Friday, 2 July 2021

YAR AGADEZ PAGE 32

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 32}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com



Yau ta kama monday kasancewar Sultan ya kwana biyu bai fita fada ba gaba daya yau tunda ya sa kafa ya fita bai dawo ba sai wurin karfe uku, tana zaune bayan tayi lunch sai missing din Sultan takeyi, ga wani tukukin bakin ciki da takeji yana tasan mata hakanan ana zaune kalau sai ta fara jin haushi? Tana zaune tana kallo kawai sai taji ya shigo da sallama, ta dago ta kalleshi hade da murmushi shima ya mayar mata, saidai har ya karaso ya zauna kusa da ita yana lura da mood dinta yasa yayi magana "Habibty bakida lafiya ne "Habibty bakida lafiya ne yau? Naga kinyi wata kala? Naga yau ko tarbata bakiyi ba..." ya fada yana kamo hannunta. Kawai sai ta fashe masa da kuka ita tama kasa gane ko haushin me takeji, kawai dai tasan ranta na yawan baci kwanan nan, lallashinta yayi kafin tace "Sultan rannan na fada maka wurin marata yana mun tauri amma har yanzu baka kaini asibiti ba sai ka dinga cewa bakomai is normal? Tou ni kwatakwata bangane is normal din da kake fada min ba, yanzu haka nan without any reason sai in kama jin haushi, gashi naga cikina yana dan turowa har wani motsi nakeji kamar kifi na swimming cikin ruwa, ni wallahi banason abun tsoro yake bani." Ta fada wasu hawayen na kuma taruwa cikin idanunta rungume ta yayi a ransa kuwa yana cewa ya tabbatar ciki ne ita, sai dai yana gudun in ya fada mata baisan ya zatayi reacting ba, shi dai kasa magana yayi har taci kukanta ta gama, dago da idanunta tayi da suka sauya kala tace "Kodai aljannu ne ke min yawo a ciki? Allah tsoro nakeji idan naji haka, kuma kaga sai kumburi yakeyi kodai illata ni zasuyi wayyo Sultan!" Kankame shi tayi tana kuka wane ranta xai fita, Sultan dariya ta su6uce masa amma bai bari taji ba, dagota yayi yana kokarin danne dariyarsa kar ta fito, ganin dai da gaske kukan take yasa Sultan ya fara magana "Hoodah don Allah ki daina kuka, kiyi shiru kinji? Maganar kumburin kuma zan kaiki asibiti su baki magani, babu wasu aljannu da suka shige ki balle har su tabaki, am here with you nothing will happen, everything is gonna be alright kinji habibty na?" Ya fada yana mai goge mata hawayenta gyada kai tayi tana kara bata fuska, cikin shagwa6a ta fara magana "Kagani ko Sultan, kusan 3 months kenan bana period, nidai bai taba min haka ba sai nayi tunanin ko wata cuta ce ta kamani ko wani infection dai, har tunani nake kodai mayu ne? Kuma kaga shanye min jini zasuyi kafin su kasheni?" Kuka take bil hakki mikewa yayi ya tafi kitchen anan ne ya samu damar sakin dariyarsa don he can't hold it anymore, saida yayi mai isarsa sannan ya dauki cup ya zuba ruwa a ciki, parlon ya koma ya zauna gefenta ya fara tofa addu'oi acikin ruwan, ya dauki lokaci a haka sannan ya mika mata tasha kafin yasamu hankalinta ya kwanta, mikewa tayi ta kawo mashi lunch dinsa itama ta kara ci, tana ci tana masa complain wai yanzu cin abincinta yayi yawa ga kuma kwadayi da take yawan ji, shidai Sultan bai ce mata komai sai kallonta da yakeyi.

Wajen karfe goma Hoodah tace ma Sultan bacci takeji yace tou su tafi daki su kwanta, wanka ta shiga tayi sai kara nacin maganar nan takeyi shidai yayi shiru, yana gudun yace mata ciki gareta kawai baisan ya zatayi reacting ba, har sun kwanta tace masa yunwa takeji ya tafi ya dafa mata indomie, bayan ta gama suka kwanta, kan kirjinsa ta dora kanta tana wasa da hannunta kafin tayi magana "Ina sonka Sultan, idan na mutu ka kara aure ka aure wacece zata kula da kai tamkar yadda zan kula dakai...?" ganin kallon da ya mata yasa don dole ta rufe idonta tayi shiru don wani irin mugun kallo yake binta dashi "Hoodah meye haka? Ba nace maki ki bar maganar kumburin cikinnan ba? Babu abinda zai sameki lafiya lau zaki haifa mana babynmu ki rayu......" shiru yayi da sauri yana wurga idanu yana adduar Allah yasa bata gane me yake nufii ba. Zumbur Hoodah ta mike zaune shima ya biyota suka tashi zaune "Sultan naji kace zan haihu? Me kake nufi da hakan? Ciki gareni?" Tana tambaya tana kallonshi ko kyaftawa babu, Saurin girgiza kai yayi tare da rumgume ta, "It was a mistake, bawai ina nufin ciki bane, ni ba babynki bane ba? Ko bakiso ki rayu dani?" Ya tambaya yana mata wink, sauke numfashi tayi alamun relief kafin ta saki murmushi tana kallonshi tace. "Zan rayu dakai mana, wallahi naji tsoro ne da naji kace ciki gareni, don Gaskiya idan har cikin ne sai dai a zubar dashi, don bazan barshi ya zo duniyar nan ba yasha azabar rayuwa ba, wannan duniyar cike take da azzalumai marrasa tsoron Allah," ta fada da alamun tausayi tana riko hannunsa irin he should reason with her, "Zubarwa kuma Hoodah?" Ya tambaya in a shock don ya tabbatar da abinda ta fada, gyada mashi kai tayi "Eh mana Sultan ko bazaka yarda ba? Kaga daya zo duniya yasha wahala a banza yazo ya wahala gara in rabashi da duniya cikin kwanciyar hankali." shiru Sultan yayi yana binta da ido yana hango gobarar da ke gabansa don ko giyar wake yasha bazai yarda a zubar da cikinnan ba saidai ayi duk bala'in da za'ayi, can kasan makoshinsa ya furta "Aikuwa akwai bala'i." Kallonshi tayi tace "Me kace Sultan?" Girgiza mata kai yayi alamar babu komai, jawota yayi kafin yace "Hoodah dare ne banason ana maganar aljannu yanzu just keep quiet let's sleep." Jin maganar aljannu yasa Hoodah saurin rufe idanunta a hankali bacci yayi awon gaba da ita. Sultan kasa rintsawa yayi yana kwance bacci ya kaurace wa idanunsa, tunaninshi bai wuce ranar da zata gano ciki gareta ba don wallahi saidai sama da kasa ta hade babu mai kashe masa baby. Ko minti goma baiyi da bacci ba ya dinga jin kakarin amai a bathroom, bude ido yayi yanajin aman Hoodah kamar zata amayar da yan cikinta, dafe kai yayi "Allah sa dai ba abinda nake gudu bane zai faru?" Cikin hanzari ya nufi bathroom din ya taimaka mata ta wanke jikinta kafin ya gyara wurin su fito.

Zaunar da ita yayi kan gado yaje ya debo mata ruwa da kyar take sha kamar wacce ake ba madaci kallonshi tayi hawaye nabin kumatunta "Sultan kwadon zogale nakeson ci wanda yaji kuli kuli da yaji, sai kwakumeti, da aya da gyada soyayya, kuma ina son cin tuwo miyar yakuwa..." ta fada tana tsare shi da idanu kamar wacce ta bashi ajiya idanunta fal hawaye. Sultan kamar ya dora hannu saman kai ya kwala ihu yanzu fisabilillahi ina zai samo wannan abubuwan shidai? Gara tuwon ma zai iya mata order miyar ce matsalar ina ya wani iya wata miyar yakuwa shi? Shi tunda yake ma bai taba jin miya haka ba, "Yanzu ina zan samu...." bai karasa magana sai ganinta yayi ta tashi da gudu tayi bathroom da sauri ya bita nan yaga tana amai tamkar yan hajinta su fito, gashi babu komai a cikinta sai ruwa, mugun tausayi ta bashi kamar yayi mata kuka, tana fitowa ta zube kan gado shakaf tana maida numfashi tace "Sultan kodai mu tafi asibiti? Naga wannan infection din nema yake ya kasheni ko kuwa aljannun ne dai? Kaga idan mukaje aka dubani aka ga basu bane sai mu dawo gida ko?" Saurin girgiza kai yayi "A'a basai munje ba, kinsan inada number din family doctor dinmu bari kigani in kirashi, kinga dana masa bayani zai fada man maganin daya kamata a baki..." ya fada yana marairaicewa kamar ya fashe da kuka, "A'a nidai nafiso mu tafi asibiti Sultan, gara a dubani agani idan yaje ya bani wrong medication fa? Tunda ba ganina yayi ba? Nidai ka kaini asibiti in bakaso in mutu." Ta fada tana bubbuga kafarta harda dan guntun hawayenta. Babu yadda Sultan ya iya illa ya amince ya kaita asibitin don haka cewa yayi su tafi ta mike ta dauko hijabinta. Car key dinsa ya dauka ya fita da sauri ya kira number Doctor amma bai dauka ba, yau dai yasan karshe asirinsa ne zai tonu, babu abinda yakeyi sai addua har suka isa asibitin. Suna shiga sai ga Dr Nafisa kasancewar sun saba da ita ta iso inda suke don su gaisa, office dinta tace su biyota, nan ta shiga ma Hoodah tambayoyi tana bata amsa harda nuna mata cikin, fatanta Allah dai yasa ba aljannun bane. Ba karamin dariya Dr Nafisa tayi ba ganin shirmen Hoodah wai ace ta kasa gane tana da ciki? Can dai ta natsu kafin tace "Shekarunki nawa?" Hoodah tace "Sha bakwai zanyi wata mai zuwa... yanzu dai sha shidda." Dr Nafisa ta kalli Sultan "Yanzu kai ace matarka tanada juna biyu amma baka lura ba? Anyway maybe soyayya ce ta rufe maka ido." Ta fada tana yar dariya, sai kuma ta maida dubanta kan Hoodah wacce tayi mutuwar zaune, tabbas tasan in akace juna biyu ana nufin ciki ko? "Congrats amarya, you're almost 3 months pregnant, ya kamata kin fara zuwa antenatal da wuri amma dai ki dawo next week InshaAllah don duba lafiyar dan baba." Ta fada cike da zolaya, Can ta mike ta nufi kofa saboda an kirata an kawo emergency "Kuje pharmacy ku karbi pregnancy care da sauran maganungunan da na rubuta mata ni zan tafi yanzu emergency nake da take care." 

Kamo hannunta Sultan yayi suka fita suna shiga mota ta kalli Sultan da idanunta da sukayi narai narai "Sultan bana son in haihu, ina jin tsoro abinda ya faru dani ya faru da babynnan, duniyar nan wicked people sunyi yawa cikinta, kar wata rana ka sake yin aure tazo ta man yadda step mom dina tayi mun..." Sultan ya kalleta almost speechless yama rasa abinda zai ce mata "Wai Hoodah kar ki sake cewa zaki zubar da cikinnan dan halak ne! Gaskiya bazai yuwu ba, ni sam ban yarda da wannan excuse din naki ba it is pointless, kuma da kike maganar duniyar nan akace maki ke taki kaddarar irin ta abinda zaki haife ce? Kowa fa yana da tashi kaddarar." Ya fada cikin nutsuwa don ta fahimce shi, Hoodah wasu hawayen suka gangaro mata itafa har ga Allah da gaske take har kasan ranta take fada mashi maganar nan, "Nifa ba wasa nake maka ba, ina so in zubda cikinnan, don bazan zo in haife shi ba in such a cruel world, ni na dandani enough, gara ma ya koma cikin kwanciyar hankali!" Ta fada in an angry tone tana kallon Sultan cikin masifa, Sultan kuwa ranshi ya kai kololuwar baci dama abinda yake gudu kenan don tasha fada masa bataso tayi ciki ta haihu tun ma kafin ta samu cikin, sheyasa ma tunda ya fahimci ciki ne da ita ya kasa fada mata, don ya kula Hoodah batasan komai  gameda da abubuwa da dama ba, sheyasa ko dramar da tayi masa daxu na cewar ko aljannu ne suka shafeta baiyi mamaki ba, yasan ba laifinta bane first of all hannun kishiya ta tashi wacce bata koya mata komai na rayuwa, ta dai san ciki in mace nada ciki amma batasan ya experience din yake ba, though Hoodarsa is a dramatic queen, yasan for sure tayi exaggerating abun, "Hoodah baby, ki gane kowa da kaddararshi, kuma komai yana da karshe ba gashi komai ya zama tahiri ba? So please kima daina maganar nan zaki haife shi InshaAllah babu makawa." Wani kallo ta masa sannan tace "Bana so inta maka musu a mota, let's just go home." Bai ce da ita komai ba kawai ya juya steering wheel ya hau, tun da suka fara tafiya Hoodah ke kuka tana murzar cikinta, shi kuwa Sultan haushi ma ya ishe shi, yaushe 6atan basira ya shiga Hoodah? Meyasa ta kasa gane kaddara ce har yasa Abbanta yayi aure ya auro wacce ta kashe Amminta? What the heck is wrong with Hoodah? This is madness and it has to stop! Dole duhun daya shige mata cikin kai ya koma haske don ya gano kanta a cikin duhu yake! Suna isa gida ko karasa tsayawa baiyi ba ta bude mota ta fito a guje ta wuce cikin gida, kashe motar yayi ya bi bayanta yana shigowa ya wuce dakinsa, kowa da tunanin da ke ransa yayi bacci, Hoodah ta kuduran ma ranta bazata haifi babyn nan ba shi kuma Sultan yayi alkawari sai ta haife shi komai zai faru.

Washe gari da safe haka Sultan ya fito daga dakinsa kasancewar yanada aiki da yawa a fada, ganin dining wayam yasa yayi murmushi sannan ya wuce kitchen yana girgiza kai, kettle ya hada sai ya soya fried egg, oats ya hada ya sha nashi ya aje mata nata kan dining din, don yasan indai taga abinci tou zataci, shi kuma ta lafiyar babynsa yake in ba haka da sai yayi punishing dinta da yunwar cikinta. Bayan ya fita sai ga Hoodah ta fito, abincin tabi da kallo tana wani yamutsa fuska, har ta juya zata tafi daki sai ganin paper tayi gefen cup din daya aje mata dauka tayi ta warware take ta fara karantawa.... "Good morning my beautiful sunshine, I know you didn't sleep well yesterday so do I, you have to try and keep yourself healthy, make sure you eat very well, I will be back a bit later, lot's of love, ina kuma fatan kin janye kudirin nan naki marar kan gado? Don nidai ina nan akan bakana no going back, ok I gotta go now I love you so much Maman twins, take care mua ***kisses***" hade rai Hoodah tayi wato Sultan ma ya maida ta kamar wata karamar yarinya ko? Harda wani maman twins? A'a ya manta Maman goma ne ba twins ba, "Wallahi yau zaka dawo ka sameni ayita ta kare ha'an! Bawani abincin da xan bashi haka kawai kaja cikina yayi girma da kato tou bazan yarda ba, bazan bari yaro yayita girma cikin cikina ba!"tana fadan haka ta wani wurga paper din ta jawo abincin tana ci kamar an mata dole. (Ahh su Hoodah ana son babyn ana kaiwa kasuwa🤣🤣😂tou mudai yan kallo ne muna gefe muna shan fanta🤭🤭). Sultan bai dawo ba sai can da yamma tana jin shigowarshi amma sai tayi maza ta ci gaba da cin chocolate diinta, motsinsa taji a kitchen alamun yana girki ta wani tabe baki tana mai cigaba da lasar chocolate dinta, shiru taji sai tayi tunanin ko dai fita ya sakeyi? Tashi tayi ta fita parlor tana fitowa ta ganshi baje kan carpet ya kunna laptop gefensa plate din indomie ce wadda aka cinye sai robar ruwa sai kuma cup, dauke idonta tayi daga kansa ta tafi ta dauko ruwa a fridge tazo zata wuce kenan sai Sultan ya hango chocolate din dake hannunta, cikin zafin nama ya mike ya fizge chocolate din yana fadin "Yanzu Hoodah chocolate kike ci? Lafiyan babynmu fa? Allah kadai yasan chocolate nawa kikaci a yinin yau! Tou wallahi kwashe su zanyi tas, daga yau kisan me xaki ci wani abun is harmful for the baby," ya karasa yana jawota jikinsa, wani irin mugun kallo take masa kafin ta fizge jikinta.....

No comments: