YAR AGADEZ
{Page 40}
To read all my books click the link below👇🏻
Maryamsbello.blogspot.com
Da mugun mamaki Fahad yace "Kidnapping Khadija?? Ni kidnapper ne akace maki? How can I kidnap someone all of a sudden?" Tayi murmushi "Nasan kai ba kidnapper bane, amma ay kace zaka iya mun duk abinda nakeso ko? Please help me Fahad it's urgent." Fahad yace "Naji kince sister dinki meyasa?" Tayi shiru can tace "Akan wani dalili ne." Yace "Wane dalili ne wannan? How can you ask me to kidnap your sister Khadija? Are you normal?" Ta kwantar da murya, "Bawai ina nufin real kidnapping bafa, fake one and zuwa nan da kwanaki sai ka saketa, please Fahad..." ya numfasa "A gaskiya Khadija bazan iya ba for what reason zaki sani cikin matsala? Me ma tayi maki?" Tace "Sata tayi min, kai kasanni ko a school ba'a mun sata na kyale, wallahi koma waye sai na dawo da abuna a hannuna, so yanzu haka ma bazan kyaleta ba sai ta dawo min da shi!" Fahad da mugun mamaki yace "Sister dinki ce zatayi miki sata? Is not possible Khadija!" A mugun fusace tace "Wai wannan jan ran na meye? Haba Fahad you're the only bad guy I know, kuma nasan zaka taimakeni." Fahad yace "Khadija just go straight to the point and tell me mey tayi maki?!" Ta numfasa "Ok, we're both in love with one guy, the worse part is that gobe za'a daura aurensu, bana so wannan daurin aure yayi takin place! So sheyasa nace ayi kidnapping dinta in yaso kaga baza'a daura aure ba za'a shiga cikin tashin hankali! Idan lokacin daurin auren ya wuce sai ka saketa!" Wata uwar dariya yayi yace "Wow! Tou tsakaninku keda da ita waye yake so?" A mugun fusace tace "Ina ruwanka? I just want your help zaka taimaka ko baza kayi ba?" Yayi wata dariya "Zanyi of course but not free of charge." Tace "Kudi kuma? Haba Fahad I thought we were good friends before?" Yace "Friends? Yaushe rabon da in ganki? Abeg malama ki fiddo kudi kawai ayi maki aiki!" Ta sauke ajiyar zuciya trying her best to calm down, "Shikenan naji! Nawa zan baka?" Yayi murmushi "Ba yawa ki bada 3m!" Ta wani zaro idanu waje "Ko 1m banida ita bare azo ga 3m, please ka rage mun!" Yayi dariya, "Ba aikin kikeso ba kenan! Alright then bye!" Yana gama fadan haka ya kashe wayar, tafi minti goma a wurin tana huci kafin ta fara tafiya ta koma cikin hall din. "Ina kanwar ango take ne? Muna so tazo ta bude kan amarya!" Mc din ya fada yana kalle kalle, Zarah ta kula yadda Ashraf ya shiga tension a kunnensa ta rada masa "Calm down Ashraf..." ta fada tana masa murmushi, bayan mintina kadan sai ga Hoodah ta fito tana taku d'ai d'ai da maids kusan hudu suna take mata baya, ko wanensu yana rike da dan maidaidaicin box a hannu, kowa na wurin yabita da kallo saboda fadin haduwarta ma bata baki ne tasha makeup tayi bala'in kyau, kansu kayan da ta saka sun boye mata cikinta dan ba lallai bane ka gane ba sai ta matso kusa da kai, suna ganin fitowarta sai aka fara sabon kidi mai kayatarwa gashi tana tafiya mai cike da aji... "Takawarki lafiya yar sarki jikar sarki, sarauniyar mata, sun buga dake sun barki, doguwar mace shugabar mata, sarauniyar kyau kyakkyawar mace mai dimple, sarauniya mai siffar larabawa, mai kirar larabawa jinin buzaye! In kin fito ko ba'a sanki ba sai an tambaya Allah ya kara maki lafiya!" Bag dinta ta bude ta ciro kudin da batasan ko nawa bane ta lika masu sannan ta wuce tana murmushi, warce kudin sukayi suka fara tattara su cike da murna, Hoodah ta isa inda amarya da ango ke zaune ta sunkuya kadan ta fara daga mata veil dinta, bayan ta daga gaba daya sai ta karbi turare daga hannun daya daga cikin maids dinta ta shiga fesa ma amarya ko ta ina, dago kanta tayi tana murmushi "MashaAllah." Shine abinda ta furta kafin ta umarce maids dinta da su fara aje boxes din gefen Zarah, nan kadan a dangi ango suka fito suka dinga fesa mata turare wasu na mata magana kasa kasa alamun wa'azi, nan sukayi welcoming dinta cikin family dinsu, nan ta sunkuya ta gaishe su sukayi huggin dinta, daga haka aka kira amarya da kawayenta su taka, nan aka dinga slide show din wakoki bayan sun kare duk mai so ya dinga shiga yana takawa babu abunda akeyi da likin kudi, daga haka aka ci aka sha akayi hotuna daga nan aka kammala budan kai, wasu suka bata gifts daga haka taron ya tashi aka gama event na yau...
WEDDING FATIHA
Gidansu Zarah ya cika ba matsaka tsinke shiga kawai ake ana fita, karfe biyu za'a daura aura da an daura kuma za'a dauki amarya karfe uku na rana, babu wanda bai halarci wannan taro ba, Khadija kasa dauka tayi ji take kamar zata mutu karshe ma ta kulle kanta cikin bathroom ta dinga razgar kuka, saida ta gaji dan kanta ta fito, ko da Zarah ta tambyeta me akayi mata sai tace ay zatayi missing dinta ne, amarya tana sanye cikin wani shegen lace maroon and pink, tasha makeup very light not heavy, ba karamin kyau tayi ba ko makiyinta sai ya yaba da kyanta, tun safiyar yau hankalinta ya fara tashi sanin yau za'a kaita gidanta. Don haka gaba daya yau idanun nan sunyi ja a dalilin kukan da takeyi... Karfe biyu da minti sha biyar aka daura auren Zarah da Ashraf, Yasir da Hafsat, na Ashraf akan sadaki dubu dari, na Yasir dubu hamsin, sanarwar da Khadija taji na daurin aure Zarah ba karamin gigitata yayi ba, numfashinta ya tsaya cak da aiki a yayinda zufa ta dinga keto mata ko ta ina, da sauri ta fita daga dakin daya cika makil da baki ta tafi backyard inda ta dinga maida numfashi hawaye na zuba daga idanunta, nan ta kuduri zata nemi hanyar da zata bi don tarwatsa farin cikin Zarah, cikin tsananin kuka tace "Zarah kin tarwatsa man farin ciki! You snatched away my love from me! I will never rest until I destroy your happiness the way you destroy mine, bazan taba kyaleki ba Zarah bazan kuma yafe maki abunda kika yi man ba!" Nan ta zauna ta dinga kuka kamar an aiko mata da sakon mutuwa, saida ta gaji dan kanta ta mike ta nufi cikin gidan ta cigaba da sabgar bikin ba tare data bari ta nuna komai ba. Bayan an daura auren mutane suka dinga zuwa inda Ashraf da Yasir suke suna congratulating dinsu, wani relief Ashraf yaji da aka gama daurin auren farin cikinsa ya kasa 6oyuwa he was smiling all the time. Suna zaune shida Sarki Sultan da Yasir a wurin reception din da Sultan ya hada masu nan aka dinga daukar pictures ba iyaka, abinci a takeaway aka bada tare da ruwa da drink, bayan an kare aka soma watsewa. Karfe uku saura aka fara shirin daukar amarya, ba karamin nasiha Mummy tayi mata ba, "Ki girmama mijinki, ki kiyayi abinda baya so ki so abinda yakeso, always look attractive yadda bazai gano wata a waje ba yaji yana sonta, ki rike addini da azkhar dinki, ki kasance ma'abociyar tsabta da kamshi, abincinsa ya zama ready kafin ya dawo daga aiki, daya dawo kin gama kar ya kasance sai ya dawo ya iske ki a kitchen Lokacin kike masa girki, idan yana resting ya kasance bakiyi masa hayaniya, ki maida shi abokinki, dan uwanki, mijinki ya kasance bakijin nauyin fada masa matsalarsa, ya kasance kece mutum na farko da zai fara kawo ma kukansa, ki xamo mai fahimta da sanin ya kamata, ki kaune shi da danginsa ki riritashi kamar sabon jariri, Allah ya albarkace ku ya baku zaman lafiya da zuria dayyiba, yi nayi bari na bari shine xaman aure, Allah yasa albarka tashi kuje." Da kuka aka fiddata daga gidan inda suka tashi zuwa Agadez...
Da daddare suka isa don haka straight dakinta aka kaita bayan ankaita fadar Abba ya tarbeta tare da nasiha da addu'a, daga nan sai aka wuce da ita sashenta su Hoodah ne yan kai amarya sune chest of the wedding lol.
WALIMA
Yau ta kasance walima, nan aka shirya amarya cikin kayatattun kaya tasha lalle tayi kyau abinta, nan makada suka fara nasu aikin kidin amarya da ango na xaune suna kallon event din duk sunsha kyau, nan karar algaita ta fara tashi suke fara ma amarya da ango kirari "Amarya da ango Allah ya bada zaman lafiya! Ango Ashraf Yariman agaden Allah yaja zamanin yarima!" Nan aka uamrci amarya da ango su fito fili su fara takawa kidi na tashi, daga nan aka fara aikin daukar hotuna da videos kuma, daka kalli amarya da ango kasan cikin farin ciki suke ba kadan ba ko wane yana jin son dan uwansa na kara nitsarsa cikin rai. Daga nan aka ci aka sha akayi presenting gift na dangin ango dana shi angon kansa, gab da magrib aka watse taron.
Su Hoodah suka raka amarya dakinta, nan yan ganin gida da basu gani ba jiya suka dinga shiga suna Allah yasa alkhairi.
-------
Wurin karfe tara ya shiga dakin da sallama gidan tsit alamun yan biki sun watse su Hoodah na can side dinsu tare dasu Khadija, Khadija ta dade a nan sai da kyar Hoodah taja ta can tana nunwawa ay zatayi missing Zarah ne, Hoodah tace ay zasu hadu gobe da safe.
Da sallama ya shiga dakin nan ya ganta zaune kan gadon numfashinsa har wani daukewa yayi daya hangota zaune wai yau shine mijin Zarah? He can't believe it, har ta amsa sallamarsa ma baisan ta amsa ba, kanta na kasa cikin katon veil ya dauki tray din da aka aje bisa side bed drawer ya nufi gefenta ya aje, ya zaune a hankali yana binta da kallo, a hankali yayi mata lifting veil dinta, kanta na kasa tana ta smiling nan yaga ta kara yi masa shegen kyau kamar ya cinyeta don so, "Zakici abinci?" Girgiza kanta tayi alamun aah yace "Tou kisha milk." Ya fada yana mika mata a cikin cup, daga ganinta she looks nervous and shy, bayan ta gama sha hannunta yaja sukayi alwala wadda sabbin amare keyi bayan sun kare ya dafa kanta yayi mata wasu addu'oi, bayan sun gama ya kamo hannunta, "Bari na watsa ruwa kema in zaki watsa, are you sure bakajin yunwa ko kazar bakici ba," tayi murmushi kanta na kasa "A'a bana jin yunwa." Yace "Okay, I will be back." Daga haka ya tafi yayi wanka itama ta shige wankan itama.
------
2 Days later.
Amarya da ango suna zamansu lafiya Khadija dasu Hoodah duk sun koma, ranar da zata koma Khadija ta dade gidan Zarah, a ranar sun sha fira kafin ta wuce.
Bayan ta kare sallar asuba tana zaune dakin Ashraf tana karatun qurani, tunda sukayi aure babu abinda ya taba shiga tsakaninsu saboda Zarah a ranar period dinta ya dauke, yace bari ya bari ta huta tukunna, bayan ta idar ta mike xata aje quranin mazauninsa, ta aje quranin kenan kawai sai taci karo da wata paper ta fado bisa kafarta, dukawa tayi ta dauki papern har zata aje sai wata zuciyar tace mata ta bude ta gani, a hankali ta warware ta soma karatawa, "Zarah finally Allah ya bani ke, abu daya nakeso ki sani shine! Ban taba sonki ba! Jikinki kawai yake burgeni kuma tunda yanzu na sameki zan samu abinda nakeso! Zanyi abinda naga dama da ke sannan in barki cikin jifa'i a gidana, zan maida ki sex machine dina! Sai ranar da kika gudureni in koraki gidanku!" Bata san lokacin data saki paper din kasa ba har wani kyarma takeyi, shigowa Ashraf yayi da murmushi saman fuskarshi da yake ta bashi baya yana zuwa ya dafata ta baya, "Good morning princess..." Cikin sheshekar kuka ta warce jikinta sannan ta dinga ja baya tana binshi da wani irin kallon tsana! Zuciyarta na tafarfasa ta kara fashewa da wani irin kuka, Ashraf da yayi tsaye yana binta da mugun mamaki ya matso dab da ita "Lafiya Zarah? What's wrong?" Ya fada yana kokarin kamo hannunta, "Kar ka sake ka taba mun hannu! Is that your intention dama Ashraf? Ban taba tunanin haka daga gareka ba!" Ta fada cikin wani irin gunjin kuka durkushewa tayi rike da kirji tana jin kamar zuciyarta zata fito....
Kuyi hakuri da wannan bana jin dadi yau🤗 unedited 🤦♀️🤦♀️
No comments:
Post a Comment