YAR AGADEZ
{Page 41}
To read all my books click the link below👇🏻
Maryamsbello.blogspot.com
Matsowa yayi kusa da ita cike da tashin hankali yana jin kukanta na ratsa ko wace ga6a ta jikinsa, hannu yasa ya rikota, firgit ta mike tana share hawaye, idanunta sunyi jajir sun kumbura tsabar kukan da takeyi, "Don't touch me Ashraf am warning you for the last time! Daga yau kar ka sake tabani a cikin gidannan, bana son ganinka I hate you!" Tana gama fadan haka ta fara ja baya kamar wacce taga dodo, ji tayi kafafunta sun kasa daukarta ta durkusa a nan ta kifa kanta tana cigaba da kuka kamar ana zare mata rai, "Zarah tell me nayi maki? Da zan fita you're fine and happy lafiya lau muka rabu, ta yaya daga zuwa masallaci in dawo ki birkice man lokaci daya? What happened?" Bata bashi amsa ba sai ma sautin kukanta daya karu, ji yake kamar ana zuba masa ruwan zafi a cikin kirji tsabar yadda baya son sautin kukan da takeyi. Matsowa ya kara yi dab da ita duk da yadda yaga yanayinta ba da wasa take ba, sannan she sounds so hurt and angry, ba zato ba tsammani sai taji ya rungumota gam gam, da sauri ta dago da jajayen idanunta tana mashi wani irin kallo, ture shi tayi ta mike tsaye tana faman share hawaye ta isa inda paper din take ta durkusa ta dauko a fusace, tana zuwa inda yake tayi tsaye tana kallonsa na yan seconds kafin ta bude hannunsa ta sa masa paper dinnan, hawaye kuwa wani na korar wani, "Wannan takardar fa Zarah?" Wani kallo ta watso mashi "Open and read!" A hankali ya bude ta yana kallon Zarah kafin ya sauke idonsa kasa ya soma karantawa, shi kansa abin ya bashi mamaki dagowa yayi yana girgiza kansa idanunsa sun rikide zuwa ja, yace "Zarah a tunaninki nine na rubuta wannan paper din? Yanzu har akwai ranar da zaki fara doubting soyayyar da nake maki? Na dauka ko ganina kikayi ina rubuta ta kya karyata kice ay wasa kakeyi balantawa kawai ki ganta haka kawai kice ni na rubuta ta? Zarah all this while ya kamata kisan wanene ni kisan kalar soyayyar da nake maki, inda ace jikinki nakeso da tun a gidanku zan samu abinda nakeso, ko kin manta sadda su Mummy sukayi tafiya? A hannuna aka damka ku daga ni sai ku meyasa lokacin ban maida ki sex machine dina ba sai yanzu? Zarah the love I have for you is pure and clean I love you fisabilillahi, yanzu inda zaki bukace mu zauna haka nan ba tare dana kusance ki ba I can do it for you without any hesitation, Zarah why? How can you not trust me?" Lokaci daya taji zuciyarta ta karaya tana son karyatawa amma ta kasa, wata irin kara ta saki, "I wanted to believe you Ashraf, but ka fada man wanan hand writing din na waye? Of course naka ne!" Matsowa yayi kusa da ita ya kamo mata hannu kamar ya fashe mata da kuka yakeji, a fusace ta ture shi, "Ka fita daga cikin dakinnan Ashraf I don't want to see you! Ka fita nace!" Tsaye yayi cike da mamaki kafin ya sake magana tace "Ka fita Ashraf! Who gave you the right to touch me? Tunda bazaka fita ba ni xan fita in bar maka dakin Ashraf, dama ay dakinta ne you're trying to tell me is your room right?" Tana gama fadan ta share hawayenta tayi hanyar kofa, da sauri ya dakatar da ita, bai ce mata komai ba ya bita da wani irin kallo mai wuyar fassara sannan ya fita. Yana fita ta koma can gefen gado ta cigaba da kuka, kuka take kamar ana zare mata rai, pillow ta jawo ta dora kanta ta cigaba da kuka rabon da tayi irin wannan kukan tun rasuwar Daddynta yau shekara kusan takwas kenan da wani abu, kanta kuwa ji take kamar ana sara mata guduma, lumshe idanunta tayi kafin ta ankara bacci yayi awon gaba da ita.... Can cikin baccin ne taji alamun ana knocking kofa, firgita tayi ta tashi ta bude, binshi da kallo tayi zuciyarta na kuna tana tafarfasa wane garwashi, "Come and eat..." yana gama fadan haka ko second daya bai kara ba ya juya yayi gaba, ko amsa shi batayi ba ta nufi dakinta tayi wanka tayi alwalla don tayi mamaki ashe har biyu ta kusa, nan tayi sallarta ta zauna azkhar dinta, taki tashi tayi zaune a nan, itace a nan har akayi la'sar sai da tayi sallah nan taji wata irin makirar yunwa na addabarta, linke kayan sallar tayi ta adana su sannan ta fito, har yanzu idonta bai washe ba akwai dan kumburi sannan akwai jan daga gefe, tana fitowa ta ganshi zaune a parlor ga kulolin abinci nan kala kala bisa dining daga gani Abba ne yasa aka kawo masu, da alama bai ci abinci nan ba amma yadai ya zabga wani uban tagumi, da alama ma baisan ta shigo parlon ba saboda yadda taga ya zurfafa cikin tunani, ko kallon inda yake bata kara yiba ta nufi dining ta zauna ta jawo plate guda biyu ta zuba masu kowa da nashi, tana gama zubawa ta kai masa bisa center table din dake tsakiyar parlon ta koma ta dauki nata ta zuba drink sai yaga ta tashi zata shiga daki kuma, da sauri ya dakatar da ita, "Ki tsaya a nan kici abincin." Yana gama fadan haka ya jawo abincin shi yana kallo don shi kwatakwata baida appetite, Zarah ko kallon inda yake batayi ba ta yi hanyar fita daga parlon, "Fatimah ba nace ki zauna kici a nan ba? Meyasa bakijin maganata ne yau? Tou ki dawo ki zauna nine dai kika tsana bakyason gani ko? Tou xan tashi in bar maki parlon." Yana gama fadan haka ya mike tsaye saboda ransa har ya fara baci, anya wannan Fatimanshi ce kuwa? Wadda take kaunarsa? And can go to any length to show him just how much she cares? Wai amma yanzu kwatakwata bata son ganinshi, "No kayi zamanka." Ta fada murya kasa kasa, dan xuwa yanzu kuma wani irin tausayinsa takeji yana ratsata amma she can't help it ya riga ya bata mata rai da yawa, jin muryarta can kasa ba karamin sanyaya mashi rai yayi ba, komawa yayi ya zauna dafe da fuska itama a hankali ta juyo ta jawo wata kujerar dan nesa dashi ta fara cin abincinta, kafin ya ankare har ta kusa cinyewa shiko ko ta6a nashi baiyi ba yasa ta dago daga cin abincin da takeyi tana kare ma kyakkyawar fuskarshi kallo, "Kai baza kaci abincin ba?" Ta tambaya wadda ita kanta batasan daga ina tambayar ta fito ba, ba karamin mamaki maganarta ta bashi ba bai taba tunani ba dan a yadda take ikirirani ta tsane shi bata son ganinsa har zata sauko haka da sauri? Da kallon mamaki ya bita baki sake ita kuwa da sauri ta dauke kanta ta cigaba da cin abincinta, tana gamawa ta tattara plate dinta da cup din da tasha drink ta kai kitchen zata wanke. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya fara cin abincinsa a hankali, saida ya gama ya dauki plate din zai kai kitchen suka hadu ita kuma zata fito, ko kallonshi batayi ba tace "Kawo." Tana karba ta juya ba tare data bari sun hada idanu ba ta wuce kitchen din da sauri.
Washe gari bayan sun kammala breakfast Zarah ta hau gyaren gida, saida ta tsabtace ko ina don Ashraf yana parlor ashe a nan bacci ya sure shi, wuce shi tayi ta tafi dakinsa don nan kadai ne ya rage bata gyara ba, wardrobe dinsa ta bude zata saka masa jallabiyarsa data linke a ciki kawai wata babbar envelope ta fado kasa, abubuwan dake ciki duk suka fito wasu pictures ne dake ciki sun kai kala goma, bata kawo komai a ranta ba ta tattara su zata maida ashe akwai wani daya juyo saitinsa fuskar Ashraf ta gani kawai sai ta saki envelope din kasa tana kallon hotunan, Ashraf ne da wata da alamun ba musulma bace tasha jumpsuit shi kuma daga shi sai gajeren wando, kara kallon hotunan takeyi hannunta har wani kyarma yakeyi don so take tabbatar ko dai kama ce sukeyi don ita bata yarda Ashraf zai aikata haka ba, tafi minti goma tana kallon hotunan gaba daya she is in shock, sai a lokacin hawaye suka balle mata kuka take ba kakkautawa kafin a hankali ta juya ta fita daga dakin, daidai inda yake kwance ta tsaya kawai sai ta juye masa hotunan bisa jikinsa, farkawa yayi ya ganta tsaye kansa tana kukan fitar hankali hakan yasa ya mike bai ma tsaya lura da hotunan ba ya fara tambayarta lafiya? Kasa magana tayi saboda har yanzu she's still in shock, Ashraf ganin ta kasa magana sai ya dinga bin hotunan da kallo kafin a hankali ya durkusa ya fara tattara su, juyosu yayi yana binsu da kallo baki sake zufa ce ta fara keto masa ko ta ina, kallonta yakeyi yadda take kuka kamar ranta ne ake zarewa, "Zarah wallahi I don't know anything about this photos...." ya fada yana kokarin tabata, janye jikinta tayi da sauri tana masa wani irin mugun kallon tsana, "Karka kuskura ka tabani!" Tana fadan haka ta juya da gudu tayi dakinta, da sauri yabi bayanta yana kiranta amma ina har ta shige ta sa lock, Ashraf kansa ba karamin zafi yayi masa ba, zuciyarsa kuwa ji yake kamar zata hudu kirjinsa ta fito, "Who did this to me?" Ya tambayi kansa, nan ya dinga knocking yana magiyar ta bude masa amma shiru sai karar kukanta yakeji, sulalewa yayi a nan bakin kofar wasu zafafan hawaye suna surnano masa....
Zarah kan gado ta zube tana kuka kamar wacce ake zare ma rai, wai meyasa tunda sukayi aure sun kasa samun kwanciyar hankali? Meyake shirin faruwa dasu? Tunano yadda yake rungume wannan Christian din takeyi wacce da kayan data sa gara ma babu a jikinta, wani irin ihu ta kurma jikinta har wani kyarma yakeyi, "No it can't be my Ashraf, something must be wrong somewhere! Tou what if da gaske ne? Dama ance namiji ba dan goyo bane duk halinsu daya!" A firgice Ashraf ya mike wanda yake jikin kofar har yanzu ya shiga murda kofar yaji ta gam a rufe, wani irin gudu yayi ya isa dakinsa ya shiga bincika spare key, har wani kyarma yakeyi kar dai wani abun takeyi ma kanta? Da sauri ya bude dakin hannunsa na kyarma ya shiga ciki, yana shiga ya ganta zaune gefen gado zufa ta jike mata jagab a jiki sai hawaye ke kwarara daga jajayen idanunta jikinta na rawa, da sauri ya matsa kusa da ita ya kamo hannunta, hannun nasa ta bige da karfi, "Bana hanaka tabani ba? Karka sake zuwa inda nake na tsaneka Ashraf na tsani maza, dama ashe duk haka kuke mayaudara? I hate all men! Na sanya ka a cikin raina amma kaine zaka yaudareni Ashraf? Saidai abin mamaki na kasa tsanarka kamar yadda nake ikirari amma karka dauka cewa zaka iya dinga zuwa inda nake! Da gaske bana son ganin fuskarka." Tana gama fadan haka ta tura kanta cikin pillow ta fashe da wani irin kukan fitan rai wane ana yanka naman jikinta, Ashraf babu irin magiya da lallashin da bai mata ba amma taki koda kallonsa ne, ya rasa inda zai saka kansa gaba daya abun duniya ya ishe shi, "Zarah don Allah don annabi ki tsaya ki saurareni! At least tell me you trust me baki yarda da abunda kika gani ba, Zarah kisani hawayenki sune last abinda nake fatan gani, Zarah don Allah kiyi hakuri ki daina kukan nan kiyi man magana ke kinsan irin kaunar da nake maki fa, I admit nayi soyayya da cousin dina a baya amma yanzu ya zama past kece kawai nakeso you're the only woman I love bazan taba yaudararki ba, wipe your tears now and tell me do you trust me or not Zarah?" Sai a lokacin ta dago da rinannun idanunta tana mashi wani irin kallo, "Ashraf don Allah na roke ka ba dan ni ba ka fita daga cikin dakin nan! Wallahi ganinka wani irin bakin ciki da kunci yake kara mun!" Ta fada da muryarta data rine saboda kukan da takeyi tana share hawaye, yadda tayi masa da fuska ya tabbatar babu alamun wasa a tattare da ita, Ashraf zuru yayi yana binta da kallo maganganunta sun mashi ciwo matuka, "Yanzu Zarah yau nine bakya son gani? Nine silar kukanki? Ni ne ke saki cikin kunci da bakin ciki? Fuskata Zarah? You don't trust me ko?" Ya fada kamar zaiyi kuka wani irin tukukin bakin ciki ne ya taso masa, Zarah wani irin harara ta watsa masa, "Kaga malam wallahi idan idan bazaka fita ba ni zan fitan maka daga cikin dakin nan, ka tashi ka fita don Allah." Tana gama fadan haka tawani tashi tsaye, yana ganin haka ya mike da sauri ya fita daga dakin, binsa tayi da kallo kafin ta koma ta zauna ta cigaba da aikin kukanta, har cikin ranta bata son yi masa haka amma idanunta sun riga sun rufe da kishi ta kasa controlling kanta. Tana nan zaune ta gaji da kukan tayi shiru babu abinda takeyi sai tunani, can taji an murda kofa an shigo tabi shi da kallo a sanyaye ganin yadda ya koma gaba daya yayi kalar tausayi sannan kana ganin yadda ya shiga damuwa, damuwar ta bayyana akan fuskarsa daga bakin kofar ya tsaya rike da handle yace mata "Lokacin sallah yayi ki tashi kiyi sallah." Yana gama fadan haka ya juya ya fita ya kullo mata kofar, mikewa tayi ta shiga bathroom bayan ta kammala ta fito tayi sallah. Bayan ta gama azkhar dinta da kyar ta mike ta karasa kan gado, wani irin bacci takeji aikuwa tana kwanciya ba'a dau Lokaci ba bacci yayi awon gaba da ita. Shigowa yayi don ya tadata taci abincin rana ya iske tana bacci, murmushi yayi ya karasa kusa da ita ya zauna gefenta a hankali yana gyara mata gashinta daya rufe mata fuska, kallonta yakeyi sonta na ratsa ko wane sassa na jikinsa, a hankali yayi mata kiss a kumatu marar kara ko kadan gudun kar ya tasheta daga bacci, drawer ya bude ya zaro wata jotter da pen ya rubuta mata note, gefen pillow dinta ya aje mata ya dora mata wayarta bisa, kallonta ya kara yi sannan ya juya ya fita a hankali.
Karfe hudu saura ta farka salati tayi hade da mika sannan ta mike zaune, hannu tasa zata dauko wayarta don ta duba lokaci kawai zai ganin littafi tayi aje, daukowa tayi ta bude ta fara karantawa, "Hello princess, ina wuni rankiya dade? Hope kin gama baccin lafiya? Abincinki yana kan dining, make sure kinci da yawa fa, zan fita ne amma bazan dade ba InshaAllah, do you need anything? If yes just call me or you can text me okay princess? Take care of yourself for me plus I love you so much, also forgive hubby okay? Later...." Murmushin da bata san ya fito mata ba ne ya su6uce mata, wani sabon sonsa ne taji yana taso mata, saidai data tuna mey yayi mata sai taji haushi kuma. Ruwa ta shiga ta watsa sannan tayi alwalla, wata red atamfa ta dauko dinkin gown rigar tasha stones tayi kyau sosai, tana gama kimtsayawa tayi sallar la'asar tana gamawa taje taci abinci, rice and stew ce da hadaden salad, sai kaza gasashiya, sai pepper soup din yan ciki. Tana gamawa sai ta fara zagaya gidan dama bata tsaya tawani kalli yadda yake ba, katon flat ne wanda ko wanensu yana da dakinsa da palornshi, corridor ce ta raba masu parlonsu, sai kitchen da dining area wanda duka gidan royal furnitures ne dakakku na gani na fada, gidan gaba daya yaji kayan alatu very simple yet classic and elegance. Gyalenta ta dauko ta fita ta gaida Abba ta dade a can wanda yaji dadin zuwanta, bayan sun gama fira ne sai ta tashi ta dawo sashensu wanda akwai tazara sosai, gida ne katoto ko wane da gate dinshi, mantawa ma xakayi gidan a hade yake. Tana zaune tana kallo can daddare wurin karfe takwas taji ana ta knocking, tashi tayi taje ta bude Ashraf tagani tsaye rike da basket din abinci, kallonta ya tsaya yi yadda duk ta kode idanunta sun shige tsabar kuka, ba tare data ce masa komai ba ta karbi basket din dake hannunsa da alama abinci ya anso cikin gida ta wuce dining ta aje, ya kasa mata magana yana tsoron maganar da zata fito a bakinta sheyasa ma baice mata komai ba. Dakinsa ya shiga ba'a jima ba ya fito da singlet da boxers zama yayi a kujerun parlon, tana ganin ya xauna ta mike taje ta zuba abincin, binta yake da kallo yadda take zubawa a natse kuma a cikin damuwa, tana gama zubawa taje ta aje gabanshi sannan ta nufi fridge ta dauko drink da cup ta dire a gabansa, sannan ta koma kan doguwar kujera ta kwanta ta cigaba da kallo, ko kallon Inda yake batayi ba. Sun kai minti goma a haka Zarah nata kallonta shi kuwa Ashraf abun duniya duk ya ishe shi, can ta juyo ta kalleshi ta kalli abinci taga ko taba shi baiyi ba, "Ashraf ya naga har yanzu baka fara cin abincin ba? Ko wani abun za'a dafa maka?" Ta fada cikin damuwa don bata son yadda ta ganshi duk ya zabge yayi wani iri, kallonta ya karayi kafin ya girgiza kai alamun a'ah, qular da ita yayi, "Wai bazaka iya magana bane? Kake ta faman amsa min da kai?" Shiru ya karayi sai can kamar bazaiyi magana ba yace, "Na koshi..." sannan ya mike ko kallonta baiyi ba ya tafi part dinshi ya kullo kofar. Zarah ta bishi da kallon mamaki, ko shima fushin yakeyi? Sai kuma abun ya fara damunta kuma. A bangaren Ashraf kuwa yayi hakan ne ba don komai ba sai kila idan ya nuna mata ransa ya baci kila ta daina masa haka ta sauko ta bashi hakuri. Sai wurin 9 ta tashi taje tayi dinner dinta, tana gama tattara wurin ta kashe tv da fitilu ko kallon part dinshi batayi ba ta nufi nata part dinta.
--------
ONE MONTH LATER....
Yau an kai kimanin wata daya kenan da bikinsu Zarah, suna nan babu abinda ya chanza fadan yau daban na gobe daban, zuwa yanzu ya sa mata ido tunda shi dai yasan he's innocent, itace keta haukanta da fadanta ita kadai.
Yau ta kama Wednesday Zarah na cikin bacci wurin karfe uku da kusan rabi taji mararta ta murda, a gigice ta farka dama indai zatayi period first 2 days sai tayi ciwon ciki wani lokaci har drip ake sa mata har suma takeyi, tashi tayi zaune sai taji ya karu sai ta kwanta nan ma taji ba sauki abun ya faskara, jagab ta jike da zufa tsabar wahala, wajen karfe 4 taji ciwon ya fara cin karfinta wani irin azaba taji wanda batasan lokacin data fasa wani irin gigitaccen ihu ba, a tsorace Ashraf ya dakatar abinda yakeyi a kitchen, wani ihun ya sake ji a frigice ya bude tap yana wanke hannunsa don ya baci da flour kafin ya karasa wanke hannun nasa ya sake jin wani ihun wanda yafi na dazu, a frigice ya ruga a guje gabanshi na faduwa ya shiga dakinta, in shock ya tsaya ganin yadda take mirgina a tsakiyar dakinta dafe da ciki, da gudu ya karasa inda take ya tsugunna yana faman tallabo ta, "Zarah!" Kafin ta ankara taji ya kamo hannunta zai mikar da ita tsaye, da sauri ta fizge hannunta, "leave me alone!" Ta fada cikin azabar ciwo, shi kuwa Ashraf kara damke hannunta yayi, a yadda yaga yanayinta yasan ba karamin ciwo takeji ba, ya kara kokarin kama hannun nata yana mikar da ita tsaye for the second time ta sake fizge hannunta, "Ashraf ka kyaleni nace mana! Wai bance karka sake tabani ba? Why are you so stubborn?" Ta fada cike da azabar tsiwa gamida dukewa tana cize lebe, "Wai Fatimah meye haka? Ta yaya xakice na rabu dake a cikin wannan halin? Wai bakida hankali ne? Ni mijinki ne don haka duty dina ne na kula dake whether you like it or not kina jina ko?" Ya fada tare da jawo hannunta ya kaita kan gado, "Look Mr Ashraf! The mr perfect husband! Babu abinda xaka iya mani zai tafi da kansa, well is just ciwon mara and for your information inada hankali na....!" Ta fada cike da tsiwa tana murguda baki, ji take kamar ta kama shi ta rufe shi da duka dama ga ciwo ya isheta, zaiyi magana ta fasa kara ta fara mirgina kan gadon yayi saurin kamota, "Don Allah ka rabu dani mana! Na fada maka babu abinda zaka iya yi mani ay sai ka fita ko?" Da kyar take maganar amma saboda shegen taurin kai sai masifa take mashi, "Zan iya maki wani abu, am your savior so do as I say...." yana fadar haka ya janyo ta wuri daya, kokarin fizgewa tayi shi kuwa yana kara damkota, "Kinga ki tsaya wuri daya, kar na sake naga kin motsa koda da inch daya ne, now sa hannunki ki ringa massaging marar, ki cigaba yanzu xan dawo..." ya fara tare da mikewa tsaye, a fusace ta dago kanta tana balla mashi harara, "Bazaka zo cikin rana daya ka fada mun abinda zanyi ba, I have been experiencing this pain shekara da shekaru kawai sai yanzu rana daya kace man ga abinda xanyi? Tou I will not do it ka fice man da gani mayaudari kawai!" Wani sabon ihu ta kurma saboda ko magana tayi sai taji kamar ana tsirarta,
Da Sultan yayi magana sai Zarah ta fasa kara, da sauri yayi kanta "Don't touch me!" Ta fada muryarta na kasa kasa kafin a hankali idanuwanta su rufe ruf jikinta ya saki.... ganin bata motsi ba karamin firgita Ashraf yayi ba, jijjigata yakeyi yana kiran sunanta, ganin dai da gaske bata motsi yasa ya juya ya fita a gigice har yana yin tuntube....
No comments:
Post a Comment