Thursday, 1 July 2021

YAR AGADEZ PAGE 31

 YAR AGADEZ

 

 

              {Page 31}



To read all my books click the link below👇🏻

Maryamsbello.blogspot.com




*****

Da safe Hoodah tayi wanka ta shirya cikin kananan kaya tasa jeans skirt da wata ash top mai shegen kyau, dakin ta gyara ta kimtsa yayi fes saida ta gama tayi hanyar fita tun daga parlor takejin kamshi na tashi daga kitchen, wani kayataccen murmushi tayi ta doshi kitchen din, Sultan na tsaye yana sanye da vest da short yana soya dankali da plantain, batasan lokacin da tayi dariya ba, dariyarta ta dan firgitashi hakan yasa ya juyo sannan yayi murmushi "Ma femme kin bani tsoro fa I thought bacci kikeyi." Ya fada yana dafe da kirji, ta kyalkyale da dariya "Haba Sultan sai kace ba namiji ba? Kar kabani kunya mana..." murmushi yayi ganin yadda take fari da ido, "Wait ooo menene ma femme ma? Na manta wallahi." Ta fada tana wani turo baki sannan tayi kamar tana son tunano abinda yake nufi, gwalo ya mata sannan yayi dariya "Bazan fada ba ooo, sadda ake koya mana har dariya kike mani, nasan da yanzu Ummi na nan da sai muje ta tunatar da ke, ta iya french kamar me, sheyasa ma kikaga ma na iya sosai Allah sarki Ummi..." hakan yasa yaji ba dadi tuno da Umminsa ko jiya sunyi video call Abbi da sauki sosai don yana ma dan magana, Ummi ce dai sai a hankali ita ko maganar bata iya yi sai dai ido, take expression din fuskarsa ta chanza ganin haka yasa Hoodah tayi saurin chanza zancen dan in har ta bari Sultan yayi wata magana yanzu tou ta tabbatar gaba dayansu babu mai rarrashin wani a yau, "Sultan nidai don Allah ka fada man in ba haka ba babu ruwana da kai tohm!" Ta fada very dramatically harda bubbuga kafa alamun shagwa6a, riko hannunta yayi yaja ta ya zaunar da ita bisa dan karamin table din dake tsakiyar kitchen din mai dauke da kujeru biyu, kallonta yekeyi yana wani kayattacen murmushi wanda ya kara fito da ainahin kyawunsa sannan yace "Ma femme na nufin matata." Ya bata amsa har lokacin bai daina sakar mata murmushi ba itama murmushin tayi mashi me cike da alamun ta tuna abinda yake nufi "Oh hakane fa, mon homme," ta fada cikin sigar zolaya, turo baki yayi wane karamin yaro "Ahh noo naki wayon naji abunda kika fada, sannan fa zan iya maki kishiya so Sultan dinnan shine kawai man dinki your one and only...."  Hoodah fuska tayi alamun ba wasa take ta juyar da fuskarta gefe dan gaba daya jin ya ambaci kishiya ba karamin bata mata rai yayi ba, duk da tasan da wasa yakeyi amma  tsananin kishinta bazai barta ta yarda wasa din bane ba. Kallonta yake a natse "Menayi kuma ma femme wasa fa nake miki, na isa in miki kishiya? Waye ni? Ke a takaice ma bana ganin ko wace mace da kyau ko diri in ba ke ba ke kadai ce a zuciyar Sultan, ke kadai ce matarsa InshaAllah, trust me." Ya fada yana mai kamo hannunta cikin nashi yana sauke mata gentle kiss a hannun "Tou nidai Sultan bana son irin wannan wasan gaskiya..." muryarta har tayi rauni kamar zata fasa masa kuka, dariyar daya rike tun dazu ce ta kubce masa, yi yake kamar cikinsa zai kulle har wani bubbuga kafa yakeyi yana dukewa, ita kuwa Hoodah kallonsa takeyi cike da sha'awa, shi kuwa yi yake har sai da yayi mai isarsa sannan ya dakata yana maida numfashi "Sultan dariya ma na baka ko?" Ta fada bayan taga ya gama dariyar ne, "I was just happy ne, naji dadin yadda ake kishina." Wink yayi mata don dole ta kauda fuskarta tana murmushi, da sauri ta mike tsaye ta fara arranging kayan breakfast dinsu, mikewa yayi ya dauki warmer da flask ya tafi dining din yana zuwa ya aje bisa table sannan ya zauna yana ganin ta fito zai bita da ido sai ta juyo sun hada ido sai ya sakar mata murmushi da sauri ita kuma zata kauda fuskarta gefe tana jin kunya, bayan ta gama ta masu serving sannan suka zauna suka fara cin abincin cikin nutsuwa babu wanda yake magana a cikinsu don Hoodah nauyinshi takeji kuma yanzu don daina kallonsa ma tayi don tasan yanzu haka ita yake kallo. Suna gamawa yaja hannunta suka nufi parlor don suyi kallo kafin ya tafi fada, zama yayi ya jawota ta fado bisa kirjinsa kwantar da kanta yayi bisa fadadan kirjinsa hada da lumshe idanu, sun dauki kusan ten minutes suna kallon kafin Hoodah tace "Sultan?" Ta kira sunanshi tana mai kallon fuskarshi "Na'am habibty na?" Ya fada yana mata murmushi "I was curious inaso na tambayeka jita jitan da nakeji a gari cewar Ummakhairy is pregnant, and she was tasted HIV positive? How true is that?" Ta tambaya tana tsare shi da fararen idanunta wanda suke kara mata kyau, gyara mata kwanciya yayi saman kirjinsa sannan ya riko hannunta na dama yana wasa da zoben azurfanta, "Firstly bansan ya akayi kika samu wannan labarin ba, but ina ji a cikin mafarki kikaji ko?" Dariya tayi tace "Mafarki kuma Sultan? Maganar da ta bad'e gari babu inda bata je? Rannan fa na kama maids din gidannan suna gulman fa..." shiru yayi kafin yace "A rayuwa Hoodah ana son dan adam ya zamto mai shuka alkhairi, yanzu jifa yadda Khairy ta koma abin tausayi, kwatakwata kowa ya juya mata baya harda mahaifiyarta, azabar yau daban gobe daban, ance abun ya fara affecting brain dinta ta dawo kamar mai kama da mai ta6in hankali, yanzu in takaice maki zancen yan unguwarsu da sauran yara sai kiga suna binta suna janyo mata kaya suna mata waka, wai tayi cikin shege ta kwaso kanjamau, ranar dana gani abun bai mun dadi ba saidai kuma tuno da abubuwan da tayi miki yasa gaba daya naji tausayinta ya fita daga raina, she was evil amma yanzu ya ta kare? Duniya nata koya mata hankali bakiji hausawa na cewa wuya makarantar kare ba? Tou wannan shine." Shiru Hoodah tayi tana jin babu dadi a cikin ranta "Gaskiya Khairy batayi wa kanta adalci ba, sannan kwatakwata mahaifiyarta bata kyauta ba instead ta jawota a jiki sai ta dunga hantararta? Is not fair..." yace "Tou mu meye namu a ciki? Iyayenta na they can do what ever they want su ta shafa, please don't ever bring this topic ever again, I don't want hear her name in this house again..." tayi murmushi "I won't don't worry, Khairy ta zama past dinka am now your present and your future InshaAllah..." Sultan wani murmushin jin dadi yayi, take ya fara tunano ranar daya fara ganin Hoodah kamar ya mutu tsabar bakin ciki amma yanzu ganinta ke sashi farin ciki...Hmm that's life. Labari suka cigaba da yi har azahar kafin suje suyi sallah, ranar kin fita yayi sai da yamma ya dauketa suka tafi supermarket strictly babu dogarai yace he wants his privacy kada wanda ya bisu, da kyar suka yarda suka kyalesu. Bayan sunyi uban siyayya suka dawo gida after five, suna shiga maids suka dinga kwasar kayan suna kai masu ciki, daki suka wuce suka wuce Hoodah ta cire mayafinta ta tafi kitchen don fara arranging groceries din.

Rayuwa ce sukeyi mai cike da aminci, sha'awa, girmamawa, kaunar juna hade da soyayya mai karfin gaske. 

Yau ta kama asabar Hoodah ta tashi yau da misalin karfe tatwas na safe sai naga tayi fresh da haske tayi kyau abinta daka kalleta kasan hankalinta a kwance yake don har wata yar kiba tayi, juyawa tayi gefenta ta kalli Sultan wanda ke shakar baccinsa a tsanake, tunowa da muguntar da yaya mata jiya da daddare yasa tawani yi kwafa ta mike tana murmushin mugunta, dukawa tayi daidai saitin kunnensa ta dage iya karfinta ta kurma wani irin uban ihu, a gigice Sultan ya farka tana ganin ya bude ido tayi axama tayi yar kara itama tare da yin baya ta fita a guje daga dakin tana haki don ta tabbatar da idan Sultan ya damke ta bazataji da dadi ba. Shi abunma dariya ya bashi don da ya bude ido yaga abinda tayi mashi sai ta bashi dariya, amma ganin yadda ta zabura ta fita da gudu ba karamin dariya yayi ba, mikewa yayi zaune har lokacin bai bar dariyar da yakeyi ba yace "Zaki gane kurenki yarinya." Yana fadin haka ya mike ya shiga bathroom don yin wanka.

Hoodah kuwa tayi dakinta da gudu harda sa key sannan ta fada bathroom tayi wanka cikin hanzari sannan ta fito dan hada masu breakfast. Cike da farin ciki take aikin amma can kasan ranta tsoro ne fal don tasan Sultan sarai ba kyaleta zaiyi ba ta tsorata shi baya kaunar a tsorata shi. Sultan yana fitowa ya hangota tana aiki kana ganinta kasan a mugun tsorace take, a hankali ya dinga tafiya sai dai kawai taji an chafke ta "Kin gama gudun?" Yana tambaya yana tsareta da idanu, Hoodah ganin babu digon wasa a tattare dashi sai jikinta ya fara rawa. "Am sorry please Sultan, don Allah don annabi kayi hakuri, ni wallahi da wasa nake maka..." duk ta rude tasan idan ya daure fuska haka tou ba wasa yake mata ba, kara shagwa6e fuska tayi "Sultan don Allah fa nace." Shi kuma Sultan kallonta kawai yakeyi ba ko kyaftawa ganin yadda duk ta tsure ba karamin dariya ta bashi ba amma dai ya dake ya wani faske. Hoodah ganin baida niyyar sakinta sai kawai ta kankame shi yana jin haka shi kuma sai ya saki hannunta zai rungume ta back kenan yaji ta sake shi ta ruga da gudu tana kyalkyalewa da dariya me Sultan zaiyi in ba dariya ba? Jumping take wane karamar yarinya "Nayi ma Sultan wayau, na na na naa!!" Ta fada cike da jin dadi harda masa gwalo tana wani tsalle tana rawa. Sultan baisan lokacin da yayi dariya ba kafin daga baya ya daure fuska amma duk da haka fuskarshi cike take da dariya, "Kizo ki ida abinda kikeyi fa." Ya fada fuska daure, Hoodah zurawa tayi da gudu tayi dakinta ta rufe da key, daga cikin dakin yaji ta fada da karfi "Wallahi bazanzo ba, haka kawai ka kamani! Nasan mugunta zakayi min, ka tafi wurin abincin nan kar ya kone." Bata ankara ba sai jinsa tayi bakin kofarta "Hoodah kinsan Allah ki fito, in ba haka ba zakiyi bayani." Hoodah najin haka ta fasa wani irin ihu "Wayyo Sultan abincina zai kone! Ka tafi ka duba min sai kazo ka kirani." Sultan najin haka ya wuce kitchen din yana dariya, kitchen din yaje ya kashe gas yayi arranging dining din, babu abinda yakeyi sai dariya, don bayan ya sake da Hoodah sai yake gani bai taba haduwa da mace mai drama irinta ba, dakinsa yaje ya dauko key yana zuwa ya bude sai ganinta yayi bakin gado tana latsa waya "Fito tou." Yana fadan haka yayi alalamun tazo ta wuce....

Hoodah ganin yadda yayi da fuska yasa tazo sum sum ta wuce kamar wata munafuka, tana zuwa daidai shi kawai sai ganinta yayi ta kwasa a guje. Dariya kawai yayi sannan yabi bayanta, yana isa dining din sai ya ganta tana masu serving zama yayi suka fara ci, suna gamawa Hoodah ta tattara kayan ta kai kitchen, tana dire kayan sai kawai ta kwala masa kira "Sultan kazo ka tayani wanke wanke please! And zamu gyara gidan duka." Tana gama fadan haka sai ta cigaba da abinda takeyi, tashi yayi ya shigo kitchen din hannunshi cikin aljihu yana kare mata kallo sai da yazo dab da ita sai ya tsaya yana gyaren murya, a tsorace ta juyo gabanta ya fadi sai kuma ta faske tamkar ma bataji wani tsoro ba "Ya naga ka tsaya? Ka taho muyi aikin nan jimun Sultan dinnan kai." Ta fada tana nuna masa kwanikan, juyo da ita yayi tana fuskantarsa yace "Ay wallahi yarinya baki isa ba, amma dai bari inyi aikina kafin in tayaki." Kafin ta ankare ya fara kissing dinta, saida yaga Hoodah ta fara amsar sakonsa sannan ya sake ta cike da mugunta, kallonta yayi ganin ta hade rai don tasan da gangan yayi, shi kuwa Sultan dariya ya dinga yi mata harda irin nunata dinnan a haka ya kama mata wanke wanken nan har suka kammala suna gyara kitchen din tas sai sheki yakeyi, suna gamawa kawai yaje bisa kujera ya baje harda hangame kafafuwa alamun gajiya ya rufe ido, budewan da zai ma idanunsa kawai sai ganin Hoodah yayi tsaye kansa rike da kugu, binta da kallon irin lafiya dinnan yayi ita kuwa sai ta kara rike kugu "Ni bance maka na gaji ba sai kai? Kai ji mun Sultan dinnan kai. Ba abinda ka iya in banda lalaci da mugunta." Ta fada cike da tsiwa, Sultan yayi murmushin gefen baki "Indai kinaso in tayaki sai kin min wani abu..." ya fada hade da yi mata wink, "Fada naji idan zai yuwu ina jinka kana bata man lokaci rana nayi." Ta fada tana wani karkada kafa alamar sauri take, rike baki yayi yace a ransa dama haka Hoodah take fitananniya ashe bai sani ba? Tsaye ya mike yace "Kiss nakeso a nan..."! Ya fada yana nuna lips dinsa, da shiru tayi tana kallonsa sai kuma ta kyalkyale da dariya kafin tace "Kai Sultan bakajin kunya kake wani cewa in maka kiss? Allah ya shiryeka." Sai kuma ta sake kyalkyalewa da wata dariyar shima ya tayata, gaba daya burge shi takeyi yanzu don yana son halinta sabo ko don dama can bai nutsu bane ya gane haka take? "You know what? Tou bari dai na taimaka maka kadan." Sai kuma ta fashe da dariya shima dariyar yayi, gani yayi tana tantado ta masa kiss din kadan a lips dinsa wani lumshe idanu Sultan yayi, sai data lura ya saki jiki sosai ta dage ta gantsara masa cizo kafin ta ja baya ta kwasa a guje. Tana kyalkyala dariya tana gudun, tsayawa tayi tana masa gwalo "Haka kayi min dazu ramawa nayi! Kasan Allah kazo muyi aikin nan mu gama tohm!" Tana fadan haka ta wuce store ta dauko broom, wani smirking Sultan yayi ta gefen baki yace "Zakiyi bayani anjima.." Sai da taga yazo kusa da ita da zata ruga kafin ya rikota, cike da dariya da annashuwa suka cigaba da aikinsu.

No comments: