YAR AGADEZ
{Page 46}
To read all my books click the link below👇🏻
Maryamsbello.blogspot.com
Da asuba Ashraf ya farka a hankali ya zare jikinsa daga nata sannan yaje bathroom ya dauro alwalla ya wuce masallaci, dama Zarah taji motsinsa don haka itama sai ta mike ta tafi don yin tata alwallar. Tana gamawa tare da azkhar dinta da addu'ointa ta haye gado ta koma bacci. Sai wurin karfe tara ta farka mamaki tayi yadda ta ganta kwance bisa kirjin Ashraf, saida tayi dubara sannan ta samu ta zare jikinta ta wuce dakinta, brush tayi ta wanke fuskarta sannan ta hau gyaran gida tas ta tsabtacce ko ina ta kunna turaren wuta ta fesa freshner ta kunna ac kafin kace me gidan ya fara bada wani scent mai dadin gaske. Tana gamawa tayi wanka ta shirya cikin wani dinkinta na atamfa doguwar riga tasha stone work sai kamshi ke tashi daga ko wane bangare na jikinta. Tana gamawa ta fada kitchen dama already kafin ta shiga wanka duk ta fera dankali ta yanka albasa da sauransu tana xuwa kawai ta dora wuta kan gas ta cigaba da aikinta a natse. Tana tsakar hada breakfast din tana rera waka in a low tone amma ana jin sautin kadan. "Yaya xanyi in misalta soyayya? Yaya zanyi in fisalta soyayya?.....Itace ba'a siye da kudi duk dukiya... itace mai gida na mulki shine zuciya... ta sanya mai karfi ya sunkuya..... ya zubda hawayen idaniyaaa....." ta dora mai a bisa pan da yayi zafi sai ta saka sausages din suna soyuwa sannan ta cigaba da wakarta.... "idanuna suka jani kafafu sukka ka kaini zuciya tana dauki.... nasan xan kece raini zai zamto ba kamar ni kin kirani angonki... ko nawa aka ce gareni indai har za'a bani xan biya sadakinki.... da zan zamo miji gunki... zan kare dukka hakkinki... in zamo adali a mulkinki.... mai martaba a fadarki..." Ba zato kawai taji an rungumeta ta baya, "Ashe dai idan na biya sadaki zaki kira angonki? Dont mind yanzu ay na riga na biya sadakin tuni har ma kin shigo fadata kuma zan zama adali a mulkinki..." yar dariya yayi ganin yadda ta dan xama shocked alamar batayi expecting dinsa ba. Juyowa tayi tana faman turo baki, "Ni gaskiya ka bani tsoro sannan kuma ban shiga fadarka ba."
Murmushi yayi ya lakuci hancinta, can kuma sai ya bata rai, "Ni ay fushi ma nake dake ko kice ma ya jiki ko?" Da yake kwana biyu yayi fama da ciwon kai marar dadi, ya hade rai gamida bata baya, saurin rungumo shi tayi ta baya ta rike shi gam gam, "Am sorry wallahi I didn't forget, ya jikinka? Kaji sauki ko?" Ta tambaya fuskarta cike da tausayi karara, Ashraf yayi murmushin mugunta ya juyo a hankali tare da tallabo fuskarta yana fadin, "My cry cry baby, kar dai kiyi min kuka kinji? In kina so nayi hakuri sai kin bani hot kiss wanda baki taba yi min irinsa ba a nan..." ya karasa yana nuna bakinsa wanda yake light pink naturally haka yake duk cikin fuskarsa babu abinda ke kara masa kyau kamar bakin nan nasa, Zarah ta zaro idanu waje tare da juya fuskarta cike da kunya, dama ta kwashe komai da sauri ta hada cikin warmers ba tare data sake kallonsa ba ta wuce da sauri dining tana jera kayan, tana ajiye flask din zata juya taje da dauko masu plates da cups kawai tana juyawa sai ganinsa tayi tsaye ya dauko plates din da cups yana faman yi mata murmushi ita kuwa da sauri ta sadda kanta kasa, bama taso ko da hada idanu suyi, kanta kasa ta zo zata wuce ta gabansa kenan taji ya riko mata hannu da sauri ta dago kanta tana kallonsa take yayi mata wink, janye hannun nata tayi da sauri ta wuce kan kujera ta zauna kanta kasa ta fara masu serving abincin, saida ta kammala zuba masu sannan suka fara karyawa a natse. Shi kuwa Ashraf babu abinda yake mata sai magana ita kuwa taki koda kallonsa bare yasa ran zata amsa masa. Kallonta yayi yace, "Tou Zarah nidai zan tafi office mata nacan suna jiran the most handsome man..." ya fada yana dariya kasa kasa ganin yadda take mood dinta ya chanza ta hade fuska kishi bayyane saman fuskarta kafin tace, "Wai wama ya dauke ka wannan aikin? Ni kwatakwata banso Mummy ta samo maka aikin bankin nan ba, yawancin duk mata ne ke sa matsatsun kaya ko kuma ka gansu da dogon wando, ga Christians nan duk sun sha dagaggun skirt duk kafafunsu a waje...." Dariya yayi sannan ya fara bata amsa, "Zarah kenan, ah sosai fa zan rika ganin mata kala kala har sai na darje, gara ki rike Ashraf dinnan fa kar ki bari ya fita yanzu..." Dariya tayi sosai sannan ta dan bigi kafadarsa tana cigaba da dariya. Har ya fita ya dawo yana fadin, "Am joking princess, besides yau ba aiki sai gobe inshaAllah it's a public holiday today remember?" Tayi murmushi tana gyada kai, key din gidan ya bata don yana so ya kulle ta gaba duniyar yanzu ta zama abinda ta zama, "Ga key dinnan karki sake ki bude ma wanda baki sani ba har sai na dawo." Tace "InshaAllah." Har bakin kofa ta raka shi sannan ya bata spare key din ta rufe gidan, tana dawowa ciki ta saka wayarta charge sannan ta gyare dakinsa ta wanke bathroom sai ta dora abincin rana. Saida ta kammala tas ta zauna parlor ta kunna kallo har bacci yayi gaba da ita.
******
2 WEEKS LATER...
Yau satin Zarah biyu da taje ganin gida da kuma duba jikin yar uwarta Khadija, Ashraf ji yake tafi shekara biyu bata tare dashi gaba daya gidan ya masa girma saukinsa ma yana zuwa aiki kuma kullum suna waya da chatting. Ranar da tayi shirin dawowa tayi niyyar bashi surprise kasancewar yau Tuesday ta kama tasan definitely yana office, saida ta wuce gida ta sauke boxes dinta tas sannan ta kullo gidan ta dauki hanyar bankinsu Ashraf, koda ta shigo sai ta iske wayam office dinsa babu kowa nan suke sanar mata ay sun fita shida manager din bankin sun tafi wani branch din, xama tayi kan kujera tana bin office din da kallo yadda ya kawatu duk da ba yau bane ta fara zuwa amma sai taga duk ya chanza mata lallai central bank ta hadu, bisa table din hotonsu ne na biki ansa cikin frame ya aje shi a tsakiyar table din, gefe kuma wasu files ne wanda basu kai ashirin ba, sai laptop dinsa dake ajiye a gefe kwatakwata dai office din very simple yet classy, ac duk ta cika wurin ga kamshi na musamman na tashi, murmushi tayi a cikin ranta ta kagara ya dawo, tana cikin wannan tunanin ne kawai taji alamun shigowarsa, tana juyawa ta ganshi tsaye idanunsa waje bakinsa bude yana kallonta itama cike da murna ta daka wani uban tsalle wane karamar yarinya taje ta rungume shi, shi farin ciki ma ya hana shi magana, fuskarsa cike da murna hade da mamaki, kara rungumota yayi yana rufe kofar office din nasa da kafa, "Oh my princess is back, ya Allah am so happy I really miss you princess." Ya fada yana juyi da ita tsakiyar office din ita kuwa sai dariya takeyi tana kara makalkale shi, "Meyasa baki fada man yau zaki dawo ba princess? Ko duk missing din nawa ne yasa bazaki iya kirana ba? Da ba sai inje airport in dauko ki ba?" Tayi dariya, "I wanted to surprise you ne fa, kuma ni na kosa na ganka bazan iya jira har sai kazo ba, mu tafi gida ko baka tashi ba?" Dariya yayi ya aje file din da ya dawo dashi saman table sannan ya dauko key din motarsa, hannayensu rike cikin na juna ko wanenensu fuskarsa dauke da farin ciki sai binsu ake kallo cike da sha'awa, "Kasan yadda nakeji kuwa da na tafi? Ji nake kamar zuciyata zata fashe tsabar yadda nayi kewarka." Yayi dariya tare da rungumota ta gefe, yace "Wai ya naga kin kara kyau da haske ne? Kodai wayau kikayi man kika tafi can Mummy ta dinga baki kayan dadi kina ci ke kadai a can?" Shi ya fara bude mata motar ta shiga sannan ya zaga ta side dinsa ya shiga shima tana ta dariya tana girgiza kai kafin a hankali taji saukar lips dinsa a goshinta, kunna motar yayi ya fita da reverse, saida ya hau titi ya juyo yaga ta langa6e kan kujera idanunta na rufewa sama sama ga gajiya nan bayyane saman fuskarta da kasala. "Anya Zarah? Dama na lura tun kafin ki tafi kike wannan yawan kasalar, yanzu kuma jirgi fa kika hau balle ace gajiyar hanya ce." Idanu ta bude waje da sauri ta mike tana auna maganganusa, ganin yanayinta yasa ya kyalkale da dariya yace, "Wasa nakeyi koma kiyi baccinki rankishi dade." Daga haka ya cigaba da driving dinsa can taga ya tsaya pharmacy bai jima ba ya dawo wanda batasan meya siyo ba, daga nan kuma taga ya tsaya kfc ta dago tana kallonsa, "Na dauka gida xamuje inyi wanka in chanza kaya?" Yayi murmushi "Bari na siya mana abinci tunda nasan bazaki iya mana girki ba ganin yanayinki a halin yanzu..." yana gama fadan haka ya fita daga motar yana dariya itama ta fito, family size ya siya masu da chips sai katuwar coke. A haka suka dawo gida yana driving da hannu daya dayan kuma ya rike ma Zarah hannu dashi. Bayan sun fito a mota ta tayashi daukar kayan suka shiga ciki, tayi mamakin ganin gidan tsab don ita dazu ma ko lura batayi ba ajiye kayanta kawai tayi ta fito, gidan babu datti ko guda daya kitchen dinnma haka ba karamin mamaki tayi ba, batayi zaton haka zata iske gidan ba. Tana zaune kan gado daga ita sai karamin towel tana kokarin warware kanta, rabon data data gyara kan tun kafin tayi tafiya duk ya curkude wurin daya, shigowa yayi ya aje ledar kan side drawer kafin ya zauna gefenta yana kama gashin nata yana tayata kwance inda ta kitse shi, "Wai meyasa bakyason yin kitso ne Fatima? Gashi kullum sai ya wahalar dake, dama ance duk masu gashi basu san ta6a gashinsu tou gashi nan na tabbatar dai a kanki." Dariya tayi tana tayashi warware kan nata, "Ni banma san yadda xanyi ba tunda na tafi ko ta6ashi banyi ba, Ashraf kasan yau sai nayi ciwon kai tsabar wahalar da zansha." Lumshe idanu yayi a hankali kafin ya bude, "Tou ko a wanke kan yau? Dama kin dada baki wanke shi ba nasan bazaiyi zafi ba idan har na wanke maki da kaina?" Dariya tayi tana kwantawa saman gadon tana kallon kyakkyawar fuskarsa tana murmushi. "A'a kabari sai gobe don nagaji sosai, kaji yadda nakejin bacci kuwa? Yanzu ma wanka nakeso in shiga sai in kwanta..." ledar daya aje ya jawo ya rike a hannunsa kamar za'a kwace masa ita, "Wai meye a cikin ledar nan kake ta faman rike shi kamar ranka?" Ita da wasa ta fada amma shi har ransa yaji, gyara zama yayi yana faman dagata saura kadan towel din ya fadi tayi saurin riko shi gam, "Ashraf!" Yanda ta rude sai abun ya bashi dariya, mika mata ledar yayi, ta bude nan taga PT strip ne da sauri ta dago tana kallonshi, "Wannan fa? Ba shi bane ka siyo kafin inyi tafiya muka gwada mukaga negative? So kake yanzu ma in sake gwadawa in kara ganin wata negative din ko? Kuma ranar duk ka nuna damuwarka da ya nuna negative har kwalla nayi ranar da daddare..." jawota yayi ya rungume ta a jikinsa yana kissing gashinta daya baje bisa bayanta, "I know princess, kawai mu sake gwadawa, I promised you in babu bazan sake gwadawa ba har sai ya fito da kansa cikin," gyada kayi tayi alamun eh sannan ta tashi ta shiga bathroom sai da abun yayi reading sannan ta fito ta dora shi bisa drawer ta bar wurin da sauri she don't want be disappointed again kuma. Tashi yayi bayan minti biyar ya leka abin ya dago mata shi, nan ya jawota ta fasa ihu hade da runtse idanu gabanta na faduwa, "Menene?" Da wani irin murmushi yake kallonta yana kara rungumeta, kissing fuskarta ya fara yi cike da farin ciki kafin yace, "Thank you so much Zarah! It's positive Alhamdulillah!" Rumgume shi tayi tana hawaye she can't believe wai zata haifi gudan jinin Ashraf Allah mai iko. Kara rungumeta yayi yace "I love you so much Zarah, kin biya ni yau am so happy, so so happy! Am the happiest man right now Zarah, zaki haifa man jinina! Ina sonki Zarah kinji?" Hawaye suka kara shatata daga idanunta ta rungume shi gam gam tana jin yadda farin ciki ke sauka saman zuciyarta...
--------
FEW WEEKS LATER!
Sintiri kawai yake yi a bakin kofar labour room din, Ashraf da Zarah ma ko wane cike da damuwa ji take kamar ta shiga taga meke faruwa a ciki, Ashraf kuwa damuwar data bayyana a fuskarsa yama kasa koda magana ne, sarki Sultan kasa shiga dakin labour room din yayi ba yadda ba'ayi dashi ba akan ya shiga amma fir yaki don gani yake yana shiga za'a ce mashi ta mutu amma shi kansa ya tabbatar da cewar Hoodah na mutuwa tou shima babu abinda zai hanasa ya bita. An fi minti talatin can wata Doctor ta fito duk ta hada xufa fuskarka dauke da damuwa, "Your wife's life is in danger your highness, don a halin yanzu ta kasa haihuwa da kanta kuma babu abinda takeyi sai kuka tace ka shigo ka tsaya gefenta, sannan maybe we have to save one of them ko uwar ko dan." Da wani irin expression yake kallon likitan, "What are you saying to me Doctor?" Ya fada yana goge idanunsa da hawaye ke zubo masu, suma kansu su Ashraf ko wane ya zama speechless hankalinsu tashe, gasu Ummi da isowarsu kenan suka tsaya cike da shock suna kallon doctorn, Doctor din ta sauke ajiyar zuciya, "Bance ko bazata haihu lafiya ba amma dai ina nufin rayuwarta na cikin hadari kudai tayata addu'a." Tana fadan haka ta kalli Sultan, "Wa kake da bukatar muyi saving the mother or the baby?" Kasa tsayuwa Sultan yayi nan ya fada kan kujerun da ke ajiye a nan Ashraf yayi saurin rike sa, sai ya fashe da kuka kamar karamin yaro, "Ya zakiyi min wannan tambayar doctor? You know I love my wife more than life itself, I also love my child wanda ban riga na gansa ba, but If I am to choose I will have to choose my wife over and over again, so yes Doctor save my wife first!" Ya fada cike da karfin hali kafin ya rungume Ummi yana cigaba da kuka, Zarah kasa daurewa tayi ta fita da sauri ta nufi bathroom ta dauro alwalla, ta tafi masallacin asibitin ta fara sallah tana rokon Allah yayi saving dukansu gaba daya. Nan Doctor din ta wuce ciki ta barsu cikin wani irin mawuyacin hali. Ummi ta dafa Sultan, "You did the right thing son Allah zai baku wani InshaAllah." Ya gyada kai cikin karfin hali yana goge hawaye. A hankali suke jiyo kukan jarirai har guda biyu a tare gaba dayansu suka sauke ajiyar zuciya cike da mamaki, Sultan zubewa kasa yayi yana ma Allah godiya daidai nan Zarah ta shigo da saurin jin sautin kukan babies na tashi, batasan sadda ta rungume Ummi ba tana hamdala. Bayan mintina kadan sai ga Doctor din ta sake fitowa fuskarta dauke da murmushi, "Congratulations your highness, it's twins! Matarka da yaranka suna nan cikin koshin lafiya!" Ay bata karasa magana ba Sultan ya mike da hanzari yayi hanyar dakin. Ita kuwa Ummi da Zarah kara rungume juna suke yi suna dariya kamar wasu kananan yara. Iyakar wahala tasha ta, hannunta ne taji a cikin nashi basai ta bude ido ba ta tabbatar da Sultan ne, nan ta bude idonta a hankali tana saukewa bisa fuskarsa wacce ta sauya kala tayi jajir sannan ga farin ciki nan saman fuskarsa, zama yayi gefenta yana kara kamo hannunta yana sauke mata kiss a hankali, Hoodah ta goge hawayen farin ciki ta mike zaune da kyar tana kallonsa, "Congratulations my king a boy and a girl..." ya kalleta yana juya kansa don neman babies din tayi murmushi, "An tafi dasu for general checkup." Ya gyada kai sannan yace, "Kin tuna alkawarinmu?" Ta gyada kai "And we both won!" Bata karasa magana ba ya hade lips dinsu wuri daya sun dade a haka kafin ya janye a hankali ta sadda kanta kasa, shigowa nurse din tayi hannunta dauke da jariran biyu ko wane an kimtsa shi tsab sai dan motsi sukeyi sunata baccinsu a natse, a hankali ya mike ya isa inda suke ya tsaya yana kallonsu kamar wani statue ya tsura masu idanu sosai idanunsa na kawo ruwa. Amsar su yayi take ya lumshe idanu yana jin son yaran na fizgarsa, kisses yake aika masu ko ta ina a fuska kafin ya taka inda Hoodah ke kwance ya zauna gefenta, duka su biyun ya daura mata bisa cinya sai a lokacin ta saki hawayen da take rikewa, shafa fuskarta yayi yana goge mata hawayen, yace "Banida bakin da zan gode maki kin bani kyauta ta musamman, Alhamdulillah na gode ma Allah da ya bani wannan gagarumar kyauta wanda ba kowa yake bamawa ba, yau da ace na rasa ki Hoodah de sai dai na biki nasan take zuciyata zata buga nima in mutu..." da sauri ta toshe masa baki da hannunta, rike hannun yayi ya rungume sannan ya mike ya fita ya kaiwa su Ummi yaran. Bai jima kwarai ba ya dawo ya zauna gefenta tare da rungume ta a jikinsa, "Ina fatan banyi katsalandan ba don inaso ki bani izini na maida sunan mahaifiyarki a macen..." da sauri ta kalle shi speechless toshe bakinta tayi kawai sai ji yayi ta makalkale shi tare da fashewa da wani irin kuka, "Thank you so much for this Sultan, Allah ya biya maka bukatunka na alkhairi." Wani irin kiss ya kai mata a goshi, "No need my queen you deserve the best..." a haka ta dora kanta bisa kirjinsa har bacci yayi awon gaba da ita, Sultan hannunsa ya dora bisa kan nata yana shafa gashinta a hankali yana lumshe idanu...
1 comment:
Nice write up dear, ALLAH yayi jagoranci, Amin amin
Post a Comment