Saturday, 31 July 2021

YAR AGADEZ PAGE 39

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 39}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com




-----

A hankali ta shiga bakinta dauke da sallama tsaye tayi bakin kofa dauke da tray din hannunta ganin yana faman hada kayansa cikin akwatinshi, wata yar faduwar gaba taji wai gobe fa zai tafi? Ji take kamar in ya tafi sai ya shekara bai dawo ba, dagowa yayi yana kallonta da mamaki yace "Zarah?  Me kikeyi a bakin kofa? Ki shigo mana." A sanyaye ta shigo ta aje mood dinta duk ya chanza ganinta haka yasa shima mood din nasa ya chanza a take, "Abinci na kawo maka, na kula kwana biyu ka saba zama da yunwa ko Ashraf?" Zama yayi ya jawo tray din ya bude warmers din, murmushi yayi ganin favorite dinsa ne ta kawo masa amma yau dinnan bai jin zai iya cin abincin, don kwata kwata baida appetite, cin abincin yake ba don yaso ba don shima kewarta ce ke dawainiya dashi, "Goben karfe nawa zaka wuce?" Ya hadiye abincin dake bakinsa yana dubanta yace "Wallahi flight din safe ne na karfe tara," wani abu taji kamar ta rusa ihu can dai tayi karfin halin cewa, "Tou yanzu in ka tafi sai yaushe kuma?" Shiru yayi kamar mai tunani yace "Ay bazan dade ba, da naje zanwa Abba maganar aurenmu, duk da nasan sai anyi gwagwarmaya da matarsa kila ma tasan makircin da tayi ya hana ni yin auren." Ya fadi cike da damuwa, itama da damuwa a fusakanta don kuwa ta san labarin Umma kaf ya fada mata babu abinda ya boye mata, tace "Ay Allah yafita inshaAllah, besides bamu fatan ace har yanzu tana gidansa ma ya kamata ace Abba ya gano halinta yayi waje out da makirar." Yayi murmushi "Allah yasa haka da sai nafi kowa murna, don yadda na tsani matarnan kamar na kasheta nakeji." Tace "Kar kace haka, inshaAllah ma basu tare kaga shikenan bakada sauran wata damuwa," yace "InshaAllah zanso inga irin tarbar da Abba zaiyi mun," ya fada kwalla na cika masa idanu, tayi karfin halin kawar da zancen, "Bari na tayaka packing din." Ta fadi tana mikewa ta nufi wurin kayansa tana packing din cike da nutsuwa, a haka ya tuttura abincin don kar tace ay ta kawo masa abinci amma bai ci ba. Yinin ranar a tare suka wuni jone, gaba daya ba karamin missing din juna zasuyi ba. Da ka kalli Zarah kasan gaba daya cikin damuwa take, shima ne yake dan kwantar mata hankali akan cewa fa ay sun kusa mallakar juna saura kadan ya rage InshaAllah, hakan ne ma yasa ta dan saki ranta har ma tana dan walwala kadan. A bangaren Khadija kuwa tafi shiga tashin hankali sai dai ko kadan bata bari ba ta nuna komai ba, har ma ita ke consoling Zarah tana bata baki.

Washe gari yana gama sallar asuba ya fara shirin tafiya, ya fito wanka yana faman tsane jikinsa gaban mirror Yasir dake kwance bisa gado ya farka daga bacci kenan yana kallon aminin nasa yace "Zadai ka tafi ka barmu da kewa Ashraf, kasan ance ba mutuwa ake ma kuka ba sabo ake ma kuka, zamuyi missing dinka abokina." Ashraf yayi dan murmushi yana jin wani iri a cikin ransa ya juyo sannan yace "Wannan haka yake, am going to miss you too." Daga haka ya cigaba da shiryawa, wata shadda dark blue ya saka da matching hula sai kyalli takeyi, yayi mugun kyau tsab ya kimtsa ya kara gyara akwatinsa ya kai parlor, yana kallon Yasir yana duba time yace "Karfe takwas da minti sha biyar kana ganin zaka iya kaini airport yanzu?" Yasir yace "Eh amma ka bari kayi breakfast mana sai muje ko nasan yanzu mutuniyar taka zata kawo maka ay." Yayi murmushi don yasan gaskiya ya fada amma bai jin zai iya cin abincin saidai kawai ya hada tea yasha. Aikuwa sai ga yar halak din da sallama ta shigo dauke da katon tray, kanta na kasa ta gaida Yasir da Ashraf sannan ta aje tray din, dagowa tayi suka hada ido ta sauke kanta da sauri tana murmushi, mayar mata yayi ya sauko kasa yana fadin, "Ay da baki wahalar da kanki ba Zarah, saboda tea kawai nakeso insha kafin na tafi." Yasir ya juyo yana fadin "Nidai daka daure kaci abincinnan Ashraf, traveling with an empty stomach is not right." Ashraf yace "Ay nace zansha tea, ya isheni fa." Yasir yace "Okay tou ni ka bar min su na cinye." Zarah ta mike jikinta babu kwari ta fita daga dakin gaba daya she's not herself, bata taba tunanin zata ji wannan feeling din ba sai yau. Da kyar Ashraf ya tura tea dinnan yana faman tunano yadda yaga mood na Zarah take shima sai ya dinga jin ba dadi cikin ransa, rabin cup kawai yasha ya mike ya cire charger dinsa a jikin socket, ya dauki wayarsa ya kalli Yasir "Tou nidai zan wuce Yasir." Yasir ya mike ya zura jallabiya ya dauki key din motarsa suka fito daga dakin bayan ya rufe da key. Yasir ke ja masa akwatin har bakin kofar main entrance ya barshi a nan sannan suka sa kai ciki, parlon babu kowa hakan yasa Yasir yace bari ya kira Mummy din a daki, bai dade sosai ba ya sauko shi da Mummy, Khadija da Zarah suna binta a baya, zama tayi a gefensa tana murmushi tace "Wai tafiyar ta taho haka?" Ya sunkuyar da kansa kasa ya zauna yace "Eh wallahi Mummy yanzu zan wuce ma." Tace "Ikon Allah, tou Allah ya tsare hanya Ashraf ya kai ka lafiya." Yace "Ameen Mummy, nima na gode sosai da dawainiyar da kukayi dani Allah ya saka da alkhairi." Tace "Haba babu komai Allah yayi maka albarka." Ya amsa da amin sannan ya mike duk su Zarah suka mike suma fir taki yarda su hada idanu don kiris ya rage ta fashe da kuka kuma bata so haka ta faru. Har bakin mota suka raka shi Yasir ya sa masa akwatinsa a booth, yayi ma su Zarah bakwana su Khadija ma duk sukayi masa Allah ya tsare kafin Yasir yaja motar ya fita daga gate. Har airport ya kaisa saida ya tabbatar ya shige sun fara boarding sannan ya juyo cike da kewa ya dawo gida.

-----

Gab da masauratar agadez taki kadan ya tsaya yana kare ma gidan kallo, yana murmushi yana tuna abubuwan da suka faru shekarun baya, komai yana dawo masa fresh da kalar rayuwar da yayi, nan Hoodah ta fado masa a rai saida yaji wani iri take yayi saurin kawar da tunanin daga ransa, yafi miti sha biyar tsaye ya zurfafa cikin tunani kafin ya dawo hayyacinsa da yaji guards na faman gaishe shi ko wane na kallonsa cike da mamaki da kuma farin ciki, don shi sam baima san ya iso gate ba saida yaji muryoyinsu tukunna yayi firgit, "Allah ja zamanin Yariman agadez! Allah ya kara maka tsawancin rai, barka da isowa dan sarki jikan sarki takawarka lafiya yarima! An gaishe ka yarima!" Suka fada cike da murna suna kawo masa gaisuwa, karbar masa kayansa sukayi da sauri suka wuce ciki dashi, baisan lokacin da yayi murmushi ba idanunsa cike da kwalla ya wuce ciki gabansa na dukan uku uku, "Assalamu Alaikum." Abba na zaune a fada ya juyo a firgice gamida mikewa tsaye, Idanunsa ya kwalalo waje tare da bakinsa ya bude yana kallonsa cike da mamaki, "Ashraf!" Ya furta cikin tsananin farin ciki da mamaki sannan ya fara takowa kamar mai counting steps ya iso daf dashi tare da damko masa kafadu da duka hannayensa, kallonsa yakeyi from head to toe kafin ya janye hannunsa ya fara taba masa fuska, "Ashraf kaine? Ashraf ina ka tafi ka barni lokacin da nake bukatarka a kusa dani? Ashraf ina ka shige tsawon lokacin nan ba tare da kako waiwayi gida ba, baka nemeni ba ko sau daya, bansani ba ko kana raye ko baka raye Ashraf." Ya fada baisan hawayen na zurara daga idanunsa ba, "Ka yafe man Ashraf abubuwan da nayi maka, ba laifina bane." Ya fada yana mai hugging dinsa gam gam take Ashraf yayi hugging dinsa back yana fadin, "Dole ce tasa na tafi Abba, ina ji ina gani aka rabani da Hoodah duk da kunsan irin kaunar da nake mata, how do you expect me to stay and witness her wedding? Kuma ni Abba ka daina bani hakuri abinda ya riga da wuce tun tuni wallahi ni ban kullace ba, you are like a father to me, ya za'ayi d'a ya kullaci mahaifinsa?" Ya fada yana janyewa daga hug din, Abba kuka yake bana wasa ba, kukan farin ciki, takaici hade da dana sani marar adadi, da sauri Sultan ya shiga goge masa hawayensa yana fadin "Ka daina kuka Abba, ba gashi na dawo ba?" Abba yayi murmushi sosai ya kamo hannunsa yana fadin, "Muje kaga Kaka tana can kwance tsufa ya kawo kai bata ma jin dadi sosai." Da sauri Ashraf yace "Kaka batada lafiya?" Abba yace "Kasan jikin tsufa yau da dadi gobe babu, amma dai muje ka ganta yau jikin da sauki ay." Ya fada suka ficewa daga fada. Saida Ashraf ya natsu yaci abinci, yayi wanka yayi sallah ya huta sannan suka kebe shiga Abba cikin parlor suna zaune Abba yace, "Ashraf ina ka tafi tsawon wannan lokacin baka dawo ba?" Ashraf yayi murmushi "Abba ina gidansu abokina Yasir wannan dan makarantar mu dinnan?" Abba ya ware idanu "Dama wai can ka tafi? kaji rashin sani kuma ni kwatakwata ban kawo ma raina ba." Ashraf yace "Abba ay banida aboki sama da shi, nasan xai karbeni hannu biyu biyu sheyasa ma na tafi can, kuma alhamdulillah sun bani kyakkywar kulawa." Abba yace "Alhamdulillah, ay da yake mutanen kirki ne." Ashraf ya gyara zama "Abba ina Umma?" Abba ya numfasa "Na rabu da ita Ashraf." Ashraf da wani tsantsan farin ciki and also shocked yace "Ka rabu da ita? alhamdulillah finally it has happened, na dade ina jiran wannan ranar Abba, alhamdulillah." Abba yace "Am sorry Ashraf bansan da wace kalar mace nake tare ba sai ranar da Allah ya kamata na gane komai, and that's when it hit me, na gano gaskiya da kuma halinta gaba daya, nayi da nasanin haduwata da ita, ta rabani da kowa nawa, ta rabani da matata, ta rabani da kai, ta rabani da yata, da yake banida hakki a kanta tana can asibiti rai a hannun Allah," Ashraf a sanyaye yace "Umma ay she's evil and heartless, bakomai Abba dama komai na duniya mukaddari ne haka Allah ya kaddara," sai kuma yayi shiru na yan seconds kafin yace "Abba Hoodah fa? How is she? How did she take the news that Umma killed her mother?" Abba ya numfasa "She's fine Ashraf, naje ay har Niamey nayi magana da ita, I apologize for my actions, kuma ta fahimceni amma abinda yafi bani mamaki shine Hoodah knew all along Umma ce ta kashe mahaifiyarta bata fada wa kowa ba, tace Umma ce ta mata gargadi mai tsoratarwa akan idan ta sake ta fada sai ta kasheni nida kai da kaka kamar yadda ta kashe mamanta haka zata kashe mu muma, I was so heartbroken that my own daughter endured all this pain alone." Ya numfasa "Anyways, wannan duk ya zama past InshaAllah..." Ashraf ya share hawayensa yace "Allah sarki Hoodah she endured alot, how is she now Abba?" Ya kuma tambaya out of curiosity gaba daya ya kasa hana kansa yiwa Abba wannan tambayar, Abba yayi murmushi "She's fine Ashraf, she's now a queen and soon to be mother InshaAllah." Da sauri ya kalli Abba "Mahaifin Sultan ya rasu ne?" Abba yayi murmushi "A'a, alot has happened Ashraf, he was sick I mean shida matarsa they were both attacked and almost killed, amma Allah cikin ikonsa sun dawo suna samun sauki, he just decided to step down ya bar ma dansa," Ashraf yace "Ikon Allah, su waye sukayi attacking dinsa?" Abba ya numfasa "His own blood Ashraf." Ashraf yayi salati "Wai me duniyar nan ta zama ne? Ace jininka shine yake son ganin bayanka, Allah shi kyauta." Abba yace "Ameen, so ya mutanen gida?" Ashraf yayi murmushi "Lafiya lau Abba, yanzu ma wani dalili ne ya dawo dani." Abba yace "Dama ba dawowa kayi ba kenan? Dalili ya kawo ka?" Ashraf yayi murmushi "Dawowa nayi Abba, amma kuma akwai wata magana kuma." Abba yace "Maganar mey?" Ashraf yace "Maganar aurena...." abba ya juyo da mamaki saman fusakansa da farin ciki kuma "Aure Ashraf? Who is the lucky girl?" Ashraf ya sadda kansa kasa "Abba sunanta Zarah, kanwar Yasir ce a can gidansu muka hadu, mun fahimci juna dama shine nazo maganar aurenmu." Farin cikin da Abba ya shiga ma bata baki ne, nan ya jawoshi ya rungume cike da murna "Alhamdulillah, me ake jira a fara shirye shirye? Kuma yaushe ya kamata a tura? Sai maganar lefe ya kamata azo a fara hadawa! Ya kamata na kira Hoodah a sanar mata ka dawo alhamdulillah alhamdulillah Allah yasa albarka!" Da murmushi shimfide saman fuskansa yace "Ameen thank you Abba."

-----

Khadija ce a dakin Mummy lokacin Mummy din na kasa ta sanya ta gyaren daki da wankin bathroom, bathroom din ta fara wankewa, sai ta fara tattara wasu hijabs na Mummy zata sanya mata a wardrobe, tou ita kuma tana budewa by mistake sai wani katon album da wani diary suka biyota suka watse kasa, dukawa tayi ta fara tattarawa kawai sai ta dauko wani picture tsohon hoto ne na wata mata rike da baby, sai kuma ta dauko wani hoton na same matar nan da Mummy kamar su daya kamar an tsaga kara an karya, sai ta dinga bin hotunan da kallo tana kuma dauko wasu a razane take ta dinga ganin hotunan matar nan da Mummy yawanci kamar ranar suna ne, matar na dauke da baby wanda Khadija ta fahimci kamar itace a hoton, tou amma me takeyi hannun matar kuma ya tagansu tare da Mummy? Diary din ta dauko dake yashe kasa ta fara budewa a razane ta mike tsaye tana karanta shi hawayen na sauko mata, hoton take bi da kallo kasa tsayuwa tayi ta zube bisa gado tare da fashewa da wani irin kuka, Kuka take kamar ranta zai fita kafin ta mike a fusace ta sauka kasa, Mummy na kitchen tana hada drinks tana sawa a fridge kawai sai ganin Khadija tayi rike da secret diary dinta da kuma album din da take boyewa shekara da shekaru, shocked Mummy ta zama ta nufi inda Khadija ke tsaye tana kokarin tabata, ja baya tayi da sauri tana cigaba da kuka kafin tace "Karki tabani! So dama all this while you are hiding this away from me? Mummy why?!" Mummy ta fara kuka tace "Calm down Khadija I can explain...." kuka Khadija ta fashe da shi tare da fasa wata irin razananniyar kara ta zube kasa, itama Mummy binta kasan tayi cikin karaji ta dafata, "Mummy ashe bake kika haifeni ba? And on top of that ni ba yar sunna bace? Am your niece? How is that all positive?" Mummy ta dafata wata uwar kara ta fasa tana mikewa tsaye da sauri, "Nace karki tabani Mummy you betrayed me!" Mummy ta girgiza kai "Ba haka bane Khadija, kema kinsan I have loved you more than my own children, na kula dake fiye da yadda na kula da yayan cikina, na fifita ki daban da yadda na fifita na cikina, I took special care of you, and I make sure na baki soyayyar uwa da kika rasa shekarun baya da suka shude!" Ta fada tana goge hawayen idonta, "Ni da Nafisah mun kasance tagwaye, haka muka tashi ba iskanci tayi ta sameki ba fyade akayi mata, ta rasu bayan sunanki da kwana takwas, nikuma sai na dauke ki na cigaba da baki kulawa," karar fashewar abu sukaji dukkansu suka juya suna kallon Zarah data zubar da glass cup din dake hannunta da tray, Hawaye take zubarwa kamar da bakin kwarya tana kallon Khadija da wani irin shock, "Khadija ba yar sunna bace?" Ta tambaya tana bin Mummy da kallon mamaki, a fusace Khadija ta juyo tana kallon Mummy! "This woman here betrayed me! Ta boye man gaskiya sai dana gano da kaina and now she's trying to explain things to me! I don't wanna hear anything I feel betrayed!" Ta fada tana ja baya kafin tayi sama da gudu tana kuka, Zarah ta juya zata bi bayanta Mummy ta tsaida ta "Let her be for now Zarah, bazata saurareki ba, I didn't betrayed her i am just waiting for the right time to tell her, she's my daughter too she's just angry for now but she will understand am sure, Ina sonta kamar yadda nakesonku, the reason I hide it from her is because she's too young to know her status, it's gonna ruin her entire life, she will be distracted and not to focus on anything...." hugging dinta Zarah "It's fine Mummy please stop crying, na maki alkawari xan dawo maki da yarki kamar yadda kuke da, kawai she's angry and heartbroken now, but I will fix everything inshaAllah, stop crying." Ta fada tana goge mata hawayen fuskanta....

-------

Tunda abinnan ya faru Khadija ta kulle kanta cikin daki babu abinda takeyi sai aikin kuka, kuka take razga kamar ranta xai bar jikinta, Mummy sun buga kofa sunyi magiyar, sunyi roko, sunyi lallashin amma duk a banxa, har dai Yasir babu irin magiyar da bai mata ba amma duk a banza kuma tana jinsu sarai, har spare key suka dauko amma unlucky for them ta bar key ta jikin kofar sun kasa budewa, Mummy da hankalinta ya fara tashi tace tou ko a balle kofar aga ko kalau take, jin haka yasa Khadija ta fara magana cikin dakusashiyar muryarta "Kada wanda ya balla man kofa, nace maku bazan fito ba dole ne wai? Am no longer part of your family so please leave me alone I beg all of you!" Mummy ta dafa kofar ta dora kanta bisa tana kuka tace "Ki daina cewa haka Khadija, you are my niece so kar ki sake cewa you are no longer part of our family! Khadija abinda yasa na boye maki saboda banaso ki shiga damuwa Khadija! I want you to be happy and live a normal life Khadija, Khadija you are my daughter and I love you as well, kiyi hakuri idan boye maki da nayi yayi hurting dinki it was never my intention, inda nasan haka zakiyi feeling da ban boye maki ba Khadija da tun tuni zan fada maki, amma kiyi hakuri kuma yanzu da kikasani I don't want you to feel left out mu cigaba da rayuwa kamar da! Don Allah ki bude man kofar nan yata, indai har kin daukeni a matsayin mahaifiyarki kizo kibude man kofar nan Khadija...." shiru Mummy tayi kirjinta na dukan tara tara ba zato kawai sai ji sukayi ta murda key a hankali ta bude kofar, tsaye tayi fuskar nan duk ta kumbura taci kukanta ta koshi, a hankali Mummy tayi hugging dinta tare da fashewa da wani irin kuka itama haka Khadija, "Mummy am sorry kiyi hakuri da munanan kalaman da na fada maki I didn't mean any of them, I know bake kika haifeni ba but the love I have for you is strong, I still love you Mummy!" Kara hugging dinta Mummy tayi "It's okay my daughter, komai ya wuce kinji ko?" Ta gyada kai nan tayi hugging Yasir da Zarah sannan ta juyo tana kallon Mummy, "Mummy alfarma daya nake nema a wurinki..." da murmushi fuskar mummy tace "Anything sweetheart?" Khadija tace "Inason in karasa karatuna a nan I don't want to go back to Uk anymore please Mummy." Mummy ta gyada mata kai tana gyara mata gashin kanta "It's okay, I will see what I can do okay? Muje kiyi wanka kizo kici abinci." Hannunta Mummy ta kamo suka shiga ciki tare...

********

Haka rayuwar ta cigaba da gudana, wanda aka fara harkar shirye shiryen biki babu kama hannun yaro, Abba ya tura anje sa biki don gaba daya akayi da gaisuwa da sa biki, inda aka saka bikin sati biyu kacal masu zuwa, nan kuwa Ashraf babu abinda yake hadawa sai lefe sai kuma gyaran gida akeyi bangaren da zasu zauna shida amaryarsa, su Hoodah ma nan da sati daya zasu iso, shi Sultan shida Abbi sai ranar daurin aure zasu zo. Daga Nigeria Mummy tayi hiring wata mata a maiduguri ta fara gyara mata yarta, dilka, halawa da tauren wutan jiki ake mata ba kama hannun yaro, tunda kurarren lokaci ne na kwana goma kacal ake mata, siyayya kuwa mummy take ta mata na kayan gida da decoration da sauransu don har ta kammala na kitchen kaf, saboda nisa so take sai an kusa bikin a fidda rana daya aje ayi jere. Khadija ita kadai tasan bakin cikin da take ciki amma ta dake baka taba gane komai da ita ake shirye shiryen biki ba kama hannun yaro. 

------

BUDAN KAI! 

Mutane an taru kowa kagani yasha kyau ba kadan ba, kawayen Zarah anko suka sha, hall din ya sha decoration amarya Zarah basu iso ba itada kawayenta amma mutanen yawancin sun iso, wakar kujerar tsakar gida ke tashi ga wurin sai kyalli yakeyi yasha kyau ga fitilu sai walwal sukeyi, ba'a dau lokaci ba Zarah ta iso itada kawayenta da ango da abokansa, nan mc yace kowa ya zauna amarya ta iso nan da nan mai hoto da video suka zama ready, wata wakar larabawa akasa mai shegen dadi a hankali aka fiddo Zarah daga cikin motar woooo tayi bala'in kyau tasha white bridal gown komai in white tayi amma gaba daya fuskarta a rufe take, bayan sun jera in line Khadija ce a gaba sai Zarah tsakiya sai kawayenta suka jera a baya nan aka kara sautin wakar masu hoto na gaba, suna daukarta nan suka fara shigowa ciki har suka rakata inda zata zauna wurin yasha decoration, bayan ta zauna nan mai video da hotunan sukayi nasu aikin har finally mc ya kira wata ta bude taron da addu'a, nan kuma aka fara shagulgulan biki ba hannun yaro. Khadija ce wayarta ta fara ringing can ta fita waje tana waige waige alamun marar gaskiya, saida tayi nisa inda babu kowa a wurin sannan ta daga wayar ta kai kunne ta fara magana a hankali, "Inata kiran number ka bata shiga Fahad, wani taimako nake nema da gaggawa!" Yace "You are my best friend remember in school? So ko meye just ki fada man kai tsaye zan maki inshaAllah." Kwantar da murya tayi tace "I want you to kidnap my sister!"

Wednesday, 28 July 2021

YAR AGADEZ PAGE 38

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 38}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com




----

Nada masa rawaninsa takeyi cike da gwaninta bayan ta gama tana murmushi tace "Here you go my king." Mirror ya kalla yana wani murmushi ya juyo yana kallonta cike da kauna sannan ya zagayo da hannayensa duka biyun yayi wrapping waist dinta yana kallon fuskarta, kokarin kwace kanta takeyi tana murmushi ya kara matse ta yana fadin, "Ina zakije? Stay here with me my queen." Ya fada cikin kunnenta alamun rada rada hakan yasa tayi dariya sonsa na kara ruruwa a cikin ranta. An kai kimanin sati biyu yanzu da yin nadin sarauta kuma Alhamdulillah abubuwa suna tafiya smoothly, ya fara fahimtar yadda al'amurran suke wakana da taimakon Abbi kuma yana ganewa sosai, mutane na jin dadin mulkinsa Hoodah is supportive tana kuma bashi kwarin gwiwa dari bisa dari sannan tana sashi a hanya idan taga ya kauce itama koba komai tanada experience tunda Abbanta sarki ne. Bata taba complain ba idan ya zama busy da yawa tana masa uzuri, bata complain tunda yanzu rayuwar ta chanza ba kamar da ba privacy dinsu ya rage sosai, tana girmama iyayensa da mutanensa wanda hakan ba karamin dadi yake masa ba. Kullum dada kara jin dadin zama da ita yakeyi, banda riko da addininta wanda tunda sukayi aure ya fahimci tanada sani sosai yanzu ma tare suke karatun quraninsu suna tunatar da juna, ga horse riding suna enjoying sosai a tare, sai kuma duk yamma sai ya fita da ita strolling yana rike da ita har su dawo. Jawota yayi a hankali ta zauna bisa cinyarsa yana wasa da yatsunta, shiru tayi tana so ta mike can dai tace "Zaka makara zuwa fada my king, in fact ka makara ma already bari na raka ka." Ta fada tana kokarin mikewa tsaye, a shagwabe yake kallonta yana fadin "O'o korata ma kikeyi ko Hoodah? I just want to spend some time alone with my wife." Amma ina Hoodah bata yadda ba bataso yayi late xuwa fada, "Saidai idan ba sarki bane shi kuma wannan sarkin ya makara zuwa fada oya tashi muje." Mikewa yayi kamar zaiyi kuka gaba tayi yana biye da ita a baya har bakin kofa, tsaye yayi kafin ya bude kofar hakan yasa ta juyo tana fadin, "Kayi mantuwa ne....?" Bata karasa magana ba taji ya janyo gently ta fado jikinsa, Kisses yake aika mata ta ko ina hakan yasa ta dinga dariya tana kokarin kwace kanta, saida ya gaji dan kansa sannan ya sake ta yana murmushi kafin yayi mata bankwana ya wuce fada, Hoodah tafi minti goma tsaye tana bin wurin daya bi da kallo kafin ta juya ta koma cikin gida fuskarta ta kasa daina murmushi. Tana komawa ciki da mintina kadan sabuwar jakadiya itace head of servants tadah ta shigo parlor Hoodah na zaune maids su biyu suna dan danna mata kafarta dake kumburi kadan kadan, jakadiya ta zube kasa tana bada gaisuwa "Barka da kwana ranki shi dade?" Hoodah na murmushi tace "Kina lafiya jakadiya?" Tace "Lafiya lau Sarauniya, dama abinda kikace a girka maki dazu tou an kammala Allah kara maki lafiya." Hoodah tace "Okay toh a bar man shi a dining zanci a can nagode." Jakadiya tace "Allah ya kara maki lafiya akwai wani abin da za'ayi miki yanzu?" Ta girgiza kai "A'a yanzu dai babu jakadiya kina iya tafiya." Jakadiya ta gyada kai ta sake mata kirari cike girmamawa sannan ta mike ta fita.---- 

A hankali yake taku maids dinsa na binsa a baya yasa kai cikin fada, wasu daga cikin title holders dake ciki suka gaishe shi ya amsa da murmushi saman fuskarsa bayan ya zauna ya umarce su dasu zauna suma, daya daga cikin dogarai ne ya sunkuya yana fadin "Ranka ya dade Malam Ibrahim din ya karaso, a shigo dashi ciki ne?" Ya gyada kai "Har ya karaso? Bismillah kace ya shigo." Tashi yayi ya fita ba'a jima kwarai ba suka shigo malam Ibrahim na binsa a baya ya karaso da sallama aka amsa masa, ya sunkuya yana gaishe shi "Ranka ya dade barka da kwana?" Sarki yace "Lafiya lau, Alhamdulillah malam Ibrahim yaya iyali?" Yace "Alhamdulillah nazo da yaran ranka ya dade."  Yace "Bismillah ka shigo dasu." Ya durkusa cike da girmamawa ya fita, can sai gashi ya shigo da yara maza kusan su talatin suna biye dashi zasu kai kimanin shekaru daga sha uku zuwa sha shidda. Kwanakin baya malam Ibrahim ya gayyaci Sultan saukar qurani ranar wata asabar, yaran almajiransa ne irin wadannan da ake turowa karatu daga gari gari suna zuwa bara don su samu abinda zasu ci, don wasu ma duk da sun sauke bazasu koma gida ba saboda neman na kansu da suke fafutika wasu zaka tsince su yashe a titi kwance, wasu cikin bola wasu kuma kullum suna bin gida gida suna bara, wasu sai suyi bara gida goma ma babu abinda suka samu, saidai idan wasu sun fito bada sadaka baifi su samu kosai uku uku ba ko kuma panke in kuwa masa ce da kyar suke samun biyu. Yinin ranar daya dawo gida babu abinda yake tunani sai hanyar da zaya bi don taimaka ma wadannan almajiran, wace hanya zayabi don rage yawon barace barace da suke yi? Ranar dai har Hoodah ta fahimci yana cikin damuwa ta tambayesa meke damunsa, shine ya fada mata ay taimaka ma almajirai yakeso yayi amma baisan ta wace hanya ba, "Meyasa bazaka basu jari ba su fara business don su taimakawa kansu tare da iyayensu? Dan abinda suke samu sai kaga suna dan aika ma iyayensu da wani abu, kasan dalilin da yawancinsu idan sun kammala karatu basu komawa gida? Saboda sunsan basu tara komai ba sai suga babban faduwa ce ace sun koma gida basuda ko sisi duk da sun yi ilimin, tou don hakane zakaga sun tafi wurare masu nisa suna neman hanyar da zasuyi surviving, yawancin almajiran tun suna yan kanana iyayensu ke turo su karatu, wasu iyayen suna zuwa wasu kuwa basu taba zuwa ba saidai idan sun girma su dinga zuwa ganin gida once in a while, wasu ma manta identify nasu sukeyi so kagani idan ka basu jari ba karamin taimakonsu zakayi ba su tsaya da kafuwansu, su zama responsible su san menene rayuwa. Bayan ka rage yawan almajirai da rage yawan barace barace a titi zaka iya hada committee funds na wadannan makarantu zaka iya dinga taimaka masu da abinci, ko kayan sanyi cikin sanyi, ko kuma kayan sawa ko kuma yan takalma haka slippers wallahi ina matukar tausayawa almajiran dake yawo babu takalmi haka xaka gansu kafafunsu duk a tsage abin tausayi, iyaka ka dinga zuwa duba su kana ganin abinda suke yi daga lokaci zuwa lokaci, sai ka masu alkwarin idan sun maida hankali ga karatun nasu zaka basu kudi suja jari, wannan ba karamin taimaka masu zaiyi ba kafin azo ga maganar ladarka wurin Allah," ta kare da murmushi saman fuskarta tsayawa yayi yana kallonta ba kakkautawa cikin ransa kuwa hamdala yake ga ubangiji daya bashi mata kamar Hoodah, mace ta gari mai kaifin tunani da hangen nesa da sanin ya kamata, Baisan lokacin daya rungumeta ba, tare suka zauna suna shawarwari  akan irin kasuwancin daya kamata yayi setting ma yaran, dago kanta yayi yan fadin "Allah ya saka maki da alkhairi, ya baki abinda kike nema duniya da lahira Allah yayi maki albarka ya kuma sauke ki lafiya." Yaran duk suna tsaye suna binsa da kallo abin tausayi gaishe shi sukayi, dama yayi waya da malamin nasu ya fada masa kudurinsa akan yaran bayan yayi shawara da Abbi da sauran manya suka amince masa dari bisa dari, malam Ibrahim ba karamin murna yayi ba ya dinga jera masa addu'oi ba adadi, shine sarki ya fada masa yazo mashi da yaran yasa masa rana shine ya kawo su yau. Kallonsu yakeyi fuskarsa dauke da murmushi yace "MashaAllah na tayaku murnar sauke qurani wannan shine farkon cigabanku a rayuwa InshaAllah," duk suka amsa masa da ameen cike da jin dadi, "Nasan dai malaminku ya fada maku dalilin zuwanku nan ko? Inaso mu yi wani abu kamar kasuwanci ne dani daku, zan kasance nine mai capital ku kuma entrepreneur din business din, zan baku jari ko wanenku ya fara sana'ar da tafi kwanta masa a rai, amma nidai a shawarce zaifi kuyi na siye da siyarwa amma ku tabbatar sana'arku ta halali ce karku sake ku yarda ku saida haram da kudina, na tabbatar kuna da ilimi kunsan abinda nake nufi, sannan banda riba, riba haramun ne ko a musulunci an bayyanata  a wurare daban daban a cikin alqurani da hadisin annabi (SAW), subhnallah Allah ya sa mu gane ya tsare mana imaninmu." Suka amsa a sanyaye, ya cigaba da magana "Kamar yadda na fada maku wannan sana'a tamu zamuyi fixing prices daku 50 50 duk abinda kuka samu zamu raba idan kuma kukayi asara nima zan dauki asarar tare daku hakan ba yana nufin ku zama careless ba, sannan inaso kusani zan zama responsible idan akayi asara a sana'ar da akayi ba ha'inci, duk mutanen wurin zasu zama shaida zan baku kudaden nan don haka ko wanenku ya zauna yayi tunanin kalar sana'ar da ya kamata yayi gasu nan ba iyaka, duk wacce kaji ta kwanta maka a rai sai ka fara da ita." Ya fada yana handing masu kudaden da yayi niyyar basu tare da alkwarin cewar zasu dinga reporting akai akai shima kuma zai dinga ziyartar su yasan me suke ciki, haka sukayi masa godiya sannan suka tafi cike da farin ciki marar misaltuwa. Bayan sun tafi sai ya kira malam Ibrahim don kar suji abinda zai fada masa in private yace "Maganar rabin kasona da na fada maku babu abinda zanyi da ita so nake a dinga masu saving, a hankali su dinga tarawa yadda ko aure suka tashi ba lallai bane su samu matsalar kudi, saidai banaso ko kadan su san da maganar nan a barta a yadda na fada masu cewar kudin nawa ne idan an raba da fatan ka fahimta?" Idanunsa taf da hawaye ya shiga masa godiya "Bansan da wane irin kalmomi zanyi amfani ba wurin nuna farin cikina gami da godiya da wannan taimako na alkhairi da kayi, Allah ya saka maka da alkhairi, Allah ya kara arziki Allah ubangiji ya taimakeka ya kara daukaka ya biya maka bukatunka na duniya da lahira," dukewa yayi rike da kafarsa yana kuka saboda farin ciki... "Wallahi ranki dade mungode mungode sosai Allah ya kara girma." Sultan ya dafa shi "Wannan duty dina ne so kar ka damu, kabi yaranka ka kuma kula dasu sosai kasa ido akansu amana ce a hannunka." Gyada kai yayi yana share hawaye kafin ya mike ya fita.

-----

Ki tuba kafin lokaci ya kure miki." Abinda Khairy keji a mafarki kenan kullum indai ta rufe idanunta koda idanunta biyu haka takeji ko kuma cikin bacci, haka duk ta rikice ta kasa komawa bacci tsoro duk ya rufeta, ba yadda Mama batayi da ita ba akan suje ta roki gafarar Hoodah amma abin ya gagara saboda shegen taurin kan tsiya, a yanzu Mama ke zama da ita cikin dare tana hanata yin kururuwa amma no matter what sai tayi. "Ki tuba kafin lokaci ya kure miki." Khairy tace da Mama tana mai fashewa da kuka makalkale da ita, “Kullum haka nakeji indai na kwanta sai an fada mun haka” wani kukan ta kara sawa “Ya isa Khairy ki daina wannan kukan sannan ki tabbatar kinyi addu’a kafin ki kwanta” “Mama ko nayi addu'a sai naji haka." Cikin sigar lallashi Maman tace "Nasan kinayi kuma hakan na taimaka miki sosai, kawai dai kiyi kokari ki samu bacci ko yaya ne” Ajiyar zuciya Khairy ta sauke sannu a hankali ta rufe idonta bayan ta tofa addu’oi marrasa adadi, aikuwa tana rufe idanunta take mafarkin data saba yi ya kuma dawowa har ta fara ganin wasu halittu suna nufo ta. Zaune ta mike tana share zufa don ta kuduri bazata koma bacci ba yafiye mata ta zauna idonta biyu don muddin ta rufe idonta sai ta gani, Mama ta mike jin Khairy na tabata, farkawa tayi tana binta da kallo. "Ke lafiya?" Khairy da idanunta sun kawo ruwa tace  “Mama ina son ganin Hoodah” Mama ta ware idanu "Bakida hankali? Tun tuni nake binki kije sai yanzu data zama Sarauniya wanda kinsan ganinta babban aiki ne, yanzu fa ba Gimbiya bace Sarauniya ce taya kike tunanin za'a barmu mu ganta kai tsaye?" Kuka ta fashe dashi kamar ranta zai fita tace, "Nidai don Allah ki taimaka mun Mama inganta, ganin nata shine kawai nutsuwar raina ki taimake ni” tasa kuka sosai, jinjina kai takeyi tana nazari kafin tace "Shikenan zanwa babanki magana inje gobe inga ko ganinta zai yuwu, Insha Allah." ta rungume Mama tana share hawayenta "Nagode Mama thank you." Mama tayi murmushi "Lokaci yayi da ya kamata ki sauke nauyin dake kanki ko kya huta da wadannan mugayen mafarkan da kikeyi” Khairy tace tana murmushi  “Insha Allah”  Mama tace “Kisani Allah ne yake sonki da rahama Ummalkhairy tunda har yake nuna maki a mafarki, just know that you are lucky." Khairy ta gyada kai tace “Hakane, Allah ka raba mu da son da zuciya Mama shaidan ya kaini ya baro.” Mama tace "Ameen tashi toh ki dauro alwala kiyi nafila." gyada kai tayi tana murmushi ta mike ta nufi bathroom tana jan kafa da kyar saboda cikinta da yayi mata nauyi, bayan ta gama ta idar tana kwanciya ta rufe idonta and for the first time da bataga komai ba, batayi wani mummunan mafarki ba.  Tabbas Allah mai rahama ne kuma mai jin kai ne, kuma idan har kayi wa wani laifi ko ka cuce shi ka zalunce shi idan har ka roke shi gafara ko kayi niyya zakaji kamar an wanke ka daga wani irin datti. 

Washe gari da safe wurin karfe sha biyu suka isa fada da Khairy harda iyayenta duka, saidai cikin rashin sa'a aka hanasu shiga don dogarin ma tambayarsu yayi yace "Kunada appointment da mai martaba ko ita Sarauniya?" Suka girgiza kai a sanyaye Baba yace "Kayi hakuri yaro sun sanmu ba saida appointment ba." Ina dogarin nan ya hanasu shiga sai da kyar shima wai sai dai aje a tambayo sarki in yace a shigo dasu sai a shigo dasu, shine fa ya bada izini sannan ya yarda su shiga. Sultan da Hoodah na bangaren su Abbi suka shigo da sallama don basu ma dade da gama breakfast ba lokacin. 

Ganin Ummalkhairy yasa duk suka tsorata duk ta rame ta kode in banda tsinin cikinta da haihuwa ko yau ko gobe, jikinta duk wani tabon kuraje ne sun bata mata jiki burjit, cikinta ya rinjayi sauran jikinta, tuna Khairy yar gayu mai ji da kanta da aji yau itace ta koma haka? Lallai Allah abin tsoro.  Mama ta taimaka mata ta zauna, Ummi da Abbi suka bita kallon tsoro kamar yadda Sultan da Hoodah suma suka zama shocked don sun kasa koda kwakkwaran motsi daga inda suke, “Mungode da kuka bamu izinin shigowa fada." Khairy manage to say “Sannu khairy” Mama ta fada ganin yadda take nishi kamar mai asthma, murmushin karfin hali tayi “Dama...." sai kuma numfashinta ya fara barazanar daukewa “Subhanalillah! Meyafaru haka??” Ummi ta tambaya har yanzu bata daina ma Khairy kallon tsoro ba, Mama tayi karfin halin fara magana, "Ranki shi dade abubuwa sukayita faruwa wanda nasan kin san da saninsu, tou karshe dai da aka tabbatar cutar kanjamau gareta dah kamar duka kenan tana shan magani amma yanzu bata sha ga tsohon ciki haihuwa yau ko gobe, ta yaya take tunanin zata samu sauki?” Jira sukayi har sai da numfashinta ya daidaita sannan ta fara magana. “Nasan abinda na aikata zaiyi wuya ku yafe man especially Hoodah da Sultan, abubuwan dana yi maki inda ina da hankali ko dabba akace nayi ma haka ya kamata naji tausayinta ballantana mutum mace ma kuma yar uwata. Dafarko dai zan fara da cewa, ku yafe man saboda munanan abubuwan dana aikata yanzu banida sukuni banida kwanciyar hankali, rabona da inyi bacci koda na awa biyu ne har na manta sai mugayen mafarkai, mun dade muna soyayya da sarki amma rana daya ya auro wata ba karamin ciwo abin yayi mani ba, tun daga wannan lokacin na tsani Hoodah, na dinga shuka mata abubuwa da dama a tunani na shine hanyar da zanbi in rabasu ashe Allah yafini, na dinga bin bokaye da malamai ganin na kawar da ita....”  “Subhanalillahi Khairy abin naki har ya kai haka? Hoodah bata ta6a cutar dake ba, bata shiga harkarki, kuma ay ba laifinta bane ba don nace ina sonta, why Khairy? Meyasa zakiyi shirka kinsan girman laifin shirka kuwa?” Ya fada yana huci, tace "Nasani inama za’a iya komawa baya don na gyara 6arnar dana tafka, inama za’a sake bani wata damar na gyara laifuka na? Wallahi son danake maka shi ya jawo komai, I made sure to destroy your relationship, amma sai nayi realized your bond is strong, so strong that it will be difficult to seperate you, and so a brilliant idea come to mind, I decided to kill her, a cewata shine kadai hanyar da zanbi ganin na rabaku har abada, I was so angry dana ga tanada rai, ashe nice za'yiwa fyade, so when I learnt Khairy is pregnant I to plan to kill the baby as soon as aka haifesa, but I guess Allah has other plans for me!” “You want to do what?” Sultan ya mike a fusace zai yi kanta, Abbi ya dakatar dashi “Zauna Sultan, please”  Zama yayi yana huci, Hoodah kuwa fashewa tayi da kuka wannan wace irin kiyayya ce? “Innalillahi wa inna ilahir rajiun, Khairy yanzu duk kin akaita hakan saboda kishin banza? You decided to kill Hoodah saboda kishi are you normal? You framed her several times Allah na fiddata, kin kulla mata sharri kala kala Khairy bakiyi nasara ba, am ashamed of you, you stoop so low Khairy just because you want Sultan all to yourself!” Abbi ya fada a fusace, kuka take rerawa tace  “Nasani Abbi amma yanzu na gane kuskurena, please find it in your heart to forgive me, idan baku yafe mun ba I will never have peace” “So you think it’s easy just to forget and forgive you Khairy?” Sultan yace a fusace zuciyarsa sai tafarfasa takeyi “Don Allah don annabi kayi hakuri, Hoodah, Please ku yafe mun, Abbi da Ummi ku taya ni rokon Hoodah ta yafe mun," kowa yayi shiru, can Ummi tace, “Haba Hoodah meyasa kukaki yafe mata? A cikin alquran cikin surori daban daban Allah yayi maganar yafiya kada ku zamto cikin mutanen da basa yafiya mana, Allah kansa ma muna masa laifi mu roke sa ya yafe mana, meyasa ku bazaku iya ba? Meye ba'ayi wa annabi ba? Ku dubu darajarsa wanda akayi duniya da lahira domin sa ma ya yafe balle mu karan kada miya, Allah kansa yana yafe mana idan muka nemi yafiya don haka kuyi hakuri ku yafe mata tunda ta gano kuskurenta." Numfasawa Hoodah tayi "Tabbas hakane Ummi mu su waye da bazamu iya yafiya ba? Allah kansa yana yafe mana idan mun tambayesa, don haka na yafe mata." Sultan yace "Na yafe mata shi dan adam ajizi ne sannan ina so in baki tawa guddumuwar sai ayi maki treatment da kuma bukata idan ta taso, sannan zan baki shawara idan kin sauka lafiya ki sha magani daga nan kisamu miji kiyi aure Allah ya taimaka." Cike da jin dadi Baba da Mama suka fara godiya "Allah ya saka da alkhairi ya biya maka bukatunka na alkhairi, Allah ya kara arziki ya kara girma, Allah ya jikan magabatanmu ya haskaka kabarinsu, Allah ya kara dankon zumunci ya hada kanmu dana yayanmu baki daya, Allah kuma ya tsaremu daga sharrin dukkan sharri ya karemu daga rudun zamani dana shaidan. Mungode mungode Allah yasaka da alkhairi." Khairy ba karamin kuka tayi ba, tashi yayi ya kira Hoodah ya shawarce ta akan nawa xai basu, tace "Duk yadda Allah ya hore maka kawai ka basu." Million kusan biyu ya bata zo kuga godiya ranar sun sa masa albarka sunyi murna, nan Baban yace zai fiddata waje don inganta lafiyarta....

-----

Gaskiya ne da akace duk abinda ka shuka shi zaka girba, Karimah tana nan tana rokon mutuwa ta dauke ta amma shiru, idan ciwo ya motsa ji take kamar zata mutu, amma wani lokaci kuma kamar ba abinda ke damunta, anyi admitting nata asibiti don bata taimakon gaggawa sunce yanzu stage 3 take kullum burinta bai wuce ta mutu ba amma mutuwar taki daukarta azabar yau daban ta gobe daban duk ta rame ta jeme, ga cikinta wani irin kumburi yakeyi yana neman rinjayar jikinta su kansu likitocin tsoron ta6ata sukeji, don ya kamata ayi mata surgery amma suna gudun idan suka ta6ata zata iya rasa ranta saidai suyita ja mata rai suna sa ranar aikin, idan ranar tazo sai su daga kuma gashi babu wanda ke kula da ita dama duk ta watsa ya uwanta, wasu ma tun tana gidan Abba korar kare tayi masu, sai yanzu gashi tana bukatarsu kowa ya gujeta, kuka kam babu irin wanda batayi ba na bakin ciki da dana sani, kullum adduarta Allah ya dauki ranta ta hutu amma shiru sai tarin azabar ciwo sometimes kamar zatayi hauka idan ya motsa ta dinga kururuwa kenan tana ihu, yanzu dai sunce sai sun sa mata oxygen amma fir taki tace ita batason wani taimako mutuwarta kawai take jira har magungunanta da allurai duk bata yarda ayi mata, a cewarta ay idan tayi medication zata iya warkewa gara ta mutu gashi kuma mutuwar taki zuwa, saidai kullum ta zauna taci kukanta ta koshi...

------

Monday, 26 July 2021

YAR AGADEZ PAGE 37

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 37}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com



-----

Zuwa yanzu Hoodah ta kara kyau tayi fresh tayi yar kiba abinta, kana hangen tudun cikinta ya bullo, musamman Sultan ya samo mai zama da ita don kula da lafiyarta wata yar dattijuwa. Don yanzu saura kiris cikinta ya shiga na wata shidda cip, kullum sai Baaba Hinde ta bata addu'oi tasha wasu a shafa cikin dasu, ga magungunan gargajjiya da ake bata duk dai wasu na kariya ne wasu kuma na lafiyarta ne dana babynta. 

Kamar kullum suna daki itada Sultan sun gama sallar isha'i suna lazimi Hoodah tawani yatsina fuska tana mika ta kalleshi cikin sigar shagwaba tace, "Sultan babynka yana jin kwadayi fa." Ta fada cike da zolaya don tasan tashin hankalin Sultan bai wuce ta fada masa tana jin kwadayi ba tana son wani abu especially cikin dare koda sassafe, don bata ta6a neman abu mai sauki ba kullum sai ta bashi wahala. Kallonta yake cike da tashin hankali yana fadin na shiga uku cikin ransa kafin yace, "Kai kuwa dan Baba ya zakayi man haka? I thought mun gama yarjejeniya da kai cewar babu abu mai sauki cikin dare sai da safe ko?" Yayi wata irin muryar tausayi hannunshi yana cikin na Hoodah. Itama hannunta ta dora bisa nashi idanunsu cikin na juna wata irin kaunar juna ce ke kara ratsa zukatansu, "Tou dan Baba kaji mudai bado mukesan ci da tuwon shinkafa miyar yakuwa sai gasashen kifi mai yajin nan wanda ake ci da sauce din albasa, su Daddy ayi sauri a nemo mana kar na haihu ban shirya ba." Ta fada miyanta na tsinkewa tana ji kamar ta gansu gabanta, dariya ta soma yi ganin kallon tsoron da Sultan ke binta dashi, babban tashin hankalin da yake ciki bai wuce inda  zai samo yakuwar kanta ba balle azo ga bado, da kuma kifin, tuwon shinkafar kam ba'a maganarsa. Marairaice fuska yayi "Dan baba dan Allah ka taimaka man, kuyi hakuri ku chanza abinda zai samu a gidannan, gobe idan Allah ya kaimu shine abu na farko da zan fara nemowa." Ji yake kamar yayi kuka don yasan idan ta fara haka kamar wasa to ranar babu bacci za ta fara masa kukan fitan rai in bai samo ba. "dan baba muyi ma baba hakuri a bamu oats ko custard ko pancake mu dan rage zafi." Dan tasan Sultan ya hanata shan sugar, wata ajiyar zuciya ya sauke yana fadin "Eh naji din zan hado maku kusha amma dai na yau kawai." Mikewa yayi cikin mintina yaje ya hado mata oats ya kawo mata, a hankali take sha shi kuma ya cigaba da addu'oinsa, tana gama sha a nan kan sallayar ta 6ingire ta fara bacci kallonta yayi ya saki murmushi kafin ya cigaba da abinda yakeyi. Sai da ya gama ya dauketa bayan ya cire mata hijab sannan ya kwantar da ita kan gado tare da lullubeta, saida yayi wanka sannan ya kimtsa kafin ya kwanta ya rungume ta a haka bacci yayi awon gaba dashi.

------

2WEEKS LATER 

Shopping sukaje itada Sultan na siyayyar kayan baby sun kwaso abubuwa daban daban duk da Sultan yace bayaso ayi mata scanning suga sex din baby, hakan yasa yace mata amma shidai yana son yar mace ita kuma tace namiji, gardama sukeyi akan kalar kayan daya kamata su siya nan Sultan yace "Tsaya kowa ya dauki kalar da yakeso idan kin haihu nayi winning zaki bani kyauta ta musamman idan ke kikayi wining zan baki kyauta." Tace ta yarda haka suka fara jidar pink and blue har suka kammala suka fito. A gajiye suka isa gida ko kayayyakin basu ce a sauke ba suka wuce ciki,  wanka sukayi a tare sannan sukayi sallar isha'i sukaci abinci dama pizza yayi masu order babba da juice mai sanyi. Kwance take kan gado daga ita sai rigar bacci fara wadda ta fiddo mata da cikinta, kafarta yake matsa mata a hankali har bacci ya fara surarta, wayarsa ce ta fara ringing gashi wayar na kusa da ita, bude ido tayi ta dauko wayar tana kallon screen din, Number din Abbi tagani kasake tayi rike da wayar gabanta na faduwa, "Dauka mana kisa a speaker." Tana sakawa a speaker din sukaji muryar Abbe tangaram, kamar daga sama kuma sukaji muryar Ummi itama tana fadin, "Sultan? Ya kuke? Baka rame ba dai ko? Kana cin abinci?" Da sauri Abbi ya karbi wayar yace "Sultan, alhamdulillah mun samu lafiya ana shirin sallamarmu daga asibiti ma, nasa an maku visa kaida matarka, gobe karfe 9 ku hau private get dina ku taho, driver zaizo ya daukeku karfe  tara na safe sai ku shirya." Ihun da sukeyi kamar wasu kananan yara tsalle sukeyi sosai tsakiyar gado suna rungume juna, baccin da ba'ayi ba kenan suka hau parking kaya ko wanensu bakinsa yaki rufuwa, "Abbi da Ummi are back! Safe and sound Alhamdulillah!" Daren ranar kasa runtsawa sukayi gaba daya ji suke gari yaki wayewa tsabar yadda suka kagara.---

A gajiye suka iso asibitin saidai baka gane gajiyar saboda ko wane fuskarsa shimfide take da farin ciki da kuma annashuwa, jikinsu babu inda baya rawa burinsu bai wuce suje suga halin dasu Abbi ke ciki ba, Abbi kam saidai ace ya warke tangaram saboda in ka kalleshi kamar bai taba rashin lafiya ba, Ummi da yake tafi jin jiki don ita sai last week ma ta fara magana da saidai ido, kalmarta ta farko itace Ina su Sultan? Tou tunda ta fara magana babu abinda take fada sai ina su Sultan Abbi yayi tunanin duk zafin ciwo ne har dai ya kira mata Sultan din, lokacin har ya masu visa din ma. Tsaye yayi yana bin Abbi da kallo cike da farin ciki kafin ya rugo da gudu yayi hugging dinsa cikin tsantsan farin ciki, itama Hoodah Abbi yayi mata tarba cike da murna a lokacin basu samu ganin Ummi ba sai zuwa anjima Doctors sukace zasu iya ganinsu. "Sultan kodai na kaika masaukinku ku huta zuwa anjima sai ku dawo? Nasan tana bacci ne sheyasa aka hanaku shiga yanzu." Ba don komai yace haka ba sai don Hoodah ganin dan cikinta daya bullo yasan tana tare da gajiya, nan kuwa can kasan ransa wani irin farin ciki yakeji yana ratsa shi saidai bai bari ya nuna ba, Hoodah ce tayi saurin cewa "A'a Abbi don Allah zamu jirata har sai ta tashi." Gani take tafi Sultan kagara taga Ummin nan, Abbi yar dariya yayi kafin yayi leading dinsu hanyar dakin da Ummin ke ciki bayan magiya da roko da sukayi ma Doctors din har finally suka barsu su shiga ciki. "Hoodah ke nafi tausaya mawa naga kinyi nauyi da yawa, haba Sultan shine ko ka fada man na fara siyayyar kaka ko?" Ya fada yana mai kamo kunnensa guda daya yana murdewa cikin wasa, kunya duk ta kama Hoodah shi kuwa Sultan yar kara ya saki "Am sorry Abbi ba gashi kagani ba yanzu? Kyautar me za'a ba baby?" Dariya Abbi yayi yana fadin "Kaci gidanku, kyautar kaina zan bawa dan marar kunyar wofi!" Dan duka ya kai mashi daidai time din da suka bude kofa suka shiga dakin, da murmushi a fuskarsu duk suka tsaya turus suna bin nurse da kallo tana ba Ummi medication sannan tana mata dressing ciwonta, dagowa Ummi tayi tana binsu da kallo da sauri Hoodah ta boye bayan Sultan don wata irin kunya taji ace Ummi wai zata ganta da ciki don cikin ya bullo sosai kamar dan wata bakwai, "Sultan..." ta furta muryarta na rawa daka ganta  idanunta ya cika da kwalla, kamar wani yaro haka ya fara takawa wurin gadonta hannunta take miko mashi ya riko sai hawaye shar shar, hugging dinta yayi gaba daya sai suka fara kuka daga ita har shi sai can cikin kuka ya fara magana, "Ummi na dauka tafiya zakiyi ki barni bazan sake ganinki ba, muryanki, fuskanki komai naki kullum sai nayi mafarkinki..." breaking hug din Ummi tayi, "Haba Mummy's boy meyasa zakayi irin wannan tunanin? Ka kwantar da hankalinka everything will be okay soon InshaAllah, ya kamata ka daina kukan nan kada Hoodah tayi maka dariya." Murmushi ya kakalo yana goge hawayen dake zubo masa, Ummi kam tuni ta daina kuka saidai fa daka kalleta kasan dannewa kawai takeyi, hannunta ya sake gyara ma riko ya cigaba "I really missed you Ummi, how are you feeling now? Thanks for getting better for us all because we all need you two, and don't worry you'll soon be okay and back on your feet InshaAllah," hannun Hoodah ya kamo ta dawo kusa dasu ta tsaya tana binsu da kallo, kallon mamaki take bin Hoodah dashi baki sake a hankali idanunta suka sauka kan cikin Hoodah don dole ta saki hawayen suka zubo, a hankali Hoodah ta zauna sannan tayi hugging dinta tightly, "Ummi...." ta fada da muryar kuka, wani irin farin ciki na ratsa ta tunda take bata taba jin nutsuwa da tayi hugging Ummi ba kamar yau ji take kamar mahaifiyarta ce tayi hugging haka take jinta har can kasan ranta, "Hoodah.... Ikon Allah..." sai ta fara dariya kuma tana taba cikin sannan ta dawo tana taba fuskarta cike da soyayya ji take kamar itace ta haifeta, "Hoodah how are you? How did it went?" Ta kara tambaya tana kallonsu daga ita har Sultan din, share hawayenta Hoodah tayi da sauri sannan tace "It was not good Ummi, munyi kuka kamar ranmu zai fita, amma Alhamdulillah you're both fine keda Abbi, we couldn't thank Allah enough daya baku lafiya keda Abbi,"  Abinda Hoodah ta furta kenan tana kara hugging Ummi cikin muryar kuka, dan dukan wasa Ummi ta kaiwa Sultan tana fadin "Wace kalar mugunta kayiwa yata da bana nan? Naso ace ina nan ay da sai na rama mata duka muguntar da kake mata." Hoodah tayi murmushi cike da shagwa6a tace "Wallahi Ummi  zo kiga muguntar da ya dinga mun kamar ba Sultan dinki ba." Ware idanu yayi yace "La ila sharri zakiyi man? Ni babu wata muguntar da nayi maki." Duk da cewar Baba na tsaye ganin Ummi cike da farin ciki ba karamin dadi yaji ba shima sai suka saka shi cikin nishadi da annashuwa, yace "Indai mugunta ce akazo kan Sultan kuma an gama magana, rainon turai ne fa kema dai maman yara kinsan haka yake kika barshi da Hoodah a gida dama ay kinsan abinda zai biyo baya kenan." Ya fada yana dariya, dariya duk suka kwashe dashi don itama kanta Hoodah tasan labarin yadda Sultan baiyi zaman Niger  ba yana can gidan wata aunty dinsa can yake zama. Bayan zuwansu da sati kusan uku aka sallami Ummi dama shi Abbi tun satin da suka zo aka sallame shi, aikuwa ana sallamota da kwana biyu suka tattara suka koma gida.

Tunda suka koma gida masauratar ta kacame da baki shiga kawai ake ana fita yadda kukasan ana wani biki haka gidan sarki ya koma gaba daya ya cika ba matsaka tsinke, kowa yana zuwa yi ma su Abbi barka da arziki saida akayi kwana kusan goma ana baki sai a hankali a hankali mutanen suka dinga ragewa gidan ya fara dawowa daidai, gashi dama tunda Abbi ya kara warwarewa kawai ya hau gyaran gida gaba daya wasu wuraren rushe su akayi aka maida su modern, gidan sai ka rantse wata villa ce, duk su Sultan sun zama confuse akan dalilin gyaran nan yaki fada masu har daga karshe suka hakura suka zuba masa idanu har ya kammala nan kuwa wani shiri ne yakeyi babu wanda yasani, surprise ne yake so yayi ma kowa. Sultan ne ya fiddo wani golden box daga cikin wardrobe dinsa sai shining yakeyi, a hankali ya bude shi da sukaje India ta masa mugun kyau ya siya a boye ya adana da niiyyar yaba Hoodah abin kaunarsa, fitowa yayi daga side din nasu wanda akayi ma gyara sosai ya nufi sashen su Abbi nan ya tarar da Hoodah da Ummi zaune bisa yar varendar gidan suna shakar iskar wurin da alama suna enjoying kansu, fira suke jefi Ummi na yanka ma Hoodah apple da banana tana ci suna firarsu cike da nishadi, har kasa ya durkusa ya gaida mahaifiyar tasa yana murmushi itama ta mayar masa da murmushin tana fadin, "Wai ya kake ta mana safa da marwa a nan wurin ne? Ko don na karbe maka mata sheyasa kake ta zuwan man nan ka hanani sakat." Ta fada cike da zolaya, hararar wasa ya aika ma Hoodah wacce ke masa gwalo tana dariya kasa kasa, "Laa Ummi wallahi ba haka bane wurin Abbi zanje shine dana bi ta nan nace bari na tsaya na gaishe ku." Ya fada tare juyawa zai fita da sauri Ummi ta damko masa hannu hakan yasa Ummi da Hoodah dariya sosai, don sarai tasan meya kawo shi nan, "Words bazasu isa nayi expressing farin cikina ba, wai ace na kusa ganin little Sultan suna gudu cikin gidannan." Ummi ta fada cike da farin ciki ita kuwa Hoodah kunya ce ta lullubeta haka ta dinga wani sunna kai kasa, cikin farin ciki Sultan yake kallon Hoodah yadda duk ta zama uncomfortable kuma yanzu, Ummi ta kuma cewa. "Allah yayi maku albarka ya kuma sauketa lafiya." Yace "Ameen ya Rabbi." Yana gama fadan haka ya fice da sauri zuciyarsa fes. 

Shiga parlon sukayi bakunansu dauke da sallama Abbi dake zaune shida mutanensa ya amsa sallamar tasu sannan suka samu wuri kasa suka zaune kansu a kasa bayan sun gaishe da sarki ya gyara zama yana fuskantansu yace "dalilin dayasa na bukaci ganinku cikin gaggawa da kai da matarka Hoodah shine, inaso dukanku ku shirya gobe idan Allah ya kaimu akwai wani taron da za'ayi cikin gidannan bayan sallar la'sar, taron yanada matukar mahimmanci dan haka banason ayi wasa da lokaci sannan ya kasance kun halarci taron..." Sultan ya dago yana kallon Abbi yace "Allah ya baka yawon rai taron na menene dan musan irin shirin daya kamata muyi?" Murmushi Abbi yayi irin nasu na manya yace "Kawai kamar yadda na fada maku kuje ku shirya kawai kuyi hakan zan turo jakadiyya da kayan da zaku saka goben..." da tou suka amsa kafin ya basu izinin tafiya a sanyaye suka mike kowane yana faman sake sake cikin ransa.

Washe gari wani irin gagarumin shiri akeyi wanda babu wanda yasani daga Abbi sai Ummi amma ya hanata furta komai akan zancen, kamar yadda sarki ya gayyaci mutanen garin suma haka suke shiri basu san me ke faruwa ba, saidai kuma daka kalli kowa kasan cikin farin ciki yake tun safe aka fara gudanar da shiri masauratar Niamey ta dauki harami babu abinda kakeji sai karar algaita da kalangu, hayaniya kam ba'a magana kudi Abbi ya damka ma Ummi masu uban yawa na abinci da kaji da snacks sai drinks nan da nan ta fara aiwatar da nata shirin itama, komai yana faruwa da sauri lokaci nata matsowa, tun safe sarki ya aika masu da kayansu kamar yadda yayi alkwari cike da mamaki Sultan ke kallon kayan ita kuwa Hoodah harda uwar alkyabba mai shegiyar kyau sai kyalkyali takeyi, duk ya hada masu harda takalma tou wai shi Abbi me yake nufi? Kuma taron menene haka ya hada? Bari dai mugani. Suna gama sallar la'asar suka hau shiri nan maids din suka fara taimaka masu da shiri hanawa sukayi sukace ay zasuyi da kansu, shifa Sultan da har ya manta ana wata sarauta saida Abbi ya dawo gani yake normal mutum ne yanzu har komai ya chanza. Bayan sun kimtsa sunyi kyau sosai nan maids suka rakasu har fada inda tuni sarki da Sarauniya suke jiran isowarsu, taku dai dai sukeyi cike da kasaita wuri ya dauki sowa da kirari kala kala kowa na wurin su yake bi kallo ga fadar ta cika makil ba masaka tsinke, da king makers, title holders da sauransu duk suna wurin, bayan sun zauna wurin ya dan natsu Abbi ya mike tsaye yana rike da sandar sarautarsa ya fara magana. "Muna ma kowa barka da zuwa wannan gagarumin taro da na shirya wanda na barshi a boye ba tare dana fada ma kowa kuduri na ba, nayi hakan ne dan yazama surprise dana yarima da matarsa, ba tare da bata lokaci ba! Ina so na sanar da al'umma ta cewar daga yau da nake tsaye a nan na aje wannan sarauta...." kowa na wurin saida ya zama shocked banda Ummi data riga tasan meke faruwa sai murmushi takeyi, shima sarki murmushin yayi na manya sannan ya cigaba "Karku damu abin farin ciki ne zan fada, bakomai bane yasa nayi haka saboda rashin Lafiyar da nayi sannan jikina ya kawo karfi na fara tsufa, don haka inaso in sanar da al'ummata cewa inaso in nada dana Sultan ya maye gurbina wato ya zama sarki don ya gaje ni...." bama Sultan kadai ba harta Hoodah saidai abin ya girgiza ta mikewa tsaye sukayi Sultan ya isa inda Baban ke tsaye yana kallonsa da murmushi a fuskansa Sultan yace "Abbi I can't do this, please..." Abbi ya dafa kafafarsa yace "You can and will do it InshaAllah, wannan decision din nayi tunani a kai don haka inaso ka zama sarkin garinnan Sultan..." hannunshi ya kamo yace ya tsaya daga gaba gaba matarsa na gefensa, sarki ya kalli king makers yace "A nada masa." Alkybba Abbi ya cire ya mika masu suka sanya masa sannan a hankali suka fara masa daura masa rawani, daga shi har Hoodah idanunsa cike yake da kwalla, bayan an gama duk wani formalities aka masa handing staff of office sannan aka ce ya zauna bisa karaga, sai a lokacin abin ya natse shi yanzu shine sarki, Sultan sarkin Niamey sarki na goma sha daya a kasar Niamey! Duka title holders suka matso gabansa suka fara masa congratulations na zama sabon sarki harda Abbi da Ummi wani irin gagarumin kwalla yaji ya taho masa, shidai yasan royalty bata dame sa ba sai gashi Abbi ya bashi wannan girman da bai taba tunani ba, take gaisuwa ta fara daga mutane daban daban hade da kirari na ban mamaki! Bayan an gama roundin up sai ya tashi ya isa inda Abbi ke tsaye yana zuwa kawai sai ya zube bisa kafadunsa ya fara kuka....

Dafa shi Abbi yayi shima kamar zaiyi kukan yace "Kar kayi kuka Sultan kai fa yanzu sarki ne, sarakai basa kuka." Ya fada da murmushi fuskansa, "No Abbi bazan iya ba, nauyin da yawa a kaina Abbi." Yayi murmushi "Wannan kuma kai zakayi deciding Sultan wannan alkawari ne na dauka kuma dole sai na sauke, kuma waya fada maka bazaka iya ba? Kwarai zaka iya kawai kayi focusing and you'll see, sarauta a jininka take you were born to lead, wannan hakkinka ne dole kayi facing dinshi cike da kwazo." Ya fada babu alamun wasa a tattare dashi hannunsa ya kamo ya zaunar dashi sannan yace "Zauna ka saurareni da kyau Sultan." Ya fada yana murmushi na son nuna masa kwarin gwiwa, "Kakanka wato mahaifina kafin ya rasu ya bar man wasiyyar cewa indai da haifi namiji tou in tabbatar ya gajeni, sannan inyi masa alkwari basai na mutu ba za'a dauki sarautar a damka maka a'a da raina ya kamata ace muna dora sa kan hanya har ya iya gudanar da harkokin sarauta,  Alhamdulillah na dade ina jiran wannan ranar dama nace sai ranar daka zama responsible mutum ka kusa zama uba sannan zan karya alkwarin dana daukar wa mahaifina. Sultan bazance sarauta abu ne mai sauki ba saidai idan har ka natsu zaka fahimci tanada sauki da mutum ya maida hankali. Zama leader zai iya kai mutum wuta ko ya kaishi aljanna ka zama mutum mai adalci da sanin ya kamata, karka yarda power ta shiga kanka ka xamana mai yawan addu'a ya baka sa'a yasa ka zama adalin sarki, kayi koyi da qurani da kuma koyawar sunnar annabi (SAW), komai kaga ya faru haka Allah ya kaddara, idan ka dauki nauyin nan with seriousness and religiously bazaka kaga komai ba sai alkhairi InshaAllah, ina maka fatan alkhairi Allah ya albarkaci rayuwanku ya baka ikon aikata aikin alkhairi ga al'ummarka gaba daya." Goge guntun kwallan da suka zubo masa yayi sannan ya kalli Hoodah da murmushi shimfide saman fuskarta tana gyada masa kai, ya ce "Nagode Abbi Allah ya saka maka da alkhairi ya kara maka lafiya da tsawancin kwana, thank you." Abinda ya furta kenan saboda bai samu kalmomin da suka dace ya fada masa a daidai wanann lokacin ba, bayan ya gama sauraren dogon bayanin Abbi sai yaji sanyi cikin ransa da relief. Daga nan aka cigaba da gudanar da shagulgulan nadi, makada suka cigaba da kidinsu, kirari suka cigaba dayi ma sarki da Sarauniya Hoodah, daga nan akaci aka sha nan kuma aka dinga gudanar da kyaututtuka, manya manyan mutanen da suka samu halarta taron sune suka dinga kawo masu gift wasu kayan jarirai ne, wasu shadda, wasu atamfa, wasu lace, wasu rawani, wasu alkyabba, wasu jewelries, kai komai aka dinga basu as a gift, nan makada suka zagaye Hoodah suna mata kirari suna kidi, "Sarauniya Hoodah yar gaban goshin mai martaba, farar mace turar mata, farar mace alkyabbar mata, Allah yaja zamanin uwar gida a gidan mai martaba ya sauke ki lafiya." Babu abinda takeyi sai murmushi sai da aka lafa Ummi tazo tasa mata alkyabbar sarauta sanann aka zaunar dasu bisa karaga itada sarki, hannunta ya kamo yana murmushi sannan yakai fuskarsa daidai kunnenta yana fadin, "You look stunning my love." Batace komai ba kanta dai na kasa tana murmushi, haka aka cigaba da gudanar da shagali har saida suka ji kiran sallah sannan aka kare daga haka taron ya fara watswa, burinshi bai wuce ya dawo daga sallar isha'i ba ya tafi wurin Sarauniyarsa yasan tana can tana jiransa.....

Karfe kusan tara ya shiga da sallama turus ya tsaya kamar yau ne ranar farko daya fara ganinta saboda kyan da tayi masa don kuwa ta chanza shiga tayi kyau MashaAllah har yanzu bata cire alkyabbar ba, har ta amsa sallamar tasa baiji ba saboda yayi nisa a kallonta, a hankali yake taku har ya shiga cikin dakin sosai ya zauna kusa da ita, a hankali ya kamo hannunta cikin nashi yace "Ya kike?" Ta sadda kanta kasa tace "Alhamdulillah my king." Murmushi ya su6uce masa yana kallon fuskarta yace "Naga bakici abinci ba a wurin taro nasan kina jin yunwa ko?" Ta girgiza kanta da sauri "A'a banaji, nasha fura." Yace "Kin tabbatar?" Ta gyada kai yace "Okay then bari na zuba maki koda yoghurt ne ki kara dashi." A cup ya zuba mata yoghurt din yasa ta shanye kafin ya gyara zama yana fuskantarta, "Welcome to the life of a queen Hoodah, na maki alkawarin cigaba da kula da ke iya karfina, zan cigaba da kokarin baki hakkinki kuma InshaAllah bazaki taba nadama ba a tare dani ba, zan cigaba da baki kulawa ta musamman har ki haihu lafiya," shiru yayi dan yayi catching numfashinsa kafin ya cigaba "I promise to be the king of my kingdom and also promise to be your king my queen, do you also promise to be the queen to my kingdom and the queen to my heart?" Ya tambaya fuskarsa dauke da murmushi ta gyada kai wani guntun kwalla na zubo mata daga idanu, hannu yasa ya share mata yana fadin "Duk kwallan da zaki zubda a gidana saidai ya zama na farin ciki InshaAllah." Hannunta ya kamo "Muje muyi wanka sai muzo mu kwanta ko?" Mikewa tayi har yanzu bata bar murmushi ba don ji take kamar wasu sababbin couples duk komai ya dawo mata sabo, bayan sun fito daga wankan suka kimtsa suka hau gado, dora mata kanta yayi bisa kirjinsa yana shafa gashinta a hankali take rufe idanu haka har bacci yayi awon gaba da ita. 

Washe gari maids suka hada masu ruwan zafi bayan sunyi wanka Sultan ya fara yi nan ya zauna jiranta parlor, shiru yaji nan ya tashi ya leka sai ganinta yayi ta kimtsa da sauri ya nufi dakinsa ya bude wardrobe dinsa ya dauko box dinnan ya koma daki, yana komawa dakinta ya nufeta da murmushi yace "Close your eyes my queen." Da hesitating tayi sai kuma ta rufe, gab da ita ya matsa ya bude box din ya jawo golden necklace dinnan sai shining take, sanya mata yayi sannan yace "Open your eyes now my queen." A hankali ta bude idanunta tana bin sarkar da kallo, kallonsa tayi ya sakar mata murmushi "You deserve it my queen, naki ne is all yours." Bata san lokacin da tayi hugging dinsa ba tana fadin "Thank you my king you are the best." Murmushi yayi yace "Ke nake jira mu wuce, and don't forget to put on your alkyabba please." Ta gyada kai tana murmushi daga haka ya fita ita kuma ta karasa sannan ta fito, hannunta ya kama suka fito waje nan guards suka fara kai masu gaisuwa da kirari. Da takun kasaita suka isa sashen su Ummi guards na biye dasu, Ummi suka gaida sannan suka zauna yin breakfsat, bayan sun kare suka mike don zuwa gaida Abbi. Message din Abba ya shigo wayar Hoodah ta bude tana murmushi yace "Assalamu Alaiki ya ke diyata, kiyi hakuri bansamu halarta taron da akayi ba na nadi ayi man afuwa wani abu ne ya tsaida ni amma InshaAllah zanyi tattaki har nan zanzo in tayaku murnar wannan abun alkhairin daya sameku, ki gaida Sultan da duk sauran mutanen gidan, Bissalam." Murmushi tayi tana kokarin maida kwallan dake neman zubo mata. Bayan sun gama suka fita Sultan har sashensu ya raka Hoodah sannan ya juya guards na biye dashi zuwa haraba, yau ce ranar farko da zai fara duty dinsa a matsayinsa na sarki....

Saturday, 24 July 2021

YAR AGADEZ PAGE 36

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 36}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com




A ranar Zarah kasa rintsawa tayi gaba daya abubuwan da suke faruwa ba karamin girgiza ta sukayi ba, wai mey ya shiga kan Khadija ne? Anya kuwa yar uwarta ce ta jini? Bata tunanin wanda suke fito ciki daya zaiyi mata haka, maganganun da Ashraf ya fada mata kafin ta kwanta ba karamin amfani sukayi mata ba, dan kuwa data samu tayi bacci da kyar tana farkawa da misalin karfe uku saura sai taji ranta ya saki sannan tana jin natsuwa cikin kirjinta, kasa komawa tayi sai kawai ta sauka daga kan gadon ta nufi bathroom ta dauro alwalla ta fito ta dinga jera nafilfili sai da data ji kiran sallar asuba sannan ta tashi tayi sallah bayan ta idar, tana nan har gari ya washe tangaram mikewa tayi ta kwanta nan da nan bacci yayi awon gaba da ita. Karfe goma da kusan rabi da farka, daga bisa bene ta tsaya cike da mamakin ganin gidan fes an share an goge sai kyalli yakeyi, galala take bin parlon da kallo, a sanyaye ta sauko kasa ta nufi kitchen mai aikinsu ce wacce ta tafi gida hutu ce ke tsaye tana goge cooker, da mamaki Zarah tace "Mama Hauwa!" Mama Hauwa ta juyo ta saki murmushi, da sauri Zarah ta nufeta ta makalkaleta cike da murna, Mama Hauwa mai aikinsu wacce kakarsu kafin ta rasu taba Mummy ita tun tana yar yarinya har ta girma ta mata aure, bayan an mata auren shekara da shekaru mijinta ya rasu ba tare da sun samu haihuwa ko daya ba, aikuwa bayan ta kare takaba shine Mummy ta sake daukarta tunda bawani shekaru gareta masu yawa ba, auren wuri akayi mata Mama Hauwa batada matsala ko kadan tana xaune dasu tsakani da Allah, ba karamin shakuwa Zarah tayi da ita ba, duk wata matsalarta tana fada ma Mama Hauwa da kuma shawarwari in ta kama, tunda Mummy bata cika zama ba tana harkar kasuwancinta bata ba yaranta enough attention yadda ya kamata, "Yaushe kika dawo Mama Hauwa?" Zarah ta tambayeta still tana rike da ita, Mama Hauwa tayi murmushi tace "Tun karfe takwas na iso, ina ta bubbugawa naji shiru har baba mai gadi ban gani ba? Ina yaje? Sai can naga wani bako ya fito daga bangaren Yasir ya zo ya bude man gate, tou shine ma yasa makulli ya bude man ta kitchen bayan na fada masa ko ni wacece, ina shigowa na hau aikace aikace, gida ba kowa babu Hajiya in ba Khadija data fito hada shayi da safe ba ashe tazo hutu? Na tambayeta kina ina tace bata sani ba." Zarah ta girgiza kai "Allah sarki Mama Hauwa ay bamuson zaki dawo yau ba, eh baki gane shi ba yaya Ashraf ne abokin Ya Yasir kin manta shi? Wai daga zuwa sai ki hau aiki Mama Hauwa bazaki ma ko huta ba keda kika sha hanya? Hmm wallahi baba mai gadi fa baya nan shima yayi wata tafiya gidan mu kadai ne Mummy ma basu nan sunyi tafiya amma gobe zasu dawo InshaAllah, aiko Khadija tazo hutun semester amma ta kusa komawa itama." Mama Hauwa tace "Ayyo tou babu damuwa, bari in karasa aikina." Daga haka ta cigaba da aikinta har ta kammala ta kwashi buckets da tsummanan ta fita zata wanke, karatun Qurani Zarah ta kunna tana bi tana girki, koda Mama Hauwa ta dawo zata kama mata ce mata tayi ta barshi kawai zata karasa taje ta huta, Zarah aikinta ta cigaba dayi a natse tana gamawa ta jera komai kan dining sannan ta shiga wanka. Tana fitowa daga wankan aka hau kwankwasa kofa gyara towel dinta tayi ta zumbula hijab har kasa sannan tace "Wanene?" Muryar Khadija taji tana fadin "Nice Zarah ki bude min kofa." Wani irin yawu ta hadiye mai daci kafin ta karasa bakin kofar ta bude mata, "Kin tashi kenan?" Abinda Khadija ta furta kenan tana yamitsa fuska kamar wacce ke tauna Panadol, sai  can kuma ta saki fuskarta tana murmushi, ita dai Zarah tsayawa tayi tana binta da kallo yadda take wani tauna chewing gum, kasa boye mamakinta tayi can tace "Na tashi, lafiya kike man knocking kofa kamar kin bani aiiya a ciki?"  Khadija tayi murmushi "Haba sis me yayi zafi haka? Nifa bada tashin hankali nazo maki ba, in fact nayi nadamar abinda na aikata maki nazo na baki hakuri, don Allah kiyi hakuri wallahi sharrin shaidan ne..."  Kasa magana Zarah tayi don ta kasa yadda da maganganun da tazo mata dasu, "Ya kikayi shiru? Baki yadda dani ba ko?" Zarah ta saki baki tana binta da kallon mamaki kafin ta ankare Khadija ta zube kasa tana zubda kwalla, abinka da mai taushin zuciya tuni Khadija ta bata tausayi hannunta ta kamo tana share mata hawaye, "Indai har kin tabbatar kinyi nadama ba ha'inci tou na yafe maki, Allah ya yafe mana gaba daya," Murmushi Khadija tayi sannan tayi hugging Zarah tana fadin "Alhamdulillah, nagode Zarah InshaAllah bazaki sake samun matsalar komai ba daga gareni," Zarah tayi murmushi "Bari na sa kaya sai muje ki ba Ashraf hakuri sannan sai muje muyi breakfast ko?" Tou tace kafin Zarah ta shiga daki ta kimtsa cikin wata material purple mai manyan flower irin mai madaurin nan a ciki, sai tasa hula hannunta Zarah ta kamo har side din Ashraf yana danne danne a laptop suka shigo, da da farko murmushi yayi ma Zarah sai da yaga Khadija tuni ya hade rai kamar bai taba dariya ba, karasawa sukayi ciki ya mike yana binsu da kallo kafin yace "Zarah me wannan take min cikin daki? Don't you know how much I hate her? Bana son ganin bakar fuskarta kamar yadda zuciyarta take baka!" Durkusawa Zarah tayi cikin taushin murya tace "Nasan abinda Khadija tayi bata kyauta ba tabbas, she hurt both of us kuma nasan ba lallai bane mu duka mu manta da abin farat daya, amma kuma Khadija tayi nadama ta bani hakuri ka dubi girman Allah ka yafe mata koba komai yar uwata ce kayi hakuri ni na riga na yafe mata, please mi amor." Ajiyar zuciya ya sauke a raunane yace "Zarah ko kare kika nemi alfarmarsa kisani zan saurare shi bare kuma kanwarki ta jini, na yafe mata kuma ina fatan tayi nadama har can kasan ranta." Khadija ta durkusa "Nagode sosai yaya Ashraf, Allah ya yafe mana gaba daya." Yace "Amin." Zarah tace "Kazo muje muyi breakfast." Yayi murmushi "Azumi nakeyi yau." Tace "Oh yau monday right?" Ya gyada kai "Kuje kuci abincinku dear." Murmushi tayi kafin su mike itada Khadija su fita daga dakin. 

Kan dining suka zauna Zarah ta bude kulolin abincin tana murmushi tace "Yaushe rabon dana girka wannan abincin ci kiji idan har yanzu na iya?" Ta fadi tana mika Khadija plate dinta tana murmushi wani dadi na ratsata yadda yar uwarta ta shiryu haka tashi daya "Ay bazaki manta yadda ake girkin nan ba Zarah, ni zanzo ma in fara daukar lesson very soon." Sukayi dariya gaba daya a haka suka cigaba da cin abincinsu cikin nishadi da annashuwa. ---

Washe gari babu abinda sukeyi sai gyaren gida saboda dawowar su Mummy, Zarah da Khadija gyara suke bil hakki kafin sha daya na safe sun tsabtaccen gidan sai kamshi ke tashi, Mama Hauwa tuni ta gyare kaji tas Zarah ta dora peppered chicken ita kuwa Khadija na hada Chinese fried rice. Ashraf kuwa yana gefe yana dura zobo da kunun aya cikin jugs da kwalabe, suna aikin suna fira. Mama Hauwa ta gyara kayan salad Zarah ta hada hadadden rich salad wurin sha biyu sun kammala komai sun jera bisa dining gida sai kamshi yake, wanka duk suka tafi sukayi suka shirya cikin atamfa wata sallah aka dinka masu ita iri daya kawai color ne ya bambanta, basu karasa shiri ba suka ji karar gate aikuwa da sauri suka fita a guje suka nufi waje ashe shi Ashraf ma har ya rigasu fita nan ya tarosu, suna fitowa daga motan sukayi hugging dinsu Mummy, Mama Hauwa ce ta fito itama tana "Lale lale dasu Hajiya, sannunku da zuwa sannunku da zuwa." Wani irin farin ciki Mummy taji na ganin Mama Hauwa, nan ta tarbesu cike da murna bayan an gama gaggaisawar yaushe gamo kafin kuma Mummy tasa a shigo da kaya ciki, wasu irin manya manya kwalaye ne aka dinga jida ana kaiwa ciki, akwati kam yafi kala hudu wanda aka shiga dasu, nan Khadija ta fahimci ay kayan kitchen ne Mummy ta siyo ma Zarah, a parlor suka baje ana fira Ashraf yace da Yasir "Gaskiya nayi fushi dakai Yasir, gaba daya ka tafi ka manta dani a nan ko?" Yasir yayi dariya "Ah haba wallahi Mummy ce ta tsaida ni ay ni da tuni na dawo ma," Ashraf yace "Tou ya hanya?" Yace "Alhamdulillah, tashi muje ka rakani na watsa ruwa." Daga haka suka mike suka fice Yasir yana dafe da shoulders din Ashraf. Mummy ta kalli yan matanta tace "Am sorry girls, wallahi wata hidima ta tsaida ni sheyasa ma ban dawo ba, wasu kaya na tsaya clearing da fatan dai babu wani matsala?" Zarah tace "Wallahi Mummy komai lafiya, wai wadannan uban kayan fa?" Mummy tace "Wallahi kayanki ne Fatimah, kinsan gara in rarrage wasu abubuwan don Yasir ya fada man Ashraf yace masa so yake da mun dawo yaje gida maganarku dashi, tou nasan dai bazai dau lokaci mai tsawo ba, tou sheyasa na rage kayan kitchen don gaskiya na siyo abubuwa da dama so nake mu zauna dake sai ki fadi man abubuwan da kikeso na kitchen sai a kara maki." Tunda Mummy ta fara magana gaban Khadija ke faduwa daurewa tayi ta kalalo murmushin dole, "Gaskiya kam Mummy haka yafi, tou ya kamata kuyi sallah ga abinci nan kuci." Mummy ta mike "Hakane har watsa ruwa zanyi, please ku kwaso kayannan ku kai man shi sama box room a jera su a ciki." Da toh suka amsa kafin su mike su fara tattara kayan suna kaiwa sama, ko kadan Khadija bata bari ta nuna wani abu ba ta danne. 

Suna kan dining suna cin abinci ne Mummy tace da Ashraf "Kayi hakuri Ashraf nasan kana so kaje gida na tsaida ka ko?" Yayi murmushi "Ba damuwa Mummy." Tace "Tou yaushe kakeso ka tafi?" Yace "Nan da kwana hudu haka zuwa biyar." Tace "Allah kaimu, da fatan dai yaran nan basu baka wata matsala ba ko?" Ya kalli Khadija wacce kanta ke kasa tana juya spoon, idanunsa na kanta yace "Ko kadan babu wata matsala, everything was okay." Mummy tace "Tou MashaAllah, ke kuma Khadija yaushe zaki koma school har yanzu hutun naku bai kare bane?" Ta dago kanta tace a sanyaye "Ya kusa karewa Mummy nan da 3 weeks." Mummy ta kalleta "Wai wannan hutun dai ya dade kin tabbatar baki kara kwanaki ba?" Ta girgiza kai da sauri "Ban kara ba Mummy." Mummy tace "Tou shikenan, Yasir ma sun daidaita da Hafsat InshaAllah ina sa ran hada bikinsa dana Ashraf gaba daya." Kowa na wurin yayi murmushi yana fadin MashaAllah, Allah ya tababtar da alkhairi mummy tace Ameen, da haka suka karasa cin abincinsu suna cigaba da fira. 

*________

"Idan har kinaso Ashraf ya soki sai kin kwantar da hankalinki kin daina tashin hankali kin jawo hankalinsa gareki cikin siyasa, dole fa ya fara sonki muna nan dake aure shida Zarah baza'ayi ba, da fatan kin fahimta?" Wannan shine shawarar da wata kawar Khadija ta bata a yayin data kai mata kukanta wata rana, tou shine fa taje ta bada hakuri ta nuna tayi nadama. Zaune take a restaurant tana jiran order din abinci, tuno da magaganun kawarta tayi tana tunanin hanyar da zata bi don jawo hankalin Ashraf gareta wani dan guntun murmushi ya subuce mata, wayarta ta dauko ta kirashi bai dauka ba, ta kuma kira a karo na biyu bai dauka ba fidda rai tayi nan ta zauna jugum, message ta tura masa kafin ta aje wayar aka kawo mata abincinta. Godiya tayi mata kafin ta gyara zama yadda zata ci abincinta, kamar daga sama taji muryarsa yana fadin "Khadija yane?" Ya fada tare da janyo kujerar dake gabanta ya zauna harda kiran mai abinci, Khadija bata san lokacin data sauke wata boyayyar ajiyar zuciya ba, kallonta yakeyi tana cin abincinta a natse  kafin yace "Naga sakonki na kina son ganina a lokacin da kika kirani ina masallaci sheyasa kikaga ban daga kiranki ba, tou yanzu ya akayi meyafaru? Meyasa kike son ganina a nan ba a gida ba?" Tayi murmushi "Hakane, dama ba wani abu bane kawai inaso ka bani shawara me zanba Zarah as a wedding gift? Sheyasa na kiraka a nan bana son tasani surprise zan mata sai ranar bikin she will be shocked!" Ya kalleta da sauri "What do you mean she will be shocked?" Ta gyara murya da sauri tana fadin "I mean wane irin gift zan bata da zataji dadi sosai?" Yace "Komai kikaga ya dace ki bata ki bata mana, gasu nan kala kala, ki siya mata ko mota, ko ki bata jirgi...." a daidai lokacin ne mai kawo mashi abinci ya kawo masa, bayan ya aje abinci ya tafi Khadija ta kalli Ashraf tace "Jirgi da mota? Ina naga kudin siyan wadannan abubuwan? Ka rufa man asiri yar karama dani." Yar dariya yayi ya fara cin abincinsa, "Wai yar karama dake kiji tsoron Allah Khadija, masu shekarunki a kauye suna can sun fara tara jikoki bama yaya ba." Hararar wasa ta mashi, yayi dariya yace "Zan fadawa Mummy gaskiya ya kamata a aurar dake a huta haka nan." Dariya tayi "Sai inga da abinda za'a aurar dani ay, badai siyen gida da kayan dake ciki ba in zauna, sai a jira na samu saurayi tukunna." Dariya ya kuma yi "Saurayin ma ay zaki samu very soon, yanzu dai maganar gift ki bata something special wanda zatayi appreciating ta kuma ji dadi sosai." Ta gyada kai "I will think about it InshaAllah, nagode da amsa kirana da kayi thank you very much." Koda suka gama cin abinci har titi ya rakata ya tsaida mata adadaita don shi yace mata ba gida zai je ba yanzu sai anjima zai dawo zaije yayi renewing passport nashi, yayi booking flight dinsa. Saida ya samu mai napep din ya kalleta yana fadin "Wannan murmushin dai sai ki adana ma wanda zaki aura don zai ji dadi sosai." Dariya tayi "Dole kam yaga murmushin nan mai tsada don shi kadai ya cancanta ya gani," daga haka ta shige shi kuma ya juya, da murmushi ta karasa gida zuciyarta fes, "A hankali a hankali dai." Ta furta cike da jin dadi. Wani irin farin ciki takeji yana ratsa ta kamar ta kira Sumayya ta fada mata sai kuma ta tuno da labarin zaifi dadi da ido bata waya ba sai ta hakura. A da tana ganin kamar bazatayi nasara ba amma sai daga baya ta fahimci yafi komai sauki, daga karshe ma da yamma garden ta koma da dan lemunta da snacks tanaci tana latsa waya, batasan da zuwan mutum ba saidai taga an daukar mata cookies guda daya, gabanta saida ya fadi tana dagowa taga Ashraf ne yana zaune gefenta da laptop a gabansa yana duba wasu boxes da zai siya na lefe yana so yayi order, bai kalleta ba idonsa na kan laptop ita kuwa kallonsa tayi na seconds kafin ta dauke idonta da sauri, sunfi minti sha biyar a haka karshe ma cup din da take shan juice din ya dauke ya maida gabansa, "Wai dan Allah meye haka? Idan kanason sha kasa a kawo maka naka mana ni ba bakuwar zafi bace kasan kawo maka zanyi ay." Da mamaki yake kallonta kafin yace "Maida wukar malama juice bazai hadani fada dake ba," cup din ya turo gefenta kafin ya dauko wayarsa yayi dialing yakai a kunne, yace "Dearie please kawo mun juice ina garden." Dayan bangaren tace "Wane iri?"  Ya karkato ya kalli wanda takesha kafin yace "Pineapple and coconut." Kallonsa take bako kyaftawa tace "Wai kana nufin baka san wasa ba?" Ko kallonta baiyi ba ya cigaba da abinda yakeyi ya hade fuska kamar bai taba dariya ba, "Wai kyamata kike da baki iya hada cup daya dani Khadija?" Cup din ta aje tana kallonsa "Yaushe mukayi haka dakai? Nifa wallahi ba haka nake nufi ba wallahi wasa nake maka." Kara hade rai yayi "Wasa ko? Nan gaba kuma ay zagina zakiyi Khadija." Juyowa tayi suna facing juna "Nifa ba kyamarka nake ba me kake nufi wai daga wasa don Allah?" Shiru yayi ya daga kai tare da hango Zarah tafe dauke da tray,  ya kalli Khadija "It's okay gashi nan an kawo mun nawa." Karasowa tayi tana murmushi ta aje tray din gefensa ta zauna, ta kalli Khadija "Halan rowa kikayi masa? Kedai kinji haushi wallahi." Ta karasa tana tsiyaya masa a cup sannan ta mika masa, "Kayi hakuri don Allah Khadija sai a hankali," Ashraf yace "Wai fada take dani akan ordinary juice." Zarah tayi murmushi "Ah Khadija Ashraf din yau ake fada dashi he's your friend now remember?" Khadija ta kakalo murmushi "Fada kuma? Wasa fa nake masa shine ya dau abin da zafi..." Wata irin dariya Ashraf yayi yana fadin "Rabu da ita mutum sai rowar tsiya." Khadija ta mike ta murguda baki ta yi gaba tana fadin "Kaidai kasani kaji dashi dai, ni karma ka kara nuna kasanni daga yanzu." Zarah ta fashe da dariya tace "Ah Khadija sai nazo biko gaskiya ayi hakuri!" Take itada Ashraf suka kyalkale da dariya, xama sukayi suna fira cike da nishadi yana nuna mata akwatinan da yakeso yayi order, runtse idonta tayi gam gam wai don kar ta kalla shi kuwa Ashraf yace "In baki kalla ba zakiga ana jide ghana must go a kofar parlor." Wata irin dariya ta kyalkyale dashi kafin ta mike tayi ciki da gudu, me Ashraf zaiyi in ba dariya ba?

Washe gari cousins dinsu Zarah su biyu kusan tsararraki ne sukazo daga Yemen, wani irin ihun murna sukayi cike da murnar ganinsu, daya ke sunfi shiri da Zarah a dakinta suka sauka haka suka baje suna firar yaushe rabo. Daren ranar bayan sunyi dinner suna dakin Zarah, gyara zama Raihan tayi tana kallon Zarah da guntun murmushi a fuskarta, "Wai ni Raihan bangane wannan murmushin da kikeyi tayi ba tun dazu wai meyafaru haka?" Dariya Raihan ta fashe dashi tana gyada mata kai, Ammah da kamar an kunna radio ta fara bata labarin su itada Ashraf ita kuwa Raihan dariya kawai takeyi, "Dan darajar Allah? Kai amma naji dadi wallahi bansan waye angon ba saida kika fadi man yanzu." Ammah tace "Dama na fada maki kiris ya rage bikin nasu wannan irin kauna haka?" Dukan wasa Zarah ta kai mata "Nifa wallahi banki ba a daura auren ba yau, keni wallahi..." kukan shagwaba tafara harda bubbuga kafa, Raihan da Amma suka kyalkyale da wata irin dariya, "Wayyo Allah diyar mutane ta afka kogi bari inje in fadawa Mummy karki lalace mana cikin gida." Wata irin janyowa tayi mata har saida ta fada kan gado "Ke dalla banza sharri zakiyi mani? Ni ba aure nakeso ba shi din dai nakeso." Dariya sukeyi ba kakkautawa harda tafawa "Yanzu dai tsaya aurenshi kikeso kiyi ko da gaske?" Amma ta tambaya tana murmushi, Gyaran murya Raihan tayi harda gyara zama, Zarah tace "Gaskiya kunga ko? Wallahi ina sonsa ni banma san ya akayi ba na fara sonsa haka ba, I think love at first sight." Ganin yadda tayi maganar da mahimmanci yasa suka girgiza kai suna kara bata attention, "Lokacin da ya Yasir yace zaizo da bako gidannan har haushi naji irin kawai sai yazo yayi mana zaune a gida, daga baya kuma naga yanada tausayi yanada kirki, da mutunci sosai tou nidai I don't know how it happened na fara sonsa, kuma alhamdulillah he loved me back and now we are getting married soon InshaAllah," fira suka cigaba dayi cike da nishadi kafin wayar Zarah ta fara ringing mikewa tayi tana murmushi ta nufi parlor tana rungume da throw pillow, "Ina wuniiii!" Kalmar taja cike da kwanciyar hankali, "Fadimatu na ya kike?" A shagwabe ta tabe baki yau ce ranar da farko daya kirata da fadimatu na, "Yau kuma Fadimatu na koma? Kuma baza'a amsa gaisuwata ba?" Yayi murmushi "A'a na isa? Lafiya Zarah ya kike ya yau?" Tace "Lafiya wai yanzu ka kusa tafiya ka barni ko? Gaskiya zanyi missing dinka sosai." Yace "I will miss you more dearie... kuma ay ba dadewa zanyi ba zan dawo, kinga dana dawo sai ayi maganar aurenmu ko?" Khadija ce taga ta fito daga kitchen kamar daga sama, wani irin tsoro Zarah taji da taga mutum batayi zaton akwai kowa kitchen ba don bataji alamu ba, batasan lokacin data latse wayar ba ta mike jikinta na bari, "Zarah nice fa, wai tsoro na baki?" Zarah ta wani saki ajiyar zuciya tana sauke numfashi "Wallahi naji tsoro dama kina ciki shine banji motsinki ba? Kina tafiya sai sahun taku kawai akeji kuma dare yayi sosai." Dariya tayi tana sosa kai "Tou kiyi hakuri kina waya na baki tsoro, ku cigaba da soyewa amma fa karku kone." Tana gama fadan haka ta wuce sama kamar zata fashe da kuka.




Da fatan kowa yayi sallah lafiya? Tou Allah ya maimaita mana amin.🥰🥰i

Wednesday, 7 July 2021

YAR AGADEZ PAGE 35

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 35}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com



Wannan page din naku ne my pipu, Faty Mansur, Maryam Mansur, Farida Bature, Hafsat Bashir, Ayshat Fareedat and Nana Aisha❤️❤️❤️🤝🤝your comments always keep me going thank you 🥰👌



Kamar wata mahaukaciya haka ta nufi inda take aje magunguna, zazzago su tayi ta fara bincike idanunta kuwa jajir kamar wata zombie, cin karo tayi da wani maganin bacci dauko shi tayi da sauri tana karantawa, da azama ta mike ta leka parlor nan taga Ashraf kwance bacci yana fizgarsa sama sama, dakinsa taje cikin sa'a ta iske ya aje ruwa wanda ya fara sha a bottle da cup a gefe, da sauri ta bude bottle water din ta jefa tablet kusan guda biyar a ciki sai data tabbatar yayi diluting a ciki ta kara shaking kwalbar, rufewa tayi dasauri ta fito bayan wata kujera ta buya yadda ba'a ganinta, tafi minti 20 a nan sai can taji alamun shigowarsa, leke ta fara yi taga ya sa kai cikin dakin ya shiga, da rarrafe ta fito a hankali ta tsaya wurin kofa daga baya baya tana leken abinda yakeyi, gefen gado taga ya zauna yana latse latse a waya, yafi minti goma a haka kafin ya kishinga kan gadon, komai yagani kuma sai ya mike zaune ya bude ruwan nan ya zuba half cup ya kafa kai yana sha, shidai har sai daya gama shan ruwan nan sai yaji taste dinsa ya chanza, har yana tunanin kodai bakinsa ne? Juya cup din yakeyi kafin ya aje shi, can kuma yamike ya shiga bathroom, yana fitowa sai ji yayi kansa ya sara masa idanunsa na ganin biyu biyu, dafe kai yayi yana jin dakin na juya masa da kyar ya iso bakin gado da kyar yake gani sai faman bude idanunsa yake forcefully amma ina kafin kace me ya zube kan gado, Khadija na ganin haka ta mike da sauri ta shigo dakin ta rufe kofar, tsaye tayi bakin kofa tana harde hannuwa, "Yau ce ranar da Zarah zata fara tsanarka a duniya, today will mark the end of your relationship, and beginning to ours my dear Ashraf." Smirking tayi ta fara takowa inda yake kafin ta fara unbuttoning masa riga, ta window take leke bayan kusan minti sha biyar sai ganin Zarah tayi ta shigo gidan, sauri tayi ta gyara masa kwanciya kafin ta yaga rigarta, gashin kanta tayi squeezing duk ya watse kamar wata sabuwar mahaukaciya ta haye gadon tana murmushin mugunta. 

Zarah na shiga side dinsu direct dakinta ta nufa, ta cire hijab dinta ta saka wayanta charge sannan ta fada bathroom don yin alwala ganin lokacin sallar azahar har ya dan gota, bayan ta fito tayi sallah tayi addu'ointa ta mike ta linke prayer mat din da hijab din ta aje su inda suke, fita tayi ta sauka kasa kitchen ta shiga tace bari kawai ta dafa spaghetti tunda sunada miya cikin fridge inta dafa sai ta kai ma Ashraf nasa daki ko kuma tunda ta lura yafison zaman dining yanxu sai taje ta kirashi yaci a nan, a natse take aikinta tana tunanin ko yaushe ya Yasir zai dawo daga Abuja shida Mummy? Don ta kirasu jiya suka ce mata har yanzu basu sa date din dawowa ba, da wannan tunanin ta kammala aikinta ta gyara kitchen din, dining taje tayi arranging tana murmushi kafin ta nufi 6angaren su Ashraf, tana shiga parlor din ta fara takawa ciki ta jiyo wani irin ihu har saida ta firgita, tsayawa tayi ko zata kara jin ihun kodai kunnenta ne ya jiye mata ba daidai ba? Kara jin wani ihun tayi wanda yafi na dazu, a tsorace ta fara takawa dakin dafe da kirji har ta isa bakin dakin ta kasa shiga, ita kuwa Khadija dama saida ta tabbatar ta taho side din kawai sai jawo Ashraf tayi ta rike masa wuyan riga, wannan ihun nata shi ya tashe sa yana ganinta ya razana ya fara kokarin kwace kansa ita kuwa ta kama rigarsa gam gam ta rike, jin yadda ihun ke fita kamar na Khadija ay Zarah batasan lokacin data murda kofar ba ta shiga ciki, wata irin mutuwar tsaye Zarah tayi, batasan lokacin data saki tray din juice din data dauko masa ba da cup duk suka watse kasa, tsayawa tayi cak bata kwakkwaran motsi, jikinta har wani rawa yakeyi har hannuwanta da kafafuwanta, ji take kamar an soka mata wuka a kirji, makoshinta kuwa bayan bugawar da yakeyi har ji takeyi kamar zai shige cikin kirjinta, hawaye kuwa kamar an bude pampo, ita kuwa Khadija ta rike masa riga tana ihu tana ganin Zarah sai ta sake shi taja gefe ta rakube tanata kuka, shi kuwa Ashraf yana ganinta ya mike tsaye a razane yana girgiza kai, ji yake kamar zuciyarsa zata bar kirjinsa, matsowa yayi dab da ita yana ta faman girgiza kai, "Is not what you think...."  Zarah wani irin wawan ihu ta kurma tana gunjin kuka "Dont come near me Ashraf," nuna kanta takeyi jikinta na 6ari tace "Kanwata Ashraf? Khadija is my sister dama ashe son karya kake man? Innalillahi wa inna ilahir rajioon..." ta fara ambata tana masa wani irin kallo, kwatanta yanayin da Ashraf ya shiga ma bata baki ne, ba abinda bakinsa ke furtawa illa "Is not what you think, ban san ya akayi haka ta faru ba...."  kuka yake wiwi ji yayi ya nemi numfashinsa ya rasa gaba daya hankalinshi ya gushe, Zarah toshe bakinta tayi da hannunta kafin ta juya ta fita daga dakin a guje, zubewa yayi kasa hawaye masu zafi na sauko masa, ji yayi zuciyarsa na masa wani masifaffen radadi da ciwo, this is the worse day of his life, mikewa yayi yana ma Khadija wani irin mugun kallo, ji yayi bai taba tsanar mutum a duniya ba kamar yadda ya tsani Khadija, she's heartless and selfish gaba daya karfinsa yasa ya damki Khadija, batayi arba ba taji wani irin masifaffen mari a kumatunta har ji tayi kunnenta yayi dif, kara mata wani yayi a dayan kuncin nan ta fara ihu tana kokarin kwace kanta amma ta kasa, wata irin azaba ce ta rufe fuskarta don wani irin naushi ya kai mata a hanci, wani irin ihu ta saki ta fara kukan fitar hankali, "Ashe dama ke muguwa ce makira bansani ba? Nace maki bana sonki bana kaunar ki, tsanar da nake miki a da ta linka sau dubu, I hate you!" Yana gaman fadan haka ya damko hannunta har akaifa yasa mata nan taji wani zafi ya shigeta, a haka ya dinga janta daga cikin dakin yana fita waje yayi jifa da ita nan ta fadi kasa ta bige kai, nan fuskarshi ta koma ja jijiyoyin wuyansa suka firfito waje zuciyarsa sai tafasa takeyi, ita kuwa Khadija tsoro ne ya shige ta bata taba ganinshi haka ba, nan tsoro da fargaba suka dirar mata, mikewa tayi da niyyar guduwa ya wani damko ta, "Where do you think you're going? Babu inda zakije sai kin fada min abinda kika zuba man nasha." Dukanta yake kamar Allah ya aiko shi jikinta yayi rudu rudu, ihu kawai take kurmawa fuskarta duk ta kumbura, damko ta yayi fuskarshi na wani shaking "Zakiyi magana ko sai na kasheki?" Wani irin dagata yayi ta fara shure shure, dagata yayi zai cillota kasa ta fasa wata irin razananniyar kara tana fadin "Zan fada maka na tuba, kayi hakuri don Allah don annabi, kar ka wullani!" Saukota yayi tare da damke gashin kanta "tell me now!" Kyarma ta fara yi tace "I drugged you, amma wallahi nayi ne saboda ka rabu da Zarah, I want you all to myself!" Wasu marukan ya sauke mata a kuncinta hagu da dama kafin ya fara dragging dinta har side din nasu... 

A 6angaren Zarah kuwa jikinta babu kwari tayo cikin gida. Saidai ta tsinci kanta cikin dakinta zaune akan gado, bata ma san ya akayi ta iso ba tsabar bata cikin hayyacinta, wani irin tukukin bakin ciki ke cinta cikin ranta, hawayen ma sun kasa daina zuba daga idanunta kuka takeyi kamar ranta zai fita, kanta ya fara mata ciwo tsabar kukan da takeyi ba sassauci, data tuno Image din Khadija da Ashraf sai ta sake rushewa da kuka, tana zaune sai ji tayi an banko kofar da karfin bala'i, jajayen idanunta ta daga masu digar hawaye tana kare masu kallo, a tsorace take kallon Khadija ganin kammaninta sun chanza, Ashraf kuwa kamar bashi ba idanunsa sunyi jajir fuskarshi ma haka, tunkud'o ta yayi ta fado gefen Zarah ji kake tim, karasowa yayi cikin dakin ya silale kasa ya kamo rigar Zarah, ganin haka yasa Zarah ta mike da sauri tana sauke numfashi, fizge kafarta tayi wasu hawayen na sake zubo mata nuna shi take da yatsa har wani kyarma takeyi tace "How dare you come into my room Ashraf? Ka fita! Ka fita nace!" Ta kurma wani uban ihu a gigice ya mike idanunsa na fitar da kwalla, "Can't you see? Khadija tayi planning don ta rabamu kin manta sona takeyi? And she can go to any length ta raba mu, wallahi tallahi bansan ya akayi haka ta faru dani ba, I think she drugged me Zarah," Takawa bakin gadon yayi ya finciko Khadija da jini duk ya bushe mata a fuska, gaban Zarah ya wullota har sai data hade da Zarah, ture ta Zarah tayi tare da matsawa baya, Ashraf yace "Ki fada mata! Kifada mata abinda kikayi tell her is not my fault, ke kikayi drugging dina tell her what you just told me outside!" Shiru Khadija tayi nan Zarah ta kure ta da idanu Khadija kuwa ta kasa furta koda kalma daya ce, can ta shiga girgiza kai tana hawaye "Haba Ashraf! What do you think of me? Yes ina sonka amma bazan taba stooping so low ba haka, believe me Zarah ba abinda na aikata..." matsowa tayi kusa da ita tana girgiza kai kamar ta kirki tana sunkuyar da kanta kasa, "Bayan kin tafi sai ya ce min na kawo masa ruwa, ba tare da tunanin komai ba na tafi kai masa ashe kuma yanada mummunar manufa akaina," ta fada tare da rushewa da kuka, Ashraf kallonta yakeyi in shock not able to believe his ears. Ba zato ba tsammani sai jin hannun Zarah Khadija bisa kuncinta, a razane ta dago tana kallon Zarah dafe da kunci, kafin Zarah ta fara magana a fusace "Karya kike makaryaciya! Khadija na tabbatar zakiyi abinda yafi haka ma don ki kwaci Ashraf a hannuna! Amma kisani my love for him is pure and I believe what he just told me..." ta karasa tana kallon Ashraf, cak Ashraf ya tsaya yana kallonta baki sake, wani irin farin ciki ne yaji marar misali, kirjin Khadija wani irin bugawa yayi... Dariyar jin dadi Ashraf ya saki irin dariya sosai dinnan kafin ya matso daf da Khadija "Alhamdulillah naji dadi da Zarah ta yarda dani you are nothing but evil, selfish and heartless! You tried to separate us but your plan has failed! Khadija na tsane ki tsana mafi muni! Ban taba jin na tsani mace ba kamar yadda na tsane ki Khadija! Kuma wallahi komai zakiyi bazan taba sonki ba bazan kuma aure ki ba," Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon Zarah, "Zarah ina sonki son da ban taba yi ma wata ya mace a duniya ba! Bazan taba iya cutar da ke ba, bazan taba iya jefa ki cikin ko wane  irin mugun hali ba, baxan taba so na zama sanadin zubar hawayenki ba, bazan so in ganki cikin bakin ciki ba ko yaya yake, I respect women alot burina bai wuce na saki farin ciki ba, da kika gudu daga side dinmu na tsorata a tunanina shikenan zaki tsaneni ashe ba haka bane, ban taba haduwa da mace mai saurin fahimta ba kamar ke, I will never forget yardarki agareni, thank you so much Zarah..." bazan iya kwatanta maku irin kallon da yake mata ba a yayin da yake fada mata wadannan kalaman, gaba daya jikin Zarah ya mutu baki sake take kallonsa tsabar yadda yake furtar kalamansa with pure sincerity, Khadija kuwa tsabar bakin ciki ma fita tayi daga dakin don ji take bata taba yin abu yayi failing ba kamar yau, murmushi Zarah tayi tana share hawayen farin ciki kafin tace "Koda kaga na bar side dinku zafin abinda nagani ne da kishi ba komai ba, amma na yarda dakai nasan bazaka taba cin amanata ba," Shiru yayi cike da farin ciki, yana kallonta, kallonta yakeyi cike da so da kauna kafin ya juya ya fita daga dakin yana murmushi, ya fita parlor daidai kofar fita yaji an damko masa hannu, juyowa yayi yana binta da kallon tsana, wani irin wawan mari ya dauke ta dashi har sai da sawun hannunsa suka bayyana saman kuncinta, nunata yake da yatsa kafin yace "Ki fita daga harkata babu ruwanki dani! Kuma kar ki sake tabani daga yau, if not sai na yanke hannuwanki." Muryarshi har wani rawa takeyi sannan ya tunkudeta ta fada kan kujera, kafin ya juya a fusace ya bar parlon....




Kuyi hakuri da wannan ba charge nepa sunki kawo mana wuta kuma😂❤️🤝

Monday, 5 July 2021

YAR AGADEZ PAGE 34

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 34}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com




Da asuba Sultan yana tashi yaga babu Hoodah a kan gado wani irin yawu ya hadiye don a tunaninshi har ma tayi tafiyarta, yanzu duk magiyar da yake bazata hakura ba? Masallaci ya wuce yayi sallah hade da azkhar kafin yayi karatun qurani, sai wajen 7:30 ya dawo, yana shigowa yaga Hoodah a kitchen tana hada breakfast a hankali ya shiga kitchen din yana gyaran murya hakan yasa ta juyo, "Good morning habibty." Ya fada yana jingina da counter din kitchen din, kallo daya ta masa ta kauda fuska, can kasan makoshinta ta amsa "Morning." Sannan ta cigaba da abinda takeyi, kallonta yakeyi har ta kammala aikinta taimaka mata yayi suka fara jera abincin kan dining, Sultan debar abincin yayi ya tafi parlor ya zauna Hoodah ta bishi da kallo sannan ta tabe baki, bayan sun gama kawai sai yaje dining din ya jawo hannunta, "Meyafaru ka jawoni nan parlorn ina xaman xama?" Kallonta yakeyi kafin ya numfasa "Yanzu ke Hoodah tsabar rashin yarda da kaddara ta kai haka? Wai meke damunki? Tou ko Ammi tana raye babu abinda takeso face taga jikokinta ballantana mu da muke son ganin jininta, yanzu ke butulci zaki ma Allah bayan ya baki kyautar da ba kowa yake bamawa ba? Wasu fa da kudi suke zuwa kasashen waje nema basu samu, wasu kuma kullum cikin kuka suke don dai kawai Allah ya basu amma basu samu ba, wasu kuwa shekara da shekaru da aure babu haihuwa sai ke don ya baki kike neman ki butulce masa? Shin Hoodah hankalinki daya kuwa? Kuma da kike cewa zakibi Abba in kin haihu zaki maido man baby shin da wane ido xaki kalli babyn in ya girma? Kice kin rabu da mahaifinsa saboda baki yarda da kaddara ba ko kuwa akan wane dalili? Tsakani da Allah ki chanza tunani, na biki na roke ki na lallashe ki amma duk a banza haba Hoodah? Bai kamata kina bari shaidan yana cin galaba a kanki ba har ki dinga furta man irin wadannan munanan kalamai ina mijinki kice wai xaki zubar da ciki, yo ko dan shege ne ay babu kyau zubarwa bare kuma dan sunna," Hoodah har hawaye sun fara kawo mata a idanunta tace "Nidai tou ina so inje koda kwana biyu ne m wurin Abbana." Sai hawaye shar shar, Sultan ya gyada kai "Ay dama bawanda zai hana ki zuwa wurin Abba, amma yanzu fisbailillahi bakiiji wa'azin dana gama yi maki ba Hoodah? Kiyi hakuri mana babu kyau abubuwan da kikeyi." Kamo hannunsa tayi "Wallahi naji don Allah dan annabi kayi hakuri, wallahi sharrin shaidan ne da kuma fargaba, hakan bazata sake faruwa ba na yarda zan haihu wallahi kayi hakuri, please call Abba na bashi hakuri akan ya janye batun kishiyar nan." Murmushi yayi kafin ya miko mata waya ta ansa tana share hawaye kafin ta danna call, bayan ya dauka suka gaisa sai tace "Abba don Allah kayi hakuri wallahi na gane kuskure na, bazan sake zancen xubda ciki ba, na yarda zan haihu wallahi sharrin shaidan ne don Allah kayi hakuri, ka yafe man sannan ka janye batun karin aurennan." Abba matse speaker din yayi ya saki dariya sosai kafin ya maida ya daure fuska "Ke yanzu kina tunanin wannan dan rokon da kikayi man yasa zan chanza maganata? Abinda har nayi magana da shi abokin nawa akan batun yarsa, aiko aure babu fashi ba dai taurin kai ba tou na fiki iyawa." Sultan ya kalli Hoodah ganin tashin hankalin dake kan fuskarta, karbar wayar yayi yasa a speaker sannan yace "Abba don Allah tace kayi hakuri, ta gane kuskurenta har yanzu baka hakura ba? Kaifa kace mana hakuri shine ginshikin zaman duniya." Ya fada kamar zai fashe da kuka, ji yayi Hoodah ta kamo hannunsa alamun yayi shiru, "Kai Sultan kasan Allah? Ka kiyayeni ni, nafa riga na gama magana har abokina na masa maganar auren, duk waya jawo? Ashe haka kake malalaci wato kai har nema mata yafiya kakeyi ko? Aure dai nace babu fashi," yafada on a serious note, tuni jikinsu yayi sanyi, wani daci ne ya ziyarci zuciyarta, "Don Allah Abba kayi hakuri." Ta fada cikin sheshekar kuka, kuka take tamkar ranta zai bar jikinta har tsoro taba Sultan wanda don dole ya tashi ya tafi kitchen don kawo mata ruwa, babu musu ta karba ta sha, tana gama sha ta fada jikinshi hade da aje wayar gefe tana wani irin kuka, babu abinda yake mata dadi a zuciyarta wani daci takeji har kasan ranta. Rocking dinsu yake a hankali "Kiyi shiru don Allah Hoodah, ko kinaso wani abu ya samu babynmu?" Ya tambaya kamar zaiyi kuka yana kara riketa gam, cikin sheshekar kuka ta fara magana "Sultan wallahi nayi nadama bazan sake ba, kaba Abba hakuri yayi hakuri ya janye maganarshi, wallahi sharrin shaidan ne da kuma tsoro gudun abinda ya faru da Ammi ya faru a kaina, amma yanzu nayi nadama kuyi hakuri." Sultan da kyar ya iya saita kanshi "Hoodah kiyi shiru ki bar kuka, na tabbatar ya yafe maki, wannan kukan bashi bane zai maki magani..." kafin ya rufe baki sai jin muryar Abba sukayi ta cikin waya "Hoodah ki saurareni kina jina?" Har kyarma take ta dauko wayar ta rike suna saurarensa, yayi murmushi "Alhamdulillah ala kulli halin da kikayi realizing wannan babban kuskuren da kike neman ki tafka, amma tunda kin gano kuskurenki na yafe maki komai ya wuce indai har kin tabbatar da kinyi nadama ta gaskiya shikenan maganar ta wuce, na fasa maganar auren, abinda xan fada miki shine ki kula sannan ki kiyaye kinajina? Ita rayuwa da kike ganinta komai rubuce yake sannan kowa da kaddararsa, dan haka ki bi mijin ki Hoodah Allah yayi maku albarka," yana gama fadan haka ya kashe waye yana murmushi,  wani irin farin ciki ne marar misaltuwa ya ziyarce su, fadin ma farin cikinsu bata baki ne, haka sukayita ihun murna cike da jin dadi da annashuwa, Sultan ta kamo ma  hannu tace "Bansan da wane baki xan gode maka ba, hakika na zama butulu da ace na zubar da cikinnan, nayi rayuwar gata hade da kunci da bakin cikin rayuwa, rayuwa ce wadda babu digon farin ciki a cikinta, banason abinda zan haifa ya dandani koda rabin abinda na dandana, I can vividly still see my mother on the floor jikinta gewaye da jini, gaba daya floor wall duk jininta ne," zuwa yanzu ji take zuciyarta ta kafe da sauri Sultan ya debo mata wani ruwan tasha, bai ce mata kala ba don shima yayi experiencing kusan abinda tagani ta kuma taji, a hankali ya jawo ta yayi hugging "Say no more Hoodah say no more...." hugging dinsa tayi back kafin ta lumshe idanu tana murmushi "Thank you Sultan I love you." Wani kayataccen murmushi ya saki zuciyarsa cike da farin ciki yace "I love you more Habibty na, Allah ya sauke ki lafiya." 

*****

Kallonsa take gabanta na duka tara tara, a lokacin kuma taji zuciyarta tamkar wuta take ruruwa a ciki, kallonta yake a natse take ta sadda kanta kasa tari ne ta sarke ta da sauri ya mika mata cup din ruwa tasha, "Zarah menene?" Ya tambaya yana kallonta saida ta tabbatar natsuwarta ta dawo sannan ta fara magana "Ni ka daina kallona ko so kake na kara kwarewa?" A dan masife tayi maganar dan ita har ga Allah idan ya kalleta zuciyarta bugawa takeyi, yar dariya yayi yana nuna mata abincin dake gabanta, da kamar bazataci ba sai kuma ta fara gyara wurin, tasan jira yake ta zuba masa shiru tayi jin ya fara magana "Yau kuma bazaki zuba min ba?" Ay bata jira ya ida magana ba sai tace "Nan ma gidanku ne ko? Kai zakayi serving kanka ko a kira maka Khadija idan baka iyawa?" Da sauri ya mike yasan kishi ne ke dawainiya da ita yasa yace "Bai kai haka ba baiwar Allah." Tana kallonshi ya gama zuba masu abincin a hankali ta fara ci shima haka, kamar daga sama taji takun Khadija ta taho hannunta dauke da cup din dessert, fuskarta dauke da kyakkywan murmushi ta karaso cikin wani matsiyacin lace maroon color dinkin fitted gown, ba abinda ke tashi sai kamshi, ido suka zuba mata har ta karaso yadda kukasan zata tafi dinner wannan kwalliyar datayi, cream caramel din da yayi mugun kyau ta aje gaban Ashraf tana kallonsa sannan ta zauna gefensa tana ma Zarah wani irin kallo, tace "Ya zaki kawo masa abinci babu dessert? Haka ake kula da saurayi ke kuwa baiwar Allah? Yaya Ashraf idan ka gama cin abincin gashi na maka da kaina na hada maka please kasha." Ko kallonta baiyi ba ya kalli Zarah "Kamar naga akwai ice cream a freezer ko?" Ta gyada kai a sanyaye yace "Jeki kawo min zansha," ya kalli Khadija data zama speechless yace "Sorry am not interested in your dessert, zaki iya zuwa kisha kayanki, thank you."  Hawayen data rike ne sukayi nasarar saukowa nan take ta fashe da kuka kamar ranta zai fito, baki sake Ashraf yake kallonta "Khadija ya da kuka kuma? Lafiya dai ko?" Ya fada yana kokarin tashi tsaye, girgixa kai amma ta kasa magana karshe ma kukan nema yake yaci karfinta, tsaye yayi in shock yana mata kallon irin lafiya dinnan? "Abinda na fada ne ya bata maki rai?" Girgiza kai tayi tana kara fashewa da wani sabon kukan "Yaya Ashraf soyayyarka taci karfina, wannan rejecting na abinda na kawo maka ba karamin impact yayi ma zuciyata ba, yaya Ashraf ina sonka wallahi tallahi ina sonka, bansan ya zanyi da raina ba..." ta kifa kanta bisa table tana shesheka kamar zata shide, turus yayi yana kallonta, in baccin yaga hawaye da sai yace she's trying to get his attention, da kyar ya samu ya furta "Am sorry Khadija, hakuri zakiyi ki cireni daga ranki, Am in love with your sister Zarah, I love her with every part of my being, bazan iya maki karya ba Khadija karan kanki kinsan a addinin musulmi haramun ne! Dole zaki cire ni aranki I belong to somehow else...."  Girgiza mashi kai tayi tana kukan fitar hankali kafin tace "Nasani, amma ka duba girman Allah ka tausaya min, ko yanzu da kake fada man wannan kalaman ji nake kamar ruwan zafi ne ake yayaffa mun, ka taimaka man kar sonka ya kasheni..." Zarah ce ta karaso zuciyarta na tafasa gadan gadan tayo kan Khadija kamar zaki tana fadin "Ko zaki mutu saidai ki mutu! Amma wallahi Ashraf ya maki nisan da bazaki iya kamo sa ba, wannan wane irin abu ne haka? Tou wallahi baki isa ba Khadija! I told you times without number abinda kikeyi ba daidai bane, you're trying to come between two lovers that are madly in love with each other! Enough is enough na gaji! Na baki last warning ki fita harkarsa a gidannan in ba so kike nida ke a kwashi gawar daya tsakani da ke ba!" Tana gama fadan haka ta ruga da gudu tayi waje tana fita ta zube a nan ta fashe da wani irin kuka tamkar ranta zai fita, da sauri Ashraf yabi bayanta bayan yayi ma Khadija wani irin mugun kallo, har ya juya zai fita yaji Khadija ta wani damke masa hannu kallonta yake zuciyarsa na tafarfasa kafin ya fizge hannun nasa ya fita nan ya barta tsaye hawaye nabin kuncinta, yana fita ya iske Zarah zube kasa tana kukan fitar rai, wani irin tausayinta yakeji da sauri ya duka inda take tana ganinsa ta kara sa kuka sosai zuciyarta kamar zata bar kirjinta, "Yaya Ashraf ka aureni kona huta da wannan bakin cikin da Khadija ke kunsa man! Just let's get married da munyi aure shikenan zata hakura ta kyale mu..." gyada kai yayi ya fiddo hanky ya fara goge mata hawaye, "Zan aure ki Zarah, jira nake Mummy ta dawo in fada mata zan tafi gida daga nan zan turo da manyana, kinji? Ki kwantar da hankali ita Khadija ta isa ta aure ni ne? Ba ni ne namiji ba? Ke zan aura InshaAllah tashi muje ki wanke fuskarki a tap." Mikewa tayi bayan ta gyada kai kamar wata karamar yarinya sannan ya rakata ta wanko fuskarta ta, sadda suka koma ciki Khadija bata nan, dining suka nufa ya sake zuba masu wani abincin, bayan ya gama yace "Ki daure kici abinci." Murmushi tayi masa a haka suka cin abincin har suka kammala.

Can cikin dare da misalin karfe biyu na dare sai wayar Ashraf ta fara ruri, a firgice ya bude ido yana mai jawo wayar tasa daga kan bed side, kasa gane number din yayi ba tare da tunanin komai ba ya kara a kunne, "Hello yaya Ashraf! Da fatan ban tashe ka a bacci ba ko?" Da mamaki yake saurarenta har wani faduwa gabansa keyi wai wannan wace irin mayyar yarinya ce? "Da alama bacci kakeyi na tashe ka ko?" Daure fuska yayi tamau yace "Lafiya kike kirana Khadija da tsohon daren nan? What's wrong with you?" Wata makirar murmushi ta saki cike da salo na kwarewa gamida yaudara tace "La kayi hakuri yaya Ashraf naga miss call dinka ne da wannan layin nawa shine ma nake ta mamaki nasan ba kowa yake da layin ba sai special people kadai," ta karasa tana murmushi, "Ni na kiraki da wannan layin? You must be mistaken, ni ban taba kiranki da original layinki ba bare wani special line, look duk wani salo na yaudara da kike son ki tsiro dashi bazan taba fadawa ba no matter what you do, nasan irinku sarai mayaudara masu kwacen saurayi gorrit?" Maimakon ta bata rai sai ta saki murmushin yaudara "Ayya kayi hakuri idan na bata maka rai is not my intention, toum bari dai na barka kayi baccinka kar na cika ka da surutu, good night!" Kit ta kashe wayar ta bar Ashraf sagale da waya a kunne, wannan abun na Khadija sai anzo an fara taimaka mata da addu'a ta fara hauka ne, kwanciya yayi cike da tunani kala kala a haka bacci yayi awon gaba dashi. Da safe tun karfe bakwai na safe Khadija ta tashi tayi wanka ta shirya cikin wani baggy trouser sai wata yar ficit din riga marar hannu sosai, hada hada takeyi a kitchen tana kokarin kammalawa da sauri, saida ta tabbatar ta hada komai saman tray kawai sai ta nufi bangaren nasu tana zuwa ko knocking batayi ba ta fada ciki, Allah ya rufa masa asiri ma ya kammala sanya kayansa yana balle ma6alli, a razane ya dago yana kare mata kallo zuciyarsa na tafasa, a fusace yace "Wai ke wace irin dabba ce? Ke a gidanku ba'a koya miki sallama bane da zaki fado min cikin daki sai kace ajiya kika bani?" Murmushi ta saki ta karaso ta aje abincin sannan tace "Kayi hakuri don Allah nayi sallama maybe baka ji bane, am so sorry please, Dama breakfast na kawo maka naga Zarah kullum ita ke faman dawainiya da kai shine nace bari na taimaka mata yau ta huta..." daga mata hannu yayi "Wallahi ko zan mutu da yunwa bazanci abincinnan ba, don haka maza maza zo ki dauka ki fita dashi."  Bata ce komai ta tsugunna ta fara masa serving abincin sai da ta gama ta taso dab da dashi ta mika masa plate din tana binsa da kallo daga sama har kasa, tace "Kayi hakuri kaci don Allah, I made it with love and care..." kafin ta karasa magana sai ji tayi ya kifar mata da plate din saman riga wanda a sanadin haka duk ta bace da sauce ga zafi dama, wani uban ihu ta kurma, hannunta ya damko ya shiga dragging dinta kamar zai tashi sama saida ya fita daga side din kwata kwata sannan ya cillata yana mata kallon tsana, "Bana sonki bana kaunarki! Kuma daga yau na sake ganin kin shiga harkata a gidannan wallahi sai kinsha mamaki ki fita hanyata for the last time! And kafin na dawo make sure you clean that mess up or else..." ya matso dab da ita fuska daure yace "I will deal you in this house!" Yana gama fadan haka yasa kai ya fita kamar zai tashi sama nan ta bishi da kallo zuciyarta na tafasa kamar ta bar kirjinta. 

Ciki ya koma nan ya tarar da Zarah har ta kammala breakfast tana faman hada masa a tray, sautin murmushinsa kawai taji shi ya tabbatar mata da isowarsa, "Basai kin kai min daki ba a kan dining kawai zanci." Juyowa tayi, tayi murmushi sannan ta nufi dining ta kai ta jera komai, zama sukayi Zarah tace "Ina kwana? Halan yanzu ka tashi daga bacci?" Yayi murmushi yana tsiyaya ruwan zafi cikin cup ya dan dakata yana kallonta cike da so da kauna "Waya fada maki yanzu na tashi?  Ay tun asuba yau ban koma bacci ba..." itama murmushin ta maida masa kafin tace "Okay, naga idanunka sunyi wani kala, me xan zuba maka? Akwai chips, plantain, pancakes akwai sauce me kakeso wane combination?" Ya gama hada tea dinsa sai ya dora hannunsa bisa table yace "Duk abinda kikaga ya dace zan ci, after all ke kika man serving dolena inci." Ya karasa yana mata wink,  sadda kanta kasa tayi murmushin fuskarta ya kasa boyuwa, a haka sukayi breakfast din bayan sun gama yaga ta fara kokarin tashi tsaye, ganin ya tsare ta da idanu yasa tace cikin muryar shagwaba "Banki zanje banaso in iske layi," ya kalleta "Tou gashi nikuma ban gaji da ganinki ba?" Har kasan ranta taji sanyin maganar. Dama akwai wanda akeso ayita kallo kamar wata tv? Saurin kawar da tunanin tayi kafin tace "Tou ay kasan bank yadda yake in mutum baije da wuri ba layi zai iske." Yayi murmushi "Tou kizo in rakaki bankin?" Tayi saurin girgixa kai alamun a'ah tana murmushi, Ashraf yace "Tou kafin ki tafi kice zakiyi missing dina." Shiru tayi tana auna kalamansa, tabbas kona second daya bata tare dashi ba karamin kewarsa take ba, a hankali tayi murmushi tace "Zanyi missing dinka sosai ba kadan ba, kafin na dawo zan maka tsaraba." Yar dariya yayi na alamun jin dadi yace "Na hutar dake yan mata, banason wata tsaraba, ke kadai nakeso ba abin hannunki ba." Murmushi tayi ta wuce ciki da sauri ya bita da kallo, can sai gata ta fito tana sanye da pink hijab da hand bag dinta, kallonta yakeyi yadda hijabs ke mata kyau shidai bai taba ganin ta fita koda da mayafi ba, hakan ba karamin kara masa sonta yake ba, kallon juna suka tsaya yi kafin tayi hanyar fita kanta kasa, kusan cin karo da Khadija tayi a bakin kofa nan suka tsaya suna kallon juna cikin ido kafin Khadija tayi murmushin mugunta, "I can see you're claiming what's going to be mine, kisani wannan na kankanin lokaci ne kukeyi kafin nayi taking over, sai kinyi kuka da idanunki amma a lokacin bakida mafita illa ki dau kaddara da hakuri..." Zarah itama irin murmushin da tayi mata irinshi ta maida kafin ta fara zagaye Khadija tana mata mugun kallo sai dai taxo daidai gabanta ta tsaya tana kallonta from head to toe, "Am sorry to say Khadija but Ashraf will never fall for someone like you, ko inuwarki bazai so ba ballantan kuma ke." Ta fada tana nuna ta da yatsa sannan ta cigaba "No matter what you do, you'll never succeed InshaAllah, shi Allah bai bari a cutar da innocent person no matter what happens, keep on dreaming zaki farka ne kiga na zama mallakin Ashraf halak malak, and then me xakiyi? Nothing right?" Ta fada tana mata wani kallo daga sama har kasa, daga haka ta sa kai ta fita tabar Khadija tsaye tana jin kamar zata kamu da ciwon zuciya, dafe bango tayi hawaye ya taran mata a idanu kafin tace "I will never let you take hime away from me, is either na aure shi ko kuma mu rasa shi gaba daya!"