfully she's okay, hiv negative etc. Mutumin ya halbeta ba a ciki ba iyaka which badly affected her womb, I really don't want to say this to you amma dole ku sani..." Ya numfasa gaba daya gabansu faduwa yakeyi, "Na farko shine Khadija bazata taba haihuwa ba her womb was damaged completely, sai buguwar da tayi da ya wurga ta kasa ta bugu a bayanta whiich badly affected her spinal code, zaiyi wuya ta sake takawa I thought we can fix it but sadly we couldn't, she has to be on wheelchair for the rest of her life, am so sorry for this news ba yadda zanyi dole in fada maku.... and lastly, she broke her hand ya taba mata jijiyar hannu which caused the side to be paralyzed in zaki kula dazu tana ta kokarin tashi zaune ta kasa sannan zaki lura hannun hagunta kadai take dagawa dayan bata daga sa, inshaAllahu with time zamu dinga mata physiotherapy zata dawo da hannunta, sai kun dinga daurewa shima maganarta ya danyi affecting amma kadan thankfully ba da yawa bane in no time zata dawo da hannun and her speech will be clear. Sai kun bata kyakyawar kulawa sannan you have to support her through this journey har Allah ya iyakance mata, maganar karshe you don't have to tell her now zaku barta har sai taji sauki in ba haka ba it will worsen her condition, keep any bad news apart just try and make her happy..." zuwa yanzu Mummy bata iya kwakwaren motsi, a sanyaye Ashraf da Sultan suka mike suma kansu sun saka magana suka fice daga office din,  a hankali Yasir ya kamo Mummy wacce ta kura ma Doctor din idanu tun dazu, ta mike tsaye Yasir yace "Mungode Dr." daga haka yaja mahaifiyarsa wacce ke behaving kamar marar lakka, bakin kofar dakin ICU din ya zaunar da ita sannan ya zauna gefenta hannunshi cikin nata, yana zama ta jinginar da kanta bisa shoulders dinsa ta runtse idanu wasu hawaye masu shegen dumi suka gangaro mata, suma su Zarah hankali tashe suke tambayar lafiya babu wanda yake da energy din magana saidai Yasir ya bisu da idanu kafin yace, "Please don't stress Mummy with questions for now, yanzu Mummy tana bukatar hutu in ba haka ba she will also fall sick, please ku kula da ita da kyau." Ya fada yana mikewa tsaye, da sauri su Zarah suka zauna gefenta sai faman magana suke mata kamar ma bata san sunayi ba, karshe ma da suka isheta sai ta mike tsam batace dasu komai ba tayi dakin ICU din ta shiga a hankali, jingina tayi da kofar tana kallon Khadija wacce ke bacci da alama tayi nisa a baccin nata, a hankali take tafiya har ta isa bakin gadon har yanzu bata dauke idonta a kanta ba, zama tayi tare da kamo hannuwanta ta damke tare da dora kanta bisa hannun ta lumshe idanu, dagowa tayi tana kallonta hawaye na gangaro mata tace "Khadija ko kinyi ma wani ko wata laifi ne? Ko kuwa Allah kikayi ma laifi?" Mummy ta tambayeta tana tsareta da idanu kamar tana jinta, tafi minti goma tana kallonta kafin ta goge hawayenta da sauri ganin ta fara motsi...

2 DAYS LATER...

A hankali ta bude idonta ganin Mummy gefenta ya sanya ta fara kokarin tashi, Mummy tace "No Khadija don't move please, na fada maki da aiki a kasanki ba'a son yawan motsi." Daina motsin tayi ta koma ta kwanta tana bin Mummy da kallo, can tace "Can I ask you a question?" Mummy ta gyada mata mata kai "Sure darling what is it?" Khadija tace, "Bayan na suma what happened after that? I can't recall anything abinda kawai na iya tunawa kawai shine ina jin ana tafiya dani bisa emergency bed but daga nan bansan meyafaru ba after that." Mummy tayi murmushi gamida kamo hannunta, "Nothing much sweetheart, meyasa kikeso kisani yanzu?  Ki bari idan kinji sauki I will tell you everything, but for now you rest and rest, that's all you need to do for me okay?" Khadija tayi murmushi, "Okay but please one last question Mummy?" Mummy tayi ajiyar zuciya tace "Okay ya akayi?" Tace "Where's my dad?" Shiru Mummy tayi na yan seconds kafin tace "He's where he deserves to be right now, he is in police custody Khadija, kuma InshaAllah za'ayi masa hukuncin daya dace dashi so please don't worry okay?" Khadija tace "I know, can I see him amma?" Mummy ta bata rai, "Me xakiyi masa after what he did to you he doesn't deserve to be called a man or a father!" Mummy ta fada a fusace, Khadija tace "I know Mummy, I just wanted to tell him some things he should know, sannan to tell him how much hate I have for him in my heart!" Mummy ta shafa kanta, "Don't stress yourself because of that monster, that's exactly how he did to my sister, he dated her for 5 months thinking he was the right guy for her, but then he showed his true colors, he did exactly what he did to you." Ta fada wane cikin bacin rai, Khadija feeling hurt tace "Then why did you let him get away with it back then?" Mummy ta share guntun hawayenta tace "We tried our possible best Khadija, but that man left this country, kinsan dai tunda ya riga ya gudu wata kasa we don't have any right to do something har sai dawo." Khadija tace "He's wicked and heartless," Mummy ta kakalo murmushi "Hakane, saidai babanki ne no matter what ba'a chanza ma tuwo suna, addu'a kadai zaki taya shi Allah ya shiryeshi kinji??" Ta gyada kai, Mummy tace "That's my brave girl, now what do you want to eat?" Ta girgiza kai, "Nothing bana jin yunwa." Mummy tace "A'ah, you have to eat koda liquid ne don kisha magungunan ki." Tana fadan haka ta mike ta nufi waje don samo mata wani abu har Mummy ta kai kofa Khadija ta tsaida ta, Mummy ta juyo da murmushi saman fuskarta tace, "Do you need something?" Khadija tace "Can I speak to Zarah and you Mummy?" Mummy ta dawo kusa da ita tace, "Meyafaru haka? Me kikeso kice mana?" Khadija tace "I will say it if Zarah is here." Mummy tace "Alright let me get her," Mummy ta tafi ba'a juma ba sai gata itada Zarah sun shigo, Khadija tace so take ta jingina a gadon Mummy ta taimaka mata, bayan ta gyara zaman nata ne ta kallesu sannan ta fara magana, "A wannan zamanin baza'a taba samun butulu ba kamar ni...!" Cike da mamaki Mummy ta matso kusa da ita ta zauna harda rike mata hannu tace, "Subhnallah Khadija! Ki daina furta kalmomi makamantan haka! Kar ki sake kiran kanki butulu a ina kika yi butulci? Kuma wa kikai mawa? Please keep that word out of your mind!" Girgiza kai Khadija ta shiga yi, "It's true Mummy! Nayi maku butulci, ban kyauta ba I am ashamed of myself now I don't deserve your love Mummy Instead I deserve your hatred!" Mummy ta kalle ta cikin shock idanunta a waje tace, "Why are you talking in riddles? Explain yourself!!" Zarah tace "Khadija maganar nan ya wuce basai kinyi wani bayani ba please a manta da abinda ya riga ya wuce..." Mummy ta juyo tana kallon Zarah sannan ta mike tsaye ta isa dab da ita tace "What are you hiding from me Zarah? Me Khadija tayi miki da ni banida labari?" Zarah ta hadiye kukanta amma still saida stubborn one ya zilalo mata, Mummy ta girgiza ta tace, "Talk to me Zarah! What happened between you two?" Zarah dai batace komai ba sai kukan da takeyi, Mummy ta juyo tana kallon Khadija, Khadija ta fara magana cikin karfin hali kanta na kasa, "Bayan na dawo hutu sai naga Ashraf a gidanmu at first I was pissed off sai daga baya na kamu da sonsa! I started becoming jealous of Zarah ina neman hanyar da zan raba su, I even drugged him, na kwanta dashi saboda Zarah taji haushi ta rabu dashi, but none happen! I keep plotting against Zarah even after I find out we are not related, ban tsaya a nan ba na rubuta mummunar letter lokacin bikinta bayan ta tare kafin na dawo gida, a letter din na rubuta abu mafi muni inda na sa suka fara fada tsakaninsu bayan nan naje nayi photoshop fuskar Ashraf da wata kafira tsirara na aje a wardrobe din Ashraf, I guess sun gano ni sheyasa suka shirya, despite what I have done Zarah bata taba fada maki ba ta rufa man asiri cuz tasan idan kika sani zata bata relationship dinmu dake! I know sheyasa abinnan ya faru dani my father raped me meyafi wannan bakin ciki? Ina girbar abinda na shuka gradually! Da haka nake cewa Mummy ki yafe man nasan I don't deserve your forgiveness. But you are a good person kin rike ni fiye da yadda kika rike yayan cikinki amma ga abinda na saka maki dashi, please forgive me Mummy na tuba...!" Tunda Khadija ta fara magana Mummy ta zama shocked tsaye tayi har ta gama saurarenta kafin ta fara ja baya a hankali, "Khadija...! Dama ashe haka kike?" Khadija ta fara girgiza kai ga ba halin tasowa, "Mummy don Allah kiyi hakuri ki yafe man wallahi na gane kuskurena! And I love you please don't punish me by not forgiving me I cannot bear it..." Zarah ce ta taro ta ganin har ta kai kofa amma ina kafin ta karasa har Mummy ta fita da sauri daga dakin, Zarah ta kwala mata kira sannan ta bita a guje, Khadija kuwa kokarin moving takeyi har sai da ta kai karshe gado ta zube akan gadon saboda bata iyawa, wani kuka na fitan hankali tasa tana fadin, "I made a huge mistake please forgive me Mummy!" Kuka take kamar ranta zai fita ji take gaba daya duniyar ta isheta kuka ta dinga rigza tana kiran Mummy har baccin wahala ya dauketa.

Tun daga ranar Mummy ta fita harkar Khadija, gaba daya ta janye daga jinyarta da takeyi ko tazo saidai tazo ta duba ta amma bata wani bata kulawa kamar da, amma komai tanayi duk wani payment da medication dinta bata fasa ba, saidai ta chanza mata sosai, Zarah da Hafsat kadai ke faman jinya Hoodah kuma sun koma itada Sultan cikinta ya cika wata takwas cip sheyasa ma Mummy tace su tattara su koma haka nan. Abinnan ba karamin damun Khadija yakeyi ba har sunyi sati uku yau babu abinda ya chanza itama Mummy taji babu dadi amma ta dake she's just so angry at her. Satinta hudu chip aka sallameta sun siya wheelchair sannan za'a dinga dawowa physiotherapy sau biyu a sati. Khadija ba karamin shiga senses dinta tayi ba duk ta chanza ta zama shiru shiru da ita. Zarah ma sun tattara sun koma Agadez itada angonta Ashraf.

--------

A hankali ta bude idonta a daidai lokacin ne duk abubuwan da suka faru a daren jiya suka dawo mata, wani irin faduwar gaba taji at the same time kuma zuciyarta fal take da farin ciki marar adadi ji take kamar a mafarki. A hankali ya turo kofar dakin ya shigo da wani irin kayataccen murmushi a fuskarsa, saurin kauda kai tayi tare da lumshe idanunta sabuwar kunya taji ta ziyarce ta, wata irin kunya taji wacce bata taba zato zataji ba. Zama yayi gefenta har lokacin ta kasa bude idanunta, "Princess ba gaisuwa? Ko yan masifar ne suka taso?" Batasan lokacin data bude idanunta ba harda murguda baki, "Wai suka taso sai kace wata mai aljannu!" shiru yayi kawai yana binta da kallo yana jin sonta na kara shigarsa yana ratsa ko wace jijiya da kuma ga6o6insa. Saida ta bari ta mike tayi hanyar kofa sannan tace "Ina kwana?" Tana fadan haka sai ta fita daga dakin gaba daya. Yar dariya yayi kafin ya mike ya shiga bathroom don yin wanka. Side dinta ta tafi ta wanke bakinta tayi wanka, har ta karasa wankan nan murmushi bai bar lips dinta ba kaunar mijinta na sake linkuwa a cikin ranta da ruhinta. Tana fitowa ta shafa creams wanda Mummy tasa akayi mata hadin kamshi ta shafa ta fesa sprays kala kala a jiki, wata red gown ta atamfa ta saka ta daura dankwalinta tasa costumes, kwalli kawai ta shafa sai lipstick kadan tayi kyau ba kadan ba, wayarta ta dauka ta fito tana ta kamshi dama gidan baiyi wani datti ba dan kara kimtsa shi kawai tayi sannan ta tafi kitchen tana faman tunanin abinda zata dafa da rana. Cak ta tsaya tana bin dining din da kallo yadda ya cika shi da abinci yayi setting dinshi gwanin ban shaawa. Yadda kuka san shine matar gidan, wani irin dadi taji a ranta, zuciyarta fal haka ma fuskarta ta kasa daina murmushi haka ta juya da niyyar tafiya side dinsa sai gashi ya shigo waya kara a kunnensa, babu abinda ke tashi parlon sai kamshin turarensa, binshi tayi da kallo sai ma taga bai taba mata kyau ba irin na yau sanye yake cikin wata dakakkiyar shadda blue color hular kansa ta shiga da kayan da ya sanya, yanata waya fuskarsa cike da annuri sai murmushi yakeyi, take sai taji tukukin kishi ya taso mata wai dawa yake waya haka sai wani murmushi yakeyi? "Ah haba na isa in manta dake?... haha kin fiya abin dariya wallahi... yanzu dai kinsan tsada garemu ki biya in kinaso a bata." Jin alamar da mace yake waya sai kawai tasha kunu ta zauna kan dining gamida zuba abincin tana wasa dashi gaba daya sauraren conversation din nasa takeyi. Tun yana tsaye yana wayar har yaja kujerar dining ya zauna yana fuskantarta yafi minti sha biyu sannan taga ya katse wayar, kallonta yayi yadda take ta juya abincin fuskar nan a tamke wane tana jiran dambe, yar dariya yayi sannan ya matso gefenta ya zagayo da hannayensa saman wuyanta yana kissing gefen fuskarta, "Sana'ar ta taso kenan?" Wata irin harara ta watsa masa ta gefen ido tana ture hannayen nasa dake sargafe saman wuyanta. "idan ka gama wayar sai kazo kaci abinci, ko wayar ta kosar da kai ne?" Wata dariyar ta su6uce masa ba shiri yana jin nishadi a cikin ransa, plate ya janyo ya tura gabanta, "Ayi hakuri ranki ya dade bata kosar dani ba yet, zanci abincin." Zuba masa tayi cikin masifa ta hankada masa plate din gabansa, murmushi yayi ya girgiza kai sannan ya fara cin abincinsa a natse, a hankali ko wanensu ya fara cin abincinsa gaba daya zuciyar Zarah cike take da tunanin dawa yake waya haka? Kodai Khadija ce ta kirashi da salon kara yaudara? Nan take taji zuciyarta har tafasa takeyi, "Zarah kodai in tafi wurin aiki ne?" Da sauri ta dago da wani irin expression a kan fuskarta tace, "Bangane ka tafi aiki ba, dama bazakaje aikin ba?" Danne dariyar shi yayi yana shan tea a hankali kafin yace, "Kin manta na dauki hutu wurin aikina? Amma naga kullum fada muke Zarah ba gara in tattara inawa inawa ba in koma wurin aiki ba? Idan baki ganina kila kin fi jin dadi," kallonsa takeyi kafin tace, "Tou ay kwana biyu bamuyi fada ba."  Batasan lokacin da maganar ta fito daga bakinta ba, murmushin data ga yanayi ne yasa tayi saurin cewa, "Idan wurin wacce kuke waya zakaje tou ka gayyace ta tazo gidannan kaga sai ku huce takaicin rashin ganin juna da bakuyi ba." Tana gama fadan haka ta mike da sauri ta tattara kwanukan tayi kitchen dasu don wankewa, gaba daya kishi duk yabi ya addabeta gashi yaki gaya mata dawa yake waya. Wanke kwanukan ta farayi duk ranta babu dadi, ba zato kawai taji ya rungumeta ta baya nan ta fara mutsu mutsu akan ya saketa, "Wai bakaga aiki nake ba?" Ya kara matse ta, "Tou kawo in tayaki wai princess fushin na menene? Kefa da bakinki kike cewa mun daina fada why can't we continue living that way happily?" Taji ya fara kissing bayanta da kanta lightly, tace "Ba kace aiki zaka koma ba halan tayi missing dinka tace ka dawo ta ganka?" Gimtsa dariyarsa yayi sosai kafin yace "Wai wacece wannan ake ta fushi akanta?" Ta kara hade rai "Wacce kuke waya dazu da ita mana! Sai wani narke murya kake kana kashe mata murya, indai haka ne gaskiya na fasa soyayyar da kai sai ka tafi wurinta tunda ita kakeso yanzu bani ba!" Ta karasa gamida murguda baki, a hankali Ashraf ya juyo ta, "Zarah da Hoodah fa nake waya, wannan kasa da murya da kika inayi nace mata ay bacci kike kar na tashe ki, Zarah a tunaninki zanyi waya da wata a gabanki nasan daga ni har ita bazamu tsira ba wurinki? Besides ni matata kuma princess dina kawai nakeso, ita kadai ta samu damar mallakar zuciyata." Harara ta watsa masa duk da cewa fuskarta dauke take da murmushi alamar taji kunyar abinda ya faru, "Ni ka daina man haka kunya nakeji, sai kayita man rashin mutunci sai kuma a dawo ana cewa ana sona ehe!" Dan peck yayi mata a goshi zuciyarsa cike da farin ciki sannan yasa hannayensa ya zagayo dasu saman waist dinta ta sunkuyar da kanta fuskarta dauke da murmushi, Ashraf yace "Niii Ashraf yaushe nayi rashin mutunci? Ya zaayi in wa matata rashin mutunci duk yadda nake kaunarta?" Yar hararar wasa ta masa, "Da wannan maganar dama kawai hakuri ka bani da yafi," hancinta yaja yana dariya, "Kiyi hakuri kinji princess? My love, my chicken peri peri, my curry, my onion..." wata irin dariya takeyi har dukewa takeyi shima yana tayata hugging dinsa tayi tana kyalkyatar dariya shima yana dariyar yakeyi sai da tayi mai isarta sannan ta tura shi waje ta rufe kitchen din, "Go and watch football or news ka barni nayi aikina in peace abeg!" Tana juyo dariyarshi yana fadin "Your wish is my command your highness!" Aikinta ta cigaba da yi cike da nishadi kafin wayarta ta fara ringing, AirPod dinta ta dauko ta jona a kunne tana dariya tace "Hello..." ta furta farin ciki mamaye a zuciyarta.. Can bangaren tace, "My Inlaw how far ya kike?" Zarah tace "Wallahi lafiya lau mai girma Sarauniya! Ko kin haihu ne mu taho?" Hoodah tayi dariya sosai tace, "Kaji ki da zolaya Fatima, ay kafin in haihu zan kiraki ki garzayo kece zakiyi raino!" Zarah ta kyalkyale da dariya, "Ba dole ba ay shima babyn bai isa ya fito ba sai uwarsa tazo!" Hoodah cikin dariya tace, "Gaskiya bai isa ba, yanzu dai ina wuni? Ya kuke? Ya amarci? Ya ango? Ina fatan ana kula min da yayan nawa yadda ya kamata?" Zarah tayi dariya cike da nishadi tace, "Wannan tambayoyi haka Sarauniyar mu? Hehe Tou komai kalau kalau wallahi ya gajiyanku?" Hoodah tace, "MashaAllah, ah gajiya tabi jiki ay ya me jiki kuma?" Zarah tace, "Haka akeso ay, me jiki dasauki alhamdulillah mungode fa da dawainiya Allah ya kara girma da arziki." Hoodah tayi dariya "Ah meye na godiya kuma? What are family for? Aa ni kam ki daina mun godiya." Zarah tayi murmushi kurum, Hoodah tace "Gaskiya Zarah you're a great person, dan zaman da mukayi asibiti na shaku dake we became good friends, tunda na dawo nakejin ba dadi I really miss you all." Zarah tace "Same here my dear, am glad we met, yanzu ay mun zama yan uwa." Hoodah tace, "InshaAllah... tou bari naje dama na kiraki mu gaisa naga kin wani manta dani kina ta amarci ko?" Zarah ta kyalkyale da dariya,  "Wallahi ba haka bane, nagode sosai Sarauniya, take care regards to sarki..." Hoodah tace "You too InshaAllah." Suka katse wayar zukatansu fes a haka ta karasa aikin ta kimtsa kitchen din sannan ta fito parlor.  Tana fitowa parlor taji an fizgo ta, a tsorace ta saki kara Ashraf ya saki dariya yace, "Lallai yarinyar nan kin cika tsoro, daga na jawoki sai ki kama tsorata? Wai dama raki gareki a haka zaki haihu?" Ta saki dariya, "Haihuwa kuma? A ina zan iya haihuwa yar yarinya dani?" Dariya ya kyalkyale da ita harda dukewa, ta saki baki galala tana kallonsa, can yace "Yarinya kuma? Kodai rowa zakiyi man? Nida nake sa ran by next year muna nan rike da babynmu?" Ta wangale idanu cikin wasa tace, "Ni Ashraf? Rufa man asiri in haihu ay nayi yarinya da haihuwa, banma iyawa gaskiya." Ya daga mata gira daya sama "Haka kikace? Tou ko nazo na gwada ne?" Kauda fuskarta tayi gefe tana wata irin dariya, "Kuut Ashraf ko kunya wani wai ka gwada, kuma mutum yana kusanto ni zan fasa ihu mai gadi ya shigo ehe!" Dariya yayi sosai yana hugging dinta ta waist a hankali ya fara matsowa saida ya zo gab da fuskarta tuni ta fara zille zille tana neman guduwa, "A'a ki tsaya mu gwada mana mugani, kinga kenan nan da wata tara cip lokacin mun gama soyayyar mu har mun gaji." Tayi dariya cikin jin kunya tace, "La la wai dama idan akayi aure rashin kunya akeyi wallahi da ba haka kake ba, ni ka kyaleni tafiya xanyi in kwanta in danyi bacci." Kara rungume ta yayi, "Me nayi nakawai inyi iskancin da hujja." Wara idanu tayi sannan tasa hannunta ta toshe bakinta alamun mamaki, "Na shiga uku nidai ba ruwana kar kaja man sharri." Dariya yayi yana faman kissing din kanta yana kara matseta sosai hade da lumshe idanu, "Ina sonki Zara'u sosai fa ba kadan ba." Dagowa tayi tana kallonshi wani irin kallo as in kallo na masoya wani soft look mai kwantar da hankali, hannu tasa saman zuciyarsa hade da lumshe idanu, "Ay ga zuciyarka nan na bugawa tana dim dim dim!" Shiru yayi yana kallonta, pecking lips dinta yayi lightly sannan yace "Tunda da gaske bacci kikeji muje mu kwanta tou." Kokarin zillewa takeyi tana dariya ya riketa gam; "Kaida wa?" Yace "Da matata mana." Murmushi yayi ya jawo hannunta suka tafi daki duk son zillewarta haka ta hakura suka kwanta hannunshi rike da nata kamar wanda akace za'a sace masa ita a haka bacci yayi awon gaba dasu....




Tou yan team Zarah sai ku shirya zuwa suna nan da wata tara nikuma yar team Khadija (zuba ido hade da tagumi)😔

Sunday, 8 August 2021

YAR AGADEZ PAGE 43

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 43)



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com





Biji biji take gani kafin a hankali ta bude idanunta, dakin duhu babu abinda ke ciki yafi kama ta kango don dai an shafe siminti, daure take gam bisa wata kujerar karfe wacce da alama tare aka gina ta da gurin don ko motsi daya bata iya yi bisa, dakin take bi da kallo kafin ta fara recalling abinda ya faru da ita, a rude ta fara kokarin magana taji ta kasa saboda an sa seal tape an daure mata bakin nata, wani irin tsoro ne taji ya mamayeta take ta fara kokarin moving daga inda take amma ina ba karamin dauri akayi mata ba, don dole ta hakura ta natsu gabanta na dukan uku uku, shiru tayi tafi minti sha biyar kafin taji an banko kofa da karfi, a hankali yake shigowa ciki fuskarsa sanye da mask baki, wandon jikinsa irin mai kusoshin nan ne sunyi zara zara sun jeru tun daga saman wandon har kasa, boot ya sanya shima black, hannunsa dauke da katuwar bindiga wasu maza majiya karfi sun kai uku suna take masa baya, suma ganinsu kadai ya isa yasa yan hanjinka su kada, tsayawa fada maku yadda Khadija ta tsorata bata baki ne har wata kyarma takeyi, yana zuwa daidai ita ya wani dora mata kafa bisa hannun kejerar da karfi ya sunkuyo yana binta da kallo, ihu takeyi ta cikin makoshi tana so tayi magana, a hankali ya zare mask din nasa nan take ta gane Alhaji Hamza ne ashe, wani irin girgiza tayi ta fara kyarma take ya kece da wata irin dariya yasa bindigar hannunsa yana shafa mata fuskarta da ita, "Khadija welcome to my life, tunda kika kawo kanki tou fa bakida mafita sai na gama abinda naga dama dake sannan zan kasheki! Hahahahah!" Ya kace da dariya, kuka ta fashe dashi take ya ba guards dinshi order akan su fita su bashi privacy, take duk suka fita suka kullo kofar, babu abinda takeyi sai kuka hannu yasa ya cire seal tape din da karfi ta saki kara cike da azaba, a hankali ya jinginar da bindigar tasa ya shiga kwance ta saida ya kwance tas amma banda hannunta dama shima akwai wani daurin daban akansa, hannu yasa ya damko mata hannu ta fasa ihu tare da kara sautin kukanta, tirje tirje ta fara yi cike da tashin hankali tace, "Don Allah ka kyaleni wai me nayi maka? I beg you in the name of Allah!" Fizgo ta yayi ta kusan fado masa numfashinsu na bugun juna, ta fara tirjewa tana faman dukewa kasa kuka take tana rokonsa akan kar ya mata komai ya rabu da ita, "Why are you behaving like a small child? Kar ki sake man tirje tirjen nan in ba haka ba sai na balla ki!" Kallonsa take da jajayen idanunta, "Baka isa kayi man komai ba sai na maka ihu! ashe haka kake? Mugu azzalumi macuci!" Hannunta ya damko yasoka akaifarsa ciki wani irin azaba taji yana ratsata, kuka ta fashe dashi gashi hannunta daure ballantana ta cire masa hannun nasa daga cakarta da yakeyi! Nan ya fara kokarin dagata tsaye tana tirjewa, nan suka fara yar kokowa ta dauka tayi nasara saida taji wani irin gigitaccen mari ya ratsa kuncinta, tsit tayi cike da shock marin na ratsata, kasa koda motsi tayi tana kura ma wuri daya ido, "Tashi!" Ya fada a fusace! Kin tashi tayi tuni hawaye sun wanke mata fuska har bata ganin gabanta, bata gama warkewa daga marin da yayi mata ba taji ya sake kai mata naushi har sau biyu a ciki, ihu tayi cike da azaba ta zube kasa, bata ankara ba ta sake jin wani naushin wanda yafi na farko don dole ta fara rolling kasa, "Ba'a ketare maganata! Duk abinda nace ayi dole a bishi ko ana so ko ba'a so!" Ya fada yana zaune dan nesa da ita ya dora kafa daya kan daya, "For the last time ki tashi! Banaso in sake maki magana!" Still tayi batada niyyar tashi don zuwa yanzu kwalwarta ta daina aiki. Ba zato ba tsammani sai ji tayi yana zaneta da belt, dukanta yake kamar Allah ya aikosa, jikinta ji take kamar ruwan zafi ne ake yayyafa mata a jiki wani irin radadi ne ke ratsata. Saida ya gaji don kansa sannan yawani damko mata gashinta da karfi ya dinga janta a kasan, wata katifa ce ke jingine a dakin ya sauko ta kasa take taji k'ura har cikin bakinta, cillata yayi bisa katifar da karfi dariyarsa taji wata irin dariya yakeyi, kamar a mafarki taji yana jan rigarta yana cigaba da dariyar mugunta, saida ya gama cire mata kayanta tas sannan ya shiga cire nasa, Khadija ta rintse idanunta tana kuka kamar ranta zai fita ga batada hannu balle tayi fighting back, nauyinsa taji bisa ita batasan lokacin da tasaki ihu ba cike da azaba tunda take bata taba experiencing pain irin na yau ba, sai da ya gama da ita sannan ya sauka a kanta yana wani irin dariyar jin dadi, "Hmm so you're a virgin I like that!" Idanunta rufe suke gam har ya bar dakin ya fita ya rufe da key, yana fita ta fasa wani irin ihu sannan tasa kuka kamar an aiko ta, jikinta gaba daya ciwo yakeyi banda ciwukan da yaji mata a wurare daban daban na jikinta, a hankali take kallon kasanta yadda jini yake jalala yana bin cinyarta ga shi ji take kamar wuta ce ake cinna mata a wurin, jikinta ta dinga ja cike da azaba har ta sauko daga kan katifar, tafi minti talatin a wurin zaune dirshen zuwa yanzu kukan ma yaki zuwa. Haka tayi zaune shiru tun tana ganin haske ta wata yar window guda daya dake dakin itama wata yar karama ce ko kan mutum bai shiga ciki har ta fara ganin duhu, tashi tayi ta sanya kayanta ko alamar bathroom bata gani ba balle ta shiga, kofar kuwa ta murda yafi a kirga taga ko zata bude amma ko motsi batayi, dole ta hakura ta koma kan katifar ta raku6e kamar mai jin sanyi ga wani irin tsoro dake shigarta, babu alamun motsi ko da na tsuntsu ne. Haka tayi kwana uku cikin dakinnan bata ji alamun shi ba, ga yunwa ta addabe ta ga kishirya ga fitsari, ga rashin sallah gaba daya a takure take, babu abinda ke cikin zuciyarta sai dana sani itama meya kaita daga haduwa da mutum sau daya ki biyo shi ba tare da kinsan ko waye ba!? Kwananta hudu tana zaune da daddare taji alamunshi a tsorace ta takure wuri daya zuciyarta na bugawa kamar zata hudu kirjinta, aikuwa shine don wata irin banko kofar yayi garam sannan ya maida yasa key ya dora key din can sama inda bata kaiwa, ita dai tana nan zaune har ya karaso ciki, gefenta ya zauna gab da ita yana binta da kallo, a tsorace ta matsa baya ya kuma matsowa ta matsa ya matso, da sauri ta tashi tsaye aikuwa yasa hannu ya damko mata gashin kanta wani irin gigitaccen ihu tasa sannan ta fashe da kuka sosai, da sauri ta zube a gurin tana jin zafin na ziyartar cikin kanta, "Get up!" Yamata umarni, kokarin mikar da ita yake amma tuni ta tashi da sauri har kyarma takeyi, hawaye ke kwarara daga idanunta har bata gani sosai tsabar yadda hawayen ke zuba, "Let's go to bed now!" Ta dake taki tafiya wani gogitaccen mari ya sakar mata mai razanarwa wani ihu ta kurma ba zato taji ya halbo ta ta fada kan katifar tim! Kayanta yake kokarin cirewa amma gam ta hana saboda dama ta samu ta kwance hannunta shi kuma bai ma lura ta kwance ba, zafin shigar dorina taji a jikinta dan dole ta kyaleshi ya gama dukanta sannan ya shiga zare mata kayan jikinta, sai da ya cire su tas sannan ya sake hawa kanta ya kara raping dinta a karo na biyu, ihu, kuka, yakushi, duka babu abinda batayi masa ba amma ina ko saurarenta baiyi ba saida ya gama abinda yayi niyya sannan ya sauka a kanta ya koma can gefe ya zauna yana maida numfashi. Ita kuwa nan tayi kwance ta kasa koda motsa yatsanta ne. Wata irin dariyar mugunta yake saki sannan ya mike ya fara sa wandonsa, "Kwadayi mabudin wahala! Kinga zuciyar nan tawa is as cold as stone, duk lokacin dana ga mace ta kwanta man a rai sai na cimma burina da ita sannan in kyaleta, in ma ta kama nayi dating dinta zanyi as long as na gama biyan bukatata shikenan! Am also a kidnapper idan nayi kidnapping mace I have to satisfy myself kafin in nemi ransom! Ya kikaga kalar nawa salon very wise ko? Bana kidnapping kamar yadda kowa yake nasa! Don haka yanzu ina so ki sa min lambar wani naki inaso zanyi magana dashi!" Da sauri ta tashi zaune fuskarta cike da tsoro da kuma shock, girgiza kai takeyi hawaye na bin kuncinta, "No please mahaifiyata batada wani kudi wallahi, she lost her husband batada wasu kudi da zaku bukata daga wurinta, don Allah kar ku kirata ku daga mata hankali I beg you, ni duk kuyi min abinda kukeso amma kar ku kirata please!" A hankali ya isa inda take sannan ya bude wayar tasa yace "Bani number din before I do something bad to you!" Ba karamin tsoronshi take ba, sheyasa ta karbi wayar hawaye na bin kuncinta tasa number din, karba yayi yana mata murmushi, "Good girl!" Ya fada yana shafa mata fuska da sauri ta kauda fuskarta gefe tana share hawaye, zamansa ya gyara sannan yayi dialing number, Mummy na zaune tsakiyar parlor babu abinda takeyi sai kuka, saboda dama tayi jiran Khadijo tazo weekend batazo ba, tana ta kiran number ta shiru bata dauka karshe ma tajita a kashe, tou shine fa hankalinta ya tashi taje har hostel din nasu a rikice nan Sakinah ke ce mata ay yau kwana uku kenan tunda ta fita da yamma bata dawo ba, ta dauka ma ko gida ta tafi, nan fa hankalinta ya tashi ta kira Yasir da Ashraf suma hankali tashi duk suka taho da matayensu. Duk inda suke sa ran zataje babu inda ba'a je ba amma ba'a ganta ba, har sun sanar ma yan sanda suma sunyi iya yinsu har yanzu shiru. Zarah ce da matar Yasir ke gefenta suna faman lallashinta dan wani irin kuka takeyi bana wasa ba, Yasir da Ashraf kuwa dama tun safe suka fita nemanta har suka dawo shiru suma suna zaune ne kowa ya rafka tagumi. Wayarta ce ta soma ringing, kamar tana jira ta dauka dayan bangaren akace, "Dawa nake magana?" Mummy tayi shiru gabanta na faduwa, can dai tayi karfin halin cewa, "Kana magana da Hajiya Hussaina ne, wanene?" Yace "Look Hussaina, bawani dogon zance ya sa na kiraki ba, yarki tana hannunmu kuma ki saurareni da kyau da kunnen basira, kudi zaki kawo idan har kina son yarki ta ku6uta daga hannunmu, muna bukatar kudin nan da kwana biyu idan har baku kawo ba tou ina mai tabbatar maki da cewar keda ganin yarki kuma sai dai ku jone a lahira! Sannan magana ta gaba bana so ki kai maganar nan ga yan sanda in ba haka ba wani munmunan mataki zan dauka akan yarki kin fahimta?" Mummy da tunda suka fara magana ta zama shocked ganin haka yasa Yasir da Ashraf suka taso da sauri suna tambayar lafiya? Wani abu ta hadiye mai karfi sannan tayi karfin halin cewa, "Tou naji nawa kuke bukata?" Ya kece da dariya sannan yace "Million talatin zaku kawo! Kuma na fada maku nan da kwana biyu zaku hado kudinnan in ba haka ba, zan aikata diyarki lahira!" Cikin kuka tace "Haba bawan Allah ina zamu samu wannan uban kudin? Ku taimaka ku rage? Don Allah!" Yace "Babu batun ragewa haka zaku kawo mana su cif! Sannan idan kun hada kudin kar ku kiramu don mu ba'a kiranmu mu zamu kiraku amma kina iya rubuto mana message! Kin fahimta?" Kuka ta fashe dashi tace "Ka taimaka ka bani yarinyar inyi magana da ita!" Yace "Sai kun fara hada kudin koda zan iya baki yarinyar kiyi magana da ita! Yanzu dai ki tashi kiyi abinda ke gabanki idan kina son yarki ta dawo hannunki da rai!" Kit ya kashe wayar! Wayar na hannun Mummy sagale ta kura ma wuri daya ido hawaye na wanke mata fuska, Yasir ya karbi wayar yaji sun kashe, jijjigata sukeyi sai a lokacin ta fada kan Zarah ta saki kuka mai ban tausayi, "Sun sace Khadija! And they're demanding a ransom of 30 million naira! Ina mukaga gansu? Innalillahi wa inna ilahir rajioon! Na shiga uku diyar mutane a hannun mugaye! Wayyo Allah na! Yasir ina muka gansu?" Cike da tausayawa Ashraf yace "Karki damu Mummy babu abinda zai gagara, yanzu zan tashi inje gida wurin Abba nasan zai bada itama cousin dita matar sarki ce zata bada InshaAllah karku damu babu abinda zai samu Khadija InshaAllah!" Kallonsa tayi tace "Tou Allah yayi maka albarka nagode!" Tashi yayi Zarah tabisa da sauri itama kukan take, a waje tayi hugging dinsa, "Zan dawo da complete kudin I promise you." Shigewa tayi cikin jikinsa tana kara fashewa da kuka sannan tace "Thank you Ashraf you're the best." Kissing din kanta yayi cike da so yace "You deserve it princess, I love you."

------

A hankali ta bude idanunta, take ta ganta kwance ya kuma daure mata hannu da baki, kanta ne ya sara mata, ta dinga kokarin kwace kanta take daga daurin amma ta kasa, magana takeson yi ba hali nan taji karar key daga waje Alhaji Hamza ne ya shigo cikin shigar bakaken kaya kamar kullum, guard dinshi ya aje mashi kujera kusa da ita yana mata murmushin mugunta. "Good morning honey pie... how are you?”  Kallonshi tayi cike da tsana kamar ta rufe shi da duka. Ya kyalkyale da dariya yana shafa gefen fuskarta, bakinshi yakai daidai saitin kunnenta yana mata magana cikin rada rada.  “I hope you're enjoying your stay with me Khadija, Ina jin dadin kasancewa dake!" Magana take sonyi cikin tsawa ta kasa.  “Relax Khadija, don’t be scared” yace yana shafa kanta, da karfi ta matsar da kanta tare da runtse ido tana jin tsanarsa na ratsa. Gashin kanta ya damqo da karfi, sannan ya yakice kyallen bakinta ya shiga kissing dinta kamar zai 6alla mata baki, cizo tasa masa da sauri ya matsa yana sosa wurin, bata tsaya nan ba ta watsa masa miyau a fuska, tana kallonsa cikin ido cike da tsana.  “How dare you!? I will teach you a lesson right now!”  Kallon guard din yayi dake tsaye ya masa signal da ido, fita kawai guarda din yayi ba’a jima ba ya dawo da bokiti hannunsa, dire bokitin yayi kasa take Khadija taga duk kankaru ne ke ciki manya manya. Alhaji Hamza ya duka ya debo ruwan sanyin nan ya daga daidai saitinta ya shiga kwara mata shi, kyarma ta farayi tana ihu, haka ya dinga zuba mata ruwan in banda ihu da kyarma babu abinda Khadija keyi, kusan rabin bokitin ya watsa mata sannan ya dakata, yana kallon yadda take shivering, bakinta ya matse da hannunshi sannan ya take mata kafarta da karfin bala'i. Wani irin ihu tasa kamar zata fasa dakin da kara, take ya toshe kunnensa da sauri. Kuka takeyi cikin azabar ciwo tace "You're the most wicked man ever lived! Wallahi ka guji haduwarka da Allah azzalumi!" Ya kyalkyale da dariyar mugunta, "No problem honey pie, zaki iya kirana da ko wane irin suna I don't care, as long kina tare dani banida problem darling!" Shafa mata kumatu yakeyi, sannan kuma ya faske ta da wani irin wawan mari. Marinta ya shiga yi hagu da dama amma ta dake ko gezau tana kallonshi ko motsi batayi ba, zuwa yanzu ta saba da marinsa,  sai daya gaji dan kansa ya bari, sannan ya kyalkyale da dariya, "Uwar kwadayi ke nan kinga me kudi kin biyosa ko? Don't worry you'll learn your lesson very soon!" Yana gama fadan haka ya tashi ya fita daga dakin ya banko kofar sannan yasa key ta waje, kuka ta fashe dashi kamar ranta zai fita, kuka take bil hakki kamar naman jikinta ne ake yanka.... 

A 6angaren su Mummy kuwa kokarin hada kudin sukeyi Hoodah da Sultan sun bada million goma Abba ya bada million goma saura million goma, nan suka sake kira ba irin rokon da basuyi masa da kyar da ji6in goshi ya yarda su bada, nan ya fada masu inda zasu kai kudin, can kuwa Hoodah tayi shirinta tsab ta hada sojojinta da yan sanda inda ta hada plan sosai yadda za'a cafke sa. Bangaren su Mummy ma ta kafe tace gaba daya zasu tafi, shiri sukayii tsab inda Hoodah ta bukaci address itama ta taho da nata mukarraban. 

Khadija na kwance duk ta wahala jikinta duk bruises ne wato tabunan ciwo, banda fuskarta duk ta kumbura babu inda baya mata ciwo, kafin Alhaji Hamza ya banko kofar da karfi ya shigo, "Yau za'a daukeki, koda wasa karki sake ki fada masu I have raped you!" Da kyar ta bude baki tayi magana "Na'am ban gane me kace ba?" Matsowa yayi dab da ita yace "Am saying this for the last time! Kar ki kuskura ki fada masu raping dinki nayi!" Da kyar take bude idanunta "Har yanzu ban...." wani irin gigitaccen mari ya kai mata, tuni idanunta sun cika da hawaye nan ta fara shesheka, "Na dai fada maki idan kika sake kika fada sai na sake kidnapping dinki and kill your mother!" Batasan lokacin data ce masa "This time you have got the wrong person sir! I won't let your filthy fingers touch my Mummy!" Wani irin wawan dariya ya sheke da ita, nan ya shako wuyanta ya daga ta sama ya dinga juyi da ita kawai ya tilla ta kasa nan kanta ya bigi kasan simintin dakin, ihu ta saki cike da azaba nan jini ya fara bubulowa ta kanta, bai tsaya nan ba yasa kafarsa ya kai mata halbi a ciki ihu tayi cike da azaba da dafe cikin nata nan ya cigaba da halbinta yanna naushinta kamar ya samu ball, har sai da taji idanunta na neman rufewa, shi kuwa bai ankara ba ashe yan sanda ne zagaye da building din bai ankara ba sai ji yayi an banko kofar da jiniyar yan sanda da sojoji, Mummy ce gaba tsaye tayi tana kallon Khadija dake yashe kasa, da gudu ta shigo tana zuwa ta duka daidai inda Khadija take su kuwa suka cafke Alhaji Hamza da bukarrabansa, Mummy ce ta dago tana kallonsa take gabanta ya fadi ta mike jikinta na bari tana nunashi da yatsa tana kallon Khadija wadda jini ke bin kafarta da kanta, hannu tasa ta toshe bakinta hawaye na wanke mata fuska tace "Hamza?!" Shima juyowa yayi cike da shock yana kallon Mummy baki saki, Mummy ta silale inda Khadije ke kokarin suma idanunta na rufewa, tace "Hamza you raped your daughter! Khadija is your daughter innalillah wa inna ilahir rajioon!" Khadija na jin haka ta fasa wani irin gigitaccen ihu nan take ta suma sai kuma su Yasir sukayi kanta!

Friday, 6 August 2021

YAR AGADEZ PAGE 42

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 42}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com





A rude ya shiga kitchen ya debo ruwa ya dawo da wani irin sauri a hankali ya dinga yayyafa mata a fuska amma ko motsi batayi ba, ba karamin rudewa yayi ba ya mike a guje ya dauki wayarsa ya kira Yasir (oops na manta na fada maku he's a gynecologist) nan ya sanar masa abinda ake mata idan hakan ta faru a gida, da sauri ya nufi kitchen yayi warming ruwa a kettle, ya samu bowl ya debo da towel dan karami, a hankali ya janye rigarta zuwa cikinta ya cigaba da danna mata ruwan zafin nan a hankali yana warming marar, minti kusan goma yana abu daya har dai ya gaji dole yabi option 2, jawota yayi ya rungume ta tsam a jikinsa wasu hawaye na zulalo masa, a hankali ya gyara mata kwanciya bisa kirjinsa sannan ya nade hannunsa yasa iya karfinsa ya danne cikin aikuwa sai gashi taja wani irin dogon numfashi, baisan lokacin da yasaki wata uwar ajiyar zuciya ba gamida yin murmushi, tana bude ido ta ganta bisa kirjinsa nan take ta nemi ciwon marar ta rasa, kara hugging dinsa tayi ta shige cikin jikinsa sosai ta fashe da kuka mai ban tausayi, shima take wasu hawayen suka fara bin kuncinsa, Zarah sai kuka take tana kara shigewa cikin jikinsa, dagota yayi yana share mata hawaye yana girgiza mata kai alamun kar tayi kuka. A hankali ya mikar da ita tsaye ya hau gado ya jawota ya kwantar da ita akan kirjinsa yana shafa kanta yana kara hugging dinta, sunyi shiru na kusan minti uku kafin ya fara magana, wannan itace damar da yake da ita zaiyi clearing duk wani misunderstanding da ya shiga tsakaninsu, "Zarah kiyi hakuri da duk abubuwan da suka faru tsakaninmu tunda mukayi aure bamuda kwanciyar hankali, bayan letter din da kika gani da wadannan photos din nasan cewa ba banza ba, so I decided to investigate and see wanene yake son shiga tsakaninmu, I had my doubt at first amma ni bana son insa ma raina Khadija is behind all this, saboda ban taba tunanin daidai da rana daya ace bata shiryu ba, amma ki fada man in banda Khadija waye kike da shi da zai maki haka? All fingers were pointing at her, as I was saying sai na kira wani abokina, I paid him yaje inda Khadija take suyi magana ya tatso man information, nace masa yace mata inma tanaso ya rabani da Zarah zaiyi, without her knowing tayi exposing kanta da kanta, nan ta bashi original photos din da tayi photoshop dani tasa fuskana a kai,  bayan ya dawo ya kirani ya fada komai tace masa harta letter dinnan itace ta rubuta don ta rabamu, Zarah Khadija is behind everything bata hakura dani ba, hakika tayi betraying dinmu abinda yafi hurting dina the most yadda kikayi saurin yadda Zarah, I can understand kishi ne amma kina tunanin zan aikata maki haka Zarah?" Ya karasa yana kallon Zarah wadda tunda ya fara magana take kuka, a hankali ta zare jikinta daga rikon da yayi mata ita kuma tana mashi kallo mai wuyar fassara, kuka take bil hakki tana jin dama bata san Khadija ba a rayuwa, fuskarta duk wani pain, heartbreak da kuma farin ciki duk suka taran mata a lokaci daya. Cikin sheshekar kuka ta fara magana, "Ashraf ka yafe man, Khadija ta cuce ni! We are not even from the same parents...." a razane yake kallonta, "Me kika ce Zarah? Khadija is not your blood sister?" Ta gyada kai wasu hawayen na bin kuncinta, "Eh hakane, Nima ban dade da sani ba, Mummy ce ta fada mana da kanta, maybe wannan ne ya kara bata kwarin gwiwar ganin zata iya mallakarka tunda ba iyayenmu daya da ita ba...."

Tana fadan haka sai ta fashe da wani kukan, bude baki yayi zaiyi magana ta tsaida shi, a hankali ta mike tsaye kai kana ganinta kasan a fusace take, don dole shima ya mike tsayen amma baice komai ba gudun kar ya kara frustrating dinta ganin yanayinta, "Wannan shine karo na karshe da Khadija zata kara shiga rayuwata! Wannan shine karo na karshe da Khadija zatayi min mugun abu! Am going to bring her down! I will take my revenge I promise you that! Khadija sai ta gwammace dama bata taba sonka a duniya ba! This will be the last time she will do something bad to us! Na gaji I have heard enough! I wil not take this anymore! Ta ja ma kanta da kanta sai na dauki mummunan mataki a kanta, tunda ita ta nuna muguwa ce azzaluma! Wannan wane irin so ne haka? So hauka ne? Ko kuwa ana so dole? Khadija have hurt me beyond major and I promise I won't rest until she apologizes to me for her mistake.....!" Durkushewa tayi don zuwa yanzu kukan yaci karfinta shi kuwa Ashraf binta yayi kasan gaba daya idanunsa sun cika da hawaye, a hankali ya rungume ta ya dunga rarrashinta wane karamar yarinya, fuskarsa daga ganin kasan yana cikin bacin rai, kunci hade da dana sani marar adadi fuskar nan tayi jajir. "Khadija was loved by my mom despite the fact that she is not her biological daughter she took care of her more than us, bata taba kawo ma ranta cewar iyayenta basa tare da ita ba saboda daidai da rana daya Mummy bata taba bari ta gane ba, wallahi wallahi da muna yara za'a iya siyo mata toys din da suka fi nawa komai da tsada, Mummy tasha nuna tafi kaunarta a kanmu, tun abin na bani haushi har na saba, da muka girma kuwa ba irin batata da ba'ayi ba da kaya what ever tace tana so Mummy zata bata, an bata freedom fiye damu, Mummy bata iya hana ta or ta kwatse ta ko kuma idan tayi laifi tayi mata fada sam batayi mata, an kula da ita fiye da tunaninka ko wannan kadai ay ya kamata ta duba ta raga man, amma da yake son zuciya ya rufe mata ido da soyayya bata ji bata gani, Allah ne ya hadamu Ashraf, Ashraf ina sonka kuma zan iya bin duk wata hanya naci uban Khadija na shiga tsakaninmu da tayi, my biggest fear is that kar Khadija ta rabamu ko kuma tasan hanyar data bi don ta aure ka, bazan iya jurewa ba Ashraf I can't let her take you away from me...." kafin ta ida magana Ashraf yayi hugging dinta saboda he can't take it anymore, Kuka ta kara fashewa da shi sannan ta kara rungume shi tsam, "Ya isa kukan nan haka Zarah", rocking dinta yakeyi alamun rarrashi kafin yace

"it's okay Zarah, let bygone be bygones, karki biye mata kice zaki hukuntata wallahi komai zatayi bazan taba sonta ba, you're the only woman for me inshaAllah har aljanna, so ki daina jin tsoron wata Khadija bata isa tayi miki komai ba wallahi sai abinda Allah yayi miki, kuma karki damu shifa Allah yana ganin komai kina zaune zai maki sakayya tunda ke kinsan bakida hakkinta." Dagowa tayi tana kallonshi shima ya kalleta a take suka sakar ma juna murmushi, "Ashraf kaje kayi sallah..." ta fada tana sakinshi alamun ya tashi, a hankali ya mike yana kallonta cike da kauna kafin yace "Will you take care of yourself?" Ya tambaya cike da kulawa, "InshaAllah I will don't worry." Murmushi ya sakar mata "Tashi ki kwanta sosai tou, ki kwanta ki huta kinji?" Ya fada yana kokarin dagata da sauri ta cire masa hannu tana girgiza kai, "No I will stain everywhere." Ta fada tana sunna kai kasa, nan ya gane abinda take nufi, "Kinma tuna man idan nayi sallah zan wuce shop sai in siyo maki daga nan." Tayi murmushi tana gyada kai yayi mata murmushi sannan ya fita. Zarah na nan shiru har bacci ya fara surarta can cikin baccin ne taji takun tafiyarsa, window ta leka taga garin har yayi duhu haka, shigowa yayi da sallama hannunsa dauke da leda yana mata murmushi,  gefenta ya zauna yana kallonta, "How are you feeling princess?" Tayi murmushi cike da kunya tace "Alhamdulillah." Yace "Haka nake sonji, ga pad dinnan jeki kimtsa ko?" Ta karba da murmushi saman fuskarta "Thank you." Tana jiran ya fita ta tashi taji shiru, "Tou ka fita in shirya." Ta fada a shagwabe murmushi kawai yayi sannan yayi hanyar kofa, harya kai kofa yaji ta kurma wani uban ihu, a rude ya juyo yana tambayar lafiya? Dariya ta fashe da ita kamar zata siqe, shi kuwa cike da sha'awa ya tsaya yana kallon dariyarta so adorably, saidai tayi mai isarta sannan tayi shiru tana maida numfashi, "Am sorry Ashraf I just wanna see your reaction and how much you care, tou mr caring find your way out please yan mata zasu shirya thank you." Ta fada cike da tsiwa harda mashi gwalo, dariyar shima yayi sannan ya fita, yana fita ya sake jin dariyarta tana fadin, "Ashraf ka daina dariya fa kar bakinka yayi ciwo..." tana fadan ta sake yin wata dariyar, har Ashraf ya isa parlor bai daina murmushi ba zuciyar fes kuma cike da kaunar matarsa Fatimah Zarah.

-------

Sultan ne ya shigo fada inda ya iske Sarauniya Hoodah da maids kusan biyar ko wace da abinda takeyi, daya na bata labari mai ban dariya, daya na mata tausa a kafa, daya jakadiya ce amma sabuwa ce tana bata wani abu kamar pap cikin bowl tana bata a hankali tana sha, daya kuma tana tsaye da katon mafecin feather mai colors a jikinsa tana ta mata fifita a hankali. Sallamarsa ce ta katse masu abinda sukeyi suka dakata suka gaishe shi cike da ladabi, "Duk wannan aikin da suke maki aikina ne ba nasu ba." Ya fada yana murmushi, ya karbi hand fan din yana fadin "Zaku iya tafiya." Duk suka mike cike da ladabi suka fita, jakadiya har ta kai kofa ta dawo da sauri ta sunkuya, "Ranki shi dade kina da bukatar wani abu? Allah shi kara maki lafiya Sarauniya..." Sultan ya juyo yana kallonta "Eh Shuwaka...." ya fada yana bin Hoodah da murmushi "Ki dafa soup din shuwaka na Hoodah, yana da kyau ga mace mai ciki, kiyi shi da dan yaji." Ta sunkuya "Tou ranki ya dade Allah ya kara girma yanzu kuwa InshaAllah." Tana gama fadin haka ta fita da sauri, gefenta ya zauna ya dauko bowl din pap din ya cigaba da feeding dinta, "Naji dadi kina cin abinci Hoodah..." tayi murmushi "Only if you feed me." Ya kalleta "Shhh oya bude bakin." Tayi dariya ta bude bakin yasa mata a haka ya dinga bata har ta shanye tas, ya aje bowl din bisa table ya juyo yana kallonta gamida da gyara mata gashinta daya fito ta gefe gefe, "So tell me wace kasa kikeso ki haihu?" Tayi murmushi tana kamo hannunsa "Here Sultan, I don't wanna go to anywhere I want to give birth right here darling." Yayi murmushi "As you wish my queen..."

------

Shirin makaranta takeyi a gaggauce saboda ta kusa makara zuwa class ga in kayi late ko kafi kuda kwakwa lecturer din koraka xaiyi, sanye take cikin dogon bakin wando da riga yar ficit ash color sai ta yafa black gyale, hills tasa masu shegen tsini sannan ta dauko bag dinta da wayarta, chewing gum ta jefa a baki tana wani cika tana batsewa, room mate nata mai suna Sakinah wacce ke kwance da novel tana karantawa sanye da kayan bacci ta dakata tana kallonta kafin tace, "Wai Khadija club zakije ko School?" Wani shegen kallo tayi mata kafin ta maka mata wani uban tsaki, "Tou uwar sa ido club zanje mtseww aikin banza." Tana gama fadan haka ta fito a fusace ta fara tafiya kai kace bata son taka kasa, har ta kusa bakin gate da yake babu nisa school din daga hostel din nasu wata bakar Prado ta paka ta gabanta, tsaye tayi baki sake har aka fara zuge glass a hankali, nan tabishi da kallo mutumin dattjo ne zai kai kimanin shekara hamsin da biyar, a hankali ya fito yana binta da kallo daga sama har kasa sannan yace "Yan mata in bazaki damu ba don Allah ki ara man lokacinki minti biyar kacal yayi yawa." Wani mugun kallo ta watsa mashi sannan ta bishi da tsaki, "Banida lokaci koda na kyauta ne balle kuma na aro, don haka inada abun yi bazan tsaya bata lokacina akanka ba, don Allah malam ka rabu dani school zanje ina da class..." kusa da ita ya matso tare da cire glass dinsa, kana ganinsa kasan ba karamin mai kudi bane naira ta xauna daram a jikinsa, wata yar dariya yayi yace "Ba damuwa..." clapping kawai yayi... Da sauri body guards nasa ko wane sanye cikin bakaken suits suka fito da katuwar jaka hannu kawai guard din yasa ya zaro kudin da baisan ko nawa bane ya mika ma ogan nasu, ogan nasu ya karba sannan ya basu izinin tafiya, kallonta yayi yana wani murmushi kafin yace "Ga wannan kisa kati ko? And also here's my card you can call me anytime don't hesitate..." baki bude take kallon kudin zasu kai dubu dari sai juya su takeyi tana washe baki tace "Tou baka fada man sunanka ba?" Yayi wani shu'umin murmushi "You can call me Alhaji Hamza, Kefa what's your name yan mata?" Tayi murmushi "Khadija." Yace "Nice name, Khadija yanxu inada meeting karfe sha daya na safe, I wish to talk to you more but am kinda busy, zaki iya zuwa gidana muyi magana a can?" Shiru tayi take taji gabanta ya fadi, "Meyasa baxako ka sameni a hostel ba? You see bazan iya zuwa gidanka ba kuma every weekend ina zuwa gida why not ka sameni gidanmu?" Shiru yayi alamun tunani yace "Dear really is fine in baki iya xuwa, besides a waje fa zamu zauna inma kina ganin wani abu, kuma gidan da mutane kawai magana ce ta fahimtar juna nida ke kinga daga nan in kikayi approving nawa sai in cigaba da xuwa gidanku, donni ba wasa nake ba aurenki nakeso inyi..." tayi ajiyar zuciya "It's okay, yaushe kake ganin ya dace inzo? And give me the address." Yace "I will text you in har xaki iya bani number ki dear, and batun zuwa around 5pm idan yayi maki lafiya lau...." tace "Okay ba matsala zanzo anjima." Yayi dariya "Okay, can I drop you to school?" Ta girgiza kai "No nayi late ma, I think zan juya in koma hostel," yace "okay, in kina ganin ba matsala zan iya turo da mota a dauke ki anjima?" Tace "Ok nagode." Daga haka sukayi sallama ta juya shi kuwa Alhaji Hamza ya bita da kallon kurilla yana hadiye yawu sannan ya shiga mota. Da yamma ta shirya cikin wani dakakken material dinkin yayi bala'in kyau, turare ta fesa ta yafa dan karamin gyale, hills tasa da wata yar kucit din handbag itadai Sakinah sai kallonta takeyi har ta gama shirinta tsab ta fito, tana fitowa motar na isowa ta bude ta shiga, ita dai tunda suka shiga take latsa waya, saida tafiyar tayi nisa ba zato ba tsammani kawai taji an fesa mata wani abu a fuska, ihu ta kurma ta saki wayar take tana jin kanta na mata nauyi idanunta na rufewa, duk yadda taso hana kanta bacci abin ya faskara a hankali ta silale bisa car seat din a yayinda duhu ya mamayeta....




Bana jin dadi sosai har yanzu sheyasa kuka jini shiru thank you🥰🤗

Tuesday, 3 August 2021

YAR AGADEZ PAGE 41

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 41}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com




Matsowa yayi kusa da ita cike da tashin hankali yana jin kukanta na ratsa ko wace ga6a ta jikinsa, hannu yasa ya rikota, firgit ta mike tana share hawaye, idanunta sunyi jajir sun kumbura tsabar kukan da takeyi, "Don't touch me Ashraf am warning you for the last time! Daga yau kar ka sake tabani a cikin gidannan, bana son ganinka I hate you!" Tana gama fadan haka ta fara ja baya kamar wacce taga dodo, ji tayi kafafunta sun kasa daukarta ta durkusa a nan ta kifa kanta tana cigaba da kuka kamar ana zare mata rai, "Zarah tell me nayi maki? Da zan fita you're fine and happy lafiya lau muka rabu, ta yaya daga zuwa masallaci in dawo ki birkice man lokaci daya? What happened?" Bata bashi amsa ba sai ma sautin kukanta daya karu, ji yake kamar ana zuba masa ruwan zafi a cikin kirji tsabar yadda baya son sautin kukan da takeyi. Matsowa ya kara yi dab da ita duk da yadda yaga yanayinta ba da wasa take ba, sannan she sounds so hurt and angry, ba zato ba tsammani sai taji ya rungumota gam gam, da sauri ta dago da jajayen idanunta tana mashi wani irin kallo, ture shi tayi ta mike tsaye tana faman share hawaye ta isa inda paper din take ta durkusa ta dauko a fusace, tana zuwa inda yake tayi tsaye tana kallonsa na yan seconds kafin ta bude hannunsa ta sa masa paper dinnan, hawaye kuwa wani na korar wani, "Wannan takardar fa Zarah?" Wani kallo ta watso mashi "Open and read!" A hankali ya bude ta yana kallon Zarah kafin ya sauke idonsa kasa ya soma karantawa, shi kansa abin ya bashi mamaki dagowa yayi yana girgiza kansa idanunsa sun rikide zuwa ja, yace "Zarah a tunaninki nine na rubuta wannan paper din? Yanzu har akwai ranar da zaki fara doubting soyayyar da nake maki? Na dauka ko ganina kikayi ina rubuta ta kya karyata kice ay wasa kakeyi balantawa kawai ki ganta haka kawai kice ni na rubuta ta? Zarah all this while ya kamata kisan wanene ni kisan kalar soyayyar da nake maki, inda ace jikinki nakeso da tun a gidanku zan samu abinda nakeso, ko kin manta sadda su Mummy sukayi tafiya? A hannuna aka damka ku daga ni sai ku meyasa lokacin ban maida ki sex machine dina ba sai yanzu? Zarah the love I have for you is pure and clean I love you fisabilillahi, yanzu inda zaki bukace mu zauna haka nan ba tare dana kusance ki ba I can do it for you without any hesitation, Zarah why? How can you not trust me?" Lokaci daya taji zuciyarta ta karaya tana son karyatawa amma ta kasa, wata irin kara ta saki, "I wanted to believe you Ashraf, but ka fada man wanan hand writing din na waye? Of course naka ne!" Matsowa yayi kusa da ita ya kamo mata hannu kamar ya fashe mata da kuka yakeji, a fusace ta ture shi, "Ka fita daga cikin dakinnan Ashraf I don't want to see you! Ka fita nace!" Tsaye yayi cike da mamaki kafin ya sake magana tace "Ka fita Ashraf! Who gave you the right to touch me? Tunda bazaka fita ba ni xan fita in bar maka dakin Ashraf, dama ay dakinta ne you're trying to tell me is your room right?" Tana gama fadan ta share hawayenta tayi hanyar kofa, da sauri ya dakatar da ita, bai ce mata komai ba ya bita da wani irin kallo mai wuyar fassara sannan ya fita. Yana fita ta koma can gefen gado ta cigaba da kuka, kuka take kamar ana zare mata rai, pillow ta jawo ta dora kanta ta cigaba da kuka rabon da tayi irin wannan kukan tun rasuwar Daddynta yau shekara kusan takwas kenan da wani abu, kanta kuwa ji take kamar ana sara mata guduma, lumshe idanunta tayi kafin ta ankara bacci yayi awon gaba da ita.... Can cikin baccin ne taji alamun ana knocking kofa, firgita tayi ta tashi ta bude, binshi da kallo tayi zuciyarta na kuna tana tafarfasa wane garwashi, "Come and eat..." yana gama fadan haka ko second daya bai kara ba ya juya yayi gaba, ko amsa shi batayi ba ta nufi dakinta tayi wanka tayi alwalla don tayi mamaki ashe har biyu ta kusa, nan tayi sallarta ta zauna azkhar dinta, taki tashi tayi zaune a nan, itace a nan har akayi la'sar sai da tayi sallah nan taji wata irin makirar yunwa na addabarta, linke kayan sallar tayi ta adana su sannan ta fito, har yanzu idonta bai washe ba akwai dan kumburi sannan akwai jan daga gefe, tana fitowa ta ganshi zaune a parlor ga kulolin abinci nan kala kala bisa dining daga gani Abba ne yasa aka kawo masu, da alama bai ci abinci nan ba amma yadai ya zabga wani uban tagumi, da alama ma baisan ta shigo parlon ba saboda yadda taga ya zurfafa cikin tunani, ko kallon inda yake bata kara yiba ta nufi dining ta zauna ta jawo plate guda biyu ta zuba masu kowa da nashi, tana gama zubawa ta kai masa bisa center table din dake tsakiyar parlon ta koma ta dauki nata ta zuba drink sai yaga ta tashi zata shiga daki kuma, da sauri ya dakatar da ita, "Ki tsaya a nan kici abincin." Yana gama fadan haka ya jawo abincin shi yana kallo don shi kwatakwata baida appetite, Zarah ko kallon inda yake batayi ba ta yi hanyar fita daga parlon, "Fatimah ba nace ki zauna kici a nan ba? Meyasa bakijin maganata ne yau? Tou ki dawo ki zauna nine dai kika tsana bakyason gani ko? Tou xan tashi in bar maki parlon." Yana gama fadan haka ya mike tsaye saboda ransa har ya fara baci, anya wannan Fatimanshi ce kuwa? Wadda take kaunarsa? And can go to any length to show him just how much she cares? Wai amma yanzu kwatakwata bata son ganinshi, "No kayi zamanka." Ta fada murya kasa kasa, dan xuwa yanzu kuma wani irin tausayinsa takeji yana ratsata amma she can't help it ya riga ya bata mata rai da yawa, jin muryarta can kasa ba karamin sanyaya mashi rai yayi ba, komawa yayi ya zauna dafe da fuska itama a hankali ta juyo ta jawo wata kujerar dan nesa dashi ta fara cin abincinta, kafin ya ankare har ta kusa cinyewa shiko ko ta6a nashi baiyi ba yasa ta dago daga cin abincin da takeyi tana kare ma kyakkyawar fuskarshi kallo, "Kai baza kaci abincin ba?" Ta tambaya wadda ita kanta batasan daga ina tambayar ta fito ba, ba karamin mamaki maganarta ta bashi ba bai taba tunani ba dan a yadda take ikirirani ta tsane shi bata son ganinsa har zata sauko haka da sauri? Da kallon mamaki ya bita baki sake ita kuwa da sauri ta dauke kanta ta cigaba da cin abincinta, tana gamawa ta tattara plate dinta da cup din da tasha drink ta kai kitchen zata wanke. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya fara cin abincinsa a hankali, saida ya gama ya dauki plate din zai kai kitchen suka hadu ita kuma zata fito, ko kallonshi batayi ba tace "Kawo." Tana karba ta juya ba tare data bari sun hada idanu ba ta wuce kitchen din da sauri.

Washe gari bayan sun kammala breakfast Zarah ta hau gyaren gida, saida ta tsabtace ko ina don Ashraf yana parlor ashe a nan bacci ya sure shi, wuce shi tayi ta tafi dakinsa don nan kadai ne ya rage bata gyara ba, wardrobe dinsa ta bude zata saka masa jallabiyarsa data linke a ciki kawai wata babbar envelope ta fado kasa, abubuwan dake ciki duk suka fito wasu pictures ne dake ciki sun kai kala goma, bata kawo komai a ranta ba ta tattara su zata maida ashe akwai wani daya juyo saitinsa fuskar Ashraf ta gani kawai sai ta saki envelope din kasa tana kallon hotunan, Ashraf ne da wata da alamun ba musulma bace tasha jumpsuit shi kuma daga shi sai gajeren wando, kara kallon hotunan takeyi hannunta har wani kyarma yakeyi don so take tabbatar ko dai kama ce sukeyi don ita bata yarda Ashraf zai aikata haka ba, tafi minti goma tana kallon hotunan gaba daya she is in shock, sai a lokacin hawaye suka balle mata kuka take ba kakkautawa kafin a hankali ta juya ta fita daga dakin, daidai inda yake kwance ta tsaya kawai sai ta juye masa hotunan bisa jikinsa, farkawa yayi ya ganta tsaye kansa tana kukan fitar hankali hakan yasa ya mike bai ma tsaya lura da hotunan ba ya fara tambayarta lafiya? Kasa magana tayi saboda har yanzu she's still in shock, Ashraf ganin ta kasa magana sai ya dinga bin hotunan da kallo kafin a hankali ya durkusa ya fara tattara su, juyosu yayi yana binsu da kallo baki sake zufa ce ta fara keto masa ko ta ina, kallonta yakeyi yadda take kuka kamar ranta ne ake zarewa, "Zarah wallahi I don't know anything about this photos...." ya fada yana kokarin tabata, janye jikinta tayi da sauri tana masa wani irin mugun kallon tsana, "Karka kuskura ka tabani!" Tana fadan haka ta juya da gudu tayi dakinta, da sauri yabi bayanta yana kiranta amma ina har ta shige ta sa lock, Ashraf kansa ba karamin zafi yayi masa ba, zuciyarsa kuwa ji yake kamar zata hudu kirjinsa ta fito, "Who did this to me?" Ya tambayi kansa, nan ya dinga knocking yana magiyar ta bude masa amma shiru sai karar kukanta yakeji, sulalewa yayi a nan bakin kofar wasu zafafan hawaye suna surnano masa....

Zarah kan gado ta zube tana kuka kamar wacce ake zare ma rai, wai meyasa tunda sukayi aure sun kasa samun kwanciyar hankali? Meyake shirin faruwa dasu? Tunano yadda yake rungume wannan Christian din takeyi wacce da kayan data sa gara ma babu a jikinta, wani irin ihu ta kurma jikinta har wani kyarma yakeyi, "No it can't be my Ashraf, something must be wrong somewhere! Tou what if da gaske ne? Dama ance namiji ba dan goyo bane duk halinsu daya!" A firgice Ashraf ya mike wanda yake jikin kofar har yanzu ya shiga murda kofar yaji ta gam a rufe, wani irin gudu yayi ya isa dakinsa ya shiga bincika spare key, har wani kyarma yakeyi kar dai wani abun takeyi ma kanta? Da sauri ya bude dakin hannunsa na kyarma ya shiga ciki, yana shiga ya ganta zaune gefen gado zufa ta jike mata jagab a jiki sai hawaye ke kwarara daga jajayen idanunta jikinta na rawa, da sauri ya matsa kusa da ita ya kamo hannunta, hannun nasa ta bige da karfi, "Bana hanaka tabani ba? Karka sake zuwa inda nake na tsaneka Ashraf na tsani maza, dama ashe duk haka kuke mayaudara? I hate all men! Na sanya ka a cikin raina amma kaine zaka yaudareni Ashraf? Saidai abin mamaki na kasa tsanarka kamar yadda nake ikirari amma karka dauka cewa zaka iya dinga zuwa inda nake! Da gaske bana son ganin fuskarka." Tana gama fadan haka ta tura kanta cikin pillow ta fashe da wani irin kukan fitan rai wane ana yanka naman jikinta, Ashraf babu irin magiya da lallashin da bai mata ba amma taki koda kallonsa ne, ya rasa inda zai saka kansa gaba daya abun duniya ya ishe shi, "Zarah don Allah don annabi ki tsaya ki saurareni! At least tell me you trust me baki yarda da abunda kika gani ba, Zarah kisani hawayenki sune last abinda nake fatan gani, Zarah don Allah kiyi hakuri ki daina kukan nan kiyi man magana ke kinsan irin kaunar da nake maki fa, I admit nayi soyayya da cousin dina a baya amma yanzu ya zama past kece kawai nakeso you're the only woman I love bazan taba yaudararki ba, wipe your tears now and tell me do you trust me or not Zarah?" Sai a lokacin ta dago da rinannun idanunta tana mashi wani irin kallo, "Ashraf don Allah na roke ka ba dan ni ba ka fita daga cikin dakin nan! Wallahi ganinka wani irin bakin ciki da kunci yake kara mun!" Ta fada da muryarta data rine saboda kukan da takeyi tana share hawaye, yadda tayi masa da fuska ya tabbatar babu alamun wasa a tattare da ita, Ashraf zuru yayi yana binta da kallo maganganunta sun mashi ciwo matuka, "Yanzu Zarah yau nine bakya son gani? Nine silar kukanki? Ni ne ke saki cikin kunci da bakin ciki? Fuskata Zarah? You don't trust me ko?" Ya fada kamar zaiyi kuka wani irin tukukin bakin ciki ne ya taso masa, Zarah wani irin harara ta watsa masa, "Kaga malam wallahi idan idan bazaka fita ba ni zan fitan maka daga cikin dakin nan, ka tashi ka fita don Allah." Tana gama fadan haka tawani tashi tsaye, yana ganin haka ya mike da sauri ya fita daga dakin, binsa tayi da kallo kafin ta koma ta zauna ta cigaba da aikin kukanta, har cikin ranta bata son yi masa haka amma idanunta sun riga sun rufe da kishi ta kasa controlling kanta. Tana nan zaune ta gaji da kukan tayi shiru babu abinda takeyi sai tunani, can taji an murda kofa an shigo tabi shi da kallo a sanyaye ganin yadda ya koma gaba daya yayi kalar tausayi sannan kana ganin yadda ya shiga damuwa, damuwar ta bayyana akan fuskarsa daga bakin kofar ya tsaya rike da handle yace mata "Lokacin sallah yayi ki tashi kiyi sallah." Yana gama fadan haka ya juya ya fita ya kullo mata kofar, mikewa tayi ta shiga bathroom bayan ta kammala ta fito tayi sallah. Bayan ta gama azkhar dinta da kyar ta mike ta karasa kan gado, wani irin bacci takeji aikuwa tana kwanciya ba'a dau Lokaci ba bacci yayi awon gaba da ita. Shigowa yayi don ya tadata taci abincin rana ya iske tana bacci, murmushi yayi ya karasa kusa da ita ya zauna gefenta a hankali yana gyara mata gashinta daya rufe mata fuska, kallonta yakeyi sonta na ratsa ko wane sassa na jikinsa, a hankali yayi mata kiss a kumatu marar kara ko kadan gudun kar ya tasheta daga bacci, drawer ya bude ya zaro wata jotter da pen ya rubuta mata note, gefen pillow dinta ya aje mata ya dora mata wayarta bisa, kallonta ya kara yi sannan ya juya ya fita a hankali.

Karfe hudu saura ta farka salati tayi hade da mika sannan ta mike zaune, hannu tasa zata dauko wayarta don ta duba lokaci kawai zai ganin littafi tayi aje, daukowa tayi ta bude ta fara karantawa, "Hello princess, ina wuni rankiya dade? Hope kin gama baccin lafiya? Abincinki yana kan dining, make sure kinci da yawa fa, zan fita ne amma bazan dade ba InshaAllah, do you need anything? If yes just call me or you can text me okay princess? Take care of yourself for me plus I love you so much, also forgive hubby okay? Later...." Murmushin da bata san ya fito mata ba ne ya su6uce mata, wani sabon sonsa ne taji yana taso mata, saidai data tuna mey yayi mata sai taji haushi kuma. Ruwa ta shiga ta watsa sannan tayi alwalla, wata red atamfa ta dauko dinkin gown rigar tasha stones tayi kyau sosai, tana gama kimtsayawa tayi sallar la'asar tana gamawa taje taci abinci, rice and stew ce da hadaden salad, sai kaza gasashiya, sai pepper soup din yan ciki. Tana gamawa sai ta fara zagaya gidan dama bata tsaya tawani kalli yadda yake ba, katon flat ne wanda ko wanensu yana da dakinsa da palornshi, corridor ce ta raba masu parlonsu, sai kitchen da dining area wanda duka gidan royal furnitures ne dakakku na gani na fada, gidan gaba daya yaji kayan alatu very simple yet classic and elegance. Gyalenta ta dauko ta fita ta gaida Abba ta dade a can wanda yaji dadin zuwanta, bayan sun gama fira ne sai ta tashi ta dawo sashensu wanda akwai tazara sosai, gida ne katoto ko wane da gate dinshi, mantawa ma xakayi gidan a hade yake. Tana zaune tana kallo can daddare wurin karfe takwas taji ana ta knocking, tashi tayi taje ta bude Ashraf tagani tsaye rike da basket din abinci, kallonta ya tsaya yi yadda duk ta kode idanunta sun shige tsabar kuka, ba tare data ce masa komai ba ta karbi basket din dake hannunsa da alama abinci ya anso cikin gida ta wuce dining ta aje, ya kasa mata magana yana tsoron maganar da zata fito a bakinta sheyasa ma baice mata komai ba. Dakinsa ya shiga ba'a jima ba ya fito da singlet da boxers zama yayi a kujerun parlon, tana ganin ya xauna ta mike taje ta zuba abincin, binta yake da kallo yadda take zubawa a natse kuma a cikin damuwa, tana gama zubawa taje ta aje gabanshi sannan ta nufi fridge ta dauko drink da cup ta dire a gabansa, sannan ta koma kan doguwar kujera ta kwanta ta cigaba da kallo, ko kallon Inda yake batayi ba. Sun kai minti goma a haka Zarah nata kallonta shi kuwa Ashraf abun duniya duk ya ishe shi, can ta juyo ta kalleshi ta kalli abinci taga ko taba shi baiyi ba, "Ashraf ya naga har yanzu baka fara cin abincin ba? Ko wani abun za'a dafa maka?" Ta fada cikin damuwa don bata son yadda ta ganshi duk ya zabge yayi wani iri, kallonta ya karayi kafin ya girgiza kai alamun a'ah, qular da ita yayi, "Wai bazaka iya magana bane? Kake ta faman amsa min da kai?" Shiru ya karayi sai can kamar bazaiyi magana ba yace, "Na koshi..." sannan ya mike ko kallonta baiyi ba ya tafi part dinshi ya kullo kofar. Zarah ta bishi da kallon mamaki, ko shima fushin yakeyi? Sai kuma abun ya fara damunta kuma. A bangaren Ashraf kuwa yayi hakan ne ba don komai ba sai kila idan ya nuna mata ransa ya baci kila ta daina masa haka ta sauko ta bashi hakuri. Sai wurin 9 ta tashi taje tayi dinner dinta, tana gama tattara wurin ta kashe tv da fitilu ko kallon part dinshi batayi ba ta nufi nata part dinta.

--------

ONE MONTH LATER....

Yau an kai kimanin wata daya kenan da bikinsu Zarah, suna nan babu abinda ya chanza fadan yau daban na gobe daban, zuwa yanzu ya sa mata ido tunda shi dai yasan he's innocent, itace keta haukanta da fadanta ita kadai.

Yau ta kama Wednesday Zarah na cikin bacci wurin karfe uku da kusan rabi taji mararta ta murda, a gigice ta farka dama indai zatayi period first 2 days sai tayi ciwon ciki wani lokaci har drip ake sa mata har suma takeyi, tashi tayi zaune sai taji ya karu sai ta kwanta nan ma taji ba sauki abun ya faskara, jagab ta jike da zufa tsabar wahala, wajen karfe 4 taji ciwon ya fara cin karfinta wani irin azaba taji wanda batasan lokacin data fasa wani irin gigitaccen ihu ba, a tsorace Ashraf ya dakatar abinda yakeyi a kitchen, wani ihun ya sake ji a frigice ya bude tap yana wanke hannunsa don ya baci da flour kafin ya karasa wanke hannun nasa ya sake jin wani ihun wanda yafi na dazu, a frigice ya ruga a guje gabanshi na faduwa ya shiga dakinta, in shock ya tsaya ganin yadda take mirgina a tsakiyar dakinta dafe da ciki, da gudu ya karasa inda take ya tsugunna yana faman tallabo ta, "Zarah!" Kafin ta ankara taji ya kamo hannunta zai mikar da ita tsaye, da sauri ta fizge hannunta, "leave me alone!" Ta fada cikin azabar ciwo, shi kuwa Ashraf kara damke hannunta yayi, a yadda yaga yanayinta yasan ba karamin ciwo takeji ba, ya kara kokarin kama hannun nata yana mikar da ita tsaye for the second time ta sake fizge hannunta, "Ashraf ka kyaleni nace mana! Wai bance karka sake tabani ba? Why are you so stubborn?" Ta fada cike da azabar tsiwa gamida dukewa tana cize lebe, "Wai Fatimah meye haka? Ta yaya xakice na rabu dake a cikin wannan halin? Wai bakida hankali ne? Ni mijinki ne don haka duty dina ne na kula dake whether you like it or not kina jina ko?" Ya fada tare da jawo hannunta ya kaita kan gado, "Look Mr Ashraf! The mr perfect husband! Babu abinda xaka iya mani zai tafi da kansa, well is just ciwon mara and for your information inada hankali na....!" Ta fada cike da tsiwa tana murguda baki, ji take kamar ta kama shi ta rufe shi da duka dama ga ciwo ya isheta, zaiyi magana ta fasa kara ta fara mirgina kan gadon yayi saurin kamota, "Don Allah ka rabu dani mana! Na fada maka babu abinda zaka iya yi mani ay sai ka fita ko?" Da kyar take maganar amma saboda shegen taurin kai sai masifa take mashi, "Zan iya maki wani abu, am your savior so do as I say...." yana fadar haka ya janyo ta wuri daya, kokarin fizgewa tayi shi kuwa yana kara damkota, "Kinga ki tsaya wuri daya, kar na sake naga kin motsa koda da inch daya ne, now sa hannunki ki ringa massaging marar, ki cigaba yanzu xan dawo..." ya fara tare da mikewa tsaye, a fusace ta dago kanta tana balla mashi harara, "Bazaka zo cikin rana daya ka fada mun abinda zanyi ba, I have been experiencing this pain shekara da shekaru kawai sai yanzu rana daya kace man ga abinda xanyi? Tou I will not do it ka fice man da gani mayaudari kawai!" Wani sabon ihu ta kurma saboda ko magana tayi sai taji kamar ana tsirarta,

Da Sultan yayi magana sai Zarah ta fasa kara, da sauri yayi kanta "Don't touch me!" Ta fada muryarta na kasa kasa kafin a hankali idanuwanta su rufe ruf jikinta ya saki.... ganin bata motsi ba karamin firgita Ashraf yayi ba, jijjigata yakeyi yana kiran sunanta, ganin dai da gaske bata motsi yasa ya juya ya fita a gigice har yana yin tuntube....