Saturday, 28 August 2021

YAR AGADEZ PAGE 45

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 45)


To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com




Bayan Mummy ta kammala bata abinci kamar kullum sai ta mike ta nufi kitchen kafin Mama Hauwa tazo ta tattara kitchen din, ita dai Khadija tabita da kallo har ta dawo hannunta dauke da cup da ledar maganinta, dawowarsu kenan daga therapy har yau Mummy bata sake mata kuma hakan ba karamin damun Khadija yake ba gaba daya ta rasa meke mata dadi, zama Mummy tayi kan kujera ta ballo mata duka magungunan nata ta zo bata kenan Khadija tasa hannunta mai Lafiyar ta rike ma Mummy hannu idanunta na kawo ruwa, girgiza kai Khadija keyi sannan ta fashe da kuka sosai kuka take kamar ranta zai fita, saida kukan ya tsaigata sannan ta dubi Mummy da itama idanunta cike da hawaye tace, "Nasan banida isassun kalmomin da suka dace inyi amfani dasu wajen baki hakuri Mummy, fushin nan da kikeyi sam banga laifinki ba saboda ya dace ma kiyi fiye da haka, na butulce ki upon irin kaunar da kika nuna min da soyayyar ki a gareni sai gashi abinda na saka maki dashi kenan..." hawayen ta share kafin ta cije lebe wasu na kuma taruwa a idanunta, "Kamar yadda nace fushin da kikeyi ya dace dani amma kuma bazan iya jurewa ba Mummy, sam bana jin dadin yadda kike treating dina saboda na saba da care dinki na saba da kulawarki, na saba da kaunarki wallahi zuciyata bazata iya dauka ba Mummy don Allah ba don halina ba kiyi hakuri ki yafe man koda na samu nutsuwa a cikin raina..." ta karasa cikin tsananin kuka, Mummy ta share hawayen fusakarta ta mika mata maganin bayan ta sha sai kawai ta mike ta kai cup din kitchen tazo tabi ta gaban Khadija zata wuce kawai sai Khadija tayi sauri ta damko mata hannu gam, Mummy ta juyo tana faman goge hawaye kafin ta janye hannun nata a hankali tayi hanyar sama, dama Khadija ta dauko wata yar karamar wuka, Mummy har ta kusa hayewa sai Khadija ta saita wukar daidai wuyanta tana kuka tace, "Fine! Tunda bazaki yafe mun ban banga sauran amfanina ba a duniya, Mummy you're my whole world, don haka barina duniya shine yafi alkhairi...." Cak Mummy ta tsaya gamida juyowa da sauri idanu ta zaro waje kafin ta juyo Khadija ta fara kokarin caka maka kanta wukar nan, aiko Mummy tana isowa ta warce wukar a tsorace tana kallon Khadija cike da shock, durkusawa Mummy tayi har wata kyarma takeyi tace "Khadija meye haka? Are you mad? Mekike shirin aikatawa?" Khadija tayi murmushi, "Dama nasan har yanzu kina sona Munmy, why are you pretending?" Mummy ta juya fuskarta gefe kafin tace, "Saboda kin aikata babban laifi a gareni! Na saki a inuwa sai kika tunkuda ni rana Khadija you betrayed me, meye namiji? Da har zaki cuci yar uwarki akansa? Haba Khadija!" Khadija Ta girgiza kai cike da karfin hali tace, "Nasani, amma yanzu na gane kuskurena, don Allah don annabi ki yafe mun, ni mai laifi ce na kuma amsa laifina, ki yafe man Mummy." Mummy ta rungumeta a hankali, "It's okay Khadija na yafe maki, ya wuce kinji? Koda wasa kar ki sake aikata makamancin haka kina jina?" Da sauri ta girgiza kai cikin kuka tace, "Never Mummy InshaAllah." 

---------

2 WEEKS LATER...

A hankali Mummy ke tura ta a bisa wheelchair har sai da suka tsaya daidai office din Dr Hafiz, Mummy ta gyara mata wheelchair din yadda zata iya tura kanta don wani botton ne kawai zata danna keken ya fara tafiya, sannan ta dan sunkuyo tana murmushi, "As always ki shiga zan jiraki a inda na saba jiranki kinji ko?" Ta gyada kai sannan Mummy ta juya ta fara tafiya, ita kuma tasa hannu ta fara knocking kofar a hankali, ji tayi ance mata "come in." tasa hannu ta bude kofar ta fara tura kanta a ciki, saida ta isa daidai table din office din sannan ta tago tana kare masa kallo, a dan tsorace ta fara kokarin tura keken nata zata fita dan ita a tunaninta ma ba office dinsa ta shigo ba saidai kuma data sake bin office din kallo tsab sai taga lallai office din nasa ne komai yana nan a yadda ta saba gani, daidaita kanta tayi sannan tace "Salam? Good morning?" Ta furta a hankali tana kallon bakuwar fuskar data tsareta da idanu, "Wslm, morning too, Khadija ko? don ya sanar dani ke kadai ce yakeda appointment dake yau ko?" A hankali ta gyada masa kai tana kallon kasa, "Ina yake?" Ta tambaya tana kara kallon kofa koda zataga Dr Hafiz din ya shigo, "Wani emergency yake attending to so bazai samu damar ganinki ba a halin yanzu, sunana Dr Aliyu yau ni ne zan maki therapy." Kafin ya mata bayani har tanada niyyar juyawa ta fita sai kuma ta dakata tana saurarensa, tana tunanin yau Allah ya hadata da mai surutu, a hankali ya mike yana murmushi ya kamo keken nata sannan ya shiga janta zuwa wata yar kofa inda zata sadaka da therapy room din. Duk wani abu da ya kamata Dr Hafiz yayi mata Dr Aliyu yayi har ma fiye, har ma cikin aikin nasa ya kan tsaya yana mata yar hira ko tambayoyi don ma ya dauke mata hankali daga pain din da takeji a jikinta, hannun nata yake massaging a hankali cikin kwarewa, ganin tana dan cije lips dinta sai ya dakata yana kallonta fuskarsa dauke da murmushi yace, "Khadija yanzu what do want to do with your life? Kinga kamar ni kullum karatun likitanci baya kare min, kullum cikin research nake amma still ina samun lokaci inyi karance karancen novels da poems, and also ina da babban shop a nan garin ina siyar da kayan maza kamar su shadda, jallabiya, shoes, hula everything da kika sani na maza ina dasu, ke me kikeso kiyi?" Ya tambaya yana cigaba da mata therapy din, dan murmushi tayi mai cike da hawaye sai tace, "Koda ina so amma a halin yanzu bazan iya yi ba saboda condition dina..." Shiru yayi yana kallonta kafin ya sauke ajiyar zuciya, yace, "No Khadija don't say that, you can do it kar ki sake bari lalurarki ta hanaki purchasing dreams dinki," tun tana yarinya babu abinda takeso kamar fashion and design especially idan ya zamana tana designing kayan da kanta tana zanawa, saidai tunda wannan abin ya faru da ita taji komai ya fice mata a kai, murmushi tayi ya taimaka mata ta tashi zaune a hankali tana sunna kai, "Ina son fashion and design especially a harkar designing kaya bawai a dinka min ba a'a na dinga dinkawa da kaina kuma ina designing, I so much love it." Murmushi yayi ganin ya samu hanyar da zai taimaka mata yace, "Tou yanzu Khadija idan aka baki paper da pen zaki iya farawa? Kuma kin iya ko kuwa kina bukatar training?" Da murmushi mai gaggawa ta daga mashi kai, a hankali yayi lifting rigarta zuwa cinyarta ya tsugunna daidai kafar ya fara mata massaging kafar, sannan ya jawo wani machine mai kamar bicycle ya dora mata kafar ta fara exercise din kafin tace, "Zanyi sosai, akwai abubuwa da yawa wanda bayan fashion and design zan iya mantawa dashi, nidai for me wannan ne kadai ke sani farin ciki I think it's the best gift, my opinion though." Mamakin kanta ma take yaushe rabon da tayi magana har haka? Balle ma ta tsaya dogon bayani, cike da salo da dubara ya cigaba da mata massage dinnan har saida ya kasance sam bataji wani wahala ba kamar yadda take ji a wurin Dr Hafiz sai taji yau salon nasa na daban ne, nan ya gama lura da ita akan cewar fa da gaske take har kasan ranta tana son fashion and design, bayan ya gama sai ta daga waya ta kira Mummy, Mummyn tace, "Ina kika yadar wayarki ina ta faman kiranki baki dauka ba?" Khadija ta duba wayar cike da mamaki tace "Wallahi Mummy ban ji ba kiyi hakuri." Mummy tace "Bakomai, dama ince maki wallahi wani emergency meeting ne manager din company dinmu ya kirani wai yana son ganina da gaggawa, tou ga Audu driver nan na kirashi yace min zaizo ya dauke ki, nace wa Mama Hauwa ta bashi key din dayar motar tawa zaizo ya dauke ki kinji? Ki samu nurses sai su taimaka maki ki shiga mota, am truly sorry daughter." Khadija ta marairace tace, "Ok Mummy bari in kira Audun yanzu." Mummy "Ok tou, sai na dawo take care kinji?" Khadija tace "Thank you." Sannan ta katse wayar ta shiga kiran number din Audu kamar da wasa taki shiga, ta dago kamar zatayi kuka tace "Number driver dinmu taki shiga, kuma Mummy ta tafi wani meeting." Dr Aliyu yace, "Tou yanzu ya za'ayi kenan Khadija?" Tace "Ko in dan kara jira nasan zaizo tunda Mummy tace tayi magana dashi." Yayi ajiyar zuciya, "It's ok, am sorry Khadija na shafa'a ko ruwa ban kawo miki ba." Tayi murmushi "Ba damuwa ay bana jin kishirwa." Zama yayi a gabanta yana binta da kallo kafin yace, "Tou malama Khadija baki fada man sunanki ba?" Da wani yanayi take kallonsa irin ba yanzu ka gama kiran sunana ba? Amma sai ta dake tayi murmushi tace, "Sunana Khadija." Ya girgiza kai, "Ni kinga sunana Aliyu Haiydar Mahmud, ke meye sunanki?"da kyar ta kakalo murmushi kafin tace "Sunana Khadija Hamza." Bata jira cewarshi ba ta juya kan wheelchair dinta ta fita daga office din, dan fadan sunanta ya taso mata da dukkanin damuwar da take kokarin dannewa. Saidai kuma idan ta tuno da abinda takeso a rayuwa wato fashion and design sai taji sanyi a ranta, tana hango kanta a matsayin fashionista sai ta saki dan karamin murmushi har ta isa harabar asibitin bisa yar verandar a waje a nan ta tsaya, bata kai minti biyar a zaune ba sai kawai taga mutum tsaye a kanta ta dago tana kallonsa amma da alama baisan abinda zai fada mata ba, can yayi yar dariya cike da zolaya kamar yadda ya saba yi mata yace, "Kece?" Ya tambaya kamar wani sakarai yana kokarin danne dariyarsa, hade fuska tayi tamau "Nice wa?" Ya hade hannu waje daya, "Sorry malama Mummy ta kirani akan nazo na dauke ki, so dana zo naga kin tasani a gaba da kallo so I thought bake bace bama." Ta kara hade rai, "Am sorry Doctor but ni ba inda xan bika saboda Mummy tace man driver ta aiko ba kai ba." Yayi yar dariya gamida zaro wayarsa aljihu yana adjusting glass dinsa, ya dadanna wayar kafin ya sa a speaker, Mummy ce ta daga, "Hello Mummy ina wuni?" Mummy tace "Lafiya lau Dr Hafiz, har ka ganta?" Yace "Eh naganta Mummy gamu nan tare gida zan kaita ko?" Tace "Eh, amma don Allah kayi hakuri doctor na taso ka aiki nace ka maidata, wallahi babu yadda zanyi ne na kasa samun driver dina don na kirashi yace man zaije har dai na gaji da jira ashe shi baima je gidan ba, sheyasa na kiraka am sorry to disturb your work." Yayi murmushi yana tsareta da idanu, "Mummy bakomai ay yanxu mun zama daya karki damu.... yauwa thank you." Daga haka ya katse wayar yana kallon Khadija wacce tunda ya fara wayar take binshi da kallo cike da mamaki, wai me yake nufi? Shi zai kaini gida kenan? Da guntun murmushi a fuskarsa ya kamo wheelchair din tata ya fara janta a hankali, "Tou malama Khadija yanzu kin yarda xaki bini kenan?" Gyada kai tayi kawai har suka isa inda ya paka motarsa ya bude gaba ya taimaka mata ya sata motar sannan ya nade kaken ya sashi booth ya zaga side dinshi ya rufe motar har yanzu fuskarshi murmushi yakeyi, bayan ya harba titi saida tafiyar tayi nisa sannan yayi magana amma can kasan makoshi, "Are you hungry? Zan tsaya restaurant na karbi abinci." Juyowa tayi taga yana magana sannan ta girgiza kai a hankali, "A'a thank you." Daga haka suka cigaba da tafiya, can sai kuma taga sun shiga gidan mai, suna nan tsaye ana zuba masu man sai ya juyo yaga idanun Khadija sunyi rau rau, da mamaki yace "Khadija lafiya?" Da sauri ta share hawayenta batasan lokacin da tace "Don Allah ka ara man kudin in ba matar can." Bata taba tambayar namiji abu ba yau ta tsinci kanta da hakan, don ko bakada imani matar sai ta baka tausayi, ta window ya dan leke ya kalli matar yaga tana kallonsu take ta bashi mugun tausayi, yasa hannu aljihu ko tsayawa kirgawa baiyi ba ya mika ma Khadija, bude motar tayi tana shafar fuskar yaron sannan ta mika ma matar kudin, "Gashi nasan ba lallai bane suyi maki maganin matsalarki amma ina rokon Allah yayi maki maganin duk wata damuwar da kike ciki ya yaye maki alfarmar annabi (SAW)." Matar babu abinda takeyi sai godiya ta sa6i yaronta wanda daga gani baida lafiya ta goya shi tana goge hawaye, bata tsammaci samun kudi koda rabin haka bane a yau, tayi masu sallama gamida godiya marar adadi sannan ta juya ta cigaba da tafiya, kofar motar ta rufe tana bin matar da kallo cike da tausayawa, daga nan Dr Hafiz yayi payment sannan suka cigaba da tafiya. Saida yayi yar tafiya kadan sannan ta juyo tana murmushi, "Nagode sosai, idan muka je gida zan mayar maka." Murmushi yayi mata ganin yadda take kokarin maida hawayenta ita ta rasa yaushe ta zama mai tausayi haka sosai? "tou ay ni kaina bansan ko nawa bane saidai ki maida man da wani abin amma ba kudi ba." Kallonsa tayi tana auna maganarshi kafin tace "Ay ba kudi zaka bani ba, amma dai me kakeso?" Lokacin ne yayi daidai da zubar hawayenta, dan jim yayi yana kallonta kafin yace, "Yanzu a bar maganar bashin nan Khadija, first of all ki goge hawayenki." Batayi masa musu ba tasa hannunta mai lafiyar tana ta faman goge hawayen amma kamar ana kara tunkudo su. Har suka isa bakin restaurant din Khadija na kuka saida ya kashe motar kafin ya juyo yana dubanta gaba daya jikinta rawa yakeyi, hanky ya ciro daga aljihunsa ya mika mata, saida tayi kamar bazata karba ba sai kuma ta amsa ta fara share hawayenta, gaba daya tausayi take bashi ko ba'a fada ba yasan tana cikin kunci da bakin ciki, yasan ba ganin almajirar nan kadai yasa ta kuka ba, dama dai akwai abubuwa cunkushe a cikin zuciyarta, tabbas kukan nan nata yanada nasaba da mummunar kaddarar data afka maka kwanakin baya amma bawai don an mata fyaden kadai take kuka ba akwai connection gameda fyaden. Saida ta gama share hawayen sannan ta mika masa maimakon ya amsa sai ya dauko bottle water dake ajiye gefensa ya mika mata, "Wash your face Khadija, kar mu shiga cikin mutane suyi tunanin sato ki nayi ko kuma cutar dake zanyi." Khadija batasan lokacin data maka masa wata uwar harara ba, (ashe ma satowa) ta fada cikin ranta, dariya ya fashe da ita, "Ashe dama kin iya masifa? Irin wannan harara haka ay sai kisa tari ya sarke ni!" Bata tanka sa ba ta karbi ruwan ta bude kofar motar ta wanke fuskarka yana zuba mata har tagama, juyowa tayi bayan ta mika masa murfin kwalbar tace, "Thank you." Haka kawai sai ta fara dana sanin kukan da tayi a gabansa ta fara tunanin kar ya fara raina mata wayau ko kuma makamancin haka. Amma duk da haka bayan tayi kukan sai takejin ranta yayi sanyi zuciyarta tayi mata wasai, tana Kallonsa ya bude motar ya fita ya zagayo ya dauko wheelchair dinta sannan ya gurgurota a gabanta, "Muje ko? Bari na taimaka maki." Da sauri ta girgiza kai, "Ay da ka barni a nan ka tafi ka karbo ni zan zauna a mota." Ta mirror take kallon kanta yadda kwayar idanunta ta kada tayi jajir, sannan ita sam bataso a ganta akan wheelchair tazo restaurant, "A'a baza'ayi haka ba Khadija, ya kamata kizo muje tare nasan bakici komai ba, kuma nasan halinki sarai yadda Mummy ke fama dake akan abinci kullum, yanzu kuma ga kukan da kika sha in ba so kike abu biyu ya hade maki ba ga damuwa ga yunwa su karasa rayuwarki gaba daya." Da kamar bazata je ba can kuma ta gyada kai da haka yayi mata murmushi sannan ya taimaka mata ta hau kan wheelchair din kafin ya rufe motar, a hankali yake janta as if idan ya tura ta da karfi zataji zafi, wuri ya sama masu kusada window suka zauna kafin ya bada order abinda zasuci dan yasan ko ya tambeyeta ba lallai bane ta fada masa abinda takeso, shiru duk sukayi alamu sun nuna Khadija ta koma duniyar tunani, dan snapping finger dinsa yayi yana daga mata kai, "Hello what happened?" Da sauri ta girgiza kai tana kakalo murmushi, "Bakomai am fine." Ya tsareta da idanu, "Are you sure?" Ta sake girgiza kai da sauri, "Am sure." Suna nan aka kawo masu order dinsu, jollof din shinkafa da half chicken sai salad, saida suka gama cin abincin ya biya sannan yajata suka tafi mota, bayan sun shiga Dr Hafiz ya juyo yana kallonta, "Dr Haiydar yace man kina son fashion and design, kina son na siya maki keken dinki?" Bata san lokacin data daga kai ba tace eh, sai can kuma ta tuna me tayi, ya za'ayi ta bari Dr Hafiz ya siya mata keken dinki? After all bada paper ake siya ba, da sauri tace, "What i mean is inaso, amma bawai aje a siya ba...." dariya kawai Dr Hafiz ya fara yi, "Karki damu zan siya maki, I will make sure nayi maki dukkanin abinda na san zai saki farin ciki Khadija..."  da sauri Khadija ta girgiza kai, "A'a don Allah kar ka siya, kai kasan bazan iya dinki ba and I also need proper training." Yayi murmushi "Tunda na hadu dake Khadija ban taba ganin farin cikinki ba sai da Dr Haiydar yayi man expressing how happy you are, and I promise myself am going to make you happy no matter what Khadija, you don't need to start using it now if you don't want to, xaki iya aje shi har sadda kikeso kinji ko?" Ya karasa yana mata murmushi sosai, gyada kai tayi cike da farin ciki marar iyaka, kafin su wuce inda zai siyo mata keken kamar yadda yayi mata alkawari, aikuwa haka akayi keke ya siya mata har guda biyu yayi making payment da komai ba tare da ya tsaya jin tsadar su ba bai ma damu da wata tsada ba shidai burinshi kawai yasa Khadija farin ciki wanda yasan cewar her happiness lies in his happiness, he don't know how it happened but all abunda ya sani shine ya kamu da kaunar Khadija kuma kauna bata wasa ba, sai daya ya gama ya biya motar da zata daukar masu har gida suma ya biyasu kudin dauka, sannan yaja ta mota babu abinda Khadija keyi sai share hawayen farin ciki, daidai harabar gidansu yayi parking yana kallonta, "Zan maki registration inda zakiyi training dinki na cikar burinki." Tayi murmushi, "Dr banida bakin da zan gode maka akan abinda kayi nagode sosai sosai, registration dinma na gode." Hanky dinsa wanda ke hannunta da ya bata dazu ta share hawayenta ta dalilin kuka da tayi ta mika masa, kin karbar hanky din yayi yace, "Shi hanky din kyauta na baki, duk sadda kikayi kuka zaki shiga mutane sai ki goge hawayenki dashi, amma da bashina na dazu da kudin registration wata rana zance ki biyani." Ya karasa yana sakar mata wani irin kayattacen murmushi, itama murmushin ta mayar masa kafin ya zagayo ya bude mata ya taimaka mata ta hau kekent, Mama Hauwa ce ta fito ta jata ciki, nan kuma yasa mai gadi ya shigar mata kekenta duka biyun cikin gida, bakin motar ya tsaya yana kallonta har saida suka shiga ciki kafin a hankali ya juya ya shiga motarsa ya tada ya bar gidan....

-------

Kusan rabin jikinta a nashi yake wai kuma a haka kallo take, robar ice cream ce a hannunsa yana bata a hankali duk da ya hanata shan abu mai sanyi amma akan ice cream sai su tada gari ta dinga mishi kuka kenan indai bata sha ba, wani lokaci da gangan zai ki bata ice cream din sai ta juyo ta kalleshi sai ya dan sunkuyo yayi mata peck a kumatu kafin ya sake bata tasha. Zuwa yanzu soyayyar da Gimbiya Hoodah ke wa Sultan ta kara linkuwa kan wacce take masa a da har ma ji take duk soyayyar da tayi masa ba komai bace compared to yanzu da take jinsa har can kasan ranta, daga karshe ma ta kwantar da kanta saman kafafunsa tana kallon fuskarsa dauke da kyakkyawan murmushi tace, "Ka gaji ko?" Aje ice cream din yayi kan center table din parlon yana kallonta, "Abba fa yazo na fada maki kuwa?" Da sauri ta kalleshi, "Abbana? Shine ko ka fada man inje in gaishe shi?" Yayi yar dariya, "Bai iso da wuri bane shine ma yayi min umarni akan kar na fada maki sai gobe da safe, amma yace da kinji sakonsa da safe ki garzaya wurinsa don yayi kewarki da yawa." Wani irin dadin murna ta fara yi wane an mata albishir da gidan aljanna shi kuwa Sultan kallonta ya tsaya yi fuskarsa cike da annuri. Sai kuma ya bata fuska, "Nifa gaskiya Hoodah ina da complain, an jima rabon da kice man I love you..." ya kara tsuke fuska, tayi dariya, "La abinda ka tsiro dashi yau kuma kenan? Tou shikenan kayi hakuri kaji?" Ya kara bata rai, "Aww tsurowa ma nayi kenan? Wato kin daina sona ma kenan ko?" Ta fashe da dariya sosai, kara tsuke fuska yayi yana kokarin dagata daga jikinsa ta makalkale shi, "Tou wai bana baka hakuri ba?" Turbune fuska tayi shima ya bata rai, "Ay ban hakura ba tunda har yanzu kin kasa furta kalaman da nake son ji a bakinki." Gani tayi dai da gaske yayi fuska  sai abin ya burgeta ba kasafai take ganin fushinsa ba da wuya kafin tagani. Akwai ranar data bashi haushi sosai yace mata, "Hoodah sonki da nake yasa bana iya fushi da ke, amma duk ranar da nace zanyi fushin da ke abin bazaiyi kyau sheyasa ban taba yarda har ma in yarda inyi fushin dake." Kara makalkale shi tayi tsam, "Tou wai fushin na menene? Ina sonka Sultan, I love you so much! Shikenan happy?" Da sauri ya kalleta amma can kasan makoshi ta furta, "Ay banji ki ba, maimaita." Dariya sukayi dukkansu ta jawo kansa ta saita bakinta daidai kunnensa ta fada cikin wani irin tsawa, "Ina sonka mijina!" Wani irin toshe kunnensa yayi ita kuwa ta kyalkyale da dariya, ji tayi ya rungumeta tsam a jikinsa, bata ankara ba taji ya dagata duk da katon cikinta kuwa bai ji nauyinta ba, idonta a rufe sai data ji karar kashe tv tayi sauri ta bude idanunta tace, "Ina zamuje?" Dariya ya danyi yana kissing kumatunta sosai, sannan ya duko daidai kunnenta yayi maganar kamar rada rada, "Bacci zamuyi mana naga yau soyayyar da gaske kike yinta." Dariya kawai tayi ta kulle idanunta hade da kara makalkale shi wani irin farin ciki yana sauka cikin zuciyarta....





Na gode da addu'oinku Allah ya bar zumunci🤝❤️

1 comment:

jadeeyant said...

Playtech launches UK live dealer slot machine - JT Hub
Playtech, 의왕 출장샵 the world's leading 김해 출장마사지 provider of 성남 출장안마 iGaming 안성 출장마사지 content, has launched its first live 창원 출장샵 dealer-slot machine 'Descent Into Dreams: Dreaming